Ni ma ɗakin na wuce na jera abu na kan mirror.
Na riga na gyara mishi daki girki kawai na karasa na shige na fesa wanka da kwalliya ɗinkunan kayan akwatina da Zainab ta aiko da su ban yi amfani da ko daya ba na dauko wata koriyar atamfa mai manyan ganye ɗinkin fitted gown ne na karkata dauri na zuba awarwaro na sanya takalmi na fito suna zaune a falo, dukkan su suka zubo min ido na wuce kawai na ja kujera har na zauna sai na miƙe na nufi kitchen don ya ga bayan da kyau zoɓon da na haɗa don shi na ciro a fridge na kawo mishi na tsiyaya na miƙa mishi ya shanye tas.
Aunty Farha ta ajiye cokali ta shiga amsa waya ko ta gaske ce ko kuma don ta bar wurin ne don mikewa ta yi ta shige ciki ta kullo ƙofa.
Hannunsa na ji saman ƙirjina kin yi kyau ya faɗi cikin miskilallar muryarsa “Da ba girkinki ba ne yau, da ya za ki yi da taɓo ni da kika yi?
Satar kallon shi na yi sai na kai hannuna don cire na shi hannun daga inda yake ta shafawa kamo ni ya yi ya ɗora saman cinyarsa yana sunsuna wuyana girkinki ya yi daɗi kamshin da kike yi mai daɗi wane irin turare ne wannan?
Ban ba shi amsa ba sai ƙoƙarin ƙwace jikina da nake gudun kar matarsa ko Iya Larai wata ta fito.
Ina samun nasarar hakan kuma na canza kujera har muka kammala Aunty Farha ba ta fito ba.
Da na koma ɗaki na yi shirin kwanciya karatun makaranta na zauna yi sai na ji ana taɓa ƙofa shi ne da ya shigo ya ce in tashi mu tafi na ce mu kwanta anan bai yi musu ba gadon ya hau na ajiye wayata a gefe na kashe wutar na dawo na kwanta saman jikinsa, a hankali na yi mishi godiyar kayan kwalliya, ajiyar zuciya kawai yake fiddawa don na yarda yau na fizgi hankalin yan mazan.
Sai da ya fita sallar azahar ya koma ɗakinsa ranar ta kama asabar ba ya fita sai yamma ni kuma zan shiga makaranta.
Da na gama yin abin karyawar shi ajiyewa kawai na yi na je na kama shirina duk da ce min ɗin da ya yi idan na shirya in zo in tashe shi ban yi hakan ba don ganin a kwanaki biyun na karshen mako yake samu ya yi barci isasshe da safe, sai na fita muka fita da direba.
Tun ana daf da tashi aka fara zabga ruwa sai da ya ɗan yi sauki na fita na shiga motar har da Rukayya Babangida da za mu sauke a hanya.
Ya Safwan ya kira ni muna hanya ya tambayi ina ina, na ce muna hanya sai ya kama min faɗa da na tashe shi da bai bar ni na fito ba.
Na ba shi haƙuri.
Da direban ya sauke ni har zan shiga ciki sai zantukan Aunty Farha suka faɗo min na mijinta mata sirara yake so na san kuma a daidai lokacin zai yi wahala ba suna zaune a falo ba.
Cikin ruwan na koma na shiga da ke sauka kamar da bakin ƙwarya nan da nan hijab ɗi na ya yi sharkaf haka kayan ciki na buɗe kofar na shiga ina ɗiga ganin su a zaunen kamar yadda na yi tsammani na zare hijab ɗin daga ni sai riga da wando na material rigar yar karama ce da ta zauna dam a jikina sai wandon Flazo na yi sallama na shiga falon, gabaɗaya suka dube ni ya Safwan cikin ɓacin rai ya ce “Kin gani kin jiƙe ko sai kin ja ma kanki mura ko?
Na ce “Sannu da gida Aunty Farha.” Ta ce “Yawwa Nana kin sha ruwa.”
Na wuce ina cewa “Wallahi kuwa . Ƙwafa ya yi ya mike ya bi bayana Aunty Farha ta bi shi da wani malalacin kallo cike da mamakin abin da ya sa ya hassala haka Allah ya sa idan ya shiga ya yi mata duka gayyar ta su ta watse addu’ar da ta yi ta jerawa a zuciyarta kenan sai ta mike don bin su ta ga wainar da za a toya sai dai kukan wayarta ya tsayar da ita ƙanwarta ce Ɗiyar Auntyn ta sun fita China da mijinta akwai sakon da Farha ta yi mata shi ne ta kira ta bayan hirar su ta nemi ta shiga Whatsapp ta ƙara turo mata kuma ta duba ita ma ta turo mata wasu kayan ko za ta canza komawa ta yi ta zauna dirshan.
Ina shiga kayan na soma cirewa sai ga shi ya shigo ban ko nuna na gane ya shigo ba sai da ya tako gabana “Ke ba ki ji ko?
Sai ya kamo kunnena na ce “Wash ya Sadauki akwai zafi hannu ya kawo kawai ya ja ni jikinsa zuwa kofa ya danna mata key, sai gado nan take zancen ya sauya.
Ya samu nutsuwa ina kan jikinsa yana mayar da numfashi wayarsa ta ɗauki ƙara dukkan mu muka kai duban mu fuskar wayar a hankali ya raba ni da jikinsa ya mike ya mayar da kayanshi sai ya sa wayar a kunne ya buɗe wata kofa da za ta fitar da kai harabar gidan ni dai ban taɓa ko taɓa ta ba.
Kwanciya na gyara in ɗan ƙara hutawa kafin in tashi in tsaftace jikina.
Sai knocking na ji na tashi da murmushi a bakina sanin kowace ce riga na dauko da sauri na sanya na tsaya kofar dakin na bude ina muttsuke ido Aunty Farha ce tsaye na ce “Aunty Farha. Sai ta fara ƙoƙarin shigowa na matsa na ba ta hanya “Na ji ki shiru ba ki fito kin ci abinci ba?
Na yi murmushi kamar ita nake mawa nan ko yadda take kallon shimfiɗar gadon yake ba ni dariya “Barci ya kama ni aunty Farha zan fito yanzu.”
Ba ta amsa ni ba ta fita da sauri dakin Safwan ta faɗa ba shi ta fito tana zaga gidan bayan dakin da Bilkisu take ta hango shi ta isa ta tsaya don zaune yake kan wata kujera “Sai neman ka nake Dear? Ya mayar da wayarsa da ya kammala aljihu “Ga ni ai.” Ya mike suka koma ciki kanta na ƙara ƙullewa da tunani da kasa yarda da an yi abin da take zargin ko ko?
Don Salma ta riƙe ta tun tana gane bayanin da take mata na kaya har ta daina ganewa hankalinta na can kan Safwan da ya shiga ya ƙi fitowa me suke yi shi ke sa ƙirjinta bugawa da abin ya ishe ta ce ma Salmar ta yi za su yi waya anjima ta ba zama sai dai ba shi a dakin to tun yaushe ya fitan shi ne abin da take so ta sani.
Aunty Farha na ficewa na yi toilet ina murmushi sai da na yi sallah na fita na zubo abinci na koma ɗaki ban fita don gyara dakin shi ba ban kuma yi mishi girki ba saboda fahimtar raba mana girki da ya yi ya yi kwana uku da ni ana hudun bai zo ba sai jiya nawa kenan yau kuma ya kama nata kenan.
Da daddare yana cin abinci muna chatting bayan na koma ɗaki ya ce mai ya sa ban gyara mishi daki ba ban kuma yi mishi girki ba? Na ce “Ba ni ke da girkin ba shi ya sa.”
Ya ce “Me zai rage ki in kin yi min na ji daɗi?
Na ce “Wadda za ta kwana ta gyara mana.”
Ya ce “Na ji in kishi ya sa kin ƙi gyara min wurin kwanciya to girkin fa wannan ai ba ita za ta yi ba.”
Na ce “To.” Ya ce “Allah ya shi miki albarka.”
Can ƙasan maƙoshi na ce Amin.
Farha har dare har gari ya waye kanta a ƙulle yake tana son gano akwai wani abu da ke faruwa tsakanin mutanen biyu ko babu? Tana cikin ƙullawa da kwancewa ta samu dabara sun tashi daga hirar dare da suke yi ta shiga ɗakinta ta sake sabon wanka ta fito tana zuba ƙamshi mai sanyin daɗi sai ɗakin Safwan.
Ba ta same shi a dakin ba ta jin motsin ruwa a ɗakin ya sa ta fahimci wanka yake yi ta haye gadon da Bilkisu ta gyara tsaf ta zuba ƙamshi a dakin.
Sai kallon dakin take kamar baƙonta, wata alama take so ta sunsuno,. rabon ta da zuwa kwana dakin tun kafin ta jajubo Bilkisu ko da wasa Safwan bai nuna yana buƙatar ta ba, amma ba ma shi ya kawo ta ba shi wannan tana ganin mazewa yake tana so ta gane yana kawo Bilkisu ne idan tana dakin ai ba wannan damar.
Ya fito ɗaure da tawul a ƙugu suka dubi juna ya wuce gaban mirror ya murza mai ya fesa turare rigar da ya ajiye zai sanya ya ɗora ya isa bakin gado ya zauna
“Akwai matsala ne? Ya ce mata kamar bai son maganar “Matsalar me? Ta ce cikin rashin fahimta “Na gan ki anan.”
Duk da zafin da maganar ta yi mata ta daure “Kwanciya na zo yi, akwai laifi ne?
Kamar ba zai magana ba ta ji ya ce “Yau dai ba ki da halin kwana anan sai dai gobe.”
Wani kallo ta yi mishi “Saboda me? “Saboda na raba muku kwana ina lissafi kuma yau kwananta ne don haka sai ki bari sai gobe.”
Farha da gaskiya ta yi mata yawa ta daure ta ce “Dama har ka tare da ita ne kake rabon kwana?
Kwanciya ya yi ya ja abin rufa “Idan kin fita ki kashe min fitilar.”
Ta zauna shiru tana son tantance gaskiya Safwan ba mutum ba ne me faɗa miskilancin shi ma ba zai bar shi ya yi ba amma tana tsoron yi mishi laifi don matakin da yake ɗauka kanta na yin banza da lamarinta yana tayar mata da hankali.
Ta samu minti ya kusa ashirin zaune kafin ta miƙe gane gane matsalar da za ta faru idan ta zauna ta kwana bayan ya ce ga tsarin shi.
Falo ta koma zama ta yi don kar ma ta kwanta mayen barcin nata ya kawo mata farmaki.
Nazari take don gano ko akwai wata alaƙa sabuwa da ta ƙullu daga dauko Bilkisu ba ta gane komai ba don duk yadda ta so ƙure shi da ido ba ta ga yana tada kai ya dube ta ba, ko yanayin dressing ɗin da ta lura yarinyar ta canza kallo ba ta ishe shi ba.
Idonta da ya rufewa alamar lokacin barcinta ya yi sam ba ta ƙara moruwa da ya yin in kuma ta kwanta in sace ta za a yi har akai inda za a ajiye ta ba za ta tashi ba.
Ta murza idonta ta gyara zama yau ta sha alwashi sai ta ɗebe shakku ba za ta runtsa ba can dai barcin ya ishe ta ta ɗan ɗora kanta jikin hannun kujera tana tsaki dole ta ga doctor Sa’a ta ba ta maganin mugun barcin nan, ta yi hamma sai ta lumshe ido tana girgiza kai take barci ya yi awon gaba da ita.
Safwan da ya koma latsa wayarsa bayan fitar ta ya duba agogo gane duk inda take yanzu barci ya yi awon gaba da ita ya sa ya miƙe har shi za ta riƙa yi wa titsiyen ya kwanta da matarsa.
Ya buɗe ƙofa ya fita murmushin gefen baki ya yi da ya isa inda take ƙafarta ya ja ya gyara mata kwanciya kar wuyanta ya yi sanyi ta daɗa juyawa, ya wuce ta.
Zaune ya same ni ina assigment ya ce “Wai sai yaushe za ki koyi kawo min kanki?
Na ce “Assigment nake? “To ajiye da safe kya ƙarasa zo mu tafi.”
Na ce “Ban yi wanka ba.”
Ki zo ki yi a can ina jiran ki.”
Ya fadi yana juyawa sai da na tattare duk abin da zan buƙata na bi bayan shi na yi mamakin abin da ya kwantar da Aunty Farha take ta kwasar barcinta kamar in matsa in tashe ta na ce ka ji ja ma kai ko ni a wa mijinta ma ya wuce ya bar ta sai ni.
Sai da na yi wankan na shirya muka kwanta.
Yana fita sallar asuba kuma na tattara ya nawa ya nawa na koma ɗakina da zai wuce masallaci ya tayar da Farha yana wucewa ta ƙara juyawa sai da ya dawo ya kara bubbuga ta sai ta tashi zumbur tana murza idonta kafin ta tashi zuwa dakinta a gurguje ta yi alwala ta yi sallah ta fito ta nufi dakin Safwan.
Yana kwance ta gadon shib ta same shi ganin shi shi kadai ya kwantar da hankalinta sai kuma ta yi ta kallon ko’ina cikin dakin, ganin ba ta ga alamar komai ba ta sauke ajiyar zuciya ta zauna kusa da shi ta kama hannunsa tana murzawa “Yaushe Nana za ta koma gidan Mami?
“Zaman nata har ya ishe ki ne? Ya tambaye ta sai ta hau fara’a “Dama na ga aro muka dauko ta.
“To ki ƙyale ta daga ba su ce ta dawo ba.”
Shiru ta yi ta rasa ma me za ta ce mishi ita kam ta fara sunsuno da na sani a ɗauko Bilkisu, inda hankalinta ke kwanciya da ba wata alama da ta gani ta ya san da zaman ta.
Ganin ya lumshe ido dole ta tashi ta koma dakinta.