Daga inda nake laɓe ina kallon danbarwar da ke faruwa tsakanin babana da matarsa wadda take cika tana batsewa tare da tsalle ta dire kan sai dai uban nawa yasan inda zai kai ni amma ba ta riƙe ni.
Ya share zufar da ke keto mishi da tsohuwar malum malum ɗin da ke jikinsa, ya ce “Yanzu dai ki bari zuwa sati ɗaya zan mayar da ita can Kaduna wurin abokan arziƙi da muka zauna tare za su yi min arziƙi su riƙe min Mai gadon Zinare.”
Ta balla wa inda yake tsaye harara ta ja tsaki ta shige ɗakinta tana ci-gaba da sababi “Ba uwarta na raye ba? Don kilibibi ka bar mata yarta mana, sai ni ce da ban san me nake ba za a bar ni da wahala.
Babana daga inda yake bai juyo ba gidan ya bari, bai shigo ba sai da na yi barci.
Daga inda na makure a saman shimfiɗata saboda yanayin sanyi da ake, na ji ana bubbuga ni ban da magagin barci nan da nan na buɗe ido babana na gani zaune gefen shimfiɗar na tashi zaune ina duban shi kwanan abincin shi ya nuna min “Za ki ƙara Mai gadon zinari? Na dubi kwanon abincin sai na ɗaga kai ya turo shi gabana ya tashi ya fita.
Na ɗauko kwanon don daga rana har dare ban ƙoshi ba, nan dai na lamushe ina zare ido na fita da kwanon na sha ruwa na ji cikina dam na zo na kwanta.
Kwanakin da suka biyo baya kafin sati ɗayan da babana ya ɗauka zai kai ni Kaduna ba ƙaramar gallazawa daga ni har baban nawa muka fuskanta daga matar tashi ba.
Ranar da za mu tafi na ɗauko kayana cikin jakar da ya sawo min ya shirya min kaya ya amsa ya riƙe, daga inda matar babana Innakeso ke zaune gindin murhu ta ce “A sauka da nauyi. Allah ya kai kaya masauki.”
Na bi bayan babana za mu fice dattijuwar ta shigo cikin gidan bakinta ɗauke da sallama, cikin girmamawa babana ya shiga mata sannu da zuwa.
Ta kamo ni “Ƙawata, sai ina da safen nan? Babana ya dubi inda Innakeso take “Kaduna zan kai ta.”
“Kaduna kuma wurin wa? Ta faɗi cikin mamaki “Wurin mutanen arziƙi da na zauna da su.”
Ta ce “Ka kai ta saboda wane dalili? An yi hutun makaranta ne? Ya girgiza kai “Gaje ta ce ba za ta riƙe min ita ba.”
Nan ma salatin ta ƙara “Shi kenan da ka kai ta duniya ba dangin iya ba na baba, ni ka ba ni ita, na san halin Gaje sarai tunda ta ce ba ta riƙewa ko na ce ta riƙen ba ruƙon arziƙi za ta yi mata ba.
Ɗa na kowa ne, za ki bi ni mai gado? Da sauri na ɗaga kai ta miƙa wa babana hannu ya ba ta kayana ta juya Innakeso ta taso “To ya za ki juya Iya ba ki shigo ba? Kai ta girgiza “Ba sai na shigo ba. Mai gadon zinari zo mu tafi.”
Na bi ta a baya babana ma ya biyo mu, kuɗaɗe ya miƙo min ya ce idan mun isa in ba Iya sanin ko ya ba ta ba za ta karɓa ba.
Mashin muka hau zuwa Funa gelle inda gidan su Iya yake gida ne na yawa kuma gidan gado ne ita da abokan haihuwarta, duk yayyanta ne da ƙannenta.
Ita kaɗai ce a wurin ta, ɗaki ɗaya ne da ita ƙaton gaske sai banɗaki da ta yi a gefen ɗakin.
Muna zama abinci ta ɗora muka ci muka ƙoshi ta sanya ruwa mai zafi ta yi min wanka wanda tunda ruƙona ya dawo hannun Innakeso ni ke ma kaina wanka, ta sanya na wanke haƙorana tana tsaye.
Da daddare muka kwanta tare ina bayanta.
Da safe duk yaran gidan sun tafi makaranta, Iya ta tafi gona kala,matan gidan suka yi ta maganar ta, haka kawai don ja ma kai ba dangin iya babu na baba ki kimkimo yarinya ita ɗiyar taki ma da take auren ubanta ta ce ba ta iyawa.
Yawan maganar ta su da kuma idan na dube su sai in ga kamar suna harara ta ya sa na fita gidan, ba kuma wanda ya ce in dawo.
Wani kango da ke jikin gidan na shiga na zauna har Iya ta dawo wadda hankalinta ya tashi da ba ta gan ni ba.
Kullum idan ta tafi kangon nan nake shigewa har ta dawo, sannu a hankali kuma na fara bin ta gonar ina taya ta ayyukan da take, saboda idan na zauna gidan ban jin daɗin yadda matan gidan ke kyara ta da hantara.
Na ce ma Iya ta sanya ni makaranta ta ce sai ta tara kuɗi sai ta sanya ni irin wadda yaran gidan ke zuwa, ta dai sanya ni Islamiyya ina tafiya tare da yaran gidan, idan mun dawo gona.
Har sai da term ya ƙare aka koma hutu sannan Iya ta samu ta kai ni makaranta, ƙwaƙwalwata a buɗe take ga shi kuma ina son karatun don haka tsaf nake kwashe duk abin da aka koya mana, ba su rage min aji ba aji biyu na suka sa ni don shekaruna takwas ne a lokacin.
Tsakanina da Innakeso sai kallo idan ta zo wurin Iya.
Babana na yawan kewayowa ya duba ni.
****
Rayuwata ta cigaba a hannun Iya wadda a kullum burin ta ta inganta min ita.
Da na gama primary ta sanya ni na ci-gaba da Secondary ta gwamnati har shekaruna suka kai sha biyar lokacin na zama budurwa har kuma sannan sau ɗaya mamana ta zo duba ni daga Taraba. Zuwan nata masifa ta yi ta wai a rasa me riƙe ni don wulaƙanci sai uwar kishiyarta.
Tunda ta tafi ban kuma jin ɗuriyarta ba, sai kuma daga bayan nan ta fara haihuwa yaranta biyu.
A Kaduna gidan hayar da babana ya zauna shi da mamana sun zauna kamar yan’uwa don haka har yau zan ce babana yana zumunci da su. Za a aurar da yarinyar ɗaya mai suna Ummi, da suka gaya wa babana bikin suka roƙe shi idan zai zo ya zo da ni, hakan aka yi da ni ɗin ya tafi.
Mun sauka Kaduna garin Gwamna yamma liƙis.
Ba ƙaramar maraba aka yi min a gidan ba bayan amarya Ummi akwai wasu yammatan biyu Maryam da Halimatu nan da nan suka ja ni cikin su, duk da sun girme min.
Kwanan mu biyu da zuwa aka ɗaura aure. Tun ranar babana ya so wucewa aka hana shi suka ce ya bari idan Allah ya tashe mu lafiya sai ya yi sammako.
Sai dai gidan dan’uwan shi ya tafi da ya ce in zo mu je dadin biki ya ɗauke ni ban bi shi ba.
Ana ta ragargaza kiɗa a ƙofar gida ina cikin ɗakin yammatan gidan zaune ina ƙara gyara kwalliyata.
Halimatu ta shigo akwai wasu yammatan a ciki sai ta yo wurina “Don Allah Bilkisu ki zo mu je mu yi rawa.” Na ɓata fuska “Allah ni ban iya rawa ba.”
“To ki zo dai mu je.” Ta faɗi tana janyo ni, dole na miƙe muka fita farar atamfa ce jikina da ta yi matuƙar amsa ta ɗinkin doguwar riga, iya ta dinka min ita musamman saboda zuwa bikin, babana ma ya yi min kala biyu.
Da farko tsayuwa na yi ina kallon masu shan rawa sai da Halimatu ta mamaye ni sai ta tura ni ciki,tafiya kawai nake don ban iya rawar ba.
Wani yaro ya zo ya tsaya kusa da ni “Ana kiran ki.” Na ce “Wa ke kira na? Da hannunsa ya nuna min “Wani saurayi ne kan mashin kin gan shi can.”
Na ce “Ina zuwa.”
Duk da ban ga kowa ba saboda cikowar wurin,ina ganin ya wuce na ci-gaba da tafiyata cikin masu rawa.
Ba a jima ba wata yarinya ta zo ita ma ƙara jaddada min ana kira na ta yi, sai dai ita ba ta yarda na yi mata yadda na yi wa yaron ba, ja ta yi ta tsaya kan kawunta ne ke kira na kuma ya ce dukan ta zai yi idan ba ta zo tare da ni ba.
Tausayin da ta ba ni ya sa ni bin bayanta har ɗan nesa da inda ake kiɗan kamar yadda yaron ya ce wani saurayi ne kan mashin ɗin zamani ta yan ƙwalisar samari ya sha shirt da wando, wandon crezy ne ya kulle ƙafarsa cikin farin Boot kamar yadda rigar take fara, kan shi sumarsa ta sha daada an gyara ta sai ƙyalli take.
Tagumi kawai na yi saboda yanayin dressing ɗinsa, maganganu ya fara min na tsari da sace zuciya, ga wani kallo da yake min wanda ya tilasta ni sunkuyar da kai na.
Mun daɗe sosai da shi yana kashe ni da tausasan kalamai na sace zuciya, kuma ba ƙarya ya iya soyayya, sai da Halimatu ta zo ya bar ni na tafi.
Suka haɗu ita da Maryam suna faɗin Aminu kika samu lallai za ki sha soyayya, ga gayu mata na son shi don ɗan ƙwalisa ne. Na ce “Ku ina kuka san shi?
Suka ce gidan da ke jikin nasu na iyayen shi ne kafin maman shi ta tashi.
Ana kai amarya gidanta sai ga Aminu ya aiko aka kira ni, nan ma tsare ni ya yi da kalamansa irin yadda ya kamu da so na daga kallo ɗaya. Bai tafi ba sai da ya sa zuciyata ta kamu, har kuma aka ƙare bikin kullum sai ya zo cikin matuƙar gayun da ke ƙara sace min zuciya.
Na jima a Kaduna, sai da na shafe wata guda cif babana ya ce in dawo hakanan. Sam ban san barin garin saboda sabon da na yi da mutanen arziƙin, muhimmi kuma son da ya kama ni mai tsanani na Aminu.
Na koma gida Iya ta lura da sabon canji a tattare da ni na waya kullum da Aminu, ta tambaye ni na faɗa mata har ma na nuna mata hotunan shi da ke cikin wayata da wani saurayina Alhassan ya ba ni.
Kama baki ta yi “Anya mai gadon zinari wannan gashi haka da ya kama ya mummurɗe ga wando duk a yayyage?
Yar dariya na yi “Ka ji Iya gayun kenan, wandon kuma ba yagewa ya yi ba haka yake.”
Ta taɓe baki “Ni dai da za ki ji tawa da kin auri Alhassan abin ki, duk garin nan ba wanda bai san mahaifinsa ba in bai zo na daya a manyan manoma ba zai zama na biyu, ya’yansa masu tarbiyya ne da abin yi.”
Na zumɓuri baki na tashi na shige ɗaki.
Ko da babana ya zo Iya ta yi mishi magana yabon mahaifin Aminu ya yi ta yi ya ce mutumin kirki ne kafin Allah ya yi mishi rasuwa. Dole Iya ta hakura gane abin da nake so shi babana ke so.
Sai da na yi watanni biyar da dawowa Aminu ya zo ya yi kwana biyu.
Magabatansa sun zo an yi maganar aure har aka sanya rana.
Babana ya aika wa mamana da zancen aurena amma ba ta zo ba sai ana saura kwana uku biki ita da yan’uwanta.
Washegari kuma Aminu ya iso da yan’uwansa mata biyu maza biyu sai abokansa masu tarin yawa.
Mamana ta tsaya kai da fata ta ce sai an je an yi gwaji don ana ta binciken ta ji an ce yana bin yammata, haka dai rayuka suka jagule da wannan zance nata gatsau, dole kuma aka fasa daurin auren safe da aka sanya muka nufi asibiti.
Maryam litee