Skip to content
Part 3 of 9 in the Series Munafukin Miji by Nimcyluv sarauta

Caca

Bilal

Har wani jan hawaye ne ke kwanciya a idanun Bilal, wanda yake ƙara tabbatar da mai kallonsa halin da zuciyarsa ke ciki a bayyane, duk da haɗiye abubuwan daya zama ɗaya daga cikin ɗabi’arsa. Babu abinda yake ɗaga masa hankali irin kalmar sana’ar “Ƴar tsala” da Ridayya take.

Meta rasa a duniya? Ta zaɓi miji sama da komai.

Ƙiitttt! Sautin ƙarar haɗuwar motoci biyun ya bayar, cikin saurin driven ɗaya motar ya riƙe nashi kan motar, da hanzari ya ɗago da nufin sauke bala’in dake cin ransa tun a hanya, wanda ya gani cikin ɗaya motar ya sanya bakinsa tsayawa a hangame sai kuma ya buɗe ya ce. “Bilal” A fili kuma da ƙarfi Junaid ya furta hakan saboda ta’ajjujin ganin Bilal gashi a tsakiyar titi amma tunaninsa da hankalinsa ya rabauta.

Junaid ya zuro kansa ta gilashin motar ya ce “Bilal! Bilal!” A gigice Bilal ya dawo tunaninsa yana take motar a fili ya ce

“Su.. Subuhanallahi”

Ya faɗa da ƙyar, sarai; ya gane mamallakin muryar kawai ya zo masa a bazata ne, baya so, da gaske sam baya son kutse cikin lamarin shi, ya daidaita nutsuwarsa har lau bai kalli Junaid ba. “Bilal ina magana ka manshe ni banza.”

“Junaid zanci Ubanka, wallahi zanci Ubanka ka sake kiran ko kalmar B balle Bilal ka tsahirta mini” Tun da ya ji Bilal ya yi zagi ya san ba sauƙi, a hankali ya ce. 

“Girman naka ne idan ka yi zagin ma babu laifi, ka sassauta ka yi parking da motar taka mu yi magana.” Junaid ware idanunsa akan Bilal.

Bilal ya yi shiru, domin danja ke riƙe da shi dama da tuni ya san inda dare ya yi masa.

“Karka ce mini akan Ridayya kake haka, ban yi zaton haka daka gareka ba, ko da kowa a mafarki ne, Ridayya dai? Uhmm!”

Kammala maganar ya yi daidai da bada damar shigewa Bilal ya take giyar motarsa, da sauri Junaid ya mara masa baya, ganin da gaske ba zai daina binsa ba ya sanya Bilal juyawa ya ɗauki hanyar gida kai tsaye. Bilal na zuwa ya fita daga cikin motarsa, daidai nan Junaid ya fito yana faɗin “Don Allah ka saurare ni, Amma ta turo ni, kai ba a iya gane halin da kake ciki balle hukuncin da zaka ɗauka.” Bilal ya tsaya yana ware idanunsa akan Junaid, wata kalar dokawa zuciyarsa ke masa baya ƙaunar jin maganar da duk ta shafi Ridayya. A fili ya ce

“Junaid ka haife ni ne? Shayar dani ake? To; tun kafin na fasa maka baki ka saurara mini.”

Ya shige bayan kammala maganar, sashin Baba ƙarami ya nufa, Junaid kuma ya shige sashin su Amma. Tunani fal a ransa na abubuwan da suke faruwa a rayuwar Ridayya.

Zameer tun sassafe bayan dawowa daga masallaci ya shirya tsaf cikin yadi mai laushi ya yi kyau sosai, kwarjinin da nutsuwarsa ta bayyana a fili, asalin kyansa wanda yake ƙara narkar da zuciyar Ridayya ya fiddo kansa da kansa, wani sahihin kyau ne da shi wanda sai ka nutsa zaka gani, baya da hayaniya a kame fuskarsa take koda yaushe. Yana ɗaura lins ɗin rigar Khairy ta dube shi sosai sai kuma ta ce

“Meer fita zaka yi ne?”

Ta furta a kasalance, wanda hakan ya yi tasirin wajan Meer, duk yadda yake kokawa da kansa wajan ganin ya gujewa kallonta haƙarsa bata cimma ruwa ba, zuciyarsa ta sanya ƙata tare da shure gargaɗin na Meer, yana riƙe kansa ba tare da zato gabaɗaya yaga idanunsa kwance akan kyakkawar fuskarta fara tas da ita, irin farin da yake so.

“Kina zalunta ta Khary, 

Karki sa na sake aikata abinda ban shirya ba.”

Khairy ta juya idanunta, fusga numfashin Meer ya fara a gaggauce, ya juya mata baya.

“Idan ka fita dame zan yi breakfast?” A taƙaice ya ce “Ina raguwar Indomie dana kawo miki katan guda?” Ta ce

“Saura biyu, ƙwan ma haka” Yana ƙanƙance ido a wannan karan duk nacin zuciyarsa ya yi alƙawarin bazai taɓa juyawa ya kalli Khary ba

“Indomie biyu Khairy bai isa ba? Ba isa ba Khairy?” Ta miƙe tsaye, daga ita sai kayan bacci.

“Ba zan samwa matarka ba, Meer ina son matarka ta san wacece ni da ma’anar zamana a gidan nan, kai da kanka kasan kaf danginka babu mai suna Khairiyya.”

Ya girgiza kai a hankali ya ce “Ke da kika san dangin nawa, Ridayya bata sani ba” Ganin yana ƙoƙarin fita ya sa Khairy shan gabansa ta ce,

“Ka daina saka mini sunan matarka cikin lamarina, na ga ji da kwana zuciyata na dokawa na barazanar da zan iya samu wajan matarka, ka zaɓa kawai.”

Ya juya ya kalleta

“Baki da hankali Khairy, zaɓa kike so na yi? Karki saka na yi abinda zuciyoyi zasu ɓaci.”

Yana faɗin hakan ya fice daga cikin ɗakin, bayan ya tabbatar Khairiyya ba zata buƙaci komai ba. Sanda ya fito ko ƙofar ɗakin Ridayya bai kalla, ya dai yi mamakin rashin fitowa taskar gida da ba ta yi ba, bai damu da rashin zuwa gaishe ba, haka bai damu sanin abinda ya hanata fitowa ɗin ba, ya yi wajan yana baza ƙamshin turaren shi, kamar kullum.

Zameer na fita P.o.s ya ƙarasa, ya cire raguwar kuɗin daya tura a wayar Ridayya, bayan cirar kuɗin wajan mai shayi ya je, ya haɗa masa shayi da biredi da lafiyayyen ƙwai, baya son abincin waje amma bashi da zaɓi, haka ƙaddara ta zaɓa masa. Wayarsa ya ji tana ƙara ganin number Ridayya ya sanya shi sakin siririn tsaki ba tare da wani dalili ba, kira biyar akai masa duk akan idanunsa har ya kammala ya tashi, kai tsaye wajan da suke caca ya nufa maza da yawa kamar shi ke jira.

“Zameer wai a haka kake son ka ciwo miliyan biyun? Baka da rabo a caca” Meer ya yi mitsi mitsi da idanu, ba tare da ya ce komai ba, yana kallon an raba ƴan wasa za a fara kartawa.

“Gaza ka rabu da shi, yana wasa damu ne sai na ƙarar masa da arziƙin matarsa.” AY ya faɗa yana dariya sosai.

“Idan bai ci miliyan biyun ba, ai ya sake ciwo mata kamar yadda ya yi a baya….,” Cikin tsawa Zameer ya ce “Bana so, zan mannawa mutum hauka yanzu ko da wasa kuka sake furta haka.”

A.y ya ce “An bar maganar yanzu na saka dubu hamsin” Gaza ya ce “Na saka dubu hamsin nima” Zameer ya yi shiru

“Kai me ka saka Meer?”

“Ɗan kunnen goal”

“Goal? Ina ka samu goal?” A.y ya furta da mamaki sosai.

Zameer bai tanka ba, burinsa ya yi nasara a wasan ya tashi da dubu wajan ɗari biyu, wasa ya yi wasa aka cinye shi tun kafin su yi magana ya miƙa musu ɗan kunnen goal ɗin ya miƙe tsaye. Yana miƙewa Usman na zuwa da mamaki yake kallon Zameer kafin ya ce “Zameer ya mai jiki kuma?” Meer ya buɗe ido alamar rashin fahimta Usman ya ce “Ashe kuma mai ɗakinka bata ji daɗi ba, hadda suma” Wani gumi Zameer ya ji yana tsastsafowa daga goshinsa da ƙyar ya ce

“Ka ce me?” Usman ya ce

“Wallahi tallahi nake faɗa maka, na ɗauka daga asibiti kake ashe baka shina ba? Ai wani mutum ne mai mota kyakkawa da shi daka gani mai kuɗi ne shi ne ya ɗauketa, kumfa nata fita daga cikin bakinta, a cewar mai ɗakina.”

A makake Zameer ke sauraron Usman tare da kallonsa, wani irin jirkitaccen yanayin Meer yana son shigarsa da gaske, idan wanda yake zato ne yaushe ya dawo gari? Bai san irin uzurin daya bawa Usman ba, ya san dai tabbas ya yi magana sai dai baya da tabbacin abinda bakinsa ya furtawa Usman ɗin.

Zameer ya yi tsaye ya rasa ta ina zai fara kashe gobarar dake shirin tunkaro shi? Bashi da ishasshen ruwan kashe ta, duk wasu gasusuwan jikinsa sai dai suka amsa yanayin da yake ciki, bashi da matsala da Ridayya, addu’ar shi Allah yasa ba wanda yasan da zaman Khairy a gidan shi. Daga wajan cacar gidansa ya shige lokacin bai samu kowa ba, sai Khairy da Zainaba ta rufeta bayan ya buɗe ƙofa Khairy ta miƙe jikinta na rawa ta ce

“Mun shiga uku Zam, meke faruwa ne wai?” Ya haɗe fuska sosai ba walwala, ganin yanayinsa ya sanya Khairy nutsuwa a hankali ta ce,

“Mene nufinka na ajjiyeni a gidanka ba tare da sanin matarka ba? Ita ƙarya fure take bata ƴa ƴa, ramin ƙarya ƙurarre ne Zam” A zafafe ya ce

“Ya isa, ya isheni Khairy, ina tunanin lokacin da zaki koma hotel da zama ya yi” Khairy ta riƙe ƙugu tare da yin shewa tana tafa hannayenta biyu.

“Like seriously? Ni a hotel? Wallahi yadda na faru zamana a gidanka mutuwa ce kawai zata raba ni da shi, zama daram mai naƙuda taga katifa.” Bai furta komai ba, sai kansa dake faman juyawa masa.

“Au yaushe akwai ɗaran bare kwanɗi? Tsoran Ridayya kake?”

Ya girgiza kai a hankali ya ce “Ni ai ban taɓa ce miki ina tsoran Ridayya ba” Khairy ta ce

“Oh! Son ta ka fara kenan? Tausayinta kake?” A karo na farko cikin rayuwar auren su ya ce “Bana nufin haka, ni bance ba kawai nasan ban shirya rabuwa da ita ba.” Ya miƙe tsaye yana duba lokaci ya ce,

“Zan je gidanmu, nasan dole za su duba Ridayya, zan duba daidai lokacin da zasu fito na kira ki ya zamana zuwanki asibitin ya yi daidai da zuwansu ku shigo kamar tare, ok.”

“Kuɗin napep?” Zameer ya dubeta yama rasa me ya sanya take son haukata shi haka kawai, ƙoƙarin shigewa jikinsa take shi kuma yana kokawa da zuciyarsa da abubuwan dake fusgarsa da gaske zuwa gare ta, fuskarsa ta shafa ta ce.

“Ina buƙatar ka.”

“Zuwa anjima” Ya furta yana mata dubu ɗayar data rage masa, ɗakin Ridayya ya nufa ya shiga dubawa cikin sa a yaga kuɗin da take ajjiyewa na tanadin haihuwarta, ya ɗauki kuɗin fuskarsa cike da nutsuwa ya duba yaga a dubu talatin da biyar ɗari takwas ne babu, hankali kwance ya fice daga gidan zuwa nasu.

Har kwana biyu Bilal bai sake dawowa ko hanyar asibitin ba. Da yamma Amma na zaune idanunta akan Ridayya da bacci ya ɗauketa ta juya ta kalli Mami ta ce

“Idan ki kaga Ridayya ta koma gidan mijinta ki ce ni ban haifo ba, koda hakan zai zama ajalinta.”

Murmushi kawai Mami ta yi bata ce komai ba, cike da baƙin ciki da kuma takaici Amma ta juya ta kalli Zainaba data zo duba Ridayya ta ce,

“Baiwar Allah karki faɗa mini abinda hankali ba zai iya ɗauka ba, don idan har ya tabbata haka ne sai na ɗaure shi.”

Zainaba ta gyara zama ta ce “Hajiya ni kaina na girgiza, bani da ƙarfin qiwwar shaida miki yarinyar ba ƴar uwar shi bace, amma ina da yaƙini zaman da suke ba mai kyau bane, tun Ridayya na amarya yarinyar take cikin gidan.”

Amma ta miƙe tsaye ta shiga safa da marwa, tashin hankali ƙarara ya bayyana akan fuskarta.

Zainaba gulma na cinta kamar mijinta ta ce.

“Allah sarki masu siyan ƴar tsala suka dinga bani saƙon gaisuwa wajanta, nina ɗauka ma haihuwa ce amma ganin kumfa na fita ta cikin bakinta ta saka jikina ya yi sanyi.”

Mami dai kanta na ƙasa tana duba azkar, Amma ta ce “Wacce irin kumfa kamar mai dafarar mutuwa, ita Ridayya ɗin?” Zainaba ta shafa kanta ta ce “Haka fa Hajiya, to dana shiga ɗakinta naga babu komai sai katifa na ɗauka ko sanyi ne ya kamata”

A gigice Amma ta juya tare da kallon Zainaba, Mami kuma jin maganar ta yi kamar saukar ruwan sama, jikinta ya yi sanyi kamar wacce akaiwa bugun shekararriyar dawa, ta kasa ɗauke ganinta daga kan Zainaba a hankali ta juya ta kalli Ridayya dake bacci, wata kyakkawar bugawa zuciyar Mami ta yi a karo na farko, duk wani rauni na uwa mahaifiya ya fito, sai yanzu ta lura da baƙin da Ridayya ta sake yi, baƙi na fitar hayyaci ga wani ƙaton ƙashi a wuyanta, babu wata sauran ƙiba a jikinta daka ƙashi sai fata, sai siririn hancinta daya sake fitowa.

Naman jikin Amma har rawa yake saboda tashin hankali ta ce 

“Innalillahi wa’inna ilahir raji’un, kina nufin duk yawan kayan ɗakin da muka kai Ridayya dasu babu? Ina suke ina suka tafi ina Ridayya takai su?”

Zainaba ta ce,

“Nidai babu abinda na gani banda katifa ko labulan arziƙi babu” Sai yanzu hankalin Amma ya dawo kan maganar Ƴar tsala kenan Ridayya ke yin ƴar tsala? Waya ta ɗakko tana duba number kiran farko ko gaisuwa bata tsaya amsawa ba ta ce “Bilkisu ki ɗauki mota yanzu ki biya ta gidan Zuhura ku je gidan Ridayya ku duba mini kayan ɗakinta” Bilkisu ta ce “Gidan Ridayya?”

“Haka na ce Bilkisu ko ba zaki iya bane?” Kamar Amma na ganinta ta girgiza kai ta ce “Ba zuwa ne ba zan yi ba, wallahi ban shirya ƙunsar takaicin Ridayya da gidanta bane, amma bari na shirya” Amma kashe kiran ta yi daidai nan Dr ya shigo ya ce,

“Hajiya ina mijin nata? Tunda ya kawota bai dawo ba kwana biyu kenan” Cike da ban haushi ta ce “Ba shi ne mijinta ba, Dr daman cike nake da kai ka saurara mini” Dr ya ce “Hajiya ki same ni a office.”

Yana faɗa ya fice daga room ɗin rai ɓace.

“Dr ka sani gaba da kallo meke faruwa ne?”Dr ya jinjina kai a hankali ta ce “Ki yi haƙuri ke da Bilal, na yi magana cikin ɓacin rai” Amma ta girgiza kai ta ce “ƙara faɗar mini da gaba kake, maganarka bata gabana kai da Bilal na san yana sane da ita, Bilal ba mijin Ridayya bane, mijinta ko ƙafarsa bata shigo asibitin nan ba har yanzu.” Dr ya dinga kallon Amma kana ya ce

“Kenan yana sane matarsa ta sha fiya-fiya shi ne ya yi sanadiyar suman da ta yi ya ƙarasa taɓa abin cikinta, banda tana da ƙararren kwana da tuni wata maganar ake ba wannan ba, idan takunka bai ƙare a duniya ba daman sai dai kawai sha wahala, amma maganar gaskiya Hajiya Ridayya tana cikin wani hali, dole a kula da ita.”

Tunda ya fara magana take kallon bakinsa kamar ta fahimta kamar bata gane ba, kalmar fiya-fiya ta tsaya mata a maƙoshi, Ridayya da shan fiya-fiya? Ko kuma Zameer ya bata?

Dr ya katse shirun ta hanyar faɗin “Za mu yi mata wankin ciki, violence ya yi yawa a zaman aurenta.”

Miƙewa Amma ta yi ba zata iya cewa ga sanda ta shigo room ɗin ba, gani kawai ta yi Junaid ya riƙeta yana faɗin.

“Amma lafiya? Gaggauta faɗa mana abinda ke faruwa” Girgiza kai ta yi idanunta cike da hawaye ko gabanta bata gane ta yi waje, sam bata lura da Zameer ba wanda ya shigo ba jimawa hakan kuma ya yi daidai da farkawar Ridayya.

Zameer ya matsa dab da Ridayya yana daidaita nutsuwarsa, a hankali take binsa da kallo kamar mai son gano gaskiyar da yake ɓoye a zuciyarsa? Ta runtse Idanunta lokacin data tuna maganar Mardiyya, ko a mafarki ba zata taɓa yarda Zameer zai ci amanar so da ƙauna, haɗi da yardar da take masa ba. Magana take son yi ta gagara sai wani hawaye mai zafi daya shiga fito mata.

Zameer ya kama hannunta duka biyun ya ɗora a saitin zuciyarsa daidai inda take doka masa yana sarƙe numfashi zuciyarsa na tsukewa tare da curewa waje guda, ya rasa inda zai lalubo abinda babu shi ko kaɗan a zuciyarsa wanda zai nunawa Ridayya a hankali ya ce

“Karki nisa dani Mai sona” Ta girgiza masa kai da ƙyar ta ce

“Idan har na yarda ba zaka ci amanata ba meyasa zan yi nisa da kai?” Meer ya sauke numfashin da yake ta riƙe a nutse ya ce

“Zuwana na biyar kenan kina bacci, kin bani tsoro, idan kin barni ke kan ki ba zaki iya rayuwa ba.”

Wani sanyi da nutsuwa Ridayya ta ji yana sauke a zuciyarsa, ciwon da ƙirjinta ke mata yana yayewa wani irin yardar Zameer ya ƙara ninkuwa fiye da ƙima a ranta.

“Ka siyar da ɗan kunnen?” Ya yi shiru ta saka hannunta mai lafiya ta juyo da fuskarsa zuwa gare ta ta ce “Mene?”

A taƙaice ya ce

“Kunyarki nake Ridha, da kunya na ce miki ɗan kunnen goal ɗin ki ya faɗi” murmushi mai kyau ta yi wanda ke ƙara fiddo ramarta ta ce

“Haba dani da kayana duk mallakina ne Rayuwata, daman kai zan bawa kuɗin ka siya mana kayan abinci da iccen wanka sbd haihuwa kuma kaga yadda Allah ya yi” Ya jinjina kai

“Kamar kin san ina buƙatar kuɗi” Ta yi saurin buɗe ido ta ce 

“Me zaka yi da kuɗin?”

Ya marairaice fuska yana sumbatar hannunta a hankali yake ɗan sauya yanayi ya ce “Mai sona kike tambayata me zan da kuɗi, sbd kulawa dake matata” Ai Ridayya duk duniya ji ta yi ba macen da tafi ta zarra da samun miji kamar Zameer

“Ka duba ɗakina ƙasan filo akwai kuɗi” Da sauri ya fara girgiza mata kai ya ce “Haba idan na ɗauka ke kuma fa Mai sona?” Ta haɗe fuska ta ce “Ka fini buƙata,kuma ina yin dashi da ribar ƴar tsala na kusa ɗauka.”

Ya yi murmushi ya ce

“I love you mai sona.”

“Kai” Suka ji an furta

Gabaɗaya suka juya Bilal ne tsaye bakin ƙofa cikin waganbari da ya yi masa kyau hannunsa zube cikin aljihu, idanunsa akan Zameer ya ce

“Zo ka fita” Zameer ya ce

“Matsayinka nawa?”

“Na wan matarka” Zameer ya miƙe tsaye idanunsa akan Ridayya ya ce “Ridayya kina gani, ƴan uwanki baza su taɓa barina dake ba, kullum cikin jure wulaƙancin su nake saboda kawai ina son ki, sau nawa ina zuwa suna hanani shigowa wajanki?” Zameer ya girgiza kai yana ƙoƙarin ganin ya bayyana rauninsa a fili yadda Ridayya zata gasgata maganar shi ya ce “Cewa sukai ni na ɗora miki fiya-fiya wai don na kashe ki, Ridayya na san lokacin da kika sha fiya-fiya, tun safe na fita ina fafutukar ganin na rufa mana asiri na riƙe ki da kyau amma basa gani, ɓaraho suke son na zama? Ko ɗan fashi da makami? Me ya sa Ridayya me na yi ƴan uwanki?” 

Ridayya jikinta ya fara rawa, Junaid mamakin munafurcin Zameer ya kashe shi a tsaye kamar wata mace? Bilal ya ce,

“Ka fita, ka zo ka fice daga room ɗin nan.”

“Ba zan fita ba, wajan matata na zo” Bilal yana zuwa ya ɗauke Zameer da mari, har ya ɗaga hannu zai rama sai kuma ya fasa ganin yadda Ridayya ta runtse Idanunta. Bilal ya ce

“Idan kai baka san darajar rayuwar Ridayya ba kamarwa wanda ya san darajarta” Zameer ya ce “Ok kana nufin na saketa ka aura? Aure zaka kashe mata ashe” Junaid ya san da gayya Zameer yaƙi rama dukan, sbd idanun Ridayya banda hakan sai dai su daki juna.

Bilal ya dunƙule hannu ya kaiwa bakin Zameer naushi da ƙarfi ya ce “YES! I do love her, I love her ka saketa idan ka haifo.”

“Bilal!!” Ridayya ta kira sunan Yaa Bilal, wanda hakan ya yi daidai shigowar su Bilkisu da Zuhura, Amma, Mami da Baba ƙarami, sai Khairy da Mama da Karimatu.

Babu wanda bai girgiza da jin sunan Bilal gatsal a bakin Ridayya ba, domin har Baba ƙarami baya iya cewa Bilal sbd darajarsa da suke gani kaf dangin shi ne babba.

“RIDAYYA!” Mami ta kira sunanta, ta nufeta zata daketa Baba ƙarami ya ce “Karki fara Fatima, ba kiga mijinta ake duka ba?” Amma ta ce

“Babu yadda za a yi Uban masu gida ya daki mijinta ba dalili kasan halinsa ba komai yake damunsa ba, yarinya ta fifita miji akan kowa?”

Bilal ji ya yi idanunsa na neman ɗaukewa, baya son yarda Ridayya ce ta furta wannan sunan daga bakin da yake jinsa har rai da mutuwa, wani baƙin ciki ya wanzu a zuciyarsa ƙirjinsa ya yi masa nauyi.

Cikin rashin sani ya sake dunƙule hannu ya kaiwa Zameer naushi nan take bakinsa ya fashe, wani irin Miskilin Meer ya yi.

A gigice ta fisge ƙarin ruwan, jini ya fara zuba sam bata damu da hakan ba, idanunta cike da wutar son mijinta..

“BILAL!” Ta kira sunan Yaa Bilal ta ce

“Mijina kake duka kamar ɓarawo haka? Da gaske mijina kake duka? Daman kai kake hana shi zuwa gidanmu?”

Da mamaki gabaɗaya mutanen wajan ke kallon Ridayya Bilal ya ce

“RIDAYYA! Sunana kike kira haka…,”

“Na faɗa BILAL, ba haka ne sunanka ba? Bana ƙaunarka kamar yadda baka ƙaunar mijina, ba zan kai ka ƙara ba, Allah ya isa dukan mijina da ka yi…,” Wani mugun mari Junaid ya kai mata ya ce “Banza, akan wannan mijin? Daman ni na sallamaki duk wata damuwarki will never be my headache.”

Ridayya ta fashe da kuka ta ce “Ko namana zaku yayyenka wallahi ina ƙaunar mijina, ina ƙaunar shi fiye daku.” Mami kallon ƴarta take tana jin wani takaici na rufeta yanzu abin tsoro yake bata, anya Ridayya lafiya take?

Bata haukace ba, Zuhura murmushin ɓacin rai take wacce irin soyayya ce mai hana ganin laifi yaushe Ridayya zata yarda Meer ba ƙaunarta yake ba?

Amma ta kalli kowa idanunta ya sauka akan Khairy sai kuma ta juya ta kalli Bilal da jiri ke neman kada shi ta kalli Ridayya data riƙe hannun Meer a fili ta ce

“Komai ya zo ƙarshe In sha Allah a yanzu ba sai anjima ko gobe ba Zameer zai saki Ridayya ba saki ɗaya ba saki uku muke buƙatar ya yi mata yanzu.

<< Munafukin Miji 2Munafukin Miji 4 >>

1 thought on “Munafukin Miji 3”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×