Skip to content
Part 4 of 9 in the Series Munafukin Miji by Nimcyluv sarauta

Ridayya ji ta yi ciwon da zuciyarta ke yi mata ya dawo sabu fil, cikin wani irin rikitaccen tashin hankali daya gama mamaye ilahirin lungu da saƙo na ƙofofin halittar ƙirjinta, wacce take ƙara kissima mata soyayyar Zameer a kullum.

“Kada ki nemi kashe ni da rai na Amma, kada ki ce zaki hukunta ni ta hanyar da zuciya, gangar jikina ba za su ɗauka ba.”

Ganin amma taƙi yadda ta kalleta, ya saka Ridayya sakinta tare da
juyawa ta kalli Zameer dake tsaye, idanunsa cike da hawayen daya gama ƙirƙirar su a wajan ta ce “Kalamanki kamar fitar dalma haka suke sauka a ƙirjina Amma, rabani da mijina kamar bayyanar ranar mutuwa ce, wallahi duk duniya ba wanda nake so sama da Zameer idan ki ka cire Mami, ina ji a jikina bayan bautar Ubangiji; Allah ya halicce ni domin na rayu da soyayyar Meer, me ya sa kuke ƙoƙarin kashe ni da rai na? Bayan ina numfashi? Kuna kallona na faɗa muku ina son shi mene ribarku idan kun rabani da shi”
Ridayya ta ƙare maganar tana jan numfashi a wahale, komai nata ya yi tsayiyuwar sojojin da suke tsaka da fareti.

Murmushin baƙin ciki da kuma takaicin halin Ridayya Junaid ya yi, duk yadda ya tursasa zuciyarsa wajan ganin bata ɓaci ba, a kan haukan da Ridayya ke yi musu a cikin asibiti abin yaci tura. “Makauniyyar soyayya ko? Ridayya anya baki haukace ba? Kin san kalaman da bakinki suke furtawa Amma? Ko giyar wake kika sha kin yi tsararo ki sauke mana ita a nan, ramin da kika haƙa kin yi
kaɗan ki faɗa ciki damu, sai dai ki kwashi turɓayar data rufe miki ƙofifin zuciyarki ki rufe kan ki da ita wallahi” A hargitse Junaid yake maganar kamar zai kai mata dukan ɓarin makauniyya.

Baki Ridha ta buɗe, a ƙoƙarinta na son fayyace musu irin so da ƙaunar da Zameer yake mata, amma sun sanya audiga mai kauri tare da toshe kunnuwansu, tilas baza su saurayi kukan nata ba, balle surutanta a wanda suke musu kama dana sabon kamo.

“Yaa Junaid wall…,”

Wani mahagon mari aka ɗauke Ridayya da shi, daga bahagon hannun daya jima bai duka ba. Mami ta rasa me zata furta akan Ridayya, da gaske duk wata kalma da zata yi futar mashi daga cikin bakinta ba zata yi kyau ba, abin ba zai haifar da ɗa mai ido ba, bata so yin mummunan kalamai akan Ridayya, domin yin haka na nufin ƙara lalacewarta, tabbatacce ne kaifin bakin uwa akan yaranta.

“Ridayya!”

Ta kasa faɗin abinda ta yi niyya, cikin hanzari kamar tafiyar hadari a saman gajimare ta fice daga cikin room ɗin.

Amma ta juya ta kalli Baba ƙarami dake tsaye yana nazarin yanayin da Bilal ke ciki, wanda kalaman Ridayya suka jefa zuciyarsa cike dake ɗauke da rufaffen kuma ɓoyayyen sirrin da yaƙi bawa kowa damar fahimta, sai yanzu da a nutse da kuma idanun basira daya saka Baba ƙarami yake wassafowa yana gina shi a tubali ma’ana.

“Ridayya ki ƙaddara silar mutuwar aurenki zai saka ki haɗiye zuciya ki mace, wallahi sai Zameer ya sakeki a yanzu.”

“Assha! Assha ban so ki ka rantse ba, ina jiye miki kaffara musamman ta azumi” Baba ƙarami ya tari numfashin Amma da hakan. Ta rusuna a ladabce cikin girmamawa ta ce “Ka yi mini haƙuri da afuwa kada ka dakatar da ƙudirana na ceton Ridayya daga duhun rijiyar data zama shekararriya, karka hana ni ina son kawo ƙarshen alaƙar dake tsakanin su biyun.”

Baba ƙarami ya girgiza kai a hankali kuma ya nemi saman kujera tare da zaunawa akai, ya jima da fahimtar idan aka biyewa mata maimakon a gyara ɗaya sai goma ta ɓaci.

Bilal zufar dake yankowa a saman goshinsa yake saka hannu a hankali tare da sharewa, dokawa zuciyarsa take da wani irin sabon sauti da bai taɓa jin irinsa ba a tattare da shi. Ya saba da bugun luguden da take masa a ko wacce da ƙika dake tafiya, ta dalilin tunanin Ridayya, al’amarin da ya gama addabar rayuwarsa ta kowacce siga.

Sunanta kaɗai yana sawa halittar gashin dake kwance a saman fatarsa mimmiƙewa, tsigar jikinsa na tashi ƙirjinsa na dokawa da ƙarfin da yake kasa fitar da numfashi. A yanzu ma haka ɗinne Bilal kokawa yake da zuciyarsa wajan ganin bai juyawa ya kalli Ridayya da yanayin da take ciki ba, baya fatan ace hawaye ne suke fita daga kwarmin idanunta, ba zai jure ba, da gaske ba zai jure yanayin da take ciki ba. Juyawa ya yi da nufin barin ɗakin jinyar dake cikin asibiti jiri na kwasarshi kasancewar yana da kyakkawan jiki a buɗe ya saka hakan bai faru ba.

“Babban mutum”

Baba ƙarami ya kira Bilal, kiran daya dakatar da shi daga ficewa, yana tsaye inda yake. “Dawo ka zauna” Ya bashi umarni kai tsaye.

Bilal gwada taurin kansa ne baya so, surutu da idanun jama’a na ƙarasa kassara masa ƙarfin qwiwarsa. A nutse ya nemi waje can gefe ya tsaya baya jin zaman komai na wajan gundirarsa yake, Junaid ma ya tsaya kusa da Bilal. Baba ƙarami ya kalli Ridayya dake durƙosa hawaye yaƙi tsaya mata ya ce “Auta dawo kan gandonki kin ji” Ta miƙe da sauri Zameer ya matsa cikin son nunawa kulawa da tsantsar soyayya ya kama hannun Ridayya a bayyane yake cewa.

“Sorry AMOIR, ina tare dake ina so da ƙaunarki.” Ya faɗa a fili a hankali daidai kunnenta ya ce “Ina son zamanki a gidana, ko babu komai gida da mutum kuma mace Rahama ne.” Nutsuwa ya shiga saukarwa Ridha a zuciya ta san aka raba auren Zameer ba zai taɓa jurewa ba, ba zai iya zama da ko wacce mace ba bayan ita.

Bayan kowa ya zauna, Amma, Mami data shigo, Balkisu da Zuhura sai ƴan’uwan Meer mama da Karimatu da Khairy wacce ke tsaye idanunta akan Bilal.

“Bamu da hujjar kashewa yarinya aure babu dalili, babu da zarafin aikata wannan ɗanyen aikin da gaske” Cewar Baba ƙarami. Amma ta buɗe baki zata yi magana ya yi saurin dakatar da ita da faɗin “Ki bani dama na yiwa Ridayya tambayoyi waɗanda amsoshinsu da su zan kafa hujjar raba auren” Ya juya kan Ridayya ya ce.

“Auta ki ji tsoron Allah ki faɗa mini gaskiya, idan kin mini ƙarya Ubangiji yana gani ba zai barki ba.”

Gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi kamar kazar da ƙwai ya fashewa, ta jinjina kanta alamar “To”
Baba ƙarami ya kalli Ridayya da kyau ya ce
“Ridayya kina samun abincin da za kici a gidan Zameer? Safe, rana, dare?” Daram! Dam! Zuciyarta ta bada sautin fashewar tayar mota.

Rabonta da cin abinci sau uku a rana tun satin amarcinta, ko abinci ta samu tana haƙura ta bawa Zameer ita tasha ruwa, tun tana ciwon ciki har lalurar ya zame mata jiki. Wanne harshe zata yi amfani da shi wajan kare kanta? Tasan waye Baba ƙarami mutum ne mai tsayawa akan ra’ayinsa kaifi ɗaya ne shi, gabaɗaya inuwarsa halayyarsa take bi zubin nagartarsu ɗaya da Bilal.

“Ridayya!” D sauri ta ce
“Na’am Abba” Ya haɗe fuska “Bani da cikakken lokacin jiranki bani amsata” Zameer ya buɗe baki da nufin cewa wani abu Baba ƙarami ya dakatar da shi ya ce “Tsahirta mini tukunna.”

Ridayya ta share duka gaskiyar data gino akai tsayin shekaru tasan a’a yana nufin mutuwar aurenta da Zameer wanda bata ƙaunar haka, ko ƙasa zata dinga kwaɓawa tana ci don yunwa ta aminta ta rayuwa da shi.

“Abba Zameer bai taɓa hanani abinci ba, kullum cikin faɗan bana son abinci yake mini ma, kafin ya ƙare ya ajjiye wani” Ba ita da ta yi ƙaryar ba, hatta shi da kansa Zameer ya jijjiga ya ɗago kai yana kallonta a ransa yake furta.

“Munafuka, maƙaryaciyya ko kwanan shinkafa ban taɓa ajjiyewa ba balle buhu, yunwa duk ta cinyeta ta ƙara mata duhun fata kamar kalwa.”

Baba ƙarami ya aminta, domin bai taɓa ji ko ganin ta zo neman abinci ko ta ce babu ba, bata taɓa cewa a bata kuɗi ba. Ridayya tasan Bilal zai rufa mata asiri, ba zai taɓa ƙaryata kalamanta ba, baya sati bai tura mata kuɗi a cikin account ba.

“Ina kayan ɗakinki suke? Mene ya haɗaki da sana’ar ƴar tsala?”

Kai tsaye ta ce “Abba gobara mukai kayan suka ƙunne da ƙyar na tsira da sauran, ƴar tsala kuma ina sha’awar sana’a shi ne dalili”

“Ƙarya kike, ɗakinki bai yi kama da inda akai gobara ba, balle tashin wutar ya cinye furnitures ɗinki” Bilkisu ta ce
“Gaskiya kam, tsaf ɗakin yake inda akai gobara daban suke” Ridayya ta ɗago kai ta kalli yayyin nata kafin ta ce,

“Na siyar, bana buƙatar su ne” Zuhura ta ce
“Kin siyar ko mijinki ya siyar Ridayya?”
Ƙirjin Ridayya ya fara ɗagawa ta fara gani bibbiyu, hawaye na biyun kuncinta ita sam ba taga dalilin da zai saka a dole sanya bakin almakashi wajan datse halataccen aurenta da masoyinta ba.

“Ya isa, tambayar ƙarshe mene ya haɗaki da shan fiya-fiya? Ba kuma shan gangan ba, shane da nufin kashe kai a wuta da rayuwar duniya, mene hujja? Duk soyayyar ce?”

Ta yi shiru domin ta fara fita daga cikin hayyacinta, hankalin Zameer yana kan Khairy da yaga ta zubawa Bilal Idanu, hankali tashe duk da dauriyar da yake son yi yake binta da kallo, ina dalilin bin Bilal da wannan kallon?

Junaid kuma idanunsa akan Zameer yana ganin yadda yake bin Khairy da kallo.

“Abba magani na ajjiye a irin kwalbar fiya-fiya ɗin, na gama abinci zan sha tsautsayi da ƙaddara ya saka na ɗauki kwalbar fiya-fiya ɗin. Abba don Allah karka tambayi wanne magani me ya sa kuka tsane ni saboda ina son mijina? Kai na tsanata zaka yi?”

Zuhura ta yi kan Ridayya zata daka Zameer ya yi saurin shiga tsakiya ya riƙe Ridayya ya ce,

“Sai dai ki dakeni, me ta yi muku? Saboda kawai na kasance mijinta? Saboda bata son wanda kuke so ai nasan cewa Bilal son ta yake shi ne hujjarku ta raba aurenmu.”

Zameer ya faɗa cike da munafurci.

Baba ƙarami ya ce,

“Saketa ta zauna likita na zuwa, yau za a yi komai a gama idan har Bilal na son Ridayya tabbatas na yi farin ciki, amma son bai masa rana ba, ya riga da YA YI SAKE, idan kuma na tabbatar yana sonta to a yanzu zaka saki Ridayya tunda babu idda a kanta shi kuma a yanzu zan ɗaura masa aure da ita.”

Wani ihu da kururuwa Ridayya ta yi kamar mahaukaciya ta ce,

“Wallahi bana son shi, bana ƙaunarsa Allah zan iya kashesa idan kuka yi gigin rabani da Zameer, ko mijina zai dinga yankar naman jikina yana ci na yarda zan zauna da shi har mutuwa, zan yi nisa daku zan manta daku mijina shi kaɗai ya Isheni rayuwa ban damu da kowa da komai ba, ba abinci, ba suttura, ba magani idan ba komai idan ƙasa ko duka zai dinga lakaɗa mini ba ruwanku zan zauna da Zameer amma ban taɓa ƙaunar Bilal ba.”

Kamar mahaukaciya haka Ridayya ta zama, ta mance cewa a gaban Baba ƙarami take wanda shi ne mahaifin Bilal, ko mutuwa tana jin kunyar idon mahaifi balle Ɗan’adam.

“Yau na tabbatar Ridayya baki da hankali, ke da bakinki kike furta kalmar tsana ga Bilal? Kin mata halaccinsa ko? Banda shi da kuma darajarsa da baki isa ki auri Zameer ba, shi ne ya yi uwa tare da makarɓiyya ya tsaya miki” Bilkisu ce ke maganar wacce ke zaune ta nuna Ridayya da hannu tamkar zata kai mata duka. Cikin ƙarin wani ɓacin ran Bilkisu ta ɗora da faɗin.

“Kalar naki halaccin kenan? Irin godiyar da zaki masa” Muryar Ridayya na rawa ta ce
“Ku kashe ni kawai idan hakan zai faranta ranku, don Allah wallahi da a rabani da Zameer gwara ni na kashe kai na.”

Gabaɗaya kallonta suke da wani irin mamaki, razani da rashin hankali.

A karo na biyu Ridayya ta kalli inda Bilal yake, cikin sa a suka haɗa Idanu. Wata tsinkewar gaba ce ta gitta ta zuciyarta, kaifin idanunsa ya sanya ta ji zuciyarta na bugawa, jikinta ya ɗauki ɓari na abubuwan da take ji a duk sanda ta kalli idanun Bilal, dukkan wata halitta dake jikinta sai data amsa yanayin da Ridayya ke ciki, wanda kallon Bilal ya haifar mata.

Yana mata wani irin kwarjini ko motsinsa ta ji gabanta faɗuwa yake ba tare da sanin dalilin hakan ba, tsigar jikinta duk sun mimmiƙe suna amsa yanayin maikama da ji da motsin buƙatar abu daga gare shi.

Cikin sauri ta ce “Asstagafirullah!”
A nutse Bilal ya juya tare da ficewa, sai a lokacin Junaid ya ce “Wacce kuma waccan?”

Meer ya kasa ɗago kansa kai tsaye ya fahimci Khairy Junaid ke magana wacce ta bi Bilal da kallo da zai shige. “Tare muke”

Kai tsaye Meer ya furta hakan ba tsoro, duk basu kawo komai ba, ganin ƴan’uwan Meer ɗin suna wajan sai hakan ya shaida musu Khairy wata ce a familyn nasu. Fita sukai daga cikin room ɗin aka bar Zameer da Ridayya wacce take cikin tsananin ciwo, tun bayan fitarsu yake chatting da ƴan mata. Saƙon Khairy ne ya shigo.

“Ka gaggauta fitowa,ina buƙatar ganinka” Ya cilla wayar cikin Aljihu tare da miƙewa tsaye. Ridayya ta ce “Ba dai tafiya zaka yi ba?” Ya dubeta ransa na ɓaci ya ce.

“To bari na tsaya na goyaki” Ta saki baki, yanzu akan idanunsa kowa na dangin ya saka ƙafa ya fice ya barsu tunda shi ta zaɓa.

“Idan ka tafi wa zai kula dani? Kana ganin babu kowa?” Ya saki tsaki cikin ɗaga murya ya ce

“Karki takura ni…,” Ko me ya tuna sai ya yi shiru a hankali a taushashe ya ce “Mai sona idan na zauna a nan ƴan uwanki zasu ɗauka da gaske zaman banza nake, dole na fita na kawo miki abincin dare da kuɗin siyan magani.”

Nutsuwa ce ta saukar mata, ta yi imani kafin samun miji irin Zameer abu ne mai wahala ta ce,

“Na fahimta RAYUWATA, Allah ya kiyaye ka dawo mu kwana tare.”

Ya motsa fuska Zameer yana juyawa Ridayya ta ce “I love you Rayuwata.”

Ko a kwalar rigarsa haka kalaman nata ya jisu, har ya je bakin ƙofa ya tsaya ya ce “A inama kuɗin suke?” Ta maimaita ya fice abinsa..

Har ƙarfe biyu na dare babu labarin Zameer, Ridayya ta ci kuka sosai ganin tana shirin mutuwa babu wanda ya dawo a gidansu hakan bai dameta ba, addu’a take Allah ya sanya Zameer lafiya yake shirun ya yi yawa.

A kari na takwas ta sake kiran number shi cikin sa a aka ɗauka a hankali ta ce.

“Rayuwata!” Wani irin tsalle da bugun casar gero cikin turmi haka zuciyarta ta yi, ihu da surutan Zameer ne ya cika kunnenta, da wani irin sauti can ƙasa wanda kai tsaye ba zata iya fahimtar kalar shi ba.

“Rayuwata! Meer!”.
Maimakon ya bata amsa sai saukar wata murya ta ji a kunnenta ana cewa.

“Ka yi a hankali, kar a jiyo muryarka, ban saba ba wannan shi ne yi na na farko…

Bakandamiya domin ku ake posting, comment ake buƙata 

<< Munafukin Miji 3Munafukin Miji 5 >>

1 thought on “Munafukin Miji 4”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×