Skip to content
Part 30 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Wani yammaci ina daki zaune Aunty Farha da ban san san da ta shigo gidan ba ta turo ƙofa “Sarkin zaman daki fito ki min rakiya.” Abin da ta fara ce min kenan da shigowar ta.”

Da murmushi na ce “Barka da zuwa Aunty Farha.”

Ta dubi agogon da ke daure a hannunta “Tashi Nana mu tafi na mike ina isa gaban mirror sai ta fita tana faɗin in yi sauri.

Ban ɓata lokaci ba na shirya kayan jikina na sauya bayan na murza hoda na fesa turare.

Ina fitowa sallama na yi wa Mami na bi bayan Aunty Farha da har ta fara tafiya inda ta ajiye motarta muka nufa ta sa key ta buɗe muka shiga sai da muka yi nisa take ce min Auntynta ce za ta aurar da yara biyu.

Don yayarta da suke ya’ya mata ita ta riƙe ta anan Abuja tun tana karama,
ita ce take auren wani ƙusan gwamnati, sun kuma yi karatu tare da ya Safwan.

Tunanin da na faɗa ya sa sama sama nake amsa hirar da take min.

A hankali na ɗaga kai na dubi ƙaton board din da ke kafe inda Farha ta tsaya. *ZAHRA SALLON* Na furta a hankali. Rufe motar muka yi bayan mun fito “Bismillah mu je Farha ta faɗi tana yin gaba na bi bayanta, wurin akwai mutane sai dai ma’aikata uku suka nufo mu daga yadda suke mana barka da zuwa na gane wurin wurin zuwan Farhan ne. Suka ba mu wurin zama amma sai ta ce ita kam tana son ganin Madam mai wurin kenan.

Ɗaya daga cikin su ta shiga ta shaida mata kafin ta fito ta yi mana jagora.
Cikin mutunci muka gaisa da matar da ta fara shiga shekarunta na girma.

Farha ta tambaye ta sun shigo da sababbin kaya za a yi bikin ƙannenta ne? Da kanta Madam ɗin ta miƙe ta cikin shagon suka ɓulla ta wata yar ƙofa zuwa wani ƙawataccan shago mai zaman kanshi, kayayyaki ne ko ta ina wasu a rarrataye wasu a cikin Closets
ɗin gilashi suturu dai na ke ce raini.
Wurin zama ta bamu amma ni kaɗai na zauna ita Aunty Farha zaɓe ta shiga yi Madam ɗin na taya ta ƙarshe aka zuzzuba kayan cikin manyan ledoji masu ɗauke da tambarin *ZAHRA SALLON* Sai sannan Farha ta juyo wurina

Daga nan wata kofar muka ɓulla nan kuma kayan shafe shafe ne ta zazzaɓa ta zaɓo min turare da ta sa na karɓa dole. Sai da aka yi mata gyaran jiki da kai don ta ce ya Safwan ya je Warri jiya yau zai dawo, ba mu bar wurin ba sai yamma liƙis.

Sauke ni kawai ta yi da isar mu ba ta shiga ba ta wuce.

Zaune na samu Mami tana cin abinci na zauna gefen ta na nuna mata turaren da Aunty Farha ta saya min murmushin su na manya ta yi ta ce “Kin gode.

Da bikin gidan su Aunty Farha ya zo tare na je da Mami da na ga gidan da Aunty Farha ta tashi na yayarta sai na gasgata lallai za ta kalli kowa ba kowa ba.

Kwanaki uku bayan nan da safe tun kafin in fito Mami ta shigo take shaida min Aunty Farha ba lafiya cikin dare ya Safwan ya kira ta suna asibiti yanzu haka, can suka kwana.

Muka yi jimami ni da ita zuwa tara muka fita zuwa asibitin da take kwance.

Mun same ta ta samu sauƙi, anan muka ji ashe ciki ne mun goce da murna likitan ya ce so samu su riƙe ta saboda lalurar mahaifarta gudun kar a rasa cikin, daga ita har mijin suka gwada rashin amincewar su, don haka aka gindaya musu sharuɗɗan da za su kiyaye.

Anan Aunty Farha ta roƙi Mami wai a bata ni in je in zauna da ita zan fi taimaka mata.
Mami ta jinjina lamarin daga bisani ta ce a dai kira Daddy a nemi amincewar shi.

Daddy ana kiran shi ya ce a’a wani daɗi na ji ya kama ni da jin bai yarda ba.

Satin ta guda aka sallame ta maimakon su wuce gida gidan Mami suka yo wai Aunty Farha ta zo roƙon Daddy da kanta, sai dai suka gaji da zama suka tafi don ana ta kiran ta ta yi baƙi. Nan suka bar Afnan Mami ta ce su kyale ta saboda lalurar uwar.

Ta waya ta kira shi ta roƙe shi ya amince ya sa a ka kira ni ina daki a zaune, na same su kamar yadda na bar su na shiga daki.
Ya ce Farha ta kira ni ta roƙe ni in bar ki ki je gidan su ki taimaka mata don da Safwan ne ba zan taɓa amincewa ba amma ita ba zan iya ce mata a’a ba tunda har ta tambayan da kanta.”

Ni ma dai saboda ba yadda zan yi na amsa umarnin Daddy na wuce na bar su yana sa ma ya Safwan dokoki na zama na a gidan na shi shi dai amsawa kawai yake don ba yadda zai yi Farha ta ja mishi.

Jan jiki na yi ta yi wurin haɗa kayan har Mami ta zo ta same ni nan fa na yi da jiki na gama na rufe jakar sai wata ƙarama da na haɗa na sanya ƙananan kayan amfanina.

Ina ɗauke da jakar Mami na riƙe min ƙaramar muka fito kamar munafuka haka na bi bayan ya Safwan Boot ya buɗe na jefa jakar.

A cikin motar ma kamar ruwa ya ci ni yayin da yake tuƙin shi cikin kwanciyar hankali.

Horn da ya yi mai gadin gidan na shi ya wangale get muka shiga tsararren gidan na shi.

Duk da zuwa na Abuja ban san iya gidajen masu duniyar da na raka Mami ba to gidan ya Safwan yana cikin gidajen da suka tafi da imanina, don ko kusa ko alama ba a ji tausayin Naira ba wurin tsara tamfatsetsen gidan

Mun taka tattausan Grass carpet ɗinda ke malale harabar gidan, furannin da ke gidan suna feso ruwa kaɗan kaɗansaboda da yammacin an yi ruwa ga ƙamshin su ya cika wurin,haske ya ƙawata harabar gidan.

Ina biye bayan shi har ya danna door bell jim kadan wata mata mata da shekarunta ba za su haura talatin da biyar zuwa da bakwai ba ta buɗe.
Cikin tsantsar girmamawa ta soma mishi barka da zuwa kafin ni ma ta gaishe ni ta karɓi jakata.

Aunty Farha na fara hangowa cikin hamshaƙin falon na su ta yi rashe rashe kujerar kusa da ita na ƙarasa na zauna ina gaishe ta da jiki, ta amsa cikin yanayinta na fara’a.

Kafin ta mayar da hankalinta kan mijinta gabaɗaya ta narke tana fadi mishi tana so ta tashi tana so ta yi wanka ga shi bai dawo ba.

Murmushin gefen baki ya yi ya ce “Ai ni kuma na gama nawa ga me ma ki duk waɗannan nan na samu nasarar karɓo ta wurin Daddy.

Ƙafarta ta buga tana faɗin ba za ta yarda ba kamar ba ya Safwan ba ya ɗaga mata hannuwansa da rarrashin ta bari kar wani abu ya samu cikin.

Daga inda nake na dage baki kamar lefen sakara ina kallon ikon Allah sai ga ni kawai na yi ya daga ta cak ya yi part ɗinshi da ita.

Ina nan zaune wucewar a ƙalla mintuna arba’in na dafe kuncina da hannuna na zuba wa TV ido, a zahiri za ka sha kallon nake amma a baɗini da na sanin zuwa na gidan nake haka za a mayar da ni wata sakarai randar waje.

Takun tafiya da na ji ya sa ni daga kaina Aunty Farha ce ta samu wuri ta zauna shi ma ya fito ita ya duba “Ya kika bar baƙuwar taki anan? Ya tambaye ta “Oh ta fadi sai ta miƙe wata hanya da ta bi na tashi na bi ta ko da ba ta kira ni ba sai don na gaji da zaman muka ji muryarsa.

“Ina za ki kai ta?

Ta waiwayo tana duban shi “Ɗakin nan na kusa da na Larai.”
Ya ce “A’a ya za ta zo don ke kuma ki kai ta can kusa da ke za ki ajiye ta. Ɗan jim ta yi a tsaye ya kuma cewa “Ɗayan bed room ɗinki za ki kai ta.”

Kamar ta yi magana sai kuma ta juya “Ok mu je muka nufi ƙofar da za ta kai ka ɗakunan barcin nata.

Sai da muka wuce wani madaidaicin falo sannan muka samu dakin farko ba shi ta kai ni ba wani can a karshen falon ta buɗe sai ta juya na shiga ciki.

Sallah na fara yi sai na ci gaba da zama har na ji barci na gyara na kwanta.

Barci na yi mai cike da mafarke mafarke da na farka na rasa wace irin fassara zan yi musu.

Ko da na yi sallah zama na na yi a dakin ina karatun Alƙur’ani tare da istigfari na cika da salatin annabi.

Kiran Aunty Farha ya shigo wayata na ɗauka na soma gaishe ta da tambayar jiki ta ce ta ji sauƙi na ce “Yaushe za ki fita zuwa Sch na ce sai 10am ta ce

“Ok za ki gyara min daki ki wanke min bathroom sai ki tara min ruwan wanka.”

Na ce “To.” Sai na miƙe na fita dakin da bathroom ɗin na fara na kuma tara mata ruwan wanka na fito na gyara gadon ta shigo ta wuce yin wankan kafin ta fito na goge tsakar ɗakin, ta fito ta zauna yin kwalliya ta ba ni umarnin kayan da zan ɗauko mata.

Bisa gado na ajiye mata komai sai da ta shirya na fita zuwa nawa dakin da aka sauke ni na yi nawa wankan na shirya na zauna ina jira a kira ni in karya in tafi makaranta amma shiru da na ga takwas da rabi ta yi sai na sanya hijab dogo na fito suna zaune suna karyawa Farha da mijinta, na gaishe shi zan sa kai in fita ya ce.

“Kin ci abinci ne?

Na ce “A’a.” Ya ce “Zo ki zauna nan.”

“To.” Na ce a raina ina zarar ido kamar na ci tsire bashi sai na ji muryarta ta cece ni “Ta dai shiga kitchen Dear, Larai na ciki.”

Kitchen ɗin na shiga mai aikin su Larai da nake ce ma Iya Larai ta ba ni abin karyawa, na ci a ciki na fito a gurguje gudun makara ya ce “Direban da ke kai Afnan makaranta zai sauke ni sai in faɗa mishi time ɗin da zai koma ya dauko ni.”

Na ce na gode. Na fice cikin takaicin rabo ni da gidan Mamina mai so na da tattalina aka kawo ni nan.

Da na dawo part ɗin mai gidan ta kai ni ta ce in gyara kan dole cike da ganin rashin dacewar hakan da kuma tsoron mai wurin da nake ji kamar yana kallona musamman wani hoton shi da ke kafe inda duk na juya sai in ga kamar shi ne ke kallon.

Na dai samu na gyara na fito tana kishingiɗe cikin cushion ta dosa sa ni aiki ni ce matsa mata yan ƙafafuwanta, haɗo min fruit salad da na lura tana son shi ko kuma cikin ya haɗa su oho mata, ɗauko min wannan, miƙo min wancan duk ta bi ta gajiyar da ni ban samu sukuni ba sai da mijinta ya dawo ya kuma shirya ya fita wurin wasannin shi .

Na koma daki ina tunanin ƙaddarar rayuwata tare da tuna Babana.

Ana yi mana hutu kuma ko ta gama bed rest din ko ba ta gama ba zan tafiyata Taraba ne.

Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya min tare da Farha da na kai maƙura wurin gundura da zama da ita saboda baƙin sa aikinta.7

Girki ne dai ba ta sanya ni wannan sai mai aikin ta ita ke ganin ta ta rayuwar, ta sa ta wannan idan ta yi ta kawo ta ce ba shi ba wani ta koma ta yo ta kawo.

Haka za ta wuni ita ma ni sauƙi na makaranta da nake fita.

Ranar wata Laraba muna kitchen da safe ni da Iya Larai, ni abin da zan sanya ma cikina in wuce Sch nake nema ita kuma tana haɗawa masu gidan abin karyawa.

Ta ƙwala mata kira ta fita cikin sauri daga inda nake ina ji tana faɗa mata mai gidan zai yi baƙi su huɗu ne don haka a shirya musu abinci kamar kala huɗu. Ina ji tana lissafo mata na yi zuru ina al’ajabi Iya Larai ta ga ta kanta abu hudu duk ita daya ga mura tana bala’in damun ta.

Na idasa shanye sauran Tea na na dire cup ɗin, da na ɗauko hijab ɗi ta da na cire lokacin da na shigo na sanya zan fita kiran wata Course mate ɗi na ya shigo Ruƙayya Babangida muna mutunci sosai da ita wata hand out da muka yi zan fito mata da ita ta yi min tuni in zo mata da ita gobe saboda malamar da za ta ɗauke mu lacture yau ta sanar ba za ta samu zuwa ba.

Na ce “Ni kiran ki taimakona ya yi da yanzu zan wuce.

Ta ce “Ba ki shiga Whatsapp ba ne an sanar a grp din yan department ɗinmu.

Muka ɗan yi magana kafin muka yi sallama.

Na fita daga kitchen ɗin Aunty Farha ba ta falo na san tana dakinta ko na mai gidan, na shige nawa dakin na ruho kafin hayyata ta san ina gidan, layin Ummu hani na yi ta nema amma sam wayarta a kashe take tun da ta tafi ban same ta ba, na yi addu’ar Allah ya sa lafiya na gyara kwanciya.

Barcin awa guda na yi na tashi na fita zuwa kitchen don in ga halin da Iya Larai ke ciki mai girki kala huɗu, ga na rana na gida da za ta yi.

Har na shiga kitchen ɗin ban ga Aunty Farha ba na samu Iya Larai aiki ya kacame mata ga girkin rana ta ɗora ga namomi ta fiddo dan girkin nasu duk nama ne za a dafa musu kamar wasu kuraye.

Ta rasa wane za ta fara don an ce ta yi fried rise ta yi pepper chicken ta soya taliya.

Na ce “Iya Larai ya murar? Ta ce “Sauki.”
Na ce “Allah ya ƙara sauƙi bari in taimaka miki.”

Ta ce “Na kuwa gode miki Allah ya ba ki miji na ƙwarai.”

A raina na amsa Amin na matsa kayan cikin da ta riga ta wanke na fara ɗora farfesun shi sannan na juya wurin pepper chicken shi ya ɗauke ni tsawon lokaci har aka yi Azahar.

<< Mutum Da Kaddararsa 29Mutum Da Kaddararsa 31 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×