Skip to content
Part 37 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Banza ya yi da ni, ina ganin ya miƙe ya tuɓe rigar da ke jikinsa surarsa ta ingarman namiji ta bayyana ban san sa’adda na yi tsalle na bar ƙofar ba biyo ni ya yi har ya ƙure ni a bango kamo ni kawai ya yi ya sa a jikinsa zuwa gado turjewa nake ina ture shi zuciyata na gaya min bai kamata ya same ni a arha ba sai an kai ni nawa gidan na ja mishi aji..

Mirginawa ya yi da ni ya dora min nauyinsa, a kunnena ya riƙa raɗa min zantuka masu nauyi da suka matar min da jiki. Damar da ya samu kenan ya shiga sarrafa ni sai da ya bi kowace gaɓa ta jikina ya bige ta ya miƙe ya kashe wutar ɗakin ya dawo gare ni.

Wannan dare ya zame min dare ma fi tarihi da ba zan manta da shi ba a rayuwata Sadauki ya gwada min ba a filin wasa kawai yake jarumi ba, a’a a fagen tarairayar mace da jiyar da ita daɗi nan ɗin ma shi ɗin jarumi ne.

Mami ba ta yi kuskure ba da sunan da ta ba shi Sadauki na fadi a hankali yayin da na ga cikin matuƙar shaukin da ya faɗa.

Ya tafiyar da ni ta hanyar kauna da tarairaya zantukan da ya riƙa saki kuwa sai da na yi tunanin ko ba shi ba ne wanda kallo ban ishe shi ba.

Bai bar ni na runtsa ba sai tsakiyar dare ya ƙwaƙwume ni ya shiga barci.

Ni neman barcin na yi na rasa da na nemi in zare jikina in koma daki sai ya daɗa ƙwaƙume ni, ban so waccan da take gani ta fi kowa wayo ta gane abin da aka yi ba yanzu nake so ta gane ba.

Daf da fara sallar asuba dabara ta fado min na ce ina jin fitsari ina jin ya sake ni na tashi komai nawa na tattare gudun barin shaida na mayar da rigata da ya jefar ƙofar ɗaki, na danna key na fita ɗakin.

Ta ɗan hasken da ke fitowa daga bed side lamp na hango Aunty Farha warwas tana barci.

Toilet na faɗa na taimaki kaina da ruwa mai zafi na gasa ko’ina nawa da nake ji ba daidai ba, na yi wankan tsarki sai na yi na sabulu na fito ɗaure da tawul, mai kawai ke kan mirror na shafa na ciro turarukan da Mami ta bani na goga na sanya doguwar riga da hijab na kabbara sallar raka’ainilfijr ina idarwa aka fara sallah na gabatar da sallar asuba addu’a sosai na yi wa kaina da Allah ya dorar min da wannan aure tare da ba mu zaman lafiya.
Ina addu’ar barci na neman cin ƙarfina na miƙe na faɗa gado ai ban san san da Aunty Farha ta bar ɗakin ba.

Barci na yi sosai da ban farka ba sai da wani mugun fitsari ya matse ni ga wata gigitacciyar yunwa.

Da sauri na faɗa toilet sai da na yi brush na fito, ganin wayata na haske na zauna bakin gadon na ɗauko ta saƙo ne ya shigo “Na jira na jira ki tashi na ji shiru idan kin tashi ki kira ni in ji yadda kike, kar ki zauna da yunwa, na ba Larai kazarki idan za ki ci. Mijinki Safwan Abdullahi Safana.

Murmushi na ji ya suɓuce a fatar bakina
na kwantar da bayana jikin pillow ina jin wani shauƙi tuna yadda dare na da Sadaukin Mami ya kasance, na rasa yadda aka yi na mance da haushin shi da nake ji.

Na shafa cikina da yunwa ke taso min sai na mike na bar wayar na sanya mayafi har kai na fita ɗakin.

Aunty Farha na zaune falo tana sana’arta ta kallo na zauna kujera nesa da ita na ce “Ina kwana Aunty Farha?

Ta ƙara fara’ar fuskarta “Wannan uban barci Nana, sai yanzu ba ki tashi kin yi break fast ba?

Na ce “Zan yi yanzu.”

Angon ma bai jima da fita ba ina ga jiran fitowar amaryar shi yake yi, daga shi ba mai daɗewa da safe bai fita ba ne.”

Ta faɗi cikin gatsali tana dariya “Ban ce mata komai ba sai miƙewa na yi zuwa danning na karya da abun da suka rage.

Duk yadda na so shiga kitchen gajiyar da ya Safwan ya tara min ba ta bar ni ba ga barci da nake ji bai ishe ni ba.

Ɗaki na koma duk kuwa da yadda Aunty Farha ta so in zauna don ta ci-gaba da yi min shaƙiyanci ta wasan dari, ita ga mai miji a hannu.

Missed call na samu har biyu daga lambar da ya turo min sako na yi saving dinta da sunan da hankali ba zai taɓa kai wa ba.

Ko ina ma ya samu lambar tawa? Na tambayi kaina yayin da kiran Zainab ke shigowa da ɗagawa ba ta ko tsaya mun gaisa ba ta fara fadin

“Kin dai fara nuna mata akwai mata akwai muna mata ko? Ki ciro kayan da muka sawo ki yi kwalliya da su ya kalli dirin da zai sa shi mance hanyar garin su.”

Na ce “Kayya Zainab ba anan take ba ba daga surar halitta ba ne daga can Head quester ne idan aka fi ki ta can ko sille ce sai ya fi rawar ƙafa a kanta.

Akwai wasu kishiyoyi da na zauna da su a Gombe uwargidan ba ta da wani dirin kirki amma ta san sirrin kayan harka, amaryar kuma diri kamar ita ta yi kanta ga tsafta da gayu duk ta fi uwargidan, kin san Allah kullum mijin na maƙale da uwargidan.

Ta ce “To mu duka ne ciki da waje, ki dage da amfani da kayan gyaran nan don Allah da na samu masu kyau ma zan kuma saya miki, ba a bori da sanyin jiki Billy, in ma ta kawo ki don ta yi miki dariya sai ta ƙare tana kuka.”

Na ce “Allah ya sa mu dace.” Ta ce. “Amin.”

Muka ajiye waya na amsa kiran Mami da ya fara shigowa ina gaishe ta ta ce ya muka kwana ya gidan ba wata matsala na ce babu Mami.

Ta ce “To a yi biyayya a zauna lafiya.”

Na ce “Ka ji Mami kamar na zo kenan.”

Murmushi mai sauti ta yi da har na ji shi a kunnena ta ce,

“Shi kenan Nanata.”

Zan ajiye wayar kiran ya Safwan ya shigo “Da wa kike waya tun dazu? Abin da ya fara ce min kenan. Na ce “Mami ce.”

“Kin ci abinci? Na ce “E. Me ya hana ki tashi tun ɗazu ko gajiyar jiya ce? Na yi shiru “Yau ma ina so zan kara.”

Kit ya katse kiran ya bar ni da kunyar da na ji kamar yana gabana, sai mamakin shi nake kamar ba shi ba da magana ke yi mishi wahala, ƙarin mamakina yadda yake nuna kamar bai san abin da ake ba aka ɗauko ni daga kawo ni ya dirar min.

Wani barcin na sha sai da na tashi na yi sallar la’asar, ban dauko kayan kwalliya ba shi ya hana ni yin wanka na zuba lulluɓi na fita zaune na same shi a dinning yana cin abinci na zauna ina mishi sannu idona a ƙasa ba aunty Farha a falon.

Ya ce “Kin ci abinci? Na girgiza mishi kai

“Zo ki ci.” Ya ba ni umarni na mike na isa wurin na zuba a flate “Me ya sa ba ki yi min girki ba? Ya faɗi kamar mai raɗa “Zan yi sai gobe.”

Daga haka na taka na sauka wurin na tafi daki a ciki na ci abincin ban ƙara fitowa ba ko da na ga saƙon shi in fito a ci abinci amsa na ba shi da na koshi ya sake turo me kike sha’awa gidan Mami zan tafi in taho miki da shi ?

Na tura ba komai.

Ina ta sauraren ko Madam Farha za ta kira ni na ji shiru.

Wanka na yi don kwanciya mai kawai na shafa na goggoga turarukan Mami sai na zura wasu riga da wando na hau gado ban tsaya taɓa wayata ba barci nake da niyyar yi da wuri.

Na fara barcin da yake ban da nauyin barci Aunty Farha na shigowa na farka rufe idona na yi don in cigaba da barcina ta ƙarata can da matsalolinta sai dai cikin barcin na ji ana niyyar sunkutata idona na buɗe ta ɗan hasken da ke fitowa cikin dakin na gan shi lub na yi har ya fitar da ni, ina jinjina karfi irin na shi da yake iya sunkutata.

Yau ma kan gadon shi ya dire ni wata sassanyar madara ya zuba min ya ce kuma sai na shanye kaɗan na rage ina dafe cikina ya karba ya je ya ajiye na ce zan yi brush ya nuna min toilet na wuce da na yi na fito hango shi ya yi ɗaiɗai bisa gado daga shi sai guntun wando ya buɗe min hannuwansa kunya ta sa na sunkuyar da kaina.

Ban san ya sauko ba sai dai na ji shi ya haɗe ni da jikinsa zuwa gado yau ma irin ta jiya aka maimaita amarci muka sha mai wuyar mantawa.

Na kuma gudu gabanin asuba ina shiga barci na yi da kuma na tashi ban ga Aunty Farha ba.

Da na yi sallah ban yarda na koma barci ba kitchen na isa ko Iya Larai ciki ta same ni da na gama kuma na shirya komai da kaina na fita na bar ta da gyaran kitchen na koma daki ina gyaran dakin na ga kiran shi ban ɗauka ba sai ya turo min Text in fito mu karya na ba shi amsa da ba yanzu ba barci zan yi sai da na yi barcin kuma da na tashi na fita na karya, aunty Farha na falon jin da na yi ta ce ba zai dawo da rana ba ya sa ban shiga kitchen ba sai na ce mata Aunty ba za a gyara part ɗin ya Safwan ba? Dan jim ta yi sai kuma ta ce “Ki gyara.”

Na tashi tsam na shige na gyare shi fes har da guzurin turaren wuta cikin turarukan Mami na dauko na sanya, na wanko bathroom.

Da yamma na shiga na yi girki mai rai da lafiya da na shige daki ya yi min Text da idan ban fito ba zai shigo ya ɗauke ni dole na fita na zauna tare da su sai na ga fuskar Aunty Farha ta canza ta bar kauɗin da take mishi. Ina gamawa na koma daki.

Yau har na yi barci ba ta zo ba ashe kofar shigowa wurin nata ta rufe ta shige ɗakinta shi kuma da ya zo ya ji a rufe ya koma ya dauko wani key ya buɗe ya zo ya sunkuce ni.

Da muka kwanta sai da ya yi min kashedin kar in ƙara guduwa in bar shi ban ji ba guduwar na yi lokacin da na saba sai dai na faɗa mishi washegari zan koma makaranta.

Sai da na haɗa mishi abin karyawa na koma daki na shirya na fito na karya tare da su da ya shirya ina zaune falon ya fito zai fice na miƙe na ce ma Aunty Farha sai na dawo na bi bayan shi yana sauke ni ya wuce.

Da na tashi direba ya zo ya mayar da ni
Na shiga da maƙalallar sallama ta ban tarad da kowa ba ko Iya Larai ban ji motsinta a kitchen ba.

Na wuce ciki muryar aunty Farha da abin da na ji daga bedroom ɗinta, da abin da na ji kamar tana faɗi ya sa na dawo baya na tsaya jikin window ta.

Ba ki sani ba Salma ni fa ban ji an min kishiya ba, to tana nan da muka je na sa iyayensa suka ba mu ita na ce taya ni hira za ta yi, don duk in samu Safwan ya daina fushin da na ce miki yana yi da ni tun zubewar cikin nan.

Ta yi shiru sai can ta ce “Kin gane wannan ba abin damun kai ba ce ba shi ya ce yana so ba baban shi ya ba shi ban kuma ta da hankalina ba saboda ba ta cikin tsarin matan da Safwan ke so ya fi son yar shafal irina doguwar mace fara, shi ya sa ko a zaren jikina tunda na dauko ta ko kallon ta bai yi ba sai wahalar girki da take mana, haka zai gama miskilancin shi ya kora musu ita ban ma son ta tare wannan gidan da ake kashe ma mahaukatan kuɗaɗe, shi ya sa na kira ta nan a yi ta ta ƙare.”

Shiru ta yi da alama sauraro take sai can ta ce “Ke don Allah ta bar ba ki tsoro ba irin ta mijina ke so ba ko za ta yi yawo hakanan.”

Wucewa kawai na yi daki na zauna bakin gado dafe da baki “Kai ɗan Adam mutum abin tsoro wai yanzu duk abin da Aunty Farha take manufarta ba me kyau ba ce.

Na tashi na kwaɓe kayan jikina na dubi kaina a madubi surata ce abar rainawar Aunty Farha don ina yi mata kawaici, tun da na zo ban fita ba lulluɓi kamar yadda na saba a baya to mu zuba za ta sha mamaki kuwa.

Fita na yi don neman abin da zan ci muka haɗu da ita ta yi min fara’a “Kin dawo? Na ce E.

Ranar ma ni na yi girkin dare da na ci kuma na koma daki a daren bai zo min ba nan na kwana har safiya.

Sai da muka fita zai sauke ni makaranta na ce “Uhmm! Ya dube ni sai ya maida idanunsa bisa titi “Kina da damuwa ne ? Na ce E “Uhumm me ya faru? Na ce “Ba ni da kayan kwalliya ya ce “Ok bari idan kika dawo sai ku fita da Farha ki zaɓi abin da kike so. Na ce “To.

Da na dawo muna zaune ya yi mata waya cewa mu shirya mu fita mu sayi kayan kwalliya. Sai da ta dubi inda nake zaune ta “Ni ina da kayan kwalliya, ita kuma tana da na akwati.”
Ya ce Ok

Text ɗin shi na gani bayan sun gama wayar ya tambaye ni in turo sunan duk abin da nake bukata na rubuta na tura mashi.

Yamma liƙis sai ga direba da kedoji biyu ya ba kowaccen mu ta karɓi ta ta a wulaƙance ta tashi fuu! Ta wuce ciki.

<< Mutum Da Kaddararsa 36Mutum Da Kaddararsa 38 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×