Skip to content
Part 5 of 9 in the Series Munafukin Miji by Nimcyluv sarauta

Ridayya ta ɗauka kunnenta ne ya sa mu matsala, cikin sauri ta zame wayar daga jikinta tare da saka hannu ta shiga bubbuga kunnen a fili ta ce “Babu mamaki ruwa ne ya shiga ciki, ya toshe ƴar ƙofar ɗaukan sautin har take naɗo mini masifa da bala’i”

Ta mayar da wayar a hankali duk da ƙirjinta dake bugawa da muryarta ke rawa bai hana ta tattaro jarumta kamar jinin Iliya ɗan mai-ƙarfi ba ta ce “Rayuwata, ni ce matarka Ridayya ka na ji na?” Ta yi maganar cike da ƙarfafawa kanta qiwwa, da share gurɓataccen zaton da zuciyarta ta yi mata akan Zameer. Shiru babu amsa sai wayar data fara shuuuu!! Kamar kammalawa shirin gidan rediyo ya yin rufewa, da yin ban kwana da masu sauraro.

“Asstagafirullah! Allah na tuba ka yafe mini, daman nasan sharrin shaiɗanne kawai yake son kissima mini wani mummunan zato akan Meer” Ta yi shiru; tana sauraran bugun zuciyarta da take mata, kamar luguden gidan biki.

Duk yadda idanunta ya su runtsawa da samawa kanta nutsuwa al’amarin ya gagara, bacci ya ƙaurace wa idanunta. “Allah ya gani ina so da ƙaunar mijina, Yaa B ka yi haƙuri ba yin kai na ba ne, bana jin zan iya rayuwa ba tare da Zameer kusa dani ba.”

Hawaye ya shiga zuba daga kwarmin idanunta, zuciyarta na tsananta bugawa ki manin daƙiƙar gudun lokaci.

Da ƙyar bacci ya ɗauketa gab da asuba, ba wani na kirki ta yi ba ta ji ƙarar wayarta alamar shigowar saƙon karta kwana, cikin ganɗoki ta ɗauka zuciyarta na faɗa mata Meer ganin wanda ba ta yi zato ba ya saka ta ƙura wa saƙon Idanu.

Alert ɗin kuɗi ne, sai gajeren saƙo daya biyo bayan alert ɗin. Ridayya ta rufe idanunta, da gaske tana buƙatar taimako, daga na kuɗi har na kulawa, tana buƙatar sharing damuwarta da wanda zai fuskance ta, wanda zai kyautata mata zato akan soyayyar Zameer ba wanda zai dinga ganin laifinta ba.

Ta zubawa sunan Bilal idanu, wanne irin abu za ta yi masa wanda zai tsane ta? Tsana mai muni ya dinga ganin baƙin ta kamar yar da a yanzu take ganin nasa?

Kuɗi ne kimanin dubu hamsin ya tura mata zuwa asusun bakinta, yasan da gaske tana buƙatar su.

“Yaa Bilal why? Me ya sa? Bana ƙaunar ka, na tsane ka gwargwadon tsanar da ka yi wa mijina, ba kai ba duk wanda zai wulaƙanta Zameer a duniyar nan ko waye zai i ya wulaƙan ta shi…”

Ta yi maganar a fili kuma a raunace, sunan Yaa Bilal data ambata yana mata amsa kuwwa! A cikin kunnenta, bugun zuciyarta na ƙaru wa duk a dalilin jin sunan Bilal ɗin ya fita a bakinta.

Har aka gama sallah tana nan a zaune, da ƙyar ta yunƙura zuwa banɗakin dake cikin ɗakin asibitin. Shiru ba kowa sai ita, ga aikin da akai mata, ga gubar fiya-fiya data sha, ga damuwar zuciya wacce take tunanin babu wanda ya haddasa mata irin danginta. Mijinta bai rage ta da komai ba.

Nas ce ta buɗe ƙofa hannunta ɗauke da kayan duba mara lafiya, ta tsaya gaban Ridayya tana mata tambayoyi da ƙyar take buɗe baki wajan amsa mata har ta kammala.

“Can i ask you dear?”

Ridayya ta kalli Nas sai ta jinjina mata kai alamar “Why not?”

“Thank you”

A hankali ta sauke ajjiyar zuciya tana kallon Ridayya dake matar da shekarunta a haife zata haifi Ridayya a nutsu ta ce.

“Tunda nutsatstan magidancin nan ya kawo ki asibiti na fahimta a kwai damuwa a tattare dake, na ji tamkar ƴata Safiya ce a cikin condition ɗin da kike ciki, ƴa ƴa na kowa ne bawa sai mai shi. Zan so ki buɗe zuciyarki ki aminta dani ba zan cutar dake ba, ki faɗa mini mene damuwarki please, i just feel your pain”

Kan Ridayya a ƙasa ta kasa cewa komai saboda yar da ba ta jin daɗin al’amarin da yake riskar ta a yanzu.

“Ki yar da dani, mene dalilin shan fiya-fiyan da kikai? Ba rashin sani bane yunƙurin kashe kai da kai kikai ɗiyata, na karanci damuwar dake shimfiɗe a fuskarki what’s going on? Waye shi? Su kuma su waye? Kyakkawan namijin nan waye?”

“Shawara kika zo bani, ko kin shirya faɗa mini mugun abu game da lafiyata? Ko kina son sanar dani mijina na cutata kema”

Ridayya ta faɗa tana mai kallon Nas ɗin da raunatacciyar muryarta.

Nas ta kama hannun Ridayya ta ce “Ta ya ya zan aibata miki miji ba tare da sanin ya zamanku yake ba? Ai mai ɗaki shi ya san inda yake masa yoyo, rumfar kara ragayar mai shi” 

Ridayya ta jinjina kai a ranta ta samu nutsuwa da nurse ɗin a taushashe ta ce “Wanda ya kawo ni asibitin nan zan iya ce miki ubana ne…,”

“Uba kuma?” Nas ta dakatar da Ridayya da faɗin haka. Ridayya ta ce

“E, Abbiey na ne” Nas Hajjara kallon Ridayya take da mamaki kuma ta kasa fahimtar abinda take faɗa ko dai bata gane wanda take nufi ba ne? “Mamaki ko? Bana ƙarya, ban san yadda ake yinta ba, mutum ɗaya ne ya taɓa sani yin ƙarya a duniya, yanzu kuma na zama shaharriyar maƙaryaciyya”

“Ba mamaki bane, abu ne mai kama da almara kin gane wanda nake magana akan shi ƴar nan?”

Murmushin takaici Ridayya ta yi da kanta ta san ba ta yi wa Yaa Bilal adalci da halacci ba, ta yi ƙasa da kanta saboda harbar da gefen kanta ya yi a hankali cikin raunatacciyar muryarta ta ce “Uhm”

“Wani fari zubin buzaye? Mai girman jiki, wani mara fara’a da rashin son magana sosai, wani mai yawan dafe kai? Wani mai tsayi da kuma faɗi…,”

Da sauri Nas Hajjara ta ce “Lallai ba shakka shi nake nufi, waye shi a wajanki? Domin na ɗauka shi ne mijinki sanda ya kawo ki asibitin hankalinsa a tashe ko takalmi babu a ƙafar shi, waye wannan ɗin?”

“Babana, Abbiey na”

“Ikon Allah, bai yi kama da babanki ba, amma mene yake faruwa tsakaninki da shi da kuma sauran?”

“Long story, _labari mai tsayi_* Ridayya ta faɗa a taƙaice domin ta fara jin hirar na hawar mata ka, yunwa take ji ga damuwa da ta yi mata ƙatutu a zuciya ki numfashi da ƙyar take haɗiya.

“Ƴar nan zan so jin labarinki da yar da akai kika auri wannan mijin naki wanda ke shirin salwantar da rayuwarki”

A gigice Ridayya ta ɗago rinannun idanunta da suka gama jirkicewa sai kuma ta saki dariya kamar mai taɓin hankali, ta girgiza kai ta ce

“Ko a mugwayen mafarkan da nake yi a kullum, bana fata da gaske bana fata na yi mafarkin rayuwata ta baya, babu komai cikinta babu kowa a wancan rayuwar sai Abbiey ba kowa cikinta, da rayuwar baya data yanzu maja ce, mizaninsu ɗaya, rayuwata a jirkice take a baibai take na shiga uku ni Ridayya….,”

Kukan da bata samu damar yinsa lokacin da idanunta ya yi mata mummunan gani a ɗakin Zameer shi ne take yinsa a yanzu, shi kansa kuka rahama ne rashin yi tauye zuciya da abinda ke cikinta yake.

Bata son tuna komai, amma abun kamar an yi masa wahayi sai gilmawa ta idanunta yake tamkar majigi.

“Innalillahi wa’inna ilahir raji’un! Ubangijn ka tausaya mini ka sa na farka naga bacci nake, wacce irin rayuwa nake ciki ne? Shin daman haka aure yake? Ko wacce mace kalar baƙin cikin da take ɗanɗana kenan ko ni ɗaya ce, daman da ake cewa aure ɗan haƙuri ne hakan shi ne haƙurin?” Sosai Ridayya ke kuka tana buga kanta da ƙarfen gadon jikinta na karkarwa, duk wanda ya ganta dole ya tausaya mata ita kaɗai tasan abinda take haɗiya, damuwar aure na son haukatar da ita shekarunta sun yi kaɗan, ƙwaƙwalwarta ta gaza ɗauka.

“Mene laifina don zuciyata ta so wanda take ganin shi daidai da ita? Mene laifina don gangar jikina ta so rayuwa da wanda take ganin shi ne mahaɗin rayuwarta, bangon da zan jinkina na ji daɗi? Me ya sa bangon ke shirin yar dani ƙasa ya ruftu mini aka? Me ya sa na kasa yar da ko gasgata abubuwa da yake mini? Idan ko wanne bawa da ƙaddarar shi tabbas tawa ƙaddarar ta _SO!_ ce, lissafin ƙaddarata _ZAMEER_ ne, Allah kar ka hukunta ni da zunubaina baya na tuba Allah na tuba kar ka hukuntani na yi ladama”

Nas Hajjara ta rirriƙe Ridayya da jini ke zuba a saman goshinta ta ce. “Babu ƙarya a lafuzzanki da gaske So jarabta ne kuma ƙaddara ne, da so kawai Ubangiji yaga dama sai ya hukunta bawansa da shi, aure ibada ne, kuma ko wacce mace a duniya haƙuri take a gidan mijinta, duk wacce zata fito ta ce miki zama lafiya ne wani abun ba a ɗauke kai a yi haƙuri ki ce mata na ce ƙarya take, domin ko tsakanin harshe da haƙori ana saɓa wa”

Nas ta kwantar da Ridayya wacce ta gama fita hayyacinta ta ce “Wallahi tallahi da na ganki na ɗauka tsohuwa ce, kin wani ranƙwafa idanu ƙwala-ƙwala ga baki da ya yi tsayi ƙashi kamar zan ajjiye jarkar ruwa, babbar matsalar yaran yanzu basa bambance SO da BIRGEWA, ƙuruciya da tashan balaga ne kawai ke ɗibansu da tsinanniyar zumar soyayyar nan ta samarin yanzu da take hurewa yaranmu kunne, yarinya ta na ce akan yaro bayan bata da tabbaci idan son gaskiya take masa”

Faɗa sosai Nas Hajjara take yi kamar zata ari baki, burinta a yanzu bai shige ta ji labarin Ridayya ba da yar da akai ta auri Zameer mene alaƙarta da Yaa Bilal wanda ta bawa sunan Abbiey?

“Who knows the truth? _Only God knows!_” Ta tambayata ta bawa kanta amsa.

 _Waye ya san gaskiya? Ubangiji ne kaɗai ya sani_. Kasancewar a file ɗin Ridayya akwai information nata da number wayar Bilal data Zameer. A kusan lokaci guda aka kira su.

Zameer na zaune bayan ya kammala karyawa lafiyayyar Indomie ya ci da ta ji kifin gwangwani ya haɗa shayi mai kauri shi da Khairy. Duk a cikin kuɗin da Ridayya ta ce ya ɗauka. Khairy dake kwance kanta a cinyarsa wandon ball ɗinsa na jikinta ba ko riga ta kifa cikinta ta ce “Baby ba kiranka ake ba?” Zameer ya yi jim ganin sabuwar number sai kawai ya share, aka ƙara kira rai ɓace ya ɗaga.

“Muna kira daga nan asibiti, muna magana da Zameer ne mijin Ridayya Bilal Mansur Rano?”

“Nine ya akai?” Daga cikin wayar aka ce “Muna buƙatar ganinka a emergency sashin gaggawa, matarka na cikin halin suma an kasa shawo kan lamarin….,”

Ƙit! Zameer ya kashe wayar can ya ja tsaki ya ce “To ina ruwana? Nina na ɗora mata ciwon ne mace sai laulayi komai ciwo kamar ni zan bata lafiya, mayya kamar dangin tattabara ko soyayyar Layler da majnun ba wata nasara mutuwa ce kema haka za ki yi ni kam ba haukacewar da zan yi”

Shi kansa Zameer bai san mene ya same shi a yanzu ba, haka kurum ya samu kansa da yin faɗa can Khairy ta ce “Ka tashi ka je mana matarka ce fa” a fusace ya ce

“Nikam bana so da gaske bana so ki daina yi mini shisshigi Khairy” Khairiyya ta juya baya tana gwalo sai kuma ta dawo ta marairaice fuskarta fara tas farin da Zameer ke mugun ƙauna ta ce “Matarka ce hakƙinta na kanta…,”

“Zan yafa miki yatsu a fuska Khairy da gaske zan sauke mini hannuna” A hargitse yake gabaɗaya, ya ture kanta ya miƙe domin ko wanka bai samu damar yi ba balle ya tsarkake najasar yana zuwa baƙin ƙofa ya ce.

“Why Khairy me ya sa?” Da rashin fahimta ta ce “Mekenan kake magana?” A hankali ya ce “You, both of you are different, difference sweetness and tasty” kafin Khairy ta yi magana Meer ya fice daga cikin ɗakin. Tunani ta shiga yi mene bambancin me kuma ita da wa, Khairy ta kasa fahimta domin bai bata wata ƙofa da zata hasko abinda yake nufi ba, a hankali ta gyara zamanta jikinta duk ciwo yake mata wannan shi ne karonta na farko.

Zameer na fita ɗakin Ridayya ya shiga ya zauna tare da yin shiru, tunani fal zuciyarsa wanda tunda yake bai taɓa zama ya yi akan Ridayya ba, kenan mata sun bambanta, kamar yar da a kamanni suka kowa da nashi? Me ya sa bai samu yar da yake so a wajan Khairiyya ba? Duk irin jiran rana da lokacin da kuma shirin da ya yi wa ranar, baya ƙaunar baƙar fuskar Ridayya ko kaɗan baƙar mace bata tsarin rayuwarsa hasalima idan yaga baƙar mace zuciyarsa tashi take, shi ya sa bai damu da zama kusa da Ridayya ba ko kallon fuskarta ba, but he lost his mind idan ya raɓeta, sai ya ji shi Allhamdulillah! Ba yar da ya zaci baƙar mace ba. Babban damuwar Zameer a yanzu ko rabin matakin Ridayya Khairiyya bata ɗauka ba a wannan ɓangaren, ya zacci yadda fuskarta ke da haske kamar hasken farin wata ɗan goma sha biyar haka sai samu nutsuwa a wajanta. A hankali ya miƙe tsaye ya shiga safa da marwa can ya ce “Me hakan ke nufi?”

Kyan fuskar na banza ne? Munin shi ne abin so ganin ya gaza sanya ko wanne a mizani ya fice daga cikin gidan a ransa yana ayyana Allah ya sa ya samu nasara a caca ya ciwo miliyan biyun nan.

Duk suna zaune a madaidaicin parlon gidan suna jiran shigowar Baba ƙarami tunda Abban sama baya nan ya je can Rano. Balkisu ta ce “Yanzu babu mai zuwa duba Ridayya a asibiti?” Zuhura ta ja siririn tsaki da zuwanta gidan kenan ta ce “Uwar me za a yi mata? Akan Idanunki ta ci mutuncinmu ta zaɓi mijinta fiye da dangi”

“Yaya Zuhura hannunka baya taɓa ruɓewa ka yanke ka yar, naka shi ne naka jininka wuya za shi, gobarar data kunno a gidan Ridayya muke da ruwan kashe mata ita, dole ace ita jininmu ce dole a ce ita ƙanwarmu ce, ko babu komai akwai hakƙinta akanmu na zumunci….,”

A fusace Amma ta ce “To uwar ƴan farsafa da tsara zance kamar wata marubuciya, daman da ɗan jarida da marubuci gindin ɗaya suke, muddin Ridayya bata ji tausayin kanta ba babu mai jin tausayinta, ni kai na ba kuga me ta yi mini ba?”

A hankali Balkisu ta ce “Ki yi haƙuri Amma, Allah ya kiyaye”

“Na gaba, domin wannan ya riga daya faru Balkisu ki raba kan ki da shiga shara ba shanu, yau ko yayyanka namanta wancan ɗan iskan marainin yaron zai yi ba mai hanawa.”

Bakinsu ta ce “Allah ya rufa asiri, Allah ya sauƙaƙa mata daman bakina kun riga kun yi wa aurenta tun kafin a yi ai” Balkisu na faɗin haka ta ja bakinta ta rufe ta fara danna wayarta.

Duk abinda ake Mami na zaune ita da Zainura ba wanda ya tanka ƙasan zuciyarta ba abinda yake banda zafi. A hankali kowa ya dinga shigowa ɗaya bayan ɗaya, Junaid, Aliyu, Usman, Umar sai Abubakar. Amma da Mami da Yaya Zuhura, Balkisu da Zainura sai Baba ƙarami mahaifin Bilal, baban Ridayya mijin su Amma daman baya gari ya je can asalinsu Rano.

A hankali Baba ƙarami ya kalli kowa can ya ce “Bilal fa?” Aliyu dake zaune ya ce “Banga Ustaz ba yau gabaɗaya” Baba ƙarami ya juya da nufin tambayar Junaid don shi yake ɗan samun kusanci da Bilal kafin ya yi magana Junaid ya ce 

“Banga Ustaz ba Baba ƙarami, ni kam tun jiya idan har akan maganar Ridayya ne ai ina tunanin ba wani meeting ta zaɓi abinda ya kamata da ita ne”

“Yaya Junaid Ridayya yarinya ce gabaɗaya bata rufe sha bakwai ba girma ne ba hankali da ruɗun ƙuruciya, idan mutum na matakin adolescence babu abinda ba zai iya ba, ko wanne bawa da kalar nashi ƙaddarar…,”

“Na bi adolescence da gudu ba wando, zan watsa miki tafi a nan wajan Balkisu, ina cewa gata duk muka je nema mata amma ta shafa wa idanunta kwallin rashin kunya ta baɗa masa ƙasa a idanu, idan na tuna abinda ta yi wa Ustaz kamar na zunduma ihu haka na ke ji ni da kai na kunyar haɗa idanu nake da shi.”

Balkisu ta ce “Ba haka nake nufi ba Yaya Junaid, abinda Ridayya ta yi bata kyauta ba amma ba tsana zamu nuna mata ba, ba zamu guje ta ba, tana buƙatar nutsuwa a kuma jata a jiki, ina cewa kaima akwai naka zanen ƙaddarar saboda matsalar Genotype har yanzu ba ka yi aure ba, duk wacce ka samu da sunan mata ana yin gwaji za a ga Genotype ɗinku bai yi daidai ba” Ganin abin na neman zama wani daban ya sa Baba ƙarami kiran Bilal a waya ya ce yana buƙatar ganinsa cikin gaggawa ya umarci kowa ta shigo.

Sallamar Ustaz ya sa suka kalle shi baƙin wagambari ne a jikinsa, sai wata ƴar ƙaramar riga kamar top da wacce akaiwa aiki a jiki ya ɗora hula akan shi, ɗaya hannun rigar a tattare ga audiga a jiki gabaɗaya ya fi kowa girma a wajan hakan yasa ya yi kwarjini sosai. Kansa a ƙasa yana dafe kai saboda jiri jinin da aka ɗiba a jikinsa yasa jiri ke kwasar shi. Ya nemi waje ya zaune ya harɗe ƙafa da ƙaramin carbi a hannunsa can ya juya ya ce “Sannu Abba, gani” Yana faɗa ya yi shiru.

“Na ganka, Ina ka shiga Ustaz?” Junaid ya ce “Baba ƙarami ba ina Ustaz ya shiga ba, cewa za ka yi me ya sameka Ustaz kalli hannunsa, jininka aka ɗauka?” Shi dai Bilal bai tanka kowa ba a ransa yake jin dole ya ci uban Junaid yaga raini na son shiga tsakaninsu. “To Allahamdulillah, yau zan ƙare magana ƙare kuma amsar ka shi ne zai kawo ƙarshen komai Ustaz muddin ka ce kana son Ridayya zan maka Zameer a kotu ya saketa na aura maka ita, shin da gaske kamar yar da Junaid ya faɗa kana son Ridayya?”

“Shi ne kiran Abba?” Baba ƙarami ya ce “E, bani amsa” Ustaz ya miƙe tsaye ya nufi ƙofa a hankali ya ce “Ridayya ƴata ce, kuma na san babu aure tsakanin uba da ƴarsa” Bai bawa kowa damar magana ba ya fice saboda jirin dake shirin yar da shi a wajan. Yaya Zuhura ta jinjina kai ta ce “Allah ya yi maka gyaɗar duguwa, daman mai ka ci na asham balle ka yi ramakon sallah? Me Ustaz zai yi da Ridayya yarinya duk da lalace ta zama tsohuwa, sai dugun baki da haƙora a waje, ni ɗin nan da nake yayarta na fita kyan gani hatta Amma tafi Ridayya kyan gani fa?”

Balkisu girgiza kai kawai ta yi zuciyarta bata yi mata daɗi, sauran ƴan mazan ba wanda ya tofa tashi a ciki haka Amma. Mami ta kalli Baba ƙarami kanta a ƙasa ta ce “Zan iya tafiya Baba ƙarami?” Baba ƙarami ya ce “Tashi ki je Fatima Allah ya kyauta ya sauwaƙa” Ta miƙe tsaye ta ce “Amma bari na shiga ciki” 

“Mami tun yanzu? To shikenan” Zainura ta miƙe da sauri ta bi bayan babarta, da ƙyar Mami ta kai kanta ɗaki “Mami Yaya Ridayya kar ta mutu” Ta sauke numfashi ta ce “Babu abinda zai sameta, ko wacce kalar mace da kalar ƙalubalan da take fuskanta a gidan aurenta, na yi imani baƙin cikin ɗa namiji ba zai taɓa kawo ƙarshen rayuwar Ridayya ba kamar yar da bai kawo ƙarshena ba, da yawa wasu burinsu kawai su yi aure ba tare da tunanin kalar rayuwar da zasu fuskanta a gidan miji ba, Zainura babu soyayyar har abada fa, da yawa wasu matan haƙurin su yasa ake ganin kamar basu da matsala a gidan aurensu.”

Kwana biyar da yin rigimar asibitin, amma Zameer sau ɗaya ya leƙa shima a gigice cikin dare da buƙatar kai da kai ta kaishi, duk yar da yake son samun nutsuwa da Khairy sai ya ji ba kamar Ridayya ba, baya buƙatar komai a wajan Ridayya sai wannan abun. Tana kwance sai numfashi take da ƙyar kamar daga sama ta ji mutum ya faɗa mata ka, za ta yi ihu ya ce “Kee nine Rayuwarki ne, mai sona”

Numfashi ta sauke tana rufe ido “Ina ka je?”

A taushashe ya ce “Aiki nake domin rufin asirinmu da gujewa raini” Ta yi shiru can ta ce “Kwanaki na kira ka cikin dare na ji surutai da wata murya ana cewa a yi a hankali ban saba ba.”

Dam! Kirjinsa ya buga sai kuma ya ce “Ƴan fashi, wallahi ƴan fashi ne Ridha wuƙaƙe sun fi talatin akai na” Tunda daga sama har ƙasa ta dinga kallonsa ba ta yi magana ba irin kallon da take masa yasa shi faɗin “E, dake na sha maganin tauri ai wuƙa bata yankata da tuni sun kashe ni” Gabanta ya faɗi ita kam aka kashe Zameer bata da wani saurin gata a hankali ta ce “Na ji sai ihu kake kam” Cikin rashin sani ya ce “Ihun daɗi ne”

“Daɗi kuma” Ya haɗe fuska tare da mitsi mitsi da ido ya ce “Bala’in daɗi ma, saboda wuƙa bata shigata kuɗin da kika bani kawai suka kwashe ai” Ganin yana sauya salo ta riƙe hannunsa ta ce “Bani da kuzari, yunwa na ke ji ka bar ni” Zameer ya ƙara haɗe fuska da kyau ya ce “Ridayya na bar ki hakƙin nawa?” Idanunta na zubar da hawaye ta ce “Shi kansa tarayya sai da nutsuwa da cima mai daɗi Meer, bani da nutsuwar hakan ba zan iya ba”

Ya miƙe tsaye ya ce “shikenan ba komai kwanta na haƙura ko zan mutu ban taɓa ki” Tausayinsa ya kamata tasan hakanma soyayya ce ta ce “Bismillah”

Kuka take sosai saboda tsananin azaba kamar ta yi amai, Zameer ko a jikinsa buƙatar maje hajji sallah ya miƙe yana goge zufa sai yanzu yake jin damuwarsa duk ta kau Ridayya bata da wani amfani gare shi bayan wannan. “Tafiya za ka yi ka bar ni?” Ya haɗe fuska ya ce “Ina da uzuri” yana faɗin hakan ya fice ta kifa kanta ta saki wani irin kuka mara sauti. 

Washegari da yamma Baba ƙarami ya zo duba Ridayya ganin ko zama ba ta yi ya sa shi buɗe mata ido tare da kwasarta zuwa gida a cewarsa ba zata koma gidan Zameer ba sai ya gyara halinsa.

Babu wanda ya san Ridayya na gidan ya gargaɗe ta kar ta faɗawa Zameer inda take yana fita daga ɗakin ta masa message ya yi haƙuri ya yafe mata kar ya zo asibiti bata nan tana gidan Baba ƙarami. Sanda saƙon ya isa Zameer na ɗaki Khairy kwance a gefensa tsaki ya ja don tafiyarta bai dame shi ba muddin ba hakƙinsa yake buƙata ba.

Cikin dare Ustaz ya shigo domin ya jima a waje saboda a gobe ne zai koma Lagos har ya shige kitchen ya ji kamar motsi, ya dinga mamakin waye a kitchen kuma cikin dare? Har zai juya sai kuma ya juyo ihu da da kuma ƙarar faɗuwar kwanoka da sauri ya nufi kitchen ɗin domin ganin waye a ciki…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Munafukin Miji 4Munafukin Miji 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×