Skip to content
Part 23 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Gabana na ji ya buga na dai ƙarasa cirewa na shiga falon sai na ga duk sun yi tsuru-tsuru suna duba na.

Mama na fara gaidawa ta ce “Kin yi wuyar gani karatu ya ɓoye ki Bilkisu.” Na yi murmushi ta ce “Allah ya taimaka ya bada saa.”

Na ce “Amin.”

Na fita, har na haura sama ina tunanin maganar yaran wa kenan Baba ya zaɓa wa Najib? Da na samu Zainab har muka gama zantukan mu ina ta jira ko za ta yi min zancen na ji shiru sai da na fito ta raka ni take cewa

“Kun yi sabuwar baby su Billy.” Na ce “Da gaske Aunty ta haihu Zainab?

Ta yi ɗan murmushi “Allah kina fita ba jimawa suka wuce Hospital.”

Ta koma na shige kai tsaye bedroom ɗin Maman Ahmad na wuce, tana kwance babyn na gefen ta na kama fara’a na ce “Sannu Aunty.”

Ta yi ɗan murmushi “Yawwa Bilkisu.”

Na kai zaune bakin gadon na dauko babyn, ita ma kamar ta ɗaya da su Ahmad.

Na gama yi mata barka wata doguwar mata ta shigo da ɗan kaskon turaren wuta Maman Ahmad ta ce mata “Sannu Aunty na gaishe ta ta ajiye kaskon sai ta fita, Maman Ahmad ta nuna min dauko turaren wuta na ɗauko na sanya zan fita ta ce “Zauna Bilkisu.”

Na dawo na zauna wayarta ta miƙo min na karɓa ban ga komai ba sai hoton wata budurwa kyakkyawa ce fara sai dai tana da jiki, an ɗauki hoton ne a wani ƙayataccen falo.
Na gama gani na miƙa mata, ba ta amsa ba ta ce “Ki ci gaba da dubawa.” Dubawar na cigaba duk hotunan ta ne a wurare daban-daban kana ganin ta kasan yar madara ce rarrafen carpet.

Miƙa mata na yi don wani tunani da na ji ya shige ni ta yi murmushi “Wannan da kika gani Jalila kenan ɗiyar Alh Idi ɗan sarai, mai kamfanonin mai na Ɗan sarai Petroleum, ita ce kuma Alh suka yi magana da mahaifinta za su hada su aure da Najib, har sun yanke rana watanni shida masu zuwa.

Wani irin abu na ji ya taɓa zuciyata duk da nasan ba son Najib nake ba.

Na haɗiyi wani miyau ba shiri sai na fuskance ta jin ta ci gaba da magana “Na faɗi ma Alh akwai soyayya tsakanin ki da Najib na kuma yi iya kokari na ya saurari maganar amma bai yarda da hakan ba, shi ne na ga tunda bai yarda da hadin ki da Najib ba akwai yayana da muka je gidan shi da ke tun ranar da muka je ya ce min yana son ki, daga Alh bai yarda da hadin ki da ɗan shi ba, ina so ki amince da yayana duk yaran nan da za su yi aure ba wadda za ta fi ki jin daɗi zai lallaɓa ki ya tarairaye ki saboda shi ba yaro ba ne.”

Ta yi shiru tana duba na jin ban ce komai ba sai ta ce “Ba ki yi magana ba?

Na gyara zama “Ki bani lokaci zan yi tunani.”
Ta yi wani murmushi da na rasa fassarar shi.

“Ba laifi.”

Na miƙe na bar dakin ba abin da nake so irin in keɓe in yi tunani don haka ina faɗawa dakin kwanciya na yi na dunƙule wuri guda wani sabon yanayi na ji ya shige ni “Najib zai auri wata. Ji na yi ina son auren shi ina sha’awar kasancewa tare da shi.

Baba ya ƙi yarda da haɗi na da ɗan shi, ya zabo ma shi wadda take daidai ajin shi ba ni ba da ya san ba kowa ba ce.

Ita kuma waccan matar ban da na san ɗayar fuskar ta ta da sai in ce ita ce mai sona har tana ƙoƙarin Najib ya aure ni.

Na share hawaye na tashi na shiga na yi wanka ban sallah don haka mai kawai da hoda na murza sai turare da na fesa na sanya wasu riga da wando na sanyi saboda sanyi da garin ya ɗauka kasantuwar hadari da ya haɗu sai ya wuce ba tare da an yi ruwa ba hakan ya saukar da wani irin sanyi mai ratsa ƙashi.

Ahmad ya shigo ya ce Maman su na kira na. Wani siririn gyale na rufe kaina da shi sai na fito, Maman Ahmad ta fito Tea ta umarce ni in haɗa mata na haɗo na kawo mata kallo suke da matar da ta kira Aunty, ta ce in yi wa su Ahmad wanka da na yi musu kira na ta yi na fito Najib ya shigo ta ce in duba fridge farfesun da na yi da safe in ɗumama in kawo mishi na juya zuwa kitchen ɗin na kawo mishi har da ruwa yana cewa in miƙo mishi remote na yi banza da shi na shige abuna.

Kwanciya kawai na yi duk da ba barci zan yi ba don kwata-kwata ban jin shi. Muryar Maman Ahmad na ji tana kiran sunana na miƙe na fita ba Najib sai su biyu ta ce “Ki fita Najib na son magana da ke.”

Ko uwar me zai ce min na tafi ina fadi a raina, kuma saboda ban da yadda zan yi in musa mata da ba zan je ba.

Yana tsaye ya kifa kai da bango jin takuna ya waiwayo a hankali “Bilkisu.” Ya kira sunana na amsa a hankali “Kin ji labarin zan yi aure ko? Wani haushi na ji da ya sa na yi saurin kallon shi “Yes Bilkisu zan yi aure kuma auren ba zai hana ni son ki ba, ina son ki kuma zan aure ki bayan na yi wannan auren.”

Kamar in ce mishi ko ba so ba? Sai dai na dube shi kawai na ce Hmmm! “Ki yarda da ni Bilkisu ina sonki kuma zan aure ki.” Wani Hmmm! Ɗin na kuma cewa don na kasa cewa komai.
Muna tsaye iska na kaɗa mu sanyi na ratsa jikkunanmu yana maimaita min yana so na zai kuma aure ni. Ban iya ce mishi zan tafi ba sai shi ya ce min ki je ki kwanta Bilkisu.

Kamar wata ja ni talau haka na juya, ba kowa su Maman Ahmad sun tashi sai na kashe komai narufe kofa na wuce daki na kwanta lamo wayata da ke kusa da ni ta dauki ƙara Najib ɗin ne dai ke ƙara jaddada min yana so na mun dade har sai da na ji barci ya fara cin karfin idanuna na mishi sallama ina wurgar da wayar barci na ɗauke ni.

Da safe da zan tafi dakin Jarabawa shi ya kai ni, da na dawo na samu Mamin nan ta Abuja ta zo karɓar akwatunan su Zainab da za a kawo a yammacin ranar.

Kira na ta yi har gaban ta ta sanya ni jikinta tana faɗin “Ga ya ta ga ya ta.” Ta yi min addu’a sosai game da karatuna.

Zuwa yamma kuwa sai ga masu kawo akwatin na Khadijah aka fara kawowa kafin na Zainab, sun sha kaya kam ba ƙarya musamman Zainab mai set biyu.

Da masu ganin kayan suka tafi kowa ya kama gaban shi ni Mama ta sanya in kwashe akwatunan in kai wani daki da ta ba ni key ɗinsa na fara Najib ya shigo har kuma na gaba jide su yana bi na da kallo.

Da na gama zan wuce shi ma ya mike ya bi baya na sai da na kusa shigewa ya yi wani ɗan fito na waiwayo ya yafuto ni a inda nake na tsaya cak sai ya ƙaraso “Fita zan yi baby ki zo mu je ke ma ki zaɓo kayan bikin kin ga an kawo ma ƙawarki.”

Na ɗan rufe ido sai na buɗe su akan shi “A’a ba inda zan bi ka, bari in je Aunty na kira na a waya.”

Na wuce.

Da daddare ma ina yi ma Maman su Ahmad aiki ya kira wayata “Wai in zo in karɓi kayan bikin.” Na ce “Ina zuwa.”

Da sauri na kammala aikin sai na fito amma ban gan shi ba na kira na ce yana ina? Wai yana dakin shi in zo mana har da “Haba baby ba ki taɓa zuwa ɗakina ba.”

Na ce “Ba zan zo dakinka ba zan koma ciki.”
Kar ki koma ki jira ni.”

Ina tsaye ya fito janye da wata trolly ya iso gabana ya tsaya sai ya miƙo min na yi godiya sai na koma ɗaki.

Sai da zan kwanta na buɗe suturu ne na gani na faɗa kala bakwai sai mayafai da jaka da takalma.

Ni kadai na yi ta yaba kyan kayan.

Da muka yi waya ya ce sun yi na ce E. Ya ce yaushe za mu fita in sawo sauran kayan kwalliyar su agogo da su sarka da yankunne na ce a’a ba zan fita ba sai ga su ya sawo ya kawo min.

Maman Ahmad ta bani kaya kala uku ta ce in ji Baba na kwalliyar biki ta haɗa ni da direba muka je na kai ɗinki har da na ta.

Ana gama shan sunan Maman Ahmad aka shiga hidimar biki. Baƙi sun cika gidan don ma da dayan gidan na kannen shi nan ɗin ma baki masu yawa ne suka sauka.

Part ɗin Maman Ahmad dangin Baba ne suka sauka hakan ya ba ni dama na koma wurin su Zainab muka yi ta sha’anin mu.

Ana gobe ɗaurin aure Mamin Abuja ta duk kuma da cikowar gidan sai da ta sa aka nemo ni na gaishe ta.

Najib kam ya fitar da ni kunya suturun da ya sawo min masu daraja ne da na shige cikin yammata wayayyu masu ji da kanau kuma sai an kalli kwalliyata.

Gwoggo Maryama ranar ɗaurin aure ta iso da hantsi.

Daga gidan yar’uwar Maman su Zainab da muke zaune tana yi min waya na taho da murnata.

Keɓewa muka yi muna ta hira sai shi ma Baba da iyalansa albarka take yi wai sun yi min riƙo na ƙwarai daga ganin yadda na koma ban tafi ba sai da ƙawar Zainab Hanan Aliyu ta yi ta kira na.

Ana daura aure anguna suka kawo motoci aka kwaso mu, gidan ba masaka tsinke ana ta cin abinci a kujerun da aka shirya a harabar gidan ma’aikatan hotel din da aka ba kwangilar abincin ke ta rabo masu rawa na gaban masu buga musu kida da waka suna yi.

Ana ta kiran amare ni ina ta baza ido da ratsa cikin jama’a inda zan ga Gwoggona, da na gan ta na nufi wurin ta da na zauna na ce “Kun ci abinci Gwoggo? Ta amsa “Mun ci Bilkisu.” Muna ta hira matar ƙanen Baba da wata mata na hango riƙe da wata yarinya da ke ta yauƙi kamar karkashi, ban san wace ce ba sai da suka iso kusa da mu inda wata ƙanwar maman su ke zaune kusa da Gwoggo kafin zuwa na suna hira wai ita ce wadda Najib zai aura shi ne ake bi ana nuna wa dangi ita.

Wani iri na ji a zuciyata na yi shiru daga hirar da muke har Gwoggo na tambaya ta lafiya na yi shiru, na ce lafiya lau. Wayata da aka kira ta ce ce ni na tashi na bar wurin buri na in keɓe sai dai ban samu damar haka ba shirin tafiya Dinner ake ta yi so samu kar in je amma fa bikin Zainab ne, kwalliya sosai muka sha, ƙarshe muka je wurin ni da Hanan Aliyu, Najib ba bulayin neman da bai min ba amma bai gan nin ba sai a can ya kuma tsallake abokansa da suka shiga wurin tare ya zo wurin mu, ya ce idan an tashi tare za mu tafi na ce to.

Da aka tashi na gayyaci Hanan Aliyu muka tafi tare a unguwar Rimi GRA aka ajiye Zainab, muna isa ta sauka ta yi na ta wurin ya tsayar da ni maganar dai kenan son da yake min yake faɗa min har ƙafafuwana suka yi sanyi don na fita motar ina tsaye na ce zan shiga ciki barci nake ji.

Ba kowa yammatan duk suna tare da samarin su Zainab ɗin ma tana wurin angonta da na wuce su tana cewa in zo in ci nama wai yunwa take ji ya kawo mata Youghout din da take so na ɗauki ɗaya na shige na ce barci nake ji na kwanta shiru ina tuna budurwar da na gani Baba ya zaɓa wa Najib ya bar ni saboda ni ba ɗiyar kowa ba ce da ma yanzu kwarya ta bi kwarya ake don son zuciya irin tawa na kasa ganin banbancin da ke tsakanin mu aure fa hudu da saurayi ɗanye shakaf.

Da ciwon abin barci ya kwashe ni.

Da safe na so in koma gida ko don Gwoggo Maryama Zainab ta hana ni ta ce in taya ta zama sai da aka yi buɗar kai ban tsaya an yi sayen baki ba na yi mata sallama kuka muka sha na rabuwa sai da Gwoggona ta janye ni sai da muka biya gidan Khadija sannan muka wuce gida.

Tare da ita muka kwana da safe da ta shirya za ta tafi ta ce tana son gano Amir, ni na raka ta sai dai ban sauka a keke napep din da ta kai mu ba daga nesa na nuna mata gidan na kuma ba ta abin da na saya mishi ba ta jima ba ta zo muka tafi sai da na kai ta kawo ta shiga mota na ciro yan kuɗaɗen da nake da su na ba ta ta amsa da ƙyar sai na juyo.

A ranar baƙi suka yi ta tafiya wasu kuma sai da suka ƙara kwana.

<< Mutum Da Kaddararsa 22Mutum Da Kaddararsa 24 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×