Kowa ya watse aka gyara gidan muka koma rayuwarmu.
Sati guda da tashin bikin na shirya zuwa gidan Zainab, wuni na yi mata har kusan la'asar sai ga Najib shigowa ya yi aka ɗan taɓa hira da shi sai ya dube ni "Na je neman ki Aunty ta ce min kin tafi gidan Zainab shi ne na biyo ki in kai ki gida." Na kalle shi "Kasuwar fa? Ya ce "Yau Sunday ban dade ba na dawo."
Suka ɗan taɓa hira da Najib ɗin Zainab da Zainab ɗin ya ce min "Tashi mu tafi." Ban musa mishi. . .