Skip to content
Part 32 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Mai aikin Mami ta kawo abin kari. Ni dai burina in samu in tafi gida tare da Mami muka tafi na karya a can na wuce makaranta da na tashi na dawo gida Ya Safwan ya kira Mami ya ce in taho asibitin, na shirya na tafi na samu yan’uwan Aunty Farha sun zo har da Auntyn ta da ta riƙe ta, wasu mata biyu za su zauna wurin ta ya Safwan ya ce a’a gani na isa,
Suka tattara suka wuce.

Tunda yan dubiya suka natsa sai ni da ita a ɗakin, bisa kujerar nan na kwanta ina karatu aka turo ƙofa ya Safwan ne da abokansa na gaishe su na ci-gaba da karatuna, ba su jima ba suka tafi.

Ina nan zaune har barci ya fara kama ni amma na kasa haƙura in bar karatun don mun kusa fara Exam.

Aka turo ƙofar da na yi zaton likita ne ko nurses sai ya Safwan na gani na yi mishi sannu da zuwa na maida kaina kan abin da nake yi.

Kusa da gadon ya tsaya yana kallonta tana barci, wayata ta soma ƙara ganin sunan Zainab na fasa katse kiran da na yi niyya.

Samha na fara tambayarta da ta ce min har ta fara karya gwiwa za ta yi rarrafe, ta ce ya karatu? Na ce shi nake yi a taya mu addu’a za mu fara Exam. Ta yi min addu’ar fatan samun nasara,ta ɗora da gaya min Khadija ta haihu ta samu namiji, na yi murna na ce da safe zan kira ta.
Ta ce “Kin san wani abu?

Na ce “Sai kin faɗa.” “An sanya ranar Rabi’ah.”

Ido na buɗe “Dama Rabi’ah za ta yi aure shi ne ba ki taɓa faɗa min ba? Ta ce “Uhmm ki bari kawai wani yaron abokin Baba ne ya gan ta har an sa mishi rana da wata yarinya sai ta rasu, to yanzu dai wancan date ɗin shi aka sa yau saura kwana 38.”

Na kama baki “Ikon Allah su Rabi’ah an zama amarya Khadija an zama Mama, Allah ya sanya alheri, zan kira Mama da safe

Ta ce “Ki bari kawai ba wanda ya kawo ma Rabi’ah aure.”

Kukan Samha da na ji na ce me ya same ta ta ce tashi ta yi sai na ji maganar Najib, na ce “Ki rarrashe ta sai da safe.”

Na yanke kiran na kai idona kan mata da mijin da har lokacin yana tsaye ita kuma ta farka.

Na ƙudundune cikin hijab ɗi na da tun zuwa na asibitin ban taɓa zama ba ta ba.

Na rufe idona na haƙura da karatun saboda ya Safwan ban san ko yana son magana da matarsa ba.

Da yake dama ina jin barcin dandanan ya yi awon gaba da ni.

Da safe da likita ya shigo matsa mishi Aunty Farha ta yi ya sallame ta duk da hannunta har lokacin da sauran kumburi kuma naɗe yake.
Haƙuri ya bata ya ce ta bari Oga ya zo da ya Safwan ɗin ya zo kuma ya ce a’a.

Ranar ba zan shiga Sch ba karatu na zauna na yi ta yi sai washegari tun da safe ya sallame mu.
Auntynta da ta shigo lokacin ita ta ɗauke mu ni na tattara komai na kai mota ina gaba suna baya ita da Auntyn ta ta da ke ta mata faɗa “Saboda Namiji ki nemi halaka kanki, to ga shi nan kin yi ma kanki asarar cikin, kin ga yanzu sai ya yi auren da hujja,

Tunda gidansu ya’ya ake so.”

Aunty Farha ta rushe da kuka ta ce “Ki yi min shiru kuka ba ki soma ba sai ya yi auren kin ga ta tara mashi ya’yan da ake so sannan za ki yi kuka.”

Tunani na shiga watau ya Safwan ya furta mata zancen auren da zai yi shi ne ta tayar da bala’i har da su fashe fashe da ya ja mata asarar tayin cikinta.

Na jinjina kai kishiya fa ba ta da daɗi sai dai kowa da yadda yake ɗaukar lamarinta.

Har muka kai faɗa take mata.
A rumfar adana motoci ta gidan direba ya Parker motar muka fito suka wuce ciki na tsaya kwaso kayan.

Ya Sadauki na zaune a falon da aka gyara kamar ba shi aka yi wa ɗibar albarka ba.

Gaisawa suka yi da Auntyn ta tashi ta tafi Aunty Farha ta fara mishi maganar bai shigo ba yau ya yi kamar bai ji ta ba.

Sai kira na ya yi ya ce in haɗa mishi abin karyawa, na juya zuwa kitchen ina ƙara tabbatar da fushin da yake da aunty Farha tun a asibiti.

Yinin ranar da ta kasance Lahadi yana gida duk abin da za a mishi kai tsaye yake kira na in mishi idan kuma bai gan ni ba ya aiki Iya Larai ta kira ni, wanda na kula zafi sosai yake wa Aunty Farha yadda ya gwada da ita da babu duk daya a gidan.

Na kudurta gobe daga makaranta gidan Mami zan koma

Da safe ina haɗa mishi abin kari yana zaune yana amsa waya da na fahimci da Mami yake don na ji yana ce mata “Haba mana Mamina ki bar mana ita mana meye don ta taimaka mana?

Ya tsaya ya saurara sai ya ce “Shi kenan Mamina za ta dawo.

Na juya don komawa kitchen ya dakatar da ni ya shaida min Mami ta ce daga makaranta in koma gida.

Daɗi na ji ya ratsa ni don dama ina fargabar komawar ya je ya dawo da ni.

Ina yin murmushin na tuna gaban wa nake mutumin da ba wani sabo tsakanina da shi ba kuma sakin fuska, tsakanina da shi bai wuce ina kwana sai sannu da zuwa da nake mishi sai yi min kaza.

Saurin barin wurin na yi na faɗa ɗaki na yi shirin makaranta na tattara yan kayana da na zo da su.

A ƙofar Aunty Farha na ajiye jakar na shiga da sallama tana kwance bisa gadonta.
“Ya jiki Aunty? Na faɗi ina duban ta “Da sauƙi Nana.” Ta amsa min “Zan tafi makaranta, daga can zan wuce gida.”

Ta ce “To Nana ki gaishe da Mami.”
Na juya ina faɗin za ta ji.

A mota na bar jakata na shiga aji. Malami na darasin shi wayata da na sanya Silent tana haske.

Sai da ya fita na duba missed call ne rututu har goma sha bakwai daga lambar da ba suna, cike da tunanin wanda ke da kiran na kira, muryar Ummu hani da na ji ta sanya ni tashi tsaye

“Amarya kuma uwargida a gidan Habibi. Don Allah wane kalar wulaƙanci ne don kin tafi ƙasar waje sai a neme ki a rasa?

Ba ta kula wasan da na tare ta da shi ba na ji muryarta cikin ɓacin rai ta ce

“Tun yamma muka sauka Bilkisu amma Habibi ya wuce Lagos. Ina komawa Bilkisu don wulaƙanci na samu mutanen nan a part ɗin Habibi, da na kira shi wai ina nake so ya kai su daga na nuna ban maraba da su?

Ɗari na je gida neman ki Mami ta ce kina makaranta, shi ne na karɓi lambarki wurin ta, ranar da muka tafi wayata ta faɗi a AirPort.”

Na ja ajiyar zuciya “Don Allah kar ki yi musu wulaƙanci, ina hanya zan koma gida, zan kira Mami in faɗa mata zan wuto gidanki.

Katse kiran kawai na ji ta yi na juya kiran wurin Mami na gaya mata zan biya gidan Ummu hani.

Ta ce ta dawo ne ? Na ce E jiya.

Daga waje direba ya sauke ni na kwanƙwasa get mai gadin ya buɗe yana gaishe ni na amsa na wuce ciki a harabar gidan wani wuri da aka ƙawata da fulawoyi don shaƙatawa na ga an sanya gini na ce to zargin Ummu hani akwai ƙamshin gaskiya kenan.

Ban tarad da kowa a falon ba saɓanin tunanina da na sha zan taras da surukar da yan’uwan shi cwwaaike da falon.

Na wuce bedroom tana kwance ta kifa ciki ji na ta birkito na zauna bakin gadon “Ke da kika je garin Annabi, kika je ɗakin ƙaaba, kika ziyarci kabarin wanda ya fi kowa Muhammadul Aminu, amma daga dawowa kin shiga ƙunci me zai ɓata miki rai don Allah?

Gabaɗaya ta birkito “Kin san kuwa abin da na duƙufa roƙo tun zuwa na Allah ya tarwatsa soyayyar Habibi da wadda yake nema, shi ya sa tunda muka tafi ban bar shi ya motsa ba ina manne da shi.” Hakanan na ji gabana ya buga da jin addu’ar da ta yi.

“Ki dai dinga sassauta ma kanki Ummu hani ki bi rayuwa a sannu ni na zo ban ga waɗanda kike bakin ciki don su ba?

“Kin manta na ce miki suna part ɗinsa? Da safe ko abin karyawa ban bari sun nema ba na rufe kitchen ɗin sai da na dawo.”

Cike da rashin jin daɗi na ce “Amma ba ki kyauta ba.”

Su yi zuciya su koma inda suka fito su su yi aure ita kuma uwar tasu ta zauna a gidan da ya sai mata a Kanon.”

Na riƙe baki cike da mamakin ta sai na miƙe “Bari in yi sallah.”

Na shige toilet ɗinta na ɗauro alwala na fito fuskata sharkaf da ruwa ta miƙo min wayata

“Waye kuma My Man tunda kika shiga yake kira? Saura ƙiris in kasa haƙuri ki fito in ɗaga in ce ba ki nan don ya ishe ni.”

Na goge lemar hannuna na karɓi wayar fuskata ɗauke da murmushi “Allah sarki bawan Allah ya tafi ƙwadago, kwana biyu ba mu yi magana ba.

Ta dube ni “Waye shi? Na ɗauki hijab ina sanyawa “Tsohon mijina ne da ni ma uwar shi ta hana ni zama.”

Baki ta kama “Kin ji ko uwar miji ta koro ki ko?

Na ɗaga mata kai ta yi ƙwafa “Ai basu da mutunci.”

Daidai nan wani kiran ya shigo na ɗaga ina murmushi sai da na gaishe shi ya shaida min ya iso Abuja ko gida bai je ba na yi mishi sannu da hanya muka yi sallama akan sai ya shigo da yamma.

Ummu hani da tun fara wayar ta kafe ni da ido ta ce Kina min musu idan na ce Habibi zai yi aure ai kin ga ginin da ya fara yanzu shigowar ki, da muka dawo ya wani ce ya wuce Lagos jin shi kawai na yi wurin ta za shi.”

Na girgiza kai ina hawa sallaya “To zato dai zunubi ne ko da ya zama gaskiya, ki kyautatawa mijinki zato.”

Na kabbara Sallah ina jin ta tana ta maganarta “Gama sallar mu je mu yi mishi girki kafin ya shigo ina idarwa kuma muka fita kitchen ɗin.

Ni ce ƙarfin aikin ita zama ta yi tana ta karanto min ƙululun kishin da ya turnuƙe ta ina ba ta haƙuri da tuna Aunty Farha da na ta kalar kishin. Na sauke ta amsa ta zuba na mijinta na fita ɗauko wayata a ɗakinta na bar ta tana zuba namu ni da ita da na Surukarta da yan’uwan mijinta.

Na dawo ba zato idona ya gane min ta buɗe wata leda da ta ɓoye a cikin zanenta za ta zuba a abincin mijin.

Da sauri na shiga na kama hannuwanta ta baya cak ta tsaya jin na gan ta kawai ta saki ledar ni ma na sake ta na duƙa na ɗauki ledar

“Kar ki yi abin da zai raba ki da Allah saboda biyan buƙatar duniya don wani ɗa Namiji da basu da tabbas.

Ta karɓi maganin daga hannuna ta zubar ta sanya ruwa ya wuce
Sai ta fuskance ni “Ba halina ba ne amma yadda nake jin zuciyata zan iya yin komai saboda kar wata ta raɓi mijina, ban san me ya sa nake buɗe miki cikina ba, ina jin ki a raina ina hakikance ke ɗin ba muguwa ba ce kina da kyakkyawar zuciya.

A gidanmu ni ce babba kuma mace guda daya tal, ƙannena na dakinmu hudu duk maza ne haka mai bi ma Mamana ita ma yaranta kaf maza ne, amaryar Babanmu ba ta haihu ba, ban da wata ƙawa aminiya sai Mamana amma farat daya kin shiga raina ina jin ki kamar yar’uwata ta jini.

Dama wannan harkar asirin ba na son shi na kuma gode da kika nusar da ni ban aiwatar ba, don da Habibi ya ci ba ƙaramin ɓata rayuwar wadda yake sa raina yana ɓaci saboda ita ba.

Na ce “Allah ya ƙara shiryar da mu, akwai wata makarantar addini zan binciko mana yadda tsarin su yake sai mu shiga ni da ke.”

Ta ce “To.”

Ina wanke hannuna aka yi sallama daga ƙofar kitchen ɗin, ko daga barci na tashi ba zai yiwu na iya mance mamallakiyar muryar ba, na waiwaya a hankali cikin wani irin sanyin jiki ita ɗin ce dai Hajara ƙanwar Hassan da duk a cikin su ta fi wulaƙanta ni.

Ba ta lura da fuskata ba idonta na kan Ummu hani “Aunty Inna ta ce a ba mu abinci.” Ta faɗi cikin sanyin murya.

Jikina na ji ya dauki rawa shi kenan ta faru ta ƙare,take kaina ya sara.

Ummu hani ta ɗauko inda ta zuba musu abinci ta miƙa mata tana juyawa ta kamo hannuna “Zo mu je daki mu ci abinci.”
Na ce “Gida zan wuce.”

Allah ba ki isa ba, sai la’asar ɗin da kika ce.
Na ga ma duk kin wani sauya, na ce Kaina ke ciwo. Ta ja ni muka fita ” Mu je mu ci sai ki sha magani.”

Sai da muka shiga dakin ta fita “Bari in je in shirya wa Habibi na shi.”

Ta fita na shiga zagaye dakin ƙirjina na lugude tunanin yadda za ta kaya idan asiri ya tonu na dafe kai ina tunanin ko labaran da ta yi ta ba ni game da mijinta da dangin shi wane irin toshewar basira ta same ni da ban gane ba sai ka ce wadda aka liƙe kanta da tuwo.

Zabura na yi tuna Hassan na hanya zama gidan nan bai gan ni ba na suri lulluɓina da jakata na fita har na fice falon ban haɗu da kowa ba ai ina fita mutum hudu idanuna suka nuna min suna duban motar Hassan da ta tsaya suka juyo jin taku suka dube ni na dube su “Bilkisu! Inna ta faɗi cikin ɗaga murya daidai nan Hassan ya iso “Bilkisu shi ma ya faɗi cikin mamaki “Me ya kawo ki gidan nan?
Kasa magana na yi don ganin fitowar Ummu hani da alamu suka gwada nema na ta fito “Na ji kana kiran sunan ta Habibi ka santa dama?
Ita ce budurwata da kike ta zargin ina tare da wata!

Cikin wani irin yanayi ta juyo wurina “Muna tare dama kin ɗauki lambar mijina kina tare da shi?

<< Mutum Da Kaddararsa 31Mutum Da Kaddararsa 33 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×