Skip to content
Part 3 of 4 in the Series Muryar Dalili by Haiman Raees

Basimpe

 

1.

Basimpe ba shi daraja

A idon mafi yawan mata

Basimpe ba shi da kima

A wajen mafi yawan mata

Basimpe saurayin Dija

Na Asabe ne ko Karima?

2.

Kai kenan ba ka da zuciya

Kullum aikin ka tarairaya

Ka zamo raƙumi da akala

Yi nan yi can kamar gaula

Soyayya wai ka ke wa maula

An dai yi asarar ragon suna.

3.

Shahrukh Khan sarkin soyayya

Gudaliyar ake yi wa biyayya

Sai ke ce ba ka da zuciya

Da an yi magana sai hauragiya

Da ta ce uhm! To sai ‘to iya!’

Amma an yi zuciya jemammiya.

4.

Shi dai barshi riƙe da fatala

Ya yarda ya zamo mata fitila

Ya haska wata shi ya mutu

Yi nan yi can babu hutu

Bai san ciwon kai nai ba

Jaki ɗauke da tarin gafaƙai.

5.

Yo wai hauka wai ake yi?

Ba ni da wani aiki sai aike

Sai ‘yar wuya kamar rake

Ta samu rayuwa ta shaƙe

Can gare ta ka wani naniƙe

Kai! Da ma fa ka miƙe.

6.

Kaiconka kai dai Basimpe

Ganyen gwaza uban ladabi

Da ya ga doguwa ya lafe

Yar fara mai dogon hanci

Ya zura mata ido, madubi!

Maye kamar zai lashe

Zuciya ta bi ta bushe.

7.

Kai ma ka zamo mai aji

Ka da ai ta janka kamar carbi

Ka zamo shugaba ko a ina

In ka faɗa dole a ji

In za ka yi abu, bugi ƙirji

Domin yi wa Simpanci biji-biji.

8.

Alfawa duk sai mu miƙe

Mu yi yaƙi da Simpanci

Domin kare kai da wulaƙanci

Da nisanta kai da shashanci

Mu rufe ƙofar duk iskanci

Ko ma zamo masu mutunci.

 

<< Muryar Dalili 2Muryar Dalili 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×