Skip to content
Part 20 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Ƙofar gida ta ajiye mu ta wuce.

Wajejen takwas da rabi na dare muna ɗaki Mama ta shigo sai da ta zauna ta ce “Ku masu son ku, za su zo ranar asabar idan Allah ya kaimu Mamin ku ta Abuja ma za ta zo karɓar kayan, don haka muna da aiki sosai bayan abin da za a yi na tarar baƙin ga kuma zuwan Mami.” Khadijah ta ce”Mami kuwa ta rabu da zuwa gidan nan.”

Zainab ta ce “Mu ma yaushe rabon mu da Abuja tun bikin Ya Safwan.” Khadijah ta ce “Ku ne ma kuka je ni ina Exam lokacin ban je ba.”

Mama ta miƙe “Idan Allah ya kaimu safiya za mu fara aikin. Muka yi mata sai da safe ta fita.
Suka ci gaba da hirar Mamin har na ƙare na tambayi Zainab wai wace ce Mamin?

Ta ce “Yar’uwar Baba ce ita da mijinta daddyn Abuja, da maman Mami da baban babanmu da baban daddy mijinta duk uwa daya uba daya suke. Kuma daddyn Abuja abokin Baban mu ne tun suna yara suka tashi tare, ni dai ban ga Baba yana da aboki sama da shi ba.

Daddyn Abuja Soja ne yaron su guda ya Safwan ya yi aure shekaru biyu da suka wuce yana da yarinya daya. Ya riga babanmu yin aure an ce tun kafin ya tafi aikin soja ya yi babanmu kuma da burin shi kasuwanci har sai da ya fara kama ƙasa ya auro Mamanmu, shekararta guda kacal ya auro Maman ya Najib.

Da safe da muka tashi su suka fita wurin aikin da Mama ta ce ni shirin makaranta na fara na fito cikin riga da zane ta atamfa sai dogon hijab da na sanya na rataya jaka.

Ban samu kowa a falo ba duk suna kitchen, na isa kitchen ɗin na yi musu sallama, Zainab ta ce “Ga aikin Cake nan mun bar miki.” Na ce “To sai na dawo zan yi.” Na kusa get na hangi Najib tsaye a ƙofar dakinsa ya harɗe hannaye a ƙirji, na ƙara tamke fuskata na fice.

Tun ranar ban kuma ganin shi ba sai fa yau.

Da muka tashi tare da Haj Halima muka taho don ita ma tana yin lesson din da nake tsayawa ta rage min hanya.

Ina shiga gida sallah na fara na ci abincin da na gani an ajiye a dakin sai na sauko ƙasa ina shiga kitchen su kuma za su fita su yi sallah sai Baba Talatu ce suka bari a ciki.

Na tattaro kayan Cake na fara yi duk da ban san kamar yadda za a yi ba.

Da suka idar suka dawo kama baki Zainab ta yi “Wai da na ce za ki yi Cake tunanin ki da gaske ne?

Na ce “E mana.” Ta kama dariya “To ni kam wasa nake miki, akwai wani wuri na ƙwararru masu yin Snacks a can za a sawo.”
Na ce “To aikin gama ya gama sai dai a ƙaro idan bai isa ba.”

Da na gama suka ci suka yi ta santi don na ƙara koyo wurin Maman su Ahmad ita nata har da Inabi to har inabin na sanya da yake akwai shi Baba ya zo da shi da ya je Lagos.

Washegari da na dawo makaranta Cincin na yi shi ma wurin Maman su Ahmad na koye shi mai madara da kwakwa kana ci yana narke maka a baki.

Ai shi kam sai da Mama ta ɗauke don sun tasar masa za su cinye ta kai part ɗin Baba.

Na koma daki ina hutawa Zainab ta shigo, “Ina ta so in faɗa miki Billy Zahra ta haihu.” Ido na buɗe “Matar Sunusi?

Ta ɗaga kai “Sai kira na take a waya na gaza ɗagawa don gani nake ko ta ji zancen ne, sai ta yi min Text message ta samu baby girl.”

Na ce “Allah shi raya.”

“Yaushe za ki raka ni barka?

Ta tambaye ni tana wani murmushi
“Babbar magana, ke ma mu yi miki fatan ki dawo lafiya da ƙafafuwan ki biyu.”

Ta yi dariya “Dalla mun yi waya lafiya lau.
Na ce “To Allah ya fidda A’i a rogo ya sa ba lumbu lumbu suke miki ba.

Ta ce “Kina ma Allah bar ba ni tsoro.”
Na ce “Na bari.”

Wata farar takarda ta miƙo min “In ji ya Najib, foam ne na lesson din da za ki fara zuwa watanni tara za ki yi Asabar ne da Lahadi.”
Na ce “Allah ya bamu sa’a.”

“Wai me ya faru tsakanin ki da ya Najib na ga kwana biyu bai zuwa neman ki?

Na ce “Ba komai.”

****?
Ranar asabar da Mamin Abuja za ta zo ana ta soya kaji Mama ta sanya na yi miya duk ma girkin da aka yi ni na yi shi.

Da hantsi suka iso ina cikin aiki, don haka da ƙyar Zainab ta jani zuwa falon Baba muka gaishe da daddyn, da ta ce saura Mami na ce ta bari in kammala.

Na koma na ci gaba da aikina wayata ta yi ƙara Mama ce ta shaida min in haɗo abin tabawa in kawo wa baƙuwa, na zuba Cake din da Cincin da soyayyun kajin da Baba Talatu ta soya na ɗauka na tafi kai mata.

Khadijah kuma ta tafi kai ma Daddyn.
Zainab da sauran yaran suna falon Mama, Babbar mace ce da shekarunta za su yi hamsin ba ta da tsawo sai jiki akwai dai kamala suna yanayi da Baba.

Ta amsa gaisuwa ta cikin faran-faran tana tambayar Mama ina ta samo kyakyawar budurwa?

Ta ce ɗiyarsu ce diyar dan’uwan Baba na Dukku.

Ta ce “Allah sarki wanda ya rasu watannin baya? Sosai muka so zuwa gaisuwa lokacin jikin daddy ya matsa.

Ta juyo wurina “Sannu kin ji yarinya Allah ya ji ƙan mahaifinki.”

Na sunkuyar da kaina na ce “Amin na gode.” Ya sunanta? Ta tambaya Mama ta ce “Takwararki ce ta ce “Ma sha Allah

Ban daɗe ba na tashi na koma kitchen can Mama ta same ni ta ce bayan shinkafa da miyar kaji da aka yi duka gidan in yi wa Mami da Daddyn shinkafa jallop mai kayan lambu da kayan ciki.

Na ce “To.”

Da na gama na ɗauki ta Mamin na kai mata na samu ta idar da sallah da Mama ta ce ta zo a ci abinci ta ce a’a ba za ta hau tebur ba in kawo mata nan.

Na shirya mata komai gaban ta farfesun da na yi musu ita da Daddyn shi ta fara ci ta ce wa Mama “Hala kin sake mai aikin da zuwa na na karshe ana ta rikici kan bata girki Haj Sa’adatu?

Ta nuna ni aikin ya ta ne an bata baiwar iya girki indai ta sarrafa shi za ki ji ya yi daɗi.” Ta yi murmushi “Ma sha Allah Allah ya shi albarka na ce Amin a zuciyata na tashi na tafi daki don in yi wanka don ko wankan ban samu na yi ba.

Sai yamma matan ƙannen Baba da makota da abokan arzikin Mama suka shigo suka karɓi kayan sa ranar Khadija da Zainab, aka kuma faɗi watannin bikin da aka sa watanni goma masu zuwa.
Ana ta kaya-kaya ina kitchen don Mama ta ce in yi wa daddy da Mamin da Baba tuwon semo miyar kuɓewa ɗanya.

Ko da na kawo ma Mamin tana ta shi min albarka da muka zo kwanciya Zainab ke ba ni labarin ta ji Mamin na cewa Mama ita dai tana gani na ta ji na shiga ranta.

Washegari Lahadi da wuri na shiga kitchen na yi wa baƙin abin karyawa sai na koma daki na yi kwanciyata, cikin barcin na ji Zainab na tashi na “Ki tashi Billy su Mami za su wuce ta ce ba ku yi sallama ba.”

Na tashi zaune ina muttsuke ido don barcin bai ishe ni ba, ɗan gyalen da na sanya a kaina garin barci ya zame na janyo na daura muka sauko.

Gabaɗaya yaran gidan ne za su yi mata rakiya na dan ranƙwafar da kaina “Allah ya tsare Mami a sauka lfy.”

Ta tako inda nake tsaye ta kama kafaɗata ta ɗora kaina saman ta ta kafaɗar “To ya ta mu za mu tafi mun gode ƙwarai da ɗawainiya, sai Allah ya sake sada mu.”

Ta sake ni ta fara tafiya suka bi bayanta na harari Najib da ke tare da su na sulale na koma ɗaki.

Ta window na riƙa leƙensu har Maman su Ahmad ta fito rakiyar su inda motarsu take sai da duk ta yi wa yaran yadda ta yi min Najib kuma ta kama hannunsa sai ta shiga mota.
Daddyn kuma rafar kuɗi ya miƙa ma Asma’u shi ma ya shige motar.

Sai da direba ya tashi motar ya fice daga gidan mutanen gidan suka kama hanyar dawowa ciki sai na bar jikin windon na koma bisa gadona.

Bayan wani tsawon lokaci Zainab ta same ni “Wai ke me ya sa ba ki son shiga cikin jama’a a yi hira da ke?

Ɗan murmushi na yi mata na ce “,Sai a hankali za ki ga na saba da kowa, yanzu dai ke ai kin ga na saba da ke? Ta miƙo min kuɗi tana girgiza kai “Ga kason ki da Daddyn Abuja ya bayar.”

Na karɓa na ce “Allah ya sa ka da alheri.”
Ta fadi “Amin.” Sai ta miƙo min wata jakar leda “Wannan kuma tsarabar Mami ce.”

Na amsa ina dubawa tare da ƙara godew a,na miƙe zuwa wurin wardrobe na buɗe na ɗauko jakata da na fi zuwa makaranta da ita na sanya kudin ciki.

Sau biyu Zainab na min maganar makarantar da zan fara zuwa yin lesson, duk da tsananin son da nake ma karatun saboda ta hannun Najib abin ya biyo gabaɗaya sai na ji zan ma iya hakura don idan na biye ma abin da zai biyo ta hannunsa zan iya rasa darajata da ƙimata ta ɗiya mace kuma da muguwar rawa gwamma ƙin tashi.

Da ta yi min ta uku ta gane dai share zancen nake ta ce “To ki je ya Najib na kiran ki.”
Na ce “Gaskiya sai dai ki yi haƙuri amma ba za ni ba.” Ta kama baki “Saboda me? Na fuskance ta “Zan faɗa miki gaskiya Zainab ko da ba za ki ji daɗi ba, ɗan’uwanki yana yi min abubuwan da basu dace ba, a matsayina kuma na mace musulma dole in tsare mutuncina.”

Jikinta na ga ya ɗan yi sanyi ta ce “Haka ne ta tashi ta tafi.”

Ta ɗan jima sai ga ta ta dawo “Ki daure Billy ki fita ki samu ya Najib, da alama ya shiga hankalinsa kan boren da kika masa.

Ya ce bayani zai miki kan lesson din da za ki fara ya ce mu je tare, ki yi haƙuri mu je taren ban son ki rasa damar karatun.”

Ban ce mata komai ba dogon hijab di na na zura ta miƙe muka sauka tare.

Tsaye yake jikin part ɗin Maman Ahmad ya tokare ƙafarsa daya a bango ya rungume hannayensa a ƙirji yana bi na da wannan kallon na balla mishi harara, ya haɗe hannayensa alamar ban haƙuri na kauda kaina “Maganar lesson dinki ne baby, ranar Saturday za ki fara zuwa ten ne zuwa twelve zan riƙa kai ki in dauko ki idan kuma ban samu dauko ki ba sai in samu wanda zai dawo min da ke.”

Na juyo na dube shi ido cikin ido “Ba sai ka kai ni ba zan din ga fita in hau keke napep.”
A’a wa kika ga gidan nan na hawan ta? Na ce “To na haƙura da zuwa.”

Ya ce “Ba za a yi haka ba ki yi yadda kike son, amma don Allah ki turo min acc no in sanya miki transport na yi shiru Zainab da ba ta yi magana ba tun zuwan mu ta ce “Za ta turo ya Najib.” Na kama hanya ta biyo bayana.

Da muka je ɗaki ita ta ɗauki wayata ta tura mishi tana min tsiyar ina ja ma yayan su aji don na ga yana so na. A raina na ce da zai samu abin da yake muradi, ledar pure water sai ta fi ni mutunci a wurin shi.

Ranar asabar ɗin farko da zan fara zuwa na yarda ya kai ni shi da Zainab washegari na tafi da kaina na dawo a keke napep har ƙofar gida ya sauke ni na tura kofar da na gani buɗe na shiga ban tarar da Khadijah da Zainab a daki ba sai da na cire hijab na kwanta Zainab ta fara shigowa sannan Khadijah sai ga Mama, zaune na tashi ina gaishe ta fuskarta ba fara’ar da ba ka raba ta da ita.

Gefen gadona ta zauna ta kira sunana na amsa tare da ƙara shiga nutsuwata. “Bilkisu yau Alh ya tara mu ni da Auntyn ku ya shaida mana za ki koma wurin ta da zama. Kirjina ya ce dam! Na dube ta ina fiddo ido. Ta daga kai “Haka ya ce don tana fama da laulayi za ki dinga taimaka mata.

<< Mutum Da Kaddararsa 19Mutum Da Kaddararsa 21 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×