Skip to content
Part 21 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Wasu hawaye da ban shirya zubar su ba suka fara gudu kan fuskata “Na kifa kai na fara kuka “Ki yi haƙuri Bilkisu ai duk cikin gida ɗaya ne, za ki shigo ku yi hidimar ku kar ki sa ma kanki damuwa.”

Mama ke min wannan lallashin sai dai ban yarda da hakurin da take ba ni ba kuka kawai nake don na san matar nan ba ta nufi na da alheri “Ita za ta kitsa ma Baba, Bilkisu ta koma wurin ta don girkin da take wa Baba yana yabon dadin abincin kun san ita ba ta yarda kowa ya fi ta ba.

Da kuma ya Najib da da ma take so tun zuwan ta ya koma ɗan wurin ta ta hanyar Bilkisu da yake so za ta ga za ta samu hakan.”

Khadijah ce ta faɗi cikin muryarta da ba ta cika son hayaniya ba.

Ai kam jin zancen ta take na gasgata ta, matar nan za ta iya sanya min abin da zan ci ko sha ya batar min da hankalina Najib ya samu galaba a kaina.

Na ƙara fashewa da kuka Zainab ta matso kusa da ni “Ki yi haƙuri Billy ba abin da zai faru da ke sai alheri a kowane hali muna tare da ke.”

Mama ta mike “Ki shirya kayanki sai ki tafi.”
Cikin kuka na ce “Ni anan zan bar su.”
Ta ce “A’a yin hakan zai zama abin da za a haɗa ni da Alh, ki dai kwashe ɗin.”

Ta sa kai ta fice.

Kukan na ci-gaba da yi na tausayin makomata a wurin waccan matar, da ƙyar Zainab ta samu na yi shiru ita ta ciro ainahin jakunkunan da na zo da su ta shirya min kayana da duk suke a goge sai waɗanda ba a rasa ba ta miƙo min hijab ɗin da na dawo makaranta ta ɗauki jaka daya na ɗauki ɗaya Khadija ta ce “Ki yi haƙuri Bilkisu ai ba rabuwa muka yi ba muna cikin gida ɗaya.”

Na ce “To.”

Muka wuce da muka sauka ma su Rabi’ah ganin ina kuka suka tambayi Zainab abin da ya same ni ta faɗa musu duk suka yi jugum.
Asma’u ƙaramar ta ce “Ki yi haƙuri Aunty Bilkisu.”

Sai da na share hawaye duka a fuskata muka shiga bedroom ɗin Mama tana zaune bakin gado ta ce “Har kin fito Bilkisu? Na ɗaga kai “To shi kenan ki yi haƙuri ki bar kuka.”

Na ce “Na gode Mama bisa alherin ki a gare ni na irin ruƙon da kika yi mini shigowa ta cikin iyalinki.” Sai na wuce cikin sauri na samu Zainab ta sauko da dayar jakar da ta yi saura Dauda kuma ya iso da ta aiki Asma’u kiran shi shi ya dauki guda biyu ta riƙe daya muka fito duka yaran suka biyo mu wai za su raka ni sai ka ce wacce za ta bar gidan.

Daga ƙofar part ɗin suka juya sai Zainab da ta tsaya tana ƙara gaya min kalaman ban haƙuri.
Na share fuskata sai na sa hannu na kinkimi jakata daya na isa na kwanƙwasa ƙofa daga ciki na ji takun tafiya Muhammad ne ya zo da gudu ya buɗe na shiga a farkon shigar na ajiye jakar na koma na kwaso sauran ban kai ga zama ba ta fito tana yamutsa fuska “Kin shigo Bilkisu? Ban samu na yi girki ba ma, ki shiga kitchen ki dafa farar shinkafa akwai miya a fridge sai ki yi min pepper soup na amsa na wuce kitchen ɗin don soma aikin, ban jima ba Ahmad ya shigo wai zai sha cornflakes na haɗa mishi na ba shi can sai ga Muhammad ya ce shi ma shi din ma na haɗa mishi ya tafi.

Da na haɗa komai na fito na yi alwala na yi sallah a falo ban samu kowa a falon ba da na idar na koma kitchen su Muhammad suka shigo in basu abinci na da ma na gama farar shinkafar sai na zuba musu.

Da na gama na zuzzuba na shirya komai na dauko na kawo falo lokacin har La’asar ta kusa yunwa sosai ke sakaɗa ta amma hakanan na zauna cikin kujerun falon har sai da ta fito muka ci tare.

Da muka kammala ban ƙara zama ba kitchen ta sanya ni na gyara daga nan muka zo falo goge can kakkaɓe nan har bedroom ɗinta kuma duk abin nan jakunkunan kayana na zube a farkon shigowa falon ba ta ce in dauko ba ta nuna min masaukina har sai da aka yi magrib Najib ya shigo shi ya ce in ɗauke kayan mana in kai ciki sai ta wayance ta ce ya ban shigar da su dakin su Ahmad ba?

Na kwashe zuwa dakin luntsumemiyar katifa ce kadai a dakin sai wardrobe na buɗe ta na shirya kayana ban koma falon ba sai da na ji tana kira na na koma falon Najib ɗin na nan abinci ta sanya ni na kawo masa ta ce in yi masu Ahmad home work can bayan kujeru na ja su muka zauna a ƙasa sai da na gama musu Najib ya ce fita zai yi.

Ƙarfe tara na shige ɗakin na haye katifar na kwanta shiru ina lissafin rayuwa ban san sa’adda yaran suka shigo ba sai da na farka ƙarfe huɗu, alwala na ɗauro na zo na yi sallah raka’a biyu na yi ma kaina addu’a na koma na kwanta.

Ina idar da sallar asuba ta shigo ta kira ni, aiki ta nuna min yadda zan yi da shirya su Ahmad zuwa Sch da yi musu break fast sai da na sallame su na fara gyara wurin duk da ba wani datti amma sai an ƙara ƙalƙale ko’ina, irin mutanen nan ne masu masifar tsafta, ni dai ban samu na sarara ba sai da na yi wanka na fita gidan zuwa makaranta.

Da na dawo part ɗin su Zainab na sauka suka kama murna da ganina na je na gaida Mama, muka haye sama da Zainab muka ci abinci ni na ma manta da wani komawa ta part ɗin Maman Ahmad sai ga kiranta ina ina har yanzu ban shigo ba?

Na ce ina part ɗin su Zainab ta ce in zo yanzu.
Na miƙe muka rabu da Zainab ba don ran mu ya so ba.

A falo na same ta ranta ɓace kuma kai tsaye ta faɗa min ba ta son zuwa na part ɗin su Zainab.

Abinci ta sanya ni yi sai dai yau ita ke da Baba tare muka shiga kitchen ɗin, sai dai wuri ta samu ta zauna sai dai ta ba ni umarni.

Da na kammala zan shige ɗaki ta ce “Wanka ɗaya kike yi? Wannan ƙazanta ne mace da gyara aka san ta.” Na wuce zan yi wankan ta ce idan na gama wankan in shiga bedroom ɗinta in yi kwalliya.

Hakan kuwa aka yi don da safe mai kawai da turare na su Ahmad na yi amfani da su na tafi makaranta don ban ga fuskar tambaya ba sam ta canza daga wadda na sani tsakanin mu bayar da umarni ne.

Dole kuma na canza kaya wata riga mara nauyi tsawon ta kaɗan ya wuce gwiwa.

Ban niyyar komawa falon ba har na haye katifa in yi karatu ta kira ni na fita falon Najib na gani ya shigo ta ce in kawo mishi abinci ta fita zuwa part ɗin Baba.

Na shiryo abincin na kawo mishi ya ce in zauna mu yi hira hira ya zo min yau ko fita ba zai yi ba, na zauna cikin faɗuwar gaba sauƙi na daya su Ahmad Ahmad da ke zaune suna kallon Cartoon.

Bai tafi ba har sai da ta shiga yin shirin kwanciya da za ta tafi ta ce in rufe wurin.
Ko da na rufe tsoro na ke ji tsakiyar yaran na kwanta ina ta karanto addu’o’i.

Yau da na san abin da zan yi ina idar da sallah na fita na kama aikin abin karyawar yaran, na kammala yi musu wanka ina sanya musu unifoam na ji shigowar saƙo a wayata na kai hannu na ɗauka Auntyn ce ke shaida min in ɗora abincin karyawar Baba na ajiye wayar na tafi kitchen na haɗo musu abin karin na kawo musu sai na koma na haɗa musu wanda za su tafi da shi a lunch box sai da suka fita don tafiya tare da sauran yan’uwansu na fara aikin abin karin Baba sai sannan Maman su ta shigo duba yadda nake yi ta yi sai ta fice sai da na kusa kammalawa ta dawo cikin matuƙar kwalliya tana ƙamshi, ta tsaya na ƙarasa ta ɗauki nasu da Baba Ni na ci nawa a kitchen ɗin ina tuna yan part ɗin su Zainab da mu’amalarmu musamman Zainab ɗin.

Da na gama na shiga gyaran part ɗin na ƙaddara to na ƙaddara mana don duk rabin aikin duk ƙaƙale ne, a ƙarshe na yi wanka na shiga bedroom ɗinta na yi kwalliya na koma na sanya kaya Text na yi mata zan tafi makaranta sai ga ta wani key ta bani ta ce in ajiye wurina ni na rufe wurin ta koma wurin Baba.
Ina kallon part ɗin su Zainab kamar in shiga sai dai na hakura na wuce.

Washegari ta fita girki don haka ta ce min idan na dawo za mu fita zuwa Sallon na ce to.
Don haka ina dawowa a gurguje na yi mana girki muka shirya da muka fito ina hango Zainab tana magana da Dauda hannu na daga mata sai na sunkuyar da kaina na shiga motar da har ta riga ta tayar gefen ta na zauna na rufe.

Ta gefen Zainab muka wuce muka bar gidan.

A wurin Sallon ɗin duk irin gyaran da aka yi mata irin shi ta sa aka yi min don haka yamma sosai muka koma gida na yi mana girki muka ci har Najib.

Haka rayuwata ta koma part ɗin Maman Ahmad komai ni ke yi, aikin ta bada umarni sai dai na yarda laulayin take domin irin su masu tsaftar nan har da ta masifa ba su ma san gajiyar ba, ba su ma jira a yi musu don ita ko yar aiki ba ta da ita.

Ina ga laulayin nata na rashin son aiki ne tun ina gajiya da yawan aikin da rabin shi duk ƙaƙale ne goge can wanke can sai yawan girki nau’i nau’i da na ƙara ƙwarewa da ni kam na iya yan girke- gieken mu na gargajiya yanzu ko har da na turawan don matar yadda ka san an mata wahayin iya sarrafa abinci.

Na koma zama ni kaɗai ba ni da abokin hira gundurar da na yi da zaman sai ya darsa min komawa makarantar islamiyya.

Na same ta na ce don Allah ina so in riƙa zuwa islamiya da su Ahmad, tunda ta ce min to sai na ji shiru da na gaji sai na yi wa Najib magana don kullum yana part ɗin nan ya dawo da cin abinci yake kuma hira sayayyar da yake min ina part ɗin su Zainab bai fasa ba idan ya kawo sai ta ce in ajiye ni kuma in zan tafi makaranta sai in ɗibi abin da na san Zainab na so in fita da su ko in fakaici idon Dauda da take sa wa ya lurar mata da na shiga in yi wuf in faɗa in gaishe da Mama in ba Zainab ko in ba mai gadi in ce ya ba ta.

Najib ya same ta da zancen makarantar sai ta shiga kame-kame ƙarshe dai a ranar ta kai ni da yamma ta yi min Register.

Tafiyar da nake Islamiya da yamma idan na dawo ta rana ya rage min zaman gidan sai dai na kan makara a ranakun girkin ta don sai ba rage aiki nake tafiya, ga asabar da Lahadi ina zuwa lesson.

Ranar wata talata mun tashi makaranta ina fitowa sai Zainab na gani tsaye bakin get da murna na nufe ta muka riƙe hannun juna wurin motar da ake kai yara makaranta ta jani muka shiga ganin direba ya dauki hanya ba ta gida ba na ce “Ina za mu?

Ta ce “Amir za mu gano ke sarkin fillanci.” Na ce “Ba haka ba ne ba na son zuwa gidan mutanen nan, kina fa gani daga ganin yanayin da muka je ko sati ba a yi ba suka kwaso suka zo, ana sati uku Abu ta ƙara kira na za su zo na ce ba ni nan ina Dukku.

Shi ma Aminun ban faɗa miki ba ne ya fara damu na da waya wai zai zo sai da na taka mishi burki na yi mishi ƙal, ganin ba zai bar ni ba na yi blocking ɗin shi.”

Ta dafa hannuna “Kwantar da hankalinki yanzu ma ba gidan su za mu ba, Sch ɗin da yake Islamiya za mu tambaya sai mu same shi can.

Na ce da kin fada min da na fito da yan kuɗaɗena na yi mishi sayayya.”

Ta ce “Na yi mishi.

Rasa me zan ce mata na yi don tsakani na da wannan baiwar Allah ba ni da bakin gode mata.

Kusa da gidan muka tsaya muka yi tambaya har muka samu wanda ya mana rakiya har makarantar ana kiran shi yaron ya gane mu, mun ɗan dade tare da shi sai muka ba malamar su ledar da Zainab ta kawo mashi kaya da rokon ta rike mishi sai an tashi ta ba shi ta yi alƙawarin har gida ma za ta mika mishi.

Muka yi mata godiya muka wuce. Ina komawa na samu Maman Ahmad na jira na ta ce ina na tsaya na ce lesson kamar ba ta yarda ba ta dai yi shiru. Ranar ban samu zuwa islamiya ba saboda ita ke da girki kuma ban dawo da wuri ba, sallah kawai na yi na kama aikin.

<< Mutum Da Kaddararsa 20Mutum Da Kaddararsa 22 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×