Tuƙi yake a hankali kamar baya son yi a bakin wani tangamemen gida ya tsaya horn ya yi gate man ne ya leƙo ganin motar yasa ya koma ciki ya buɗe gate ɗin shiga ciki yayi tare da yin parking zaman sa yayi a cikin motar bai fito ba ya ɗauki gurin minti talatin a ciki sannan ya fito tsayawa yayi kana ganin shi kaga ƙarfaffan mutum da motsa jiki ya ratsa shi {Giant} ƙare wa compound ɗin gidan kallo ƙaton gida ne dan daga ciki yafi girma Part-Part ne gurin guda Shabiyar daga can gefe garden ne mai. . .
