Kirifto
1.
Assalamu Alaikum jama’a
Da fari da sunan mai sama
Al-Hadi Kai ne mai duka
Ka iya mana sarki Rabbana
Ka tsare mu sharrin aringizo.
2.
Gaisuwa mai tarin yawa
A wurin Habibu mai mu’ujiza
Annabi mai Makka da Madina
Shi ne gatan duka duniya
Manzonmu da babu kamarsa
3.
Dukiya ita ce jinin rayuwa
Da ita ake sarrafa duniya
Gwal ne ko kuma azurfa
Tagulla ce ko zubarjadi
Da Duk duwatsun alfarma.
4.
Ga dabbobi nan iri-iri
Harkar noma ce ga ta
Ko cinikayyar kayan sawa
Gona, gida ko filaye
Hannun jari ga masu da shi.
5.
Ƙarafan hawa dai ga su
Kayan amfanin yau da kullum
Kayan asibiti da na shago
Cinikayyar kayan karatu
Abubuwan dai ga su birjik.
6.
Hanyoyin samun kuɗi
Kamar duniya suna da faɗi
Akwai na haram da halali
Wani sai an nuna jan hali
Wani sai an yi fito-na-fito.
7.
Kwatsam kuma sai ga sabo
Al’amari sabo ya fito
Shi ne na haƙar Kirifto
Idan ka haƙa har ta fashe
Tabbas baki za ya washe.
8.
Idan ta maƙale kai ta zuru
Idanu su yi zuru-zuru
Ana ta jiran gawon shanu
Ana ta jiran shan man shanu
Wataƙila, ta hana bature ƙarya.
9.
Da yake haƙar ana samu
Wasu miliyoyi suke samu
Cus fa! Haka kuɗi ake samu
Sai dai mai rabo ke samu
Maras rabo yai ta jira.
10.
Wasu da yawa sun bar aikinsu
Wasu ko sun saki sana’arsu
Wasu sun bar aikin hannunsu
Sun ɗauki haƙar sana’arsu
Ita suka riƙe dare da rana.
11.
Abin na da ban mamaki
Kana zaune cikin ɗaki
Latsawa ce kawai aikin
Idan ta fashe kamar tafki
Kuɗaɗe sui ta shigowa.
12.
Lallai wannan ci gaba ne
Hanyar samun na kai ne
Kuma sauyin zamani ne
Za a rage talauci ne
Mutane za su samu sauƙi.
13.
Sai dai lamarin da jumurɗa
Malamai su na ta ja-in-ja
Wasu Kirifton sun ka haramta
Wasu shi ɗin su ka halasta
Wasu kuma suka ce la ba’asa.
14.
Daga cikin masu yin nazari
Sun ce a guji wani yanayi
Da za a ke samu a huce
Domin yana kashe zuciya
Da dakushe dukkan karsashi.
15.
To ni dai a ra’ayina
Kirifto dai ci gaba ne
Don haka zan yi abina
Ko da zan samu kaɗan ne
Na dai huce wa haushina.
16.
Aikin da nake yi na rubutu
Da aikin nazari da karatu
Na alƙalami da muryata
A tunanina da ƙwaƙwalwata
Su ma ba za na saki ba.
17.
Allahu ka sa mu amfana
Da ci gaban da ya zo mana
Wahalar mu ta yau ta zam hira
A wayi gari ba ma ƙara
Sai godiya da hamdala.
18.
Kiriftawa a dai yi hattara
Komai kafin yi a tsattsara
Wanda ba sa yi su fara
Allahu ya kiyaye hasara
Ya Zuljalalu Ya ba da sa’a.