Skip to content
Part 16 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Ban kira Babana ba mamana na kira ina kuka amma ta ƙi ɗaga kirana, don fushi take da ni tunda Aminu ya kira ta ya zazzage ni ta ce in baro mishi gidan shi tunda ba ta da mutunci a idonsa ya kira ta yana antaya min zagi.

Na kira Babana na faɗa mishi abin da ta ce ya ce in rabu da ita in yi haƙuri in zauna ɗakina.
Tun daga nan ko na kira ta sai ta ƙi ɗauka.
Na kira Babana wanda zuwa yanzu ya ce da ya ga kira na gaban shi faɗuwa yake na faɗa mishi ya ce “Jarabawa ce mai gadon zinare mu yi ƙoƙari mu ci, ki ƙyale shi ki yi haƙuri ki zauna a dakinki shi ne marufar asirin ki.”

Na ce “To Baba.”

Saboda babana na kawar da kai daga duk wani abu da zai haɗa mu.

A haka muka ƙara wata guda sai dai tsautsayi da bai wuce ranar sa, ranar mun tafi unguwa da matan yayyensa har da Mamansa yamma ta yi muka dawo da ma ni hankalina bai kwanta da rashewar da suka yi ba ga shi ban san hanya ba ballantana in dawo ni kaɗai
sai cewa nake su tashi mu tafi.

Muna isowa ƙofar gidanmu na gan shi tsaye ya rungume hannuwa a ƙirji na dafe kirji na ce

“Na shiga uku!

Gabaɗaya suka kwashe da dariya har Maman shi, ita ce ma ta ce “Wai Bilkisu yau kin tare su!
Na ce direban ya tsaya na sauka ya wuce da su na raɓa ta gefen shi na shiga gidan tun kafin in karasa shigewa ya fara zunduma min zagi na ce “Gaskiya ni dai ka daina zagar min iyaye.” Ya ce “An zage su me za ki yi?

Magana na fara ƙasa-ƙasa ina murguɗa baki ai ban yi aune ba sai dai na ji ya shaƙo ni ta baya idanuwana suka firfito sai ya fara kifa min mari ya jani zuwa daki ya fara duka tun ina ja mishi Allah ya isa har na gaji na yi shiru ya tsaya kaina ya ce sai na bar ɗakin.

Gidan Maman shi na tafi ta fita ta biya wa Maman Amina suka tafi suka yi ta ba shi haƙuri ya buɗe min ƙofa ya ce shi ya riga ya sake ni!

Rashin ba ni Amir shi ya hana ni tafiya washegari na yi ta bin yayyen shi ina roƙon su yi mishi magana ya bani ɗana, ba wanda ya samu nasarar karbo min shi sai ƙanen baban su da na fado mawa.

Ba ni da kudin da zan dauki kayana zuwa Dukku, kuma ba zan tafi in bar su
ba don idan na tafi ba lallai idan na waiwayo in same su ba.

Gidan ƙanen baban nasu na koma yana da motoci na jigilar kaya cikin su ya bada daya aka loda min kayana na shiga muka bar garin.

Daf da magrib muka shiga Dukku gidan Iya na nuna mishi ba ƙaramin tashi hankalin ta ya yi ba gani na tare da kaya yan gidan ta sanya suka kwashe ta yi kaye kayen ɗakinta aka jibge su gefe ɗaya.

A daren ta kira Babana sai ga shi suka haɗu suka yi ta jimami.

Na ci-gaba da zama wurin Iya wadda ta bar zuwa gona ƙanenta da ke cikin gidan shi ya hana ta daga wurin shi ake kawo mata abinci, zuwa na kuma bai sa an ƙara mata ba ganin tana takura ta bar mana yasa na kama aikin yi wa matan gidan su biyu da suke awara tata su biya ni da haka muke samu mu ƙara.

Na gama iddata kenan babana ya zo ya samu Iya wai limamin masallacin su ya same shi wani ƙanen shi Malami ne a Gombe yake zaune ya ce ya binciko mishi mace mai hankali da tarbiyya shi kuma sai ya yi mini sha’awar shi daga mutumin kirki ne matarsa daya da yara, zai turo shi mu ga juna.

Bayan tafiyar Babana Iya ta ce me na gani?
Duk da ban ji abin ya kwanta min ba ga auren gabaɗaya da ya sire min, na ce duk yadda Babana ya ce don hakika ina jin tausayin Babana.

Kwana biyu tsakani sai ga shi Babban mutum mai kamala ga gayu da kwalliya shekarun shi ba su wuce arba’in da biyar, an ce mishi ina shayarwa ya ce ba matsala in zo da yaron zai rike kamar na shi.

Ba a ɗau lokaci ba aka shirya maganar aure ya biya sadaki ya yi min zannuwa aka daura aure na tare a Gombe.

Malami ne babba yana da ɗalibai masu tarin yawa yaran shi bakwai da mata daya, akwai yaran yan’uwan shi da aka kawo karatu su ma nan ake ba su abinci , sai manyan ɗaliban shi su ma kwanonin su anan suke don haka girki mai matuƙar yawa ake yi Mai gidan kuma yana ƙoƙarin yin cefane.

Mai girki tana kasancewa cikin aiki mai yawa a kwanaki biyun aikinta.

Malam Sani yana matuƙar so na da tattalina idan muka kadaice.

Alheri sosai yake aikawa Babana.
Tun tarewa ta abokiyar zamana wadda kowa ke kira Hajja ba mai fitina ba ce mace mai son raha da barkwanci da gari ya waye ta wanke ya’yanta ɗakina za ta yo a haɗu da yaranta da yaran da ke wurin Malam a yi ta duduma a ɗakina, har sai azahar ta kusa mai girki za ta fita ta ɗora don haka girkin ranar mu sai wajejen La’asar ake gama shi na dare kuma sai kusan magrib ake tsuro shi.

Sai yara sun gama ci sun nabba’a za ka samu ka share gidan ka wanke shi a daren ka yi wanka ni dai saboda rashin sabo da na samu na yi wanka neman inda zan sanya haƙarƙarina nake ko kwalliyar ban tsayawa yi.
Shi kuma sai sannan yake shigowa daga waje wurin jama’a.

Ƙawata A’ilo da muka tashi tare ita ta bani shawara da ta ji har zan yi aure daga mutuwar aurena, “Ki je ki yi family planning, in ta yi ruwa rijiya in ba ta yi ba masai.

In kin ga wurin zama sai ki cire ki miƙe ƙafa.
Na yi na’am da shawarar ta na nufi asibiti aka sanya min inplant na shekara uku.

A kwana a tashi har na shekara guda sosai Malam ke nuna min yadda yake so in kasance don ba abin da yake so wurin mace irin ado da kwalliya, ni kuma ƙuruciya da shirme sun hana ni in gane sai na biye wa kishiya mu zauna a yi ta sharholiya da mutane da basu yankewa da shigowa gidan.

Muna haka Malam ya tara mu ya ce zai ƙara aure.

Ba ni ba hatta Hajja sai da ta girgiza ba mu ƙara karkaɗa ba sai da muka ji wadda zai ɗauko mana wai mijinta babban ƙusa ne a Abuja, mutuwa ya yi ya bar mata dukiya mai tarin yawa ba ta taɓa haihuwa ba.

Yamu yamu muka yi ta sam barka gidanmu ba daki sai dai a yi can da ita.

Don ciki da falo kowaccen mu ke da shi sai na shi guda daya sai kitchen da bayi a tsakar gida ɗan filin tsakar gidan namu ma ba mai girma bane.

Sai dai me muna cikin sambarkan sai ma’aikata muka gani sun fara daura gini, kafin ka ce me cikin wata biyu an ƙanƙara ginin bene mai matuƙar kyau da ban sha’awa.

Hankalinmu bai ƙololuwar tashi ba sai da aka fara shigo da kayan amarya ni dai ba a gama ba na sulale na faɗa ɗakina na dubi kujeruna da duk suka sukurkuce saboda dabdalar da ake kansu na faɗa kan dan gadon jan katako na na yi rub da ciki.

Cigaba na yi da ba Zainab labari zaman mu da amaryar Malam har mutuwar aurena komawa ta Malumfashi wurin Gwoggo Maryama, aurena da Hassan mutuwar aurena da komawata Dukku da aurena da Alh Buhari har zuwa mutuwar Babana! Daga nan ƙaddarata ta wullo ni ta kawo ni gidansu.

Zuwa lokacin da na ƙare bata labarin na yi kuka har na gaji ita ɗin ma hawaye take sharewa.

Ta dafa ni “Allah ya ji ƙan Baba. Abin da kawai zan ce miki ba za ki samu ba na canji a rayuwar ki, shi ne rasa Baba da kika yi, amma in sha Allah rayuwarki za ta canza, ki saki jikinki mu yi ta addu’a tunda kina son karatu za ki yi har sai kin ce kin gaji Baba ba zai takura miki ba. Ita kuma waccan tsinan…
Na yi saurin toshe mata baki ina zare ido “Wa za ki tsine mawa? Ta ce “Tsohuwar alakwankwan tsohuwar da ba ta arziki ba, uwar Hassan ba dai ta haifa ba in sha Allah yadda ta yi haka za a yi mata. Ta yi ƙwafa.

Shigowar Khadijah yasa ta maida hankalinta kanta tana tambayarta baƙon da ta yi har da ce mata yaushe zai shigo gida harara ta galla mata “Saboda ana hauka daga fara zuwa zance yau yau sai a kama batun shigowa gida? Ta langaɓe kai “Wai a yi a yi gari na ruwa.” Ta ce “Allah dai ya kyauta miki da wannan shegen son auren naki.” Ta buɗe ido ta ɗaga hannuwa sama “Allah ya sani ina son Najib, to ya sunan sabon masoyin? Ta ce mata Usman.

Suna ta maganganun su ina sauraren su Zainab ta miƙe tana canza kayan jikinta “To ke Billy mai sabon gado ko hawa ba ki yi ba ko kin bar min? Na yi saurin daga kai ta ce “Rufa min asiri da ya Najib, zo ki hau gadonki ko sai na kamo ki yadda ake yi wa amarya?

Murmushin yaƙe na yi na shiga toilet na ɗauro alwala na zo na yi sallar isha’i da na idar ma gadon nata na dawo na haye bayanta na yi kwanciyata.

Ta tashi zaune “Iye Lallai ma da gaske kike, ta miƙe “To ni bari in ɗana yau.”

Ta haye gadon ta kwanta “Daɗi ya bar ki Billy kin ji laushin gadon? Na ce “Ban ji ba.” Ta yi dariya na rufe idona hawaye suka fara sintiri kan fuskata saboda fami da na yi wa kaina na tuna kaddarar rayuwata.

Juye-juye na yi ta yi barci ya kasa ɗauka ta kamar yadda hawayen suka ƙi tsayuwa. Agogon dakin ya buga karfe daya na dare na share hawayena na gyara kwanciya tare da ba kaina magana na shiga barci mai cike da mafarke mafarke da Babana.

Da ƙyar na tashi na yi sallar asuba kaina kamar zai sauka don ciwon da yake komai ban iya yi ba daga sallame sallar, na haye gado na koma barci.

Ban tashi sanin inda nake ba sai muryar Najib a kaina yana ma Zainab magana ya aka yi ban hau gadon ba? Shi fa don ni ya saya.

Ta ce “Kwantar da hankalinka ya Najib, za ta hau yanzu dai ka ɗan bamu wuri in tashe ta.” Ya ce to ta yi sauri kar in makara. Ina jin takun tskslmin shi ya juya don haka tana taɓa ni na tashi zaune “Yar duniya Billy, ashe kina jin mu to darling dinki dai na jiranki.”

Na bata hararar ambaton darling sai na yi miƙa na tashi na wuce bathroom.

Wanka na yi sa’adda na fito ba ta dakin sai da na danna ma dakin key sai na dawo na zauna zura ma mirror ido na yi yadda idanuwana suka kumbura, na balle tawul din na soma shafa mai ina kallon surata tare da godiya ga buwayi gwanin iko da ƙaga halitta da ya kyautata surata, sura mai fizgar hankali
buwayi ya yi min ya mini baiwar dirin halitta ta bakin Zainab ɗin da ko mace ta gani sai ta kuma kallo amma cikin mazan nan hudu an rasa me riƙe Ni.

Ban cika wani mugun kyau ba sai dai ban da muni ba ni da haske sosai sai dai manyan ido masu kyau da nake da su da yawan sumar kai su suka ƙayata fuskata. Matsakaicin tsawo gare ni.

Na gama murza hoda da shafawa laɓɓana wet lips aka fara knocking na dubi kofar na tambayi waye Zainab ta ce ita ce na isa ba buɗe ƙofar ta ce wai saboda ya Najib kika rufe kofar? Na daga mata kai ta ajiye tray da ta shigo da shi dauke a hannuwanta. “Ki yi sauri ki karya ya Najib na jiranki idan ya miƙa ki makarantar Company zai wuce.”

Na ce “Amma dai tare da ke za mu wuce ko? Ta ce “Ke dai shirya my Billy.”

Na sanya doguwar riga ta atamfa cikin wadanda Baba ya bamu tsarabar cotono Zainab ta dauko turare tana fesa min tana faɗin irin kyan da na yi ban daura dankwali ba sai kwantaccen gashina da ya sha gyara na zauna muna karyawa sai ga shi ya shigo na sunkuyar da kaina, ya zauna bakin gadon Khadijah yana facing di na kallon da ya dame ni da shi yasa na miƙe na zura hijab ɗin da na ciro na sanya na zura takalmi mara tsinin dunduniya.

Zainab ta ɓata fuska “Ka ga ka zo ya Najib za ka sanya ta je ta zauna da yunwa.”
Bai yi magana ba sai cewa ya yi “Mu je. Na dubi Zainab ta so mu je. Ta miƙe muka fita yana biye da mu.

Wurin wata rantsattsar mota da Dauda mai kula da hidimar gidan ke gogewa ta nufa da ni.
Daga Baban har Najib suna zuwa da motoci kala kala masu tsadar gaske kasantuwar sana’ar baban kenan, amma ban taɓa ganin wadda ta kai wannan ba.

Kafin ya iso ya buɗe ta, Zainab kuma ta buɗe ta cusa ni na yi narai narai da fuska “Yanzu kin yarda ki bar ni in tafi ni kaɗai?
Da hannu ta bani haƙuri “Yi hakuri Billy ban shirya bane.”

Ganin ya ƙaraso kuma ya sha mur yasa ta rufe ni ta juya.

Duk da wani bala’in ƙamshi mai kwantar da hankali da kuma sanyin raba da suka ziyarci gangar jiki da hancina gabana harbawa yake har ya shigo shigar Suit ya yi bakake sumar shi ta sha gyara irin ta matasa da suke cikin lokacin su.

Ya tashi motar har ya fita gidan muka hau titi bai yi magana ba.

Hannuna na sa guda daya na tallafi kumatuna.
Ba wani nisa tsakanin gidan da makarantar layi biyu ne da za ka iya takawa da kafarka gidan sama ne hawa daya ya shigar da motar harabar makarantar sai ya yi parking na ƙosa ya buɗe ƙofa in fita amma na ga ba shi da alamar hakan.

“Ba ki samu sakona wurin Zainab ba? Na tsinkayi muryarsa cikin wani yanayi, ajiyar zuciya ta ƙwace min amma ko motsi ban yi ba “Ko ban miki bane? Ya kuma tambaya nan ma kai da ba ka nan in ka tanka na tanka ban aune ba sai hannunsa na ji saman hannuna da na yi tagumi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mutum Da Kaddararsa 15Mutum Da Kaddararsa 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×