Skip to content
Part 31 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Iya Larai ta kammala girkinta na fita na je na yi sallar.

Yau dai giwar ya Safwan ba ta jin fitowa na raya a raina.

Sai dai ina fitowa da na idar da sallah muka yi kaciɓis da su sun fito tana ɓata fuska na yi masu sannu na shige ina mai addu’ar kar ta ishe ni da masifaffen kiran ta.

Iya Larai ta fita tana shirya ma masu gidan abinci na ce ta yi fried rise din ni zan yi farfesun kayan cikin da pepper chicken ɗin, na kuma ƙudurta ba a yin wata soyayyar taliya na san baƙin yan iyayi ne Irin masu gidan bari in yi musu dambu in ga za su ci.

Na ɗebi shinkafa na ɓarza na wanke sai na tsane ta Allah ya taimake ni na samu gyaɗa a kitchen ɗin maimakon rama ko zogale da babu sai na yi amfani da Cabbeji akwai albasa mai lawashi na haɗa haɗaɗɗen dambu da ya karaɗe ko’ina da ƙamshi ban ƙarasa ba na ji isowar bakin,

Iya Larai ta soma fitar da kayan abincin dambun na zuba karshe ta ce “Ɗan rage min in afa wannan dambu naki da ke zabga ƙamshi mai sa haɗiyar miyau.”

Na yi dan murmushi na zuba mata maimakon juye musu duka da na yi niyya.

Sai sannan na ɗebi abincin da ta yi na zauna na soma ci.

Na kusa kammalawa Aunty Farha ta ƙwala kiran sunana kamar in fashe da kuka don ban yi niyyar su ga ko inuwata ba Allah ya taimake ni ban fitowa ba lulluɓi na janyo shi daga jikin kofa da na rataye na fito.

Kallo ɗaya na yi ma inda suke na haɗe su na yi musu gaisuwa ɗaya na wuce gabanta.

“Fruit salad za ki ɗan ba ni Nana.”

Juyawa kawai na yi na koma kitchen ɗin.
Allah ya sa akwai wanda na haɗa mata a fridge ko za ta tambaya ba ta tambaya ba na ciro na kai mata, ta ce “Ki zauna mana mu yi hira.”

Na ce “A’a zan koma daki ne.” Ban koma kan abincin ba don ya riga ya gundure ni na ɗauki na mai gadi don taimakawa Iya Larai da take zaune ta dafe kai, na fita na miƙa mashi da na dawo ba Aunty Farha a falon su ma sun sun kammala sun barke da hira.

Na ce ma Iya Larai ta je ta sha magani zan yi mata wanke wanken, amma sai na yi sallar laasar.

Da na idar na fito ba su cikin falon sai dai ina shiga kitchen na ji hirar su a daidai window kitchen ɗin wanda yake a rufe amma na ciki na ganin na waje wani gajere a cikin su ya ce

“Allah S A Safana ba ka yi ba, kai shi kenan ka dinga haɗa mata iri ɗaya.”

Wani fari da ke gefe ya ce “Wai in ƙara ganin pic din yarinyar.”

Wanda ya fara magana ya miƙo mishi wayarsa, ni ma saboda son gulma na taka saɗaf-saɗaf na ɗare bisa wata drawer ina hangen wayar, hoton wata doguwar farar mace ne sai da ya kare kallo ya ce

“Zancen Ali gaskiya ne, ka dinga abu iri ɗaya?

Ya Safwan da ke tsaye rungume da hannuwansa ya ce,

“Ba za ku gane ba, na dade tare da Nafisa tun shiga ta jami’a muke tare, tare muka yi karatu da ita.

Mun shiga shekara ta uku Farha ta ɓullo, ƙaddara ta raba ni da Nafisa na auri Farha, yanzu kuma ta dawo kuma gaskiya ina son in yi aure ko don samawa Mamina farin ciki ta ga yayana da na lura ba abin da take so irin ya’ya ina tausayin Mamina.”

Wani da bai yi magana ba ya ce “Ni fa ƙanwar nan taka da ta fito kwanaki da na gan ta gidan Mami na sha kai ake ma ajiyar ta, ga kalar aure Allah ya kawo maka har gida, ni tunda ba ka ciki ina so A A Safana, ka je ka yi ta fama da kalar taliyar.”

Suka kwashe da dariya wanda bai magana ba a cikin su ya ce “Ni ma fa na ƙyasa “A A Safana.”

A hankali na sauko da yan ƙafafuna na sauke hannu da na dafe ƙirji tun jin za a yi wa Aunty Farha amarya, wai kuma suna tallata wa ya Safwan ni A A Safana, Safwan Abdullahi Safana, na fadi a hankali sunan kuwa ya haɗe kamar yadda mai shi ya haɗe, ya dace da shi.

Kitchen ɗin kawai na bari na wuce ɗaki na zauna bakin gado sai da na gama jimami na na janyo wayata Ummu hani na duba da har yau ba ɗuriyar ta a whatsapp ko in sa ran za ta kira ni.
Na yi addu’ar Allah ya sa tana lafiya na kishingiɗa cikin tunani.

Sai da na daidaita kaina na fito zuwa kitchen don yin wanke wanken ba ya Safwan da abokansa na yi na gama ina goge hannu Iya Larai ta shigo na ce

“A ya kuma kika fito Iya Larai ya kan?
Ta ce “Na ji sauƙi ne, sannu da aiki Allah ya ba ki miji na ƙwarai.

Na yi murmushi ina mai jin daɗin addu’arta da take min duk san da na taimake ta da wani aikin, girki ne dai ban taɓa sa mata hannu ba sai yau.

“Alh yana kiran ki.”

Na dube ta sanin wa take kira Alh, ina juya kalmar yana kirana.

Na ɗaga kai Sai na ce mata ina zuwa, ta fita ni ma na fito can kan wata kujera yake zaune na isa na tsaya gefen shi na ce “Ga ni.”

Ba tare da ya ɗago ba ya ce “Wa ya yi wannan girkin? Na dubi abin da yake nuna min Flacks ɗin da a ka zuba masu dambu ne ba komai ciki sun cinye.

Na ce “Ni ce.” “Ok ina son flate daya.”
Na amsa sai na juya na fara aikin ina tuna gajiyar da na yi tun hantsi nake tsaye, da na ɗaura zamana na yi ina jiran ya turaro. Iya Larai ta shigo wanke wanken kayan da suka yi amfani da su da ban ɗauko ba za ta yi

“Allah ya sa kin sanya har Maman Afnan kar ta ce za ta ci wani abu.”

Na ce “Zai isa har ita ɗin in za ta ci.”
Ta ce “Ai kam wannan dambu naki mai daɗi ci za ta yi, shi fa baƙin suka cinye tas suka bar fried rice ɗin.”

Na dubi Flacks ɗin da take nuna min Ita kin ga sun saba da cin ta shi kuwa na marmari ne.”
“Ai duk namomin da kika yi sun cinye.”
Ta fadi su ma tana nuna min

Na ce “Suna da yawa ai.”
Rage wutar na yi na fita na yi sallah sai da na yi Isha’i na ƙara turara shi na kwashe na kai musu inda suke cin abinci na ajiye na shige ɗaki.

Da safe da na yi shirin makaranta na ayyana idan aka tashi gidan Mami zan yi tafiyata.
Da muka taho da direban na fadi mishi inda zai kai ni ina ganin gidan wani farin ciki ya lulluɓe ni musamman da na shiga na tarar da Mami ita ma farin ciki ba kaɗan ba ta yi da ganina, na shiga ɗakina na sha barcina da na tashi na shiga kitchen anan Mami ta same ni ganin ina kokarin girki ta ce “Yamma ta yi maimakon a yi shirin komawa gida an shiga kitchen.”

Ban yi magana ba sai fuska da na ɓata, “To akwai matsala a can ɗin kenan?
Na girgiza kai ” Ba matsalar komai ni na dawo Mami.”

Za ta yi magana wayarta ta yi ƙara ta daga Aunty Farha ce ta tambayi Mami na zo har yanzu ban shigo ba daga makaranta.

Mami ta ce gani nan na ce na dawo gida me ta ce wa Mamin oho ta dai sauke wayar ta fita ta bar ni ina girkina.

Tsire na yi mana ni da Mami na haɗa mana zoɓo mai daɗi.

Na gama na haɗa komai a ƙaton tray na fito ya Safwan ya shigo sannu kawai na yi mishi na wuce tsakiyar falon na ajiye tray Mami ta fito ta idar da sallah har da hijab ɗin da ta yi sallar a jikinta na ce “Tuɓe hijab Mami, na janyo Afnan da ke biye da ita muka zauna Mami ta zauna tana faɗin “Me aka yi mana mai ƙamshi haka?

Na buɗe flate ɗin na fara yanka mana ni da Afnan ina ba ta Mami ma ta soma yanka “Ya Safwan ya ce “Ni fa Mami?

Afnan ta yafuto shi wai ya zo ya ci ban yi tunanin zai zo ya cin ba sai na ga ya taso ya zauna kusa da Mami ya fara yankar naman flate ɗinta yana ci ya ɗauki cup ɗin da ta cika da zoɓon ya kai baki sai da ya shanye ya dire cup ɗin “Wane irin drinks ne wannan Mami? Akwai daɗi yar dariya ta yi “Sai ka tambayi Bilkisu.”

Ya juyo ya dubi inda nake “Ki gama ki shirya mu wuce.”

Na sunkuyar da kaina Mami ta ce “Ai ba za ta koma gidan naku ba.” Ya ce “Saboda me Mami me aka yi mata?

Ta ce “Ta gaji ta dawo gida.”

“Haba Mamina.”

Ta ce “Kai ka yi ta kanka dama don Daddy ya baku ita ne na kyale ta.”

Ya marairaice kamar ba ya Safwan ba
“Meye a ciki Mamina don kin bar mana yarki ta taimaka mana?

Tashi na yi na shiga daki tare da Afnan na bar su.

Na ba ta wayata na kwanta kawai Mami ta shigo ta ce in zo mu tafi da ya Safwan, amma ta faɗa mishi su nemi mai masu hidimar ciki nan da sati guda ba su samo ba zan zo in taho da ke.

Na ce mata “To.” Na tashi na sanya lulluɓina muka fita tare Afnan ta yadda wayar ta yi barci.

Har gaban motar ta kawo ni na shiga raina ba daɗi. Daddy ba ya nan ya je Safana.

A mota ya faɗa min daga yau in riƙa mishi abincin da zai ci da daddare.

Ban wani zauna a falon ba da Aunty Farha ke ta taɓara tun shigowar mu wai cikin jikinta ya ishe ta shi kuma ya sanya mata ido kurum.

Da na shiga daki chatting muka yi da Hassan wanda tun tafiyar shi ba mu faye waya ba sai dai chat din da shi ma ba kamar san da yana nan ba.

Tun daga ranar girkin ya Safwan ya dawo kaina don haka idan ina gidan mai wuya in zauna bayan ayyukan Aunty Farha ga girkin ya Safwan.

Ranar da ya zam kwana shida daga cikin kwanaki bakwai da Mami ta dibar musu su nemi mai aiki ko ta zo ta tafi da ni.
Ina daki da daddare muna chatting da Hassan kawai sai ƙarar fashewar abu na ji ƙirjina ya doka na ƙara saurarawa wata ƙarar da ta fi ta farko ta kara shiga kunnena sai na miƙe tsaye ina salati sai ƙara da ihu da suka sa na sandare a tsaye.

Ina nan ina jin abin na daɗa kusanto ni na gane muryar aunty Farha ce kamar in buɗe ƙofa na dai fasa amma fa ihu take da kuka ba na wasa ba, ga fashe fashen ya ƙi ƙarewa can na ji shiru sai kuma aka fara buga ƙofar ɗakina na ce Waye? “Buɗe ni ne.”

Gane ya Safwan ne sai na isa na buɗe shi ne tsaye rigar shi a kece daga samanta yana dafe da hannunsa da ke zubar jini “Fito mu je hospital.” Ya ce min yana juyawa ni ma ciki na koma na sanya dogon hijab na fita.

Ba ƙaramar kaɗuwa na yi ba ganin yadda aka ci mutuncin falon duk wani abu na glass an fasa shi a falon ga aunty Farha nan yashe a ƙasa ba ta ko motsi hannunta na ta zubar jini.

Cak ya ɗaga ta ya bar falon da ita na dafa mishi baya a baya ya shimfiɗar da ita ya ce in shiga in riƙe ta na shiga na ɗora kanta bisa cinyata har sannan ba ta ko motsi sai kuma lokacin na lura da jinin da ke fita ta ƙasanta!

Yana yin parking ya fita ya shige ciki suka dawo da nurses aka gungura ta a keken ɗaukar marasa lafiya muka bi su a baya wani daki aka shigar da ita muka zauna zaman jira.

Sai da muka shafe ya kai awa biyu likitan da ya jagoranci duba ta ya fito ya yafuto ya Sadauki ya bi shi zuwa Office.

Ina nan zaune shuɗewar mintoci ya fito sai kiran sunayen Allah yake yi yana kai da kawo ina ta gyangyaɗi a zaune don barci da ya ci idona sai da aka fito da aunty Farha aka ba ta daki muka ɗunguma can barci take ta yi har lokacin.

Akwai kujeru na masu dubiya a dakin sai na bi lafiyar daya na ƙudundune cikin hijab ɗi ta, ban san ya ya Safwan ya ƙare ba sai dai na ji muryar Mami cikin kaina tana fadin “Inna lillahi wa’inna ilaihi rajiun garin ya hakan ta faru Sadauki? Ga shi an yi asarar cikin da aka samu Allah ya bayar?

Zaune na tashi ina mamakin makarar da na yi na miƙe ban cewa kowa komai ba na faɗa toilet din da ke cikin dakin.

Na fito cikin alwala dama hijab ɗi na na jikina na yi sallah, sai da na idar na gaishe da Mami da Daddy da ke tsaye hankali tashe.

Farhan ma ta farka tana zaune ta dafe hannunta da aka naɗe da bandeji ta jingina jikinta a bango tana zubar da hawaye.

Na ce mata “Sannu Aunty Farha.” Ba ta amsa ba tana ci-gaba da kukanta na koma kujerar da na kwana Mami ma ta zauna sai Daddy da Sadaukin Mami ke tsaye shi ya Safwan kallo ɗaya ka yi mishi ba za ka kuma ba don ɓacin ran da ke kwance kan fuskarsa.

Shi ma hannunsa da ke zubar jini a jiya an naɗe mishi shi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mutum Da Kaddararsa 30Mutum Da Kaddararsa 32 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×