SHIMFIƊA
Wani irin murɗawa mararta ta yi, kafin ɗan dake cikinta ya samu damar juyawa daga hango zuwa dama, dalilin wani rikitaccen tashin hankali daya tattaro waje guda ya ruftuwa zuciyarta wacce take a ƙudundune tsayin shekaru ta tsaya mata a tsakiya, baƙar fuskarta sai maiƙo take kamar an yi ɓarin baƙin mai a saman kwalta.
"Zaki kashe ni, da gaske zaki kashe ni Mar..."
Sauran maganganun suka tsaya mata cur a maƙoshi kamar tsayi yiwuwar bushashshen itace. A gigice kuma ta yi wurgi da wayar dake maƙale a hannunta. . .
Za ki kashe kanki a banza don wani banza
Wa’iyazubillahi
Allah sarki