Skip to content
Part 22 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Bikin su Zainab na ta kawo jiki ana ta shirye-shirye shiri kuma ba na wasa ba kasantuwar karo na farko kenan da Baba zai aurar.

A lokacin aka fara sayar da Foam na jamb, Zainab ta matsa min in yi jamb din a bana duk da tsayawar da na yi ta bari sai baɗi don makarantar da nake mun yi jarabawa idan ka haye sai ka wuce zuwa mataki na gaba, ni na fi so sai na gama wannan ɗin ta ce a’a in yi bana har WAEC ɗin kawai nasara ta Allah ce.

Don haka muka je muka saya, mun dawo sai da na shiga na gaida Mama ban dai zauna ba duk da ban ga motar Maman Ahmad ba tunanina ta fita sai dai zan sa key in bude wurin na jiyo muryarta “Na samu nasarar maida Najib nawa ta dalilin wannan yarinyar Hajiyata.”

Muryar wata na ji ta amshe “Ta ya ya mutumniyata ba ni in sha.”

Na sha fama ba kaɗan ba, na yi kissa na yi salo na kwantar da murya amma Alh ya ƙi amince min yarinyar nan ta dawo wurina, sai na fake da cikin nan na ce ban iya komai, ta dawo ta dinga taimaka min ko zuwa in haihu ne sai ya amince, kuma lura da yadda Najib ya liƙe mata ya sa na rabo ta da can kuma da ta dawo nan ne sai ga shi ya dawo wurina kamun ƙafa yake da ni in shigar da shi wurin ta ya kasa samun kanta.

Ni kuma sai na yi amfani da hakan na mayar da shi saniyar tatsa ina cewa zan yi mata abu kaza da kaza.”

Matar ta ja tsaki “Amma shi ina ganin shi wayayyen matashi ashe wawa ne, macen a yanzu yana da kuɗi yake faman bi da wannan lokaci mata ke bin maza musamman kana da kuɗi.”

A’a ƙawata ba dai duka ba har yau akwai masu aji har yau, ita wannan abin duniyar ma bai dame ta ba ballantana ka ce ma za ka yaudare ta da shi.

Shi ɗin ma yana da tulin yammata har da na tsiya, wannan ɗin dai ce aka jarabce shi da ita.”

Waccan ta ce “Ko kuma saboda ta matse abin ta ta ƙi yarda ya yi mata wayo?

Suka kwashe da dariya Maman Ahmad ta ce “Yawwa ashe kin gane, kin ga ni duk abin da yake kaiwa part ɗin matar can ya dawo part dina sai dai su hanga, da tana fasa kai Najib nata ne da ma na yi ma kaina alƙawari ba zan bar mata ba.

Waccan ta yi shewa “Da kyau ta wajena.”
“Allah nake faɗa miki abin da ya ƙara ɗaga min hankali yarinyar ta iya girki da ina alfahari abincina kaɗai Alh ke ɗoki, kawai yarinyar nan na fara yi sai ya kama tunanin matar can ke yi, na ce zan yi maganin ta yanzu ko part ɗin na hana ta zuwa in ga uwar da za ta yi mata girkin.

Waya ta ɗauki ƙara sai na ji tana cewa ƙawar ta ta “Tashi kin ji mu je ciki.”

Sai da na dan basu lokaci sai na shiga ɗaki na wuce jikina a mace na kwanta bisa katifa cike da mamakin halayen wannan mata sai na tuna wata maganar Zainab da ta taɓa cewa matar ba ta abu don Allah ka ga ta yi abu tana da manufar ta ta yin hakan.

Ban san iya lokacin da na ɗauka a haka ba sai muryarta na ji tana faɗin “Bilkisu yaushe kika shigo?

Na ɗago na dube ta “Ban daɗe ba ba ni da lafiya ne.” Ta ce Allah ya sawaƙe sai ta juya.

Ranar duk yadda ta so in mata girki narkewa na yi na yi kwanciyata, sai dai yunwa da ke ta kartar yan hanjina.

Ban fito ba sai dare da Najib ya shigo yana nema na ta aiko Ahmad ya kira ni, inda nake gode mata daya ne ita kam ba ta ba Najib fuskar ina ɗaki ya antayo ba iyakar shi falo sai ko idan ya ji motsi na a kitchen ya bi ni can.

Na fito ina yamutsa fuska don yunwa nake ji cikin kitchen na nutse ta ce mishi bari ta je wurin Baba. Ya dubi su Ahmad da Muhammad ya ce su wuce daki su kwanta gobe akwai Sch suka tashi suka shige ya taso daga inda yake ya tsuguna gabana ya sha kwalliyar lallausar shadda da hula yar uban su sai ƙamshi yake.

“An ce ba ki da lafiya baby me yake damun ki? Na ce “Kaina ke ciwo.”

“Kin sha magani?”

Na girgiza kai tashi ya yi ya fita can ya dawo da magani “Kin ci abinci? Kan na ƙara girgizawa “Na shi abincin da aka jera mishi ya ce in taso in ci na mike na zauna gaban abincin mursisi na ci yana min sannu ya ba ni magani na sha wai da fita zai yi amma saboda ba ni da lafiya ya fasa.

Nan muka yi ta zama da shi har Auntyn ta dawo sai na ce mishi zan kwanta.

Ranar dai ko ƙaddararren wankan da ta mayar wajibi in za a kwanta sai an yi don har na ma fara sabawa kwanciya na yi ban yi shi ba.

Duk bayan sati biyu ko uku muke zuwa dubo Najib ni da Zainab kuma iyakar mu makarantar su.

Wani yammaci ina kitchen ina yi mana girki babu Islamiya kasantuwar ranar juma’a ce wanka na yi sai na samu kaina da zama na sheka kwalliya wata doguwar rigar material mai kyau da tsada na sanya, ɗinkin ya karɓe ni na yi kyau da gaske ga kaina da ya sha gyara don mun ziyarci Sallon da Maman su Ahmad ban daura ɗankwali ba a wuya na rataya abuna.

Ina girkin karatun Alaramma Usman Abubakar Birnin Kebbi na sanya a wayata ina saurare, har wani lumshe ido nake don daɗin ƙira’ar.

Jikina ya ba ni kamar ba ni kaɗai ba ce sai na waiwaya Najib ne a bakin kofa ya sha kyau sai ƙamshi yake kallon da na tsana yake watso min “Kin yi kyau baby.” Ya faɗi yana rage girman idanunsa harara na galla masa ya yi murmushi “Bithday za ni na abokina Habib kin dai san shi don ina zuwa tare da shi, ina son shiga da ke wurin za ki rikita gayu, ki daure yau kaɗai mu fita ki raka ni.”

Hararar na ƙara balla mishi “Idan ba so kake dan guntun mutuncin da ya saura tsakanin mu ya watse ba kar ka ƙara min wannan maganar.”

Ya haɗe hannaye “Zo mu je falo mu yi maganar.”

Na wanke hannuna na bi shi sai da muka zauna ya ƙara roƙona “Ko me kike so ki faɗi zan miki ki yarda mu fita yau kaɗai.”

Miƙewa na yi “Zan koma kan aikina daga ba ka da abin faɗa.”

Zai yi magana wayarsa ta ɗauki ƙara ya sanya ta a kunne sai ya miƙe ya fita yana fadin “Ga ni nan zuwa ina bisa hanya.

Na tabe baki sai na koma kitchen Maman su Ahmad ta yi nauyi tana daki kwance na gama na dawo falo na zauna sai na ga key na dakin Najib da dayar wayarsa, na ɗauki wayar ina shafa ta don ta ba ni sha’awa ba sai an gaya maka ita ɗin mai tsada ba ce kamar an sanya ni na shiga gwada password ɗin da aka sa, na yi na yi ta ƙi buɗewa na taɓe baki ina yaba shiga ukuna ta son buɗe wayar.

Saman fridge na ajiye mishi sai na shiga ɗaki wayata na ji tana burari na miƙa hannu na ɗauko ta Gwoggo Maryama ce cikin farin ciki na ɗaga don mun ɗan kwana biyu ba mu yi waya ba sai da na gama gaishe ta da tambayar kowa ta ce duk lafiya sai ta yi min albishir jibi tana nan zuwa ta gan ni daɗi ya rufe ni da Maman su Ahmad ta fito tana tura cikinta da ya yi matuƙar girma sai dai ya sa ta yi kumari, na faɗa mata Gwoggona za ta zo tare muka ci abinci har da su Ahmad na je da su na yi musu wanka ni ma na yi na yi shirin kwanciya.

Mun fara chat da Zainab na ce mata barci nake ji na mayar da wayar Silent na kwanta kusa da muham ba bata lokaci barci ya sace ni.
Cikin barcin na ji ana kiran sunana duk da ba ni da magagin barci ƙyar na buɗe idona don ina kan ganiyar barcin sai da na dan wattsake na fahimci muryar Najib ce sannan kuma na gane daga jikin window yake kira na na tashi zaune kafin na matsa na ƙara hasken wutar dakin da na rage “Bilkisu.” Ya sake kirana na amsa daga inda nake “Ki bani key din ɗakina.”
Na ƙara tsinkayar muryarsa na mike na bar ɗakin falo na isa inda na ajiye na dauko har wayar na koma dakin na ce “Ga su. Ba ta inda zan iya miƙa mashi ya ce “Ki buɗe ƙofa a hankali kar Aunty ta ji ki miƙo min.

Na ɓata fuska ina duban agogo sha biyu saura na dare wai sai yanzu mutum zai dawo gida na fadi a raina.

“Ki buɗe ƙofar Bilkisu.” Ya kara faɗi na ƙara kwaɓe fuska “Ni ya Najib ba zan iya buɗe ƙofar ba.”

Don har ga Allah ba zan iya buɗe ƙofar ba tsoro nake ji ina ganin da na buɗe zai cafko ni ba da ni ba gaɗa a kabari.

“To ki duba window falo ko akwai ta inda za ki miƙo min.”

Na fita zuwa falon na gama dubawa ta ba ta inda zan mika mishi “Ki buɗe ƙofar nan Bilkisu.” Na buga kafa ni ba zan buɗe ba.”ya
“Wai so kike Aunty ta ji ta san sa’adda na dawo.”

Na ce “To ka haƙura da keyn.”

In haƙura in kwana ina? Na tura baki muka ci gaba da tsayuwa can na tuna window kitchen akwai inda ake budewa na faɗa mishi ya wuce can ni ma na tafi na bude yana zagayowa na miƙa mashi na rufe window na koma daki na kwanta.

Washegari wuni na yi kan tunanin abin da zan tanadar ma Gwoggona na tarba, ko makaranta na kudurta ba zan je ba ranar da za ta zo.

Sai dai tun safe ranar da za ta zon ta kira ni ta ce ba za ta samu zuwa ba don da daddare Rahina ta fadi ta karye a ƙafa. Na yi ta salati ina jimami sai yamma na kira Rahinan na gaishe ta, dole murnata ta koma ciki.

Ranar asabar na dawo lesson Maman su Ahmad ta ce za mu fita dubiya asibiti na ce mata to na shirya muka tafi ba mu jima a asibitin ba muka tafi unguwar Sunusi wani tafkeken gida ta shigar da motarta ba mu haɗu da kowa ba har muka shiga cikin gidan, kofar wani falo ta shiga na bi bayanta wani babban mutum ne ke zaune shi kadai ganin ta ya yi murmushi ke ce tafe Jimmai ta ce “E yaya. Suka gaisa ni ma na gaishe shi ya ce “Ina kika samo yarinya? Ta ce “Ɗiyar dan’uwan Alh ce.”

Suka ci-gaba da hirar su ina sauraren su mun kusa awa guda ta ce za mu tafi ya ce “Kin shiga ciki ne? Nan da nan fuskarta ta canza “Ban shiga ba yaya.” “To ku shiga Hajiyar na nan.”
Ta ce “To.” Muka fito a hanya muka haɗu da wata mata kamar dole Haj Jimmai Maman Ahmad ta ce mata ina wuni? Ita ma a daƙile ta amsa na gaishe ta ni ma muka wuce ta shige falon da muka fito.

Zuwa wurin motar muka shiga ta tayar da ita muka bar gidan.

Sati guda da zuwan mu na ji ta tana waya a yadda na fahimci wayar ta ta Yayan nan nata da muka je gidan shi ya kira ta ya ce mata yana so na ita kuma tana faɗa ma waccan ko da take da kudiri in auri Najib haka ma za ta so in auri yayanta don ta yi amfani da ni ta saita matarsa da tun ranar da muka je na gane ba su jituwa.

Ko da ba ta min maganar ba na fahimci shi yayan nata shi ne na taɓa ji ta ce shi ya riƙe ta na rasa wace irin kidahuma matar nan ta ɗauke ni amma ina jiran ta ta zo min da zancen in ta kama sai in tattara in bar musu gidan su tunda zaman gidan ya sa take min abin da take yin.

Sai dai kodayaushe zai kira ta a waya sai ta miƙo min ta ce mu gaisa haka zai ta tambaya ta ya karatu.

Sai da muka zana Jamb wadda na samu nasara 180 na samu muka yi ta murna ni da Zainab har su Asma’u na taya mu.
WAEC ce sai ana saura kwanaki arba’in bikin su Zainab muka fara don haka ni ana ta shirin biki ina fama da fargaba Zainab na ta faɗa min ba fa wani abin damuwa sai da aka fara na ga hakan.

Ranar da muka yi maths ban shigo da wuri ba na shigo a gajiye duk da haka na ƙudurta sai na shiga na gaida Mama na ga Zainab wadda ko jiya ban gan ta ba.

Ina cire takalmana a bayan kujéra na ji muryar Ihsan tana faɗin “Baba ya iya zaɓe sai dai ta yi ƙiba.”

Rabi’ah ta karɓe wayar hannunta ta ce “Tana da kyau amma Aunty Bilkisu ta fi ta haɗuwa Baba ya kwafsa wa ya Najib ta yi ƙiba.”

<< Mutum Da Kaddararsa 21Mutum Da Kaddararsa 23 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.