Skip to content
Part 36 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Idan kika je ban ce ki kwanta kamar yadda take kwanciya mai aiki na mata komai. Kuma a gaban ki nan muka kashe rikinci kan mai aiki na gyara part ɗinshi.

Girki kuma in har yana nan ban ce ki ji ƙyashin kowa zai ci ba ki yi don shi din mai son cin abinci ne da shi kawai za ki kama shi.
Share kin da yake ban ce ki sa a rai ya dame ki ba lokaci kaɗan zai shiga hannunki sai yadda kika ga dama za ki juya shi.

Mai gayyatar ki idan da alheri ta gayyace ki shi za ta gani, in kuma akasin haka ne ma aniyar kowa za ta bi shi. Na san ki da ladabi da biyayya ki yi wa mijinki.

Amshi. Na ɗaya daga kai don ganin abin da take ba nin wani ɗan kyakkyawar akwati ne “Ki yi amfani da turarukan da ke ciki kowane akwai bayanin shi a jikinsa.
Na amsa na ce “Na gode Mami.

“Ki tashi ki haɗa kayanki in taya ki.

Sai na samu kaina da fara ɗauko kayan da muka shiga kasuwa muka saya da Zainab, na dauko wadanda ta bayar min ɗinki don har ta aiko min da su na tsinci wasu cikin kayana sai su yankunne da sarka da takalma da mayafai ta shirya min su. Ta ce akwatunan auren fa?
Na dubi inda suke ina ɓata fuska “Ƙyale su Mami ni da sati guda kawai zan yi.”

Ta ce “To mu je Sadauki ya zo ya dauka.

Gaba ta wuce na bi ta kamar mara gaskiya ta tambaye ni na yi wanka na ce E na yi da zan kwanta.

Suna zaune inda muka bar su sama muka haura wurin Daddy nasiha ya yi min duk da ina jin nauyin shi na ce,

“Ni fa Daddy sati ɗaya zan yi.”

Ya ce “Ba laifi daga ta nemi alfarma ki je ko satin ki yi.”

Na ce sai da safe.

Ya ce “Allah ya bamu alheri Bilkisu.

Muka sauko Aunty Farha kawai muka samu tana ganin mu ta miƙe muka fita gabaɗaya na ce wa Mami Afnan, ta ce za ta ɗauke ta mun samu har ya shiga mota Mami ta ce ya je ya dauko kayana karamar jakar da na ruƙo ya buɗe Boot na jefa ta ya sauka ya je ya ɗauko Mami ta juya zuwa ciki muka bar gidan.

A hanya ma ita take ta mishi hira yana sauraren ta da muka sauka mai gadi ya shigar min da kayan ita kuma ta ja zuwa dakinta da na taɓa zama a falon na zauna ita ma ta zauna shi yana tsaye can gindin fridge aka yi knocking shi ya je ya buɗe direba ne ya miƙo mishi wata leda ya yi mishi sai da safe ya juya Aunty Farha ta ce “Me aka sawo mana? Ganin yana ƙoƙarin shigewa wurin shi.

“To amarya ya za a yi rabon kwana ? Ƙwafa na yi a raina ina tuna arhar da su Mami suka ja min amma ba komai Allah ya sa biyayyar da na yi ta zame min alheri.

Na dube ta ina miƙewa “Ai ni Aunty Farha ba rabon kwana na zo ba ke na zo wa baƙunta.

Na wuce ciki zuciyata na zafi da shiga ta ban zauna ba toilet na faɗa na ɗauro alwala sallah na yi raka’a biyu na roƙi Allah sosai a sujjadata da ya shiga lamarina ya sanya ma auren nan albarka ya kare ni daga duk abin da nake tsoro.

Na tashi sai na samu kaina da dauko akwatin da Mami ta ba ni na buɗe turaruka ne kala kala masu ƙamshi na musamman na goggoga na mayar na rufe na buɗe kayana na ɗauki wata riga mara nauyi na sanya na tufke gashina na sanya hula, sai na hau gado wayata na janyo na kira Zainab duk da goma ta kusa na faɗa mata abin da Farha ta je ta yi ta ce ƙyale ta in ma da muguwar manufa ta yi aniyar ta za ta koma mata.

Na ajiye wayar na kwanta lamo ina jin tsantsar maraicin da na yi na rasa mahaifina ji na nake wata marar gata tunda na rasa shi.
Ta je ta gayyato ni daga isowa ta fara min izgilanci miji bai damu da ni ba, shi kuma wannan auren tashi kalar ƙaddarar kenan a haka zan rayu kishiya na min dariya miji bai so na.

Wasu hawaye suka taho min na runtse idanu ban damu da sharewa ba.

Turo ƙofar na ji tare da kunna fitilar dakin muryar Aunty Farha na ji tana kiran sunana na ƙara rufe ido na yi lub ta kira ni ya yi sau biyar ta ji shiru ta ce “Ita ma nauyin barcin ne da ita kenan kamar ni, ai nan zan ta gudawa ba dai na zurmaka ba don dai ka daina fushin da kake da ni ne tun zubewar ciki, sai ka gama nema na in koma ɗakina.

Ta kashe fitilar.

Ta zauna bakin gadon ta fara latsa wayarta

“Ina ta rawar ƙafa an min kishiya ko ka je ɗakina ba za ka gan ni ba sai ka sauke girman kanka da miskilancinka.

Rasa abin da zan tunana na yi wato ta nuna tana son auren da nuna ba ta da mas’ala da shi don ya Safwan na fushi da ita ne, kuma ta gayyato ni ne don ta nesanta kanta da shi sai ta ja mishi aji.

Saukar numfashinta na ji shaidar barci ya ɗauke ta na tuna cewar da ta yi tana da nauyin barci Hmmm na ce yanzu kenan nan za ta kwana ikon Allah.

Turi kofar da aka yi ya sa gabana bugawa daras! Kamar in tsala ihu sai na ji an kunna fitilar dakin na dan buɗe ido kadan sai ya Safwan na gani gabana ya cigaba da dokawa watau har ina cikin zai zo wurin matarsa? Wasu hawaye ba shiri suka wanke fuskata na ƙara damƙe idona in sha Allah har su bar dakin ba zan ga komai ba.

Ga mamakina tattausan hannu na ji an sa an tallafo ni gabaɗaya na bude ido da baki zan kwarma ihu. Sai bakin shi na ji ya sa saman nawa kafin ya wurga ni kafaɗa ya juya ya bar dakin da ni bai sauke ni ko’ina ba sai saman niimtaccen gadon shi duk da bige bigen da nake yi ina faɗin ya sauke ni.

Yana ajiye ni na tashi zaune ƙofar ya koma ya danna mata key ya zare keyn ya riƙe na diro daga gadon na kai jikin ƙofar ina faɗin ni ka buɗe min kofa. Ledar da ya amsa hannun direba na ga ya ciro har da guzurin flate ɗin shi da lemo ya buɗe kaza ce gasashshiya tana sheƙi mancewa na yi da kukan da nake na shagala da kallon shi cikin matuƙar mamaki “Ki zo ki ci kazarki amarya.” Ya fadi da wata irin murya da ta sa na tuna kuka nake sai na koma kukan ina faɗin ya buɗe min ƙofar.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mutum Da Kaddararsa 35Mutum Da Kaddararsa 37 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×