“Ta ina ta saci lambar waya a wayarki? Ai wannan da kike gani ita ce matarsa da ya rabu da ita mai ladabi da biyayya, mai son shi shi da kowa na shi. Matar rufin asiri.”
Inna ce ta faɗi haka tana takowa zuwa inda nake.
“Kuna nufin ita ce mai gadon zinare da Hassan ke faɗi? Ummu ta yi tambayar cikin ruɗewa.
“Ƙwarai ita ce.” Ƙanwar shi Ummi ta faɗi cikin tabbatarwa Ummu hani ta zube ƙasa ta fara birgima kamar yar yarinya “Wayyo na bani na kashe kaina.”
Na tsallake su na fara takawa don barin gidan har lokacin Ummu hani na zube tana gunjin kuka ina gotawa gaban ta kamar walƙiya ta miƙe ta sha gabana kafaɗuna ta yi ma wani irin ruƙo tana girgiza ni.
“Ki ƙaryata su Bilkisu ki ce min abin da suka faɗi ba haka ba ne.”
Na girgiza kai “Haka ne abin da suka fadi.” Ta ƙara girgiza ni har kamar za ta cire min kafaɗun
Kina nufin duk tare na da ke kina kallona a shashasha ina ɓarar miki da cikina?
Kan na kuma girgizawa “Ko ɗaya ban san komai ba Ummu hani, ban taɓa sanin Hassan shi ne mijinki ba sai da Hajara ta shigo kitchen.”
Ina gama faɗin haka na wuce ta ta ƙara zubewa tana Wayyo! wayyo! na kashe kaina!
Inna na ta kiran sunana ban tsaya ba Hassan ya biyo ni a sukwane yana tambayata dama ni ce kawar da Ummu hani ta yi a Kaduna?
Banza shi ma na yi da shi ina ci-gaba da tafiyata. Ya gaji da tafiyar ya ce bari ya koma ya dauko mota ya kai ni gida.
Na ci gaba da tafiya cikin matuƙar kiɗima ban san inda nake jefa ƙafata ba don zurfin tunanin da na faɗa hukuncin Allah ne kawai ya kai ni gida.
Ban tsaya neman Mami ba kamar yadda na saba na wuce ɗaki na hau gado idona a rufe ina kallon abin da ya faru yau kamar shirin majigi.
Mami kuma a daidai wannan lokaci suna falon Daddy ana case ɗin Farha da mijinta, ta gaji da sharetan da yake yi ta kawo ƙara wurin Daddy.
Sai da ya fita ita ma ta kintsa ta baro gidan, duk da har sannan ba gama wattsakewa ta yi ba.
Mami ta samu a falo, tana gama gaishe ta ta ce “Lafiya Farha kika fito ba ki gama warkewa ba?
Ta fara share hawaye Mami ta ce “Subhanallah me ya faru?
Ta share hawayen “Na zo wajen ku ne ke da Daddy.”
Ta ce “Ok ina zuwa.” Ta mike ta haura sama ta yi mishi magana ta dawo suka koma tare.
Sai da ta gaishe shi ya ce “Lafiya Farha me ya faru?
Nan ma wani kukan ta fara sai da ƙyar ta yi shiru ta faɗi tun faruwar abin nan Safwan ba ya kula ta, kuma ya faɗi mata za a aika kuɗin aure gidan su yarinyar da yake nema ta zo ne su yi mata rai su sa baki Safwan ya fasa auren waccan yarinyar, daga yana ta rantsuwar aure ba fashi to don Allah ya yi da ko ma wace ce amma ita Nafisa ce ba ta so.
Daddy ya ce “Babbar magana to bari a kira Safwan ɗin.”
Wayarsa ya ɗauka ya kira shi suna nan zaune Farha na ta kukanta ƙasa ƙasa ya iso.
Daddy ya karanta mishi ƙarar da Farha ta kawo
Ya dubi Daddyn “Amma Daddy Farha ai ba ta da hurumin zaɓar min wadda zan aura, ciki ne ta zubar saboda hauka ni kuma zan auro ta sai in ga abin da za ta yi don da ban ji zan aure ta da gaske ba, amma saboda in ga ƙarshen haukanta zan aure ta.”
Daddy ya ce “Ka haƙura da auren nan don ka samu zaman lafiya da iyalinka.”
Ya harari inda take “Amma Daddy ya za a yi in zauna da ita ita kaɗai?
Haihuwar nan ta san ita muke nema mun samu da ƙyar ta je garin hauka ta zubar, ina son yara Daddy.
Farha ta fashe da kuka “Ni na amince ya auri ko wace ce amma wannan ɗin ce nake so ya sake.”
Zai yi magana Daddy ya ɗaga mishi hannu sai da ya yi gyaran murya ta tsagaita da kukan da take ta saurara
“Kai Safwan na soke auren waccan yarinyar daga yau, na ba ka izini ka nemi Bilkisu zan kira Alh Kabiru mu hada auren da na Rabi’ah.
A tare shi da Farhan suka dubi Daddy, cikin razanar da za ka fahimta a fuskarta Farha ta share hawayenta ta miƙe ta fita.
Safwan da ya rage dafe da kai Daddy ya duba “Ya ya akwai magana ne?
Ya girgiza kai “To tashi ka yi tafiyar ka.
Ke kuma kira min Bilkisu.”
Mami da ta daskare a zaune don hukuncin Daddy da ya zo mata a ba zata, duk da da yawan lokaci tana jin ina ma hakan ta kasance sai dai ba ta so a gaya ma Sadaukin ta fi so ya kawo kan shi da kanshi ya ce yana so, duk da ko yanzu ta san halin yan kayanta sarai da bai so ba zai taɓa amsawa ba wata irin kafiya gare shi idan ya tsaya kan abu.
“Bilkisu ba ta shigo ba amma bari in duba ko ta shigo ina nan.”
Ta miƙe ta fita mai aikinta da ta haɗu da ita a falo ta tambaya ko ta ji motsin Bilkisu?
Ta ce E ta hango shigowar ta Mami ta wuce.
Tura ƙofar ta yi can karshen gado ta hango Bilkisu ta dunƙule wuri ɗaya sai zufa take ta shige ciki tana mamakin abin da ya sa ta kasa kunna ko da fanka ne ta kwanta cikin zafi “Bilkisu.” Ta kira sunanta ba ta amsa ba sai da ta matsa ta taɓa ta ta buɗe idanunta da suka canza kala
“Lafiya Bilkisu? Sai na tashi zaune “Kaina na ji yana ciwo.”
“Sannu to tashi ki ci abinci sai ki sha magani. Don na san da kin ji ba daidai ba ba ki son cin abinci.”
“Zan ci Mami.” “Fara zuwa Daddy na kiran ki idan kika dawo sai ki ci abincin.”
Na miƙe ina janyo ɗankwalina na rufe kaina na sanya hijab na bi ta a baya.
Zaune muka samu Daddy na zauna a ƙasa na gaishe shi ya ce “An dawo makarantar ? Na ce
“E Daddy.”
Ya ce “Ya yi kyau. Bilkisu.” Ya kira sunana na amsa ba tare da na ɗago ba “Ina son mu haɗa ku aure ke da yayanki Safwa.”
Daras! Na ji ƙirjina ya doka hannuna ya shiga rawa amma ban ɗago ba “Ki faɗi ma Mamin ku ra’ayin ki ta zo ta faɗa min daga ke ɗin ba budurwa ba ce kina da damar da za ki zaɓi wanda kike so. Idan kin amince zan kira Alh Kabiru a haɗa da na Rabi’ah, tashi ki je.”
Na miƙe ƙafafuwana kamar ba za su ɗauke ni ba na bar falon ina haɗa hanya na sauko na shige ɗaki.
Hawaye suka fara wanke min fuska na durƙushe a ƙasa yau na tabbatar na rasa Hassan a karo na biyu gano shi ne mijin Ummu hani da ta ɗauke ni aminiya. Ba zan auri mijinta ba wai kuma sai ga wata sabuwa ta ina zan auri ya Safwan?
Tsugune ba ta ƙare min ba kenan ni Bilkisu.
Kullum roƙon Allah nake yi auren da zan kara a gaba ya sa shi ne na karshe ya ba ni miji da zai rike ni har ƙarshen numfashina, waɗanda suka ce suna so na ba su riƙe ni ba ina ga wanda na san su Mami ne za su yi mishi tallata.
Ƙofa da na ji ana taɓawa ta sa na yi saurin tashi na share hawaye sai na isa na buɗe mai aikin Mami ce ta kawo min abinci har da magani ta ce Mami ta ce idan na ci in sha magani idan na kammala in same ta dakinta.
Na amsa na koma ciki.
Saboda ita na tuttura abincin na sha magani na faɗa toilet na wanke fuska na fito na murza mai da hoda don kar ta gane ina da wata mas’ala, ya zan yi in dubi fuskar wannan baiwar Allah in ce mata ban son ɗanta ko me auren na shi zai ja min na miƙa wuya.
Da sallama na shiga ɗakin nata ganin tana shirya kaya a wardrobe na matsa na karɓe ta sai da na gama ta nuna min gefen gado kusa da ita sai na zauna “Nana Bilkisu Daddy ya ce in tambaye ki idan kina son Sadauki ki faɗa min in je in faɗa mishi.”
Danƙari! Wannan ma ai shi ne tatsuniya don ni ce butultula uwar butulci sai in dubi Mami in ce ban son ɗanta a wannan zamani da ake ƙwarya ta bi ƙwarya su ba su ƙyama ce ni ba sun ce ɗan su ɗaya tilo ya aure ni sai ni zan dube su da wane idon in ce ban son gudan jininsu?
Da dai sun duba min da ba su haɗa mu ba daga bai ce yana so na ba.
A zuciyata na gama wannan tambihin a fili kuma sai na ce “Duk abun da kuka zaɓa min zan yi biyayya.”
Ta ce “Allah ya yi muku albarka ya albarkaci auren ku.”
Na koma ɗakina zuciyata ba daɗi jikina ba ƙarfi kiran Hassan a karo na barkatai ya kuma shigowa kallon wayar na yi ta yi har kiran ya katse sai na kashe ta gabaɗaya na sanya ta ƙarƙashin pillow.
Shi ma Hassan ɗin haushin shi nake ji tuna farkon zuwan Ummu hani gidan nan kafin ma in ƙara haɗuwa da shi tare suka zo kenan yana sane ya bar ni tare da matarsa cikin duhu har sai yau da gaskiya ta yi halinta.
A dakin na yi ta zama ban fito ba har dare sai da Mami ta aiko in fito in ci abinci, ina gamawa kuma na koma.
Daren nan ba zan ce ban runtsa ba amma na kwana cikin wani irin yanayi mara daɗi.
Yana cikin ranakun da na shiga ƙunci a rayuwata da na rasa da wa zan raba wannan matsala tawa don ya taya ni alhini kamar in kira Zainab sai na fasa sai dai karfe sha daya na safe sai ga kiran ta ina ɗagawa guɗa ta fara yi min da ba ta ko iya ba illa barazanar kashe min dodon kunne da take yi na sauke wayar na sanya hands free ina sauraren ta ta gama gudar ta ta ce “Ina taya ki murna My Billy, yau ranar farin ciki ce a gare ki gaskiya kin yi babban kamu kin shiga birnin tarayya da ƙafar dama, in sha Allah mutu ka raba.
Yanzu Mami ta kira ni ta ce in fara shiri daurin aure rana daya da Rabi’ah.”
Ni dai Hmmm nake ta ce mata har ta gama murnar ta ta ƙyale ni.
Mami ba ta ƙara min maganar ya Safwan ba ni ma kuma ban gan shi ba illa dai na faɗi mata ta gaya wa Daddy muna kammala Exam zan tafi Taraba in gano Mamana.
Daddyn ya ce haka ya kamata in faɗo mata in yi mata sallama.
Ranar da aka yi sati guda da yin maganar Daddy ya tura yan’uwan shi da ke Safana suka je Kaduna wurin Baba kai kudin zance da na sadaki.
Gwoggo Maryama ma da ta kira ni ba ƙaramar murna ta yi ba tana ta min addu’a Allah ya sa iyakar shi kenan.
Don kudin auren da aka kai ita Baba ya ba ni kuma ya turo min sadakin.
Ranar da aka kai Sadakin ranar ya Safwan ya zo gidan na dawo makaranta na same su a falo Mami da Daddy na yi ma sannu na wuce ban gaida ya Safwan ba.
Na shiga daki na sauya kayan jikina da wata riga mara nauyi.
Daddy ya dubi ya Safwan cikin nuna ɓacin rai “Tun wuri Safwan in ka san ba ka yi na’am da zaɓin da na yi maka ba kar ka sa na ji kunya tun wuri a fasa.”
Ya dubi mahaifin nasa “Me ya faru Daddy me na yi? “Ka taɓa tunkarar yarinyar nan tunda na yi zancen hada aure tsakanin ku?
Ya sunkuyar da kai “A yi haƙuri Daddy zan gyara.”
Daddy ya miƙe ya hau sama Mami ta harari Safwan “Ɗiyata mai tsada ce kar ma ka ce za ka riƙa mata wannan miskilancin naka.”
Ya ce “Saboda Allah Mami ni da ita waye gaba yanzu fa ta wuce ko inda nake ba ta kalla ba tun kuma da aka yi maganar nan ko zuwa na yi gidan nan ba ta fitowa, abincin ma da take yi ina ci da sai da ta koma can na gane ita ce me yi tun yin zancen nan ba ta ƙara yi min ba.”
Ta mike in don girki bari in yi mata magana ta zo ta yi maka.”
“Karatu nake ta zo ta same ni ta ce in zo in yi ma ya Safwan girki.
Na ce mata to na sanya mayafi na fita ta gefen ido na saci kallon shi yana latsa wayarsa na wuce shi na shiga kitchen iya cikin shi kadai na yi mishi don haka ina gamawa na juye ta a flate na ɗora saman tray na sanya ruwa har zoɓo na haɗa mishi na kai na ajiye gaban shi na wuce.
Washegari na fito lacture ni da wata yar ajinmu da muke gaisawa na yi mamakin rashin ganin mota a inda direba ya saba tsayawa yana jirana wayata na zaro cikin side bag di na na kira shi ba ta shiga ba.
Wadda muka fito tare a hostel take zaune ta yi min tayin shiga ɗakinsu in jira shi.
Na ce a’a bari in ƙara gwada kiran Mami na kira ta ce kuma ya fito tun dazu amma tana zuwa, can sai ga kiran Daddy ya ce in ƙara haƙuri za a zo a ɗauke ni.
Na yi mashi godiya.
Muna nan tsaye wani matashi dan ajinmu ya iso wurin mu ya yi mana sallama tare da faɗin ana nema na tare muka jera ya nuna mana inda wata rantsattsar mota fara sol tana sheƙi take ya ce Ga me nema na can. Na yi mishi godiya cikin mamaki muka nufi inda take don ban shaida motar ba gabaɗaya a motocin gidan Daddy babu irin ta mamallakin ta yahe kan bonet ɗinta ya bamu baya.
Zahra da muke tare ta yi min sallama ta juya zuwa ɗakinsu.
Gabana na ji ya soma bugawa don tunanin wanda nake zargi shi ɗin ne ya diro daga saman motar cikin ƙananun kaya yake da suka yi matuƙar hawan shi.