A kiɗime ta ƙara cewa “ɓarawo, Innalillahi wa’inna ilahir raji’un ɓarawo a ɗakina, Meer rayuwata ɓarawo ya shigo mana” Babu wanda ya amsa Ridayya balle kawo mata ɗauki ta tashi zaune tare jingina da jikin bango, abu goma da ashirin ya haɗe mata. Ƴar raguwar wayar da ta yi mata saura a kadara itama an rabata da ita wai meke shirin faruwa ne.
Daidai ɗaga labulen ɗakinta sa’ar da nepa suka kawo wuta, hasken wutar ya haska fuskar Zameer da yake ɗan mustsike Idanu alamar bacci cikin kulawa ya ce “sama-sama ina bacci na ji ihunki lafiya?” Ya tambaya yana daga tsaye, domin baya jin zai iya zama a ɗakin.
Ridayya ta sauke ajjiyar zuciya ta ce “Kana gidan ashe?” Ya ware Idanu kamar zai yi magana sai kuma ya yi shiru kawai.
“Ina bacci ne ɓarawo ya shigo, ya ɗauke wayata” Zameer fuskarsa shimfiɗe da damuwar daya ƙirƙira a lokacin ya ce “Waya kawai aka ɗauka?” ta jinjina kai alamar “E” Ya ja tsaki a fili ya ce “Shi ne abin ihu a kan ɗaukar waya? Ke dai Ridayya ba ki da tawakkali Kwata-kwata, kece raki idan babu lafiya, kece surutun yunwa kamar za ki yanki naman jikina ki gasa kici, duk abinda na yi miki baya birgeka bana miki gwaninta daman kece kika zubar mini da ƙima da girmana a idanun ƴan’uwanki, ni kam na auri matar ƙaddara!”
“Matar ƙaddara!?”
Ta maimaita a fili idanunta tsaye cur cikin na Zameer domin a ko wanne yanayin a duk halin da zata tsinci kanta bata shayin sanya idanunta a cikin nasa. Muryarta na rawa laɓɓanta na karkarwa saboda ciwon ciki ta ce
“Ni kake kira da matar ƙaddara Rayuwata? Ni Ridayyanka?”
Ya ɗaga kafaɗusa duka biyun yana ƙanƙantar da idanu murya ƙasa ya ce
“Kar ki mini gurguwar fahimta, kar ki mini, ai ba kece ƙaddarar ba, ƴan’uwanki da auren sune, tunda na aureki ban hutawa raina ba, Allah ya ƙara mini haƙuri, shi ya sa magabata suke cewa Allah ya saɓa halayya”
Ikon Allah kawai Ridayya ke kallo ko dai mijin nata wani abu ya sha yau? Bai taɓa mata furuci makamancin wannan ba a hankali ta ce “Don na bar ƴan’uwana baya nufin bana son su ai” Ya riƙe ƙugu ya ce “Ba shakka, idan tururuwa ta so lalacewa, daman fiffike take yi ta tashi ai”
Idanunta suka cika da hawaye fal idan da sabo ta saba da kuka tun a daren amarcinta ta ce, “me ke damunka na rayuwata? Me na yi da zafi har haka? Don Allah ka yi haƙuri ka yafe mini”
Ya ja tsaki yana juyawa. Kasancewar a waje ya yi shimfiɗe tunda ya kammala buƙatarsa da Khairy. Juyi ya dinga yi akan tabarma shi sam ba haka ya tsara gani a auren Ridayya ba, duk abinda yake buri bai samu ba sai masifa kala-kala da auren ya jefa shi.
Ridayya ta share hawayen da yaƙi tsaya mata, tana nan jingine da jikin bango, da tana da ikon tariyo rayuwarta ta baya babu shakka da ta yi hakan domin gyara ƙazantar data aikata wacce babu mamaki warinta ke bibiyarta a yanzu.
“Ƴar baƙata” Ta ji ya kirata jikinta na rawa ta miƙe zani na faɗuwa ɗuwawu a waskace saboda masifar zama waje guda ta zama tsohuwar gaske wacce masifaffiyar wahalar gidan miji ya mai da ita, daman ba kyakkawa ba domin Ridayya ko a kwatance tana cikin mutanen da za a yi kwatance da girman munin halittarsu. Domin saboda wannan yanayin nata zubin halittar ko a makarantar da aure ya datse mata ita Duduwa ake ce mata.
Kamar zata yi masa sujjada haka ta tsuguna a gabansa jikinta na rawar ɗari kar ya taɓa lafiyarta. A hankali ta ji ya ce “Sorry ƴar baƙa, raina ne a ɓace mece waya? Ni da nake saka ran siya miki zuƙeƙiya kalar ya yi, kin san komai na samu naki don ke nake fafutuka da ba ke, da tuni ina Lagos wallahi”
Ta yi shiru ya ce “Ki manta da faɗan ɗazo, zan yi miki swapping na sim ko?” A nutse ta ce, “Allah ya baka iko”
Tunawa da cewa bai tsarkake jikinsa ba ya ce “Ɗan dafa mini ruwan zafi” Ta kalle shi da sauri
“Me za ka yi da ruwan zafi a wannan tsakiyar daren?” Ya haɗe fuska da kyau yana nutsa idanunsa a nata bisa dole ya ce “Wanka, zafi ake yau” Ta dinga kallon shi haka kurum gabanta ya dinga faɗuwa ta ce
“Ba gawayi ai” kai ya bata amsa da “Amma akwai ita ce ko Ridayya?”
Muryarta a sanyaye saboda rashin ƙwarin jiki da yunwa da gajiya da surutun Zameer domin wuta take buƙata.
“Duka manya ne, babu faskararre”
A zuciye yana ɗaga murya ya ce “Kuma Allah bai azurtaki da hannu ba? Bayan rashin fasali har da nakasa ko? Ina cewa akwai gatari a gidan nan, aure ba abin wasa bane dole ki yi bautar gidan miji, da ake cewa Aljanna da wajan miji ai ba banza ba, bauta kawai aka san mace da yi a gidan miji ta yi ta wahalarta masa yana saka mata albarka, idan albarkarce bakya so sai na ji ba’asi”
Miƙewa ta yi a tsakiyar daren ta tattare zaninta shi kuma ya ɗauki wayarsa yana ƙarasa kallon wani blue film yana rufe ƙananun idanunsa. Da ƙyar ta ja itacen zufa na yanko mata haka take ɗaga gatarin tana yin faskaren ana ƙarshe tana ɗagawa ruwan gatarin ya zare ya sauka a yatsan ƙafarta wani ihu da kururuwar azaba, zafi da raɗaɗin daya ratsa jijiyar kanta ya shiga rabawa sauran jijiyoyin jikinta, ƙofofin fatar jikinta ta mimmiƙe wani zazzaɓi mai zafi ya kunno kai ya ratsa jikinta, kuka take majina na fita daga hancinta ga jini na zuba sosai.
“Ke kam an yi raguwa kamar ba mace ba? Ba har haihuwa mata na yi ba kuma su jure gabaɗaya ruwan gatarin nawa yake?”
Bata gane saboda ji take kamar ranta za a zare ya haska yatsan da wayarsa yaga farcen saura kaɗan ya cire, ya ware ido ya ce
“Tab, ɗan wannan abin?”
Kafin ta farga ya saka hannu ya fisge sauran farcen bata ƙara sanin meke faruwa ba sai da ta ji ana zuba mata ruwa ta sauke ajjiyar zuciya, lokacin ko kuka ta kasa sai jan numfashi ya ce
“Ai suma kikai wai? Ke komai na suma ne kamar mai cutar suma?” Ta cure waje ɗaya saboda bata ƙaunar tsawa sam ya ce
“To ɗoran ruwan tunda Allah ya nufa ba ki shige ƙiyama ba” bata iya cewa komai ba ta ɗora ruwan har ya yi zafi ta juye masa. Lokacin yatsar har ya kumbura.
Cikin bacci ta ji ya ce “Ridayya ke Ridayya” Yana saka ƙafa tare zungurin gutaccen kwankwasonta ta farka a firgice tana “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un don ka yi haƙuri zan dafa ruwan yanzu wallahi zan dafa” Takaici ya cika Zameer ya ce “Au ke nan har mafarkina kike? Saboda ga mugu azzalumi yaushe muka fara haka dake ina soyayyar tawa Ridayya ina zaluntarki ne?” Ta girgiza kai ta ce “A’a mafarki ne kawai da rayuwata” Ya sauke numfashi ya ce “Firfita za ki yi mini har na yi bacci zafi ya addabe ni”
Matsawa ta yi inda ya kwanta ta fara masa firfita bacci na ɗaukarta idan ta yi kamar zata kifa sai ya zunguro ta iska na busa shi a haka har ya yi bacci tana zaune.
Washegari Zameer ya shirya tsaf cikin wata shadda ash ta amshi jikinsa ya fito yana banza ƙamshi tare da murza hula, hannunsa zube cikin aljihu. Ridayya dake tsaye ta ce “Fita za ka yi?” Kai kawai ya jinjina mata bai ma kalleta ba a hankali ta ce “Babu ko hamsin ce na jiƙa kwaki?” Yana yin gaba ya ce “Sai dai ki jiƙani Ridha, neman kuɗi zan fita”, ta ce “Allah ya tsare ya bada sa a, sharrin mutum da Aljan Ubangiji ya kare ya baka halak Ubangiji ya rabaka da haramun mijina” Bai amsa ba ta ce,
“Don Allah kar ka kalli ko wacce ƴa mace ina jin kishinka har ƙasan zuciyata ina tsananin so da ƙaunarka Rayuwata” Zameer shi dariya ma ta bashi mace duk a jeme wai kar ya kalli kowa? Ya saka kai ya fice abinsa.
Kai tsaye wajan cacarsu ya nufa, yana tafiya ɗaiɗai duk ya samu team ɗinsu suna zaune A.y ya ce “Ango mijin Ridayya bada kanka a sare ka je gida kace ya faɗi, wuya ina wuya a gidan Ridayya daɗi a ina daɗi a gidan Ridayya ɗan’gatan Ridayya farin cikin Ridayya shalelen Ridayya kuma rayuwar Ridayya”
“Zan ci ubanka zan ci mutuncin ka A.y” A.y ya sheƙe da dariya sosai ya ce “Amma fa mutuina kaci uwar shadda dole mata su yi crushing a kan ka yarinya ta mace kana da kyau da zubin nagarta sai dai kai shaiɗanin ɓoye ne”
Zameer ya fara jan ajinsa da haɗe fuska. Gaza dake jinsu ya ce
“Zameer akwai caca mai kyau ƙila kana da rabo” Zameer ya ware idanu yana jiran ƙarin bayani, Gaza ya ce “kuɗaɗe ne za a samu wanda mutum da talauci sun yi hannun riga, a ƙalla ba a samu kuɗi ba shi ne miliyan 500 kai fima, mu ma duk mun shiga cacar babbar harka ce” Zameer ya ce “Kai me ka saka naka?” Gaza ya ce “Motata” Zameer ya ce “Na saka gidana” Duk suka zare ido suka ce “A’a banda gida ne idan aka cinyeka ina zaka saka Ridayya ɗin?” Ya ƙanƙance ido ya ce “Babu ruwanku da inda zan saka matata ni dai na shiga caca kuma na saka gidana” gabaɗaya suka amince Zameer ya ji cewa tabbas a wannan karan mafarkinsa zai cika akan nasarar caca.
“Wai yau wasan Barcelona da Real Madrid” A.y ya ce “Wacce match?” Gaza ya bashi amsa da “Afcon 2024”
Zameer ya ce “Madrid ne ma za su ci, su Barcelona uwar me suka iya?” Gaza ya ce “A’a fa, wallahi Barcelona za su ci wasan bana fatan gidan madara su ɗauki cup” Zameer ya zaro waya daga aljihu ya ce “Na saka wannan wayar idan Barcelona suka ci ka riƙe” Ya dinga juya wayar domin yasan ba wayar Zameer bace.
“Na saka Dubu hamsin”
Hira sukai sama-sama domin dukkansu zaman banza suke babu mai aiki arziƙi, sun fi ƙarfin aikin ƙarfi saboda sun yi degree aikin office suke jira sun ce amfanin karatun kenan. Daga nan Zameer gidansu ya shige.
Lagos
A hankali yake danna system ɗin gabansa lokaci zuwa lokaci yake ƙara danna number Ridayya amma sai ya ji baya going, ya ajjiye wayar yana sauke numfashi. Daga bakin ƙofa aka yi knocking Ustaz ya dinga kallon ƙofar haka kurum ya ji baya buƙatar ganin kowa jin knocking ya yi yawa a hankali ya ce
“Uhm” Buɗe ƙofar akai tare da shigowa. “Assalamu alaika Ustaz Bilal” Ustaz ya ɗan ware Idanu sai kawai ya jinjina kai, laɓɓansa da suka motsa ya bada tabbacin ya amsa. Nasir ya ce
“Ai tunda na shigo nake tambayar Md aka ce baka samu damar zuwa ba, ina can ɓangaren customers care naga shigowarka ta baya, fatan ka zo lafiya Ustaz” Ustaz bai ko tari ba Nasir ya ce “Yaushe ka shigo Lagos ne? Har hutunka ya ƙare?”
“Nasir” Ustaz ya kira kamar baya son magana, Nasir ya yi dariya ya ce “Da alama yau kaɗaici kake ji ka yi aure kaƙi ƙaton gauro babu mai aurenka yanzu ai”
Ustaz da idanu ya bi Nasir idan suna maganar aure mamaki suke bashi suna ɗaukar kalma kamar wasa, bayan yana da kyau kafin namiji ya yi aure ya tsaya ya yi karatu guda akan sanin ma’anar aure da haƙƙoƙin auren, amma daga maza har mata auren kawai ake domin nishaɗi da magance abinda suke kwaɗayi. Nasir zai sake magana Ustaz ya lumshe fararen idanunsa wanda suke ɗauke da dugwayen gashi sukai kwance luf saman matar idon cikin muryarsa ta ustazanci ya ce “Ya isa, ya isa Nasir”
Nasir ya kwashe da dariya ya ce “Yanzu zaka fara Asstagafirullah, Hasbunallahu kamar an yi kalmar ɓatsa ustazan nan kuna yin abu kamar baku san komai ba, bayan kun fi kowa iya shege a gidan aure” Ustaz Bilal ya juya tare da ɗaukan gwangwanin Malt ya cillawa Nasir, da sauri ya miƙe yana cafe gwangwanin ya ce
“Ohho dai nasan kai ba waliyi bane” Ganin Ustaz ya miƙe yasa Nasir ya kwasa da gudu ya yi waje, girgiza kai kawai Ustaz ya yi yana zama saman kujerar dake office ɗinsa.
Wayarsa ta fara ringing ganin sunan Abban sama mahaifin Ridayya ya sa ya ɗauka ya ce “Baffa”
Ya yi shiru can ya numfasa ya ce “Allah ya sauwaƙe ku je kawai ban jin zuwa Rano”
Yana faɗin haka ya kashe wayar idanunsa ya lumshe a hankali ya shafa ƙirjinsa dake harbawa ya miƙe ya shiga zagaye office ɗin ya ƙara komawa ya zauna a taushashe ya ce
“Ustaza” Da sauri ya ce
“Asstagafirullah!”
Baffa ne ke kaiwa yana dawowa sai sura masifa yake Mami kan ta a ƙasa Amma ke bashi haƙuri Junaid dai bai tanka ba. Ya ce “A zuri’a ta jinina har na haifi ƴar da zata nuna tafi ƙarfinmu? Wallahi ba a haifeta ba idan har ni uban Ridayya ne kuma ta haifu wallahi tallahi sai na raba aurensu da yaron nan gwara ta zauna a gabana har ta mutu babu aure” ya juya kan Mami ya ce “Babu shasha wacce bata san darajar ƴarta ba irinki Mami, ni ba haka na tashi naga ko wacce uwa na yi ba, amma kin zuba idanu ba ki da wata asara ko gawarta za a kawo miki sbd ba ki san wahalar rainonta ba” Mami kanta a ƙasa Zainura sai kuka take ganin yar da ake wa babarta faɗa kamar za a dake ta. Baba ƙarami ya ce “Saurara Bawan Allah Fatima bata da wani laifi, a haka kuka ɗora ta tun zuwan Ridayya duniya,kuma da kake hayaƙin baki a kan taƙi ɗaukan mataki daman hakƙinka ne kwatarwa Auta ƴanci”
Baffa ya ce “To wallahi idan har ina raye sai na kashe auren Ridayya” Ya ɗauki waya ya shiga kiran layin Ridayya ba jimawa aka ɗauka Zameer ya ce “Barka da yamma Baffa”
“Ina ƴata? Ka ce ina buƙatar ganinta yanzu yanzu a gida” Zameer ya ce bari na bata wayar ya cire wayar daga kunnensa ya fara cewa “Wife… Wife sweetheart Baffa yana kira” ya ɗauki seconds kafin ya mayar da wayar kunne ya ce
“Baffa wai bata buƙatar magana daku, ta haƙura daku kuma ta yi nisa daku kamar yar da ta yi muku alƙawari” Wani tari ya turnuƙe Baffa da sauri Mami ta ɗauki ruwa ta bashi ya girgiza kai yana ture hannunta ya ce
“Ni mahaifinta? Ni Ridayya take faɗawa haka ashe girman haukanta ya kai haka?” Idanuna ya sauya Baba ƙarami ya ce “A kul ka zubar da hawaye saboda ita, idan ka yi hakan to ka bata lasisin ƙara lalacewa ka yi addu’a sharrin soyayyar zamani ne kawai” Ya jinjina kai ya ce “Ku shirya gabaɗaya a yau ɗin nan zamu tafi Rano duba Hajiya Junaid harku gabaɗaya ku shirya a faɗawa Balkisu, Zuhura Ustaz ya ce zai bimu daga can Lagos ɗin zamu bar wa Ridayya garin na wasu lokaci. Nan da suka fara shirin tafiya Rano a gaggauce gabaɗaya familyn banda Ridayya da Ustaz.
Mami kuka take sosai ta cikin waya ta ce “Haba Yaya A’isha ya ake so na yi, ni da Ridayya bamu da wata shaƙuwa ina buƙatar ƴata ina buƙatar tattaunawa da ita”
“Ki je gidan nata kafin ku shige Ranon” Tana kuka ta ce “Baffa ba zai barni ba, ya ɗauki zafi ban san me mijin Ridayya ya faɗawa masa ba”
Yaya A’isha ta ce “Fatima tun farko kin yi sake a yanzu kuma kafin ki gyara kuskurenki abu ne mai wahala raina ɓaci yake idan na zo gidanki amma ni zani gidan Ridayya ɗin ki kwantar da hankalinki” Mami ta ce
“Idan har ban mutu saboda baƙin ciki ɗa namiji ba, to tabbas Ridayya ba zata mutu ba, hakƙina akan ubanta ke bibiyar tata rayuwar ina mata fatan alheri a rayuwarta Ubangiji ya kawo mata sassauci”
Ridayya kamar an tsikare ta haka ta miƙe tana saka hijabi Zameer ya kalleta ya ce “Ina za ki”
Kai tsaye ta ce “Wajan Mami ina buƙatar ƙarin haske ina son ta fahimtar dani abinda na gaza fahimta”
Ya dinga kallonta mamaki ya cika shi jin yau ta ce Mami ba Amma ba, ya ce “Tab, Baffa ya dawo na je gaishe shi ba, amma ba kiga korar karen da ya yi mini ba, cin mutunci ta uwa ta uba kuma ya ce ko da wasa ya ganki a gidansa wallahi sai ya tsine miki” Zaman ƴan’bori Ridayya ta yi kanta ya kulle ta rasa wanne irin hali take ciki ne? Tana buƙatar zama a fayyace mata ma’anar so da ƙauna, so da birgewa da kuma soyayya ta gaskiya tana buƙatar ta fahimci mene take na kuskure. Kuka ta rushe da shi kamar ta yi hauka “Na shiga uku Baffa don Allah kar ka tsine mini zan dawo gare ku wayyo Allah na” Ficewa ya yi.
Zainaba ta shigo da kwanon abinci ta ce “Ridayya don Allah don girma ki bani tarihinki wacece ke? Ki bani labarin rayuwarki da aurenki da Zameer don Allah kullum da kwaɗayin jin hakan nake kwana” Cikin kuka Ridayya ta ce “Babu komai a rayuwata sai tarin baƙin ciki da takaici sai baƙin cikin labarina ya haddasa miki ciwon zuciya ku yi mini uzuri a duk abinda na aikata wallahi ina cikin hankalina ko a mafarki bana ƙaunar tuna rayuwata ta baya” Kuka itama Zainaba take sosai ta ce “Wallahi ina tausaya miki ina jin tausayinki kayan haushinki da takaicinki ke mini yawa yana danne tausayin ji nake kamar na jaki na lakaɗa miki mugun duka wallahi, don Allah ki bani labarinki” Ridayya ta ce “Zan ba ki amma gobe da alƙawarin za ki riƙe mini sirrina” Zainaba cike da gulma da son jin zance ta ce “Kin yi alƙawari? Gobe da yaushe kuma kyan alkawari cikawa” Ridayya ta jinjina kai, a yanzu burinta bai shige ganin Mami da Baffa tana jin ko za a kasheta gobe sai ta je gida sun gana da Mami.
Tunda suka ɗauki hanyar Rano babu mai magana a babbar mota suke ciki gabaɗaya family guda ɗin, daga Kano zuwa Rano tafiyar 1 hr 18 min (68.7 km) ce kuma cikin dare suka tashi, a karo na farko Baffa ya ji wani matsanancin tausayin ƴarsa zuciyarsa ta shiga zullumi da zarar ya dawo zai dawo mata da duk abinda ta rasa a rayuwa. Junaid dake driving ya ce “Ustaz fa ba za shi wata Rano ba Baffa dabara kawai ya yi maka” Yaya Zuhura ta ce “Kai kam Junaid ka sakawa Ustaz idanu kamar wani sa’anka” Gabaɗaya cikin motar suka saka dariya banda Mami da Baffa Zainura na jikin Mami idanunta, Junaid ya shiga duba lokaci a wayarsa ɗaguwar da zai yi yaga wata ƙatuwar tirela tayo kan motarsu gadan-gadan tirelar na ƙoƙarin kaucewa motar su Baffa na ƙoƙarin kaucewa a ƙoƙarin Junaid na tsayar da motar a tsakiyar titi, gabaɗaya ya danne giyar motar kai tsaye ta yi ƙarƙashin tirelar Innalillahi wa’inna ilahir raji’un! Gabaɗaya tirelar ta bi ta kan motar ta danne jama’ar ciki baka jin komai sai salatin da jama’ar motar ke yi wasu na ihu a hankali aka daina jin motsin kowa sanda tirelar ta mirgina ta ƙarasa danne kan motar su Baffa….
Don Allah idan kun karanta a yi sharing please saboda masu nema a kuma yi comment kar ku manta free book ne.