Asibiti
Ridayya T
Ana durƙoshe dafe da turtsetsen cikinta, kwalbar fiya-fiya ɗin can waje guda wacce ta gama aunawa cikinta ita. Zufa ce take yankowa ilahirin jikinta, tun gabɓanta na motsi da rawa har ya zamana ya saki bata da kuzari da ƙarfin qiwwar taimakawa kanta. Idanunta da suke rufe ne hawaye mai zafi ya shiga bin gefensu, wani irin zafi da raɗaɗi take ji a ƙasan zuciyarta wanda sannu a hankali yake mamaye dukkan wata tsoka ta zuciyar, bata taɓa tunanin illar da fiya-fiyar zata yi wa abinda ke cikin cikinta ba, more especially da tun ɗazo ta daina jin motsin halittar ciki.
“Ya Allah!”
Ta furta a ƙasan maƙoshi daidai lokacin da kumfa ya fara fita daga cikin bakinta, ta ƙara runtse Idanunta, a cikin halin rayuwa ko mutuwa take, amma hakan baya hana mummunan abubuwan data gani a zahiri gilmawa ta cikinsu, abin na zauna daram a zuciyarta wanda ko fiya-fiya ɗin data sha bai kaita zuwa kushewa ba, tabbas abin na iya kaita kabarinta hakan yasa take kokawa da zuciyarta wajan ganin ta daina bugawa da soyayyar mijinta. Ridayya bata san adadin lokacin data ɗauka kwance saman ledar tsakar ɗakinta ba, tana faman juye-juyen kanta kafin numfashinta ya tsaya gabaɗaya ta daina jin sautin muryar MEER wacce kullum ta zame mata tamkar busar sarewar Algaita.
“Baby kamar ƙarar ƙofa na ji fa?” Ta faɗa da ƙyar cike da tsoro, domin iya adadin zamanta a gidan Ridayya bata taɓa ganinta ko zaune kujera ɗaya da MEER ba, balle ɗaki ɗaya. Zameer ya yi shiru sai kuma ya miƙe a hankali yana gyara zaman gajeren wandonshi ya nufi ƙofar tare da buɗewa, ganin ba kowa a tsakar gidan sai hasken wutar nepa ya sanya ya zura slipper ɗinsa ya nufi ɗakin Ridayya bata cikin parlon sai ya shige uwar ɗaki kai tsaye, yana shiga ya rusketa kwance a ƙasa ta baya ƙofa baya, ganin kamar bacci take ya sanya Zameer ɗaga kafaɗushi duka biyun ba tare da damuwar zuwa dubawa yaga mene ya sanya ta kifa cikinta ba, mene ya sanya ta kwanta a ƙasa ba?
Meer ya sauke ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya, yana jin fargabar data dirar masa na yayewa da alama motsin da suka ji da ƙarar ƙofar iska ce mai ƙarfi ta kaɗa tunda tsakiyar dare ne.
Yana komawa ɗakin ya samu Khairiyya tsaye tana ganinsa ta matsa ta ce “Ita ce ko?”
Ya yi shiru yana kallonta ta sake cewa “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un, Matarka ta ganmu baby”
“Keee!!” Meer ya faɗa a taƙaice yana ƙanƙantar da idanunsa akan Khairiyya kafin ya shafa sumar kansa yana yin ciki, Khairiyya ta langwaɓe ta ce
“Baby ina magana kana sharewa? Ina Ridayya take? Ta ganmu tare ko?”
Cikin tsawa cike da masifa ya ce
“Saurara, ni kam ki saurara da ihu saman kai na” Ya ɗan hargitse mata nan take, Khairiyya ta yi shiru domin ta san halin Meer ciki da waje yanzu zai zama kamar mahaukaci idan ana masa surutu akan shi.
“Ka buɗe mini ƙofa na fita” Khairiyya
muryarta na ɗan rawa ta faɗi maganar a lokacin na farko da tsoro haɗi da shakkar Ridayya ya saukar mata a zuciya wata matsananciyar kunyar ta, ta dirar mata ainun ba tare data shirya ba. Babu macen da zata jure ganin mijinta wanda ke shirin zama uban abinda zata haifa yana kula wasu ƴan matan, balle kuma har ta ganshi tare da wata mace a cikin gidansu na sunna, a ɗaki ɗaya, kwance gado ɗaya ko ita da kanta idan bata kashe yarinyar ba, to babu abinda zan hanata sanyata jinya wajan ganin ta illata ta.
“Baby ka buɗe mini ƙofa”
“Shiittt…!” Meer ya ce a kasalance yana ƙara juya mata baya, ya fahimci da gaske Khairiyya bata san tasirin da muryarta keyi a zuciyarsa ba, gashin jikinsa a mimmiƙe gudun bugun zuciyarsa ya ƙaro fiye da kima, bai san meke faruwa da shi ba, ya kuma kasa ganewa, bashi da lokacin zama ya tantance halin da yake, photon Khairiyya ne zanen daram a zuciyarsa, surar jikinta ke masa yawo cikin idanunsa.
“Wallahi ba zan iya kwana gidan nan ba, matarka zata kashe ni, zata kashe ni tana mugun son ka.”
Sai a lokacin ya juya ya kalleta yana mata mitsi mitsi da ƴan iskan idanunsa ya ce
“Tana so na, tana son abinda nake so…,” Ya ɗan ya yi jim, kafin ya ce,
“Ki nemi guri ki kwanta, kina takura ni da ganin a idanuna kina matsawa zuciyata!” Da rashin fahimta Khairiyya ta kalli Meer domin bata gane ainahin abinda kalaman shi suke nufi ba, ta rasa wajan da zata zuba su da zasu auna zancan ta fahimta.
Kokawa yake da zuciyarsa da gaske wajan ganin ta daina dokawa da tunanin Khairy, da hana kansa juyawa ya sake ganinta a karo na babu adadi, riƙe kansa ya yi da kyau a zuciyarsa yake faɗin.
“Ƙarya kike, da gaske ƙarya kike Khairy baki isa na yi tunaninki ba.”
Tunaninta ke neman jirkita zuciyarshi duk kasancewar ɗaki ɗaya suke, da ƙyar ya kauda wannan tare da zaro wayarsa ya shiga Internet, ƴan mata ya fara kalla sai dai yana da a ji ba ko wacce yake dannawa like ba, duk da ki ka kai da burge Meer.
Kamar yadda ya a saba, kafin sallar subhi ya yi alwala tare da gabatar da raka’atul fajr.
Tana tsaye gaban daƙin tana kiran sunan Ridayya kafin ta ga ji ta ce
“Ikon Allah, duk abinda ya hana Ridayya yin ƴar tsala ba ƙarami bane, Allah ya sa lafiya take.”
Ta furta tana riƙe plate ɗin hannunta, harta juya ta ji hankalinta bai kwanta ba, sunan Ridayya daya gilma ta zuciyarta ya sanyata dokawa da ƙarfi. Da sauri ta shiga bakinta ɗauke da sallama, ta manta Ridayya bata taɓa bari ka shigar mata cikin uwar ɗaka amma ta shure wannan sharaɗin, was the first abinda idanun Zainaba ya gane mata, Ridayya ce yashe a ƙasa bata motsi fatar nan ta jikinta ta ƙara yin baƙiƙƙirin kumfar bakinta har yanzu fita take, a gigice Zainaba ta yarda da plate ɗin siyan ƴar tsalar tana faɗin
“Innalillahi, Ridayya mai haƙuri mene ya sameki ƴar nan” Ridayya bata numfashi, gangara jiki baya magana, kunnenta sun jima da dauɗewa. Ganin da gaske Ridayya ta zama gawa ya sanya Zainaba fita da sauri tana faɗin.
“Bawan Allah, mijin gidan kana ina, na ce kana ina.”
Shiru ba amsa! Bata damu ba domin tana da yaƙinin bai san halin da matarsa ke ciki bane, ta nufi ɗakin Zameer kai tsaye tana ɗaga labule ta tsaya ganin mace zaune a tsakiyar katifa daga ita sai short skirt, da riga ba zata huce half-vest ba.
“Khary?” Ta faɗa a gigice
Domin ba wanda bai san cewa Khairiyya ƙanwar Meer ba ce, Khairiyya ta miƙe jiki na rawa da ɓari da ƙyarma, ta kasa cewa komai sai laɓɓanta da suke kokawa da juna
Zainaba ta ce
“Sannu Khairy”
“Don….don….,” Khairiyya ta kasa faɗar abinda take son cewa, domin ta ɗauka Zainaba da fahimci komai, itama Zainaba shiru ta yi, tayi amfani da tunaninta na mace mai hankali na daidai shekarunta ta gane akwai abinda ke faruwa _something is fishy…!_
Ta gyara tsaiwa ta ce.
“Sannu na yi miki, sannun ne bakya so Khairiyya?”
Ta girgiza kai Idanunta cike da hawaye ta ce.
“Ridayya ta turo ki yankani ko? Ta gano cewa ni ba ƙanwar mijinta Zameer bace kamar yadda yake faɗa mata kullum? Ta gano bani da haɗi da shi ta ko’ina, ta gano ni bama ƴar asalin garin kano bace balle na zama ƙanwar Meer? Ta gane hakan da gaske ta fahimta!” Zainaba ji ta yi komai na kanta ta tsaya, ƙwaƙwalwarta kamar za ta yi hooking haka take ji.
Kallon Khairiyya kawai take kamar zautacciyya kai ka ce ita akaiwa hakan. Khairy ta ce,
“Yanzu yanzu zan bar gidan wallahi don Allah karku mini komai….”
Zainaba ta girgiza kai ta ce “Bantan Uba kibar ina? Nan gida? To ai ko zaki fita a raye dole sai dana kasa a jininki, zaki rasa hannu ko ƙafa” Hawayen takaici ta goge ta ce,
“Ke macace, watarana zaki ji baƙin cikin da kika saka Ridayya, ki yi tunani rayuwar da fasiƙa mazinaciyya a gidan aurenka matsayin ƙanwar mijinka ashe duk ƙarya ne, Allah ba zai barku ba daga ke har mijin nata.”
Tana faɗin hakan ta jawo ƙofar tare da daka key ta rufe Khairiyya a ciki, da sauri ta juya inda Ridayya take amfani ta yi da wayarta ta shiga ɓangaren kira, last number da aka kira shi ne _RAYUWATA_
Ta yi masa kira biyar ba amsa, daga number sai ta sister Diyya.
Ƙara dubawa ta yi taga an saka Yaya Bilal, Zainaba bata tsaya jinkiri wajan dannawa Yaya Bilal kira ba, kamar wanda yake shirye na tsammanin kiran nata tana shiga ya ɗaga ta cikin wayar ya ce.
“Auta kiran safe haka.”
Shiru Zainaba ta yi muryar Bilal ta yi zaune daram a zuciyarta, wani dakakken sauti ne dake fita kamar busar Algaita a nutse ba hargowa, jin shiru ya sanya Bilal yin jim da gaske ba Auta ba ce, sam bai ji bugawar da zuciyarsa ke masa ba a duk sanda sukai kusa ko a waya ne, bai ji wannan maganaɗisun dake kwasar shi a kullum yana jirkita dukiyarsa ba.
Bai ce komai, don baya da zarafin cewa ɗin magana mara dalili bata tsarinsa ko waye ya kira da number Auta dole akwai dalilin kiran, sai dai ya yi imani Zameer ba zai taɓa kiran shi ba.
Zainaba ta sauke ajjiyar zuciyar da take riƙe da ita tun ɗazo, kafin ta ce,
“Your… Your…….,”
Bilal ya dakatar da ita da cewa “Riƙe ƙinƙinarki, ina take?” Da ƙyar ta ce,
“Babu tabbacin tana raye ko babu, zahirin abinda Idanuna ke ganin Ridayya ta mutu…” Ƙit! Ta ji an kashe wayar ba tare da anjira ta kammala magana ba, ta daɗe tsaye tana sake kiran number amma ba’a ɗauka, bata san lokacin data shafe tsaye akan Ridayya ba, idanunta akan screen ɗin wayar, kamar daga sama ta ji an banko ƙofar ɗakin, Zainaba ta yi saurin yin baya bata iya gane fuskar wanda ya shigo ba kowa ta sani a familyn Ridayya ba, tana iya cewa this is the first time ta Idanunta yaga wannan halittar. BILAL ya tsaya fuska haɗe ganin inuwar mutum, can kuma ya saka gaba ɗaya ƙarfinsa ya kinkimi Ridayya da ita, da cikin jikinta kai tsaye waje ya nufa ya sata a bayan motar shi, har zai shiga sai kuma ya tsaya ba tare daya kalli Zainaba dake tsaye ƙofar gidanta ba ya ce “Mi.. mijin nata?” Ya furta da ƙyar yana saka hannu wajan gyara lins ɗin hannunsa, sai a lokacin Zainaba ta kula da jinin dake kwance a goshinsa ta ce
“Ko dana shigo gidan ban tarar da shi ba, ban san yaushe ta kasance a haka ba nima Allah ne ya nufa na zo siyan ƴar tsala a wajanta zan bawa yarinya, jin shiru na shiga ɗakinta na tarar da ita a haka, na yi ƙoƙarin kiran mijinta baya gidan wai wata dana gani a daƙinsa..” hannu Bilal ya ɗaga mata tare da shiga mota da sauri yabar unguwar, Zainaba ta riƙe haɓa ta ce “Ji ƙaddara maganar ma wahala take masa, da shi da Zameer ɗin halinsu ɗaya.”
Juyawa ta yi ta shiga gidanta a ranta tana jinjinawa haƙuri da irin makauniyyar soyayyar da Ridayya kewa Meer take.
Bilal tuki kawai yake ba tare daya san inda yake cilla kan motar ba, yasan akan titi yake ya kuma san asibiti yake son zuwa mafi kusa da shi, maganganun Zainaba ke masa yawo a kunnenshi, babu abinda ya tsaya masa irin wai ƴar tsala Ridayya take yi? Me Ridayya ta rasa? Akan soyayyar miji ta wulaƙanta kanta har haka? Ta zama abar surutu a dangi da unguwa!
Yana tsaye a reception kansa a ƙasa tun ɗazo da aka shigar da ita Emergency yake kai kawo a wajan daga ƙarshe ya nemi waje ya zauna, inuwar daya gani a kansa ya sanya shi ɗaga idanuwansa akan Mami ya sauke Amma ya sauke ganinsa ya ɗan rage numfashi Amma ta ce “Uban masu gidan ya jikin na Auta? Meke faruwa ne?”
Bilal couldn’t speak, ya kasa magana ta sake cewa “Na cewa Abdullahi ya biyoni muje shi da Khalifa amma sun ce sun jima da cire hannunsu akan lamarin Ridayya mene ya faru da sassafe? Hajja A’isha taƙi cewa komai.”
Kafin Bilal ya yi magana Dr ya fito yana share zufa, ganinsa ya sanya Bilal miƙewa Likitan ya ce “Kai ne mijinta?”
“Lafiya Dr? Karka ce mana Auta Ridayya ta mutu karka faɗa zaka tarwatsa zuƙata da yawa.” Dr ya sake kallon Bilal ya ce “Mijinta ne kai?” Bilal dai kamar an sanya allura tare da ɗinke bakinsa, ya kasa cewa komai banda dokawa a ko wacce daƙiƙa babu abinda zuciyarsa ke yi, sunan Ridayya kaɗai na iya tarwatsa zuciyarsa, jin sunan yake kamar saukar dalma a ƙahon zuciyarsa, ya kasa sabawa da jinsa har yanzu, kalmar mutuwa ita ce ba zai taɓa lamunta ba, ba zai yarda akwai ta idan har akan Ridayya ne.
“Shi ne, mijinta ne.”
Amma ta bawa Dr amsa, Dr ya yarda domin zufar dake goshin Bilal ta gama bayyana masa amsar tambayar shi
“Follow me, _Ku biyoni_”
Ya juyawa zuwa office ɗin Dr ɗin. “Mai suna mu shiga mana” Ya riƙe numfashi da sauri yana girgiza kai bata jira me zai ce ta kama hannunsa zuwa office ɗin.
Dr ya kalli Bilal bayan cike cike a hankali ya ce
“Kai ne mijinta da gaske?” Bilal ya sake shiru Likita ya ɗora da
“Baka da Imani, baka da tausayi, baka cancanci zama mijinta ba, da gaske kai mugun miji ne.”
A hargitse Amma ta ce
“Saurara! Aibatawar ta mece? Kake ƙoƙarin tsine masa bayan bakai cikinsa ba balle haihuwar shi?” Dr ya ce,
“Bana da shakka ko tsoro, ya halatta tsinuwa ta tabbata a kan shi, matarka na ɗauke da ciki amma baka taɓa bata ƙwayar magani ba? Sai takura mata ake wajan tarayya? Sexual violence? Gashi abinda ke cikinta ya ruɓe yanzu haka.”
Cikin tashin hankali Amma ta ce “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un! Ɗa ya ruɓe a cikin Ridayya? Bamu da labarin bata taɓa zuwa asibiti ba.”
Dr ya yi murmushin takaici ya ce “Amma ke uwar miji ce ko Hajiya? Ƙiriƙiri kina ƙoƙarin danne laifin ɗanki? Wallahi da ina da iko maka shi zan a court ni kaɗai nasan halin da yarinyar ke ciki, ga ciwon yunwa daya kamata.”
Miƙewa Bilal ya yi yana ganin duhu a idanunsa jiri na neman yar da shi, Amma ta ce “Bilal!” Bai tsaya ba ta sake cewa “Bilal karka kuskura naga ƙafar a cikin mota balle kayi gigin yin driving.”
Sai a lokacin ya juya ya kalleta kafin ya ce
“Ki daina mini ihu Amma ki daina na roƙe ƙi.”
Ficewa ya yi ta kalli Dr ta ce “Yanzu ya ake ciki?”
Ya ce “An yi aikin an cire babyn, Allah ne ya yi da rayuwarta a gaba muna jiran tashin ta ne.”
Miƙewa ta yi ta bi bayan Bilal tana zuwa parking space na harabar asibitin motarsa na ficewa, wayarta ta ɗauka ta kira Junaid yana ɗauka ta ce,
“Maza duk abinda kake ka baro kasuwa kabi Bilal yana driving hankalinsa a tashe yake kuma.”
Junaid ya yi jim kafin ya ce “Amma ina zanga Bilal yanzu?” A tsawace ta ce,
“Da kyau, ya maka kyau ina faɗa kana faɗa Junaid duk abinda ya samu Bilal zaka sha mamaki.”
Wani mahaukacin driving yake kamar zai bar gari, yana jin yau ko zai dauwama a gidan yari a cikin biyu sai dai a yi ɗaya, ko Zameer ya kashe shi ko kuma shi Bilal ya kashe Zameer har halira, idan ya so hukuma ta kashe shi shima.
Muna godiya 👏👏