Skip to content
Part 44 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Ina son tuwon amma haka na miƙe tsohuwa Nene na ma Raihan tsiyar ta hana ni ci. Ita kuma ganin ya Sadauki ta ce min bari ta je ta dawo. Na ce mata “To.

“Zo mu je.” Abin da ya ce min kenan bayan fitar ta.

Na miƙe ina yane jikina da mayafi da ya shiga da kayan “Kai ma ba za ka bar ta ta ci ba? Ya lumshe idonsa ya buɗe “Ta ce miki za ta ci ne? Shi ma ya tambaye ta ya yi gaba na bi shi sai ya tsaya muka jera.

Ashe a cikin gidan akwai wani wadataccen fili anan ne za a gabatar da Dinner ƙwai da kwarkwata kowa ya sha kwalliya sai hasken waya ke tashi ana kashe Selph ga decoration da aka yi ma wurin ya ƙayatar ba magana.

Kallo daya na yi wa inda Baba da Mama da Mami da Daddy ke zaune na sunkuyar da kai.

Muka zauna aka soma gabatar da shirye shirye, nan ɗin ma abokan wasan shi zuwa suka yi ta yi suka samu gaba.

Mami daga ita sai yayarta su kaɗai ne mata a cikin family ɗinsu sauran duk maza ne ita ma yayar Mamin dan cikin gidan take aure shi ya sa take cikin gidan.

Na zauna wurin har na gaji da zama sai muskuce- muskuce nake shi kuma ba abin da yake sai ƙoƙarin ganin na ci abubuwan da aka tara gaban mu.

Na ce ni tuwon nan kawai nake so.
Daga gama faɗin hannuna kawai ya kama muka bar wurin zuwa wurin Nene na yi mamakin ganin ta ido biyu tana kishingiɗe dafe da Radio saitin kunnenta tana sauraro.

Ta tashi zaune “Har kun tashi abin naku kenan? Ya girgiza kai “Mu dai mun tashi, tuwonki za ki sammana.”

Ta nuna wata warmer “Ga shi can.” Ya janyo ya buɗe har lokacin da ya cire shi a leda yana tururi.

Ya zuba miya sai ya turo gabana, na yaye mayafina sai na sauka ƙasa kan tattausan carpet ɗin tsakar dakin na sanya hannuna na yanko tuwon na fara ci.

“Dama ba kai za ka ci ba. Ta tambaya tana komawa ta kishingiɗa “Gimbiya za ta ci.”
Ta ce “Iye me ka ce? Ya ce “Gimbiyarku na ce za ta ci.

Ta ce “Ka canza ni kenan? Ya ce “Kina amsa sunan Gimbiyata ne kafin ta zo.”

Ta riƙe baki “Ai shi kenan, laifina ne da na ba ka tuwon nawa, Idan kin gama akwai hura da aka shigo min da ita ki ɗauko ki sha.”

Ya miƙe zuwa wurin fridge ya buɗe ya tsiyayo hurar ya ajiye gaba na ta miƙe “Ni kam bari in je in kwanta.”

Ya ce “Ba ki ji ba Nene.”
Ta waiwayo “Mene ne? “Wancan dakin naki za ki ba mu aro.” Ta dubi ɗakin da ke duban na barcinta “Wannan ɗakin da ba komai a ciki?
Ya ce “Ke dai ki ara mana.” Ta wuce ciki tana cewa “Ga shi nan.”

Ya tashi ya fita.

Ya dawo ne ina kurɓar hurar don na gama cin tuwon har na wanke hannu, wani matashi na biye da shi da katifa sabuwa har da ledarta ya nuna mishi dakin ya shigar da ita.

Ya fito ya karɓi ledar da ya Safwan ya shigo da ita ya koma dakin, yana fitowa ya yi mana sai da safe

“Tashi mu je.” Ya bani umarni na dauke kayan abincin na shigar da su kitchen ɗinta sai na fito na shiga ɗakin, ba komai sai katifar da zanen gado da aka shimfida.

Na zauna bakin katifar ina jiran shigowar shi ya shigo da kaya a hannu na ce za ni wurin su Mami in dauko riga ya girgiza kai “Sa wannan kawai.” Ya miƙo min jallabiyar hannunsa.
Na tube rigata na sanya jallabiyar bayan yawa da ta yi min ta shanye min har ƙafata na kwanta kan katifar don ba abin da nake so irin kwanciyar.

Ya tube na shi kayan ya zama daga shi sai boxes da farar singlet ya kwanta kusa da ni ya jawo ni jikinsa a hankali ya zare min jallabiyar ya matse ni jikinsa yana fitar da ajiyar zuciya sai kuma ya sassauta riƙon yana ɗago ni “Wace irin zufa kike yi haka?

Na ce “Zafi nake ji.”

Ya mayar da ni ya kwantar sai ya miƙe ya zura jallabiyar ya fita na bi shi da ido har ya fita na rufe idona.

Shigowar shi ta sa na buɗe idona yana dauke da Stand fan da yake gidan Solar ce ya kunna ya sanya ta saitina wata ajiyar zuciya ta ƙwace min yayin da na ji iska ta ratsa ni.

Da asuba da ƙyar ya samu na tashi na yi sallah don bai bar ni na yi barci da wuri ba.

Ina yi kuma na koma na kwanta cikin barcin na ji yana taɓa ni “Ki tashi ni zan tafi.”

Na buɗe idona ganin shi cikin shiri yana sanya Safa ya sa na tashi zaune “Ina za ka? Na tambaye shi “Gida za ni. Na roƙi Mami ta bari in tafi da ke ta ce a’a.

Na tura baki “Saboda Allah bikin fa bai ƙare ba.”

Wurin ku mata ba? Ni saboda ke ma na kwana da na juya tun jiya.”

Na ja ajiyar zuciya ina sauka daga katifar na yaye malum malum ɗinshi da ya naɗe ni da ita.

Rigata na ɗauko na sanya na rufe jikina da mayafi sai na ninke mishi malum malum ɗin, na ce “Ya za a yi da ita? Ya ce “Wanda ya kawo katifa jiya zai zo ki hoi ba shi har da yar cikin da wandon.”

Ya fita na bi shi a baya.

Nene ta fito tana zaune a falon muka gaishe ta ya ajiye kudi a gaban ta wai ta sayi goro ya yi mata sallama muka fita da muka iso part ɗin Baba ya ɗan tsaya yana duban wurin “Ba zan iya shigar mishi yanzu da sassafen nan ba, kin san yanzu surukuta nake yi da shi kunyar shi sosai nake ji.

Na yi murmushi muka wuce part ɗin su Mami, Daddy ne kaɗai zaune a falo ni na zauna na gaishe shi shi yana daga tsayen ya gaida shi.

Ya ce ma Daddyn zai wuce Daddy ya dubi agogo “Tun yanzu kenan? To Allah ya kiyaye hanya. Mu sai anjima in sha Allah.
Ya ce “Amin Daddy, Mamina fa? Wayarsa ya janyo ya kira ta sai ga ta ta fito cikin lulluɓi, muka gaishe ta ya yi mata sallama yana juyawa na mike na bi shi Mami ma ta biyo mu zuwa ƙofar part ɗin, ya dube ta “Tun da kin ƙi in tafi da ita Mami, ki kula da ita ba ta son cin abinci duk jiya ba ta ci abinci ba sai da aka kusa tashi Dinner ta ci tuwo wurin Nene.”

Wani irin kallo ta yi mishi “Zan gamu da kai Sadauki, idan ba ka bar yi min rashin kunya kan Bilkisu ba. Bilkisun nan wai taka ce ko tawa?

Cikin rage murya ya ce “Tawa ce Mamina.”

Ya taka da sauri ya bar wurin.

Duk da kunyar da nake ciki sai da na bi bayan shi.

Sai da ya zauna a mota bai rufe ƙofar ba ƙafarsa daya na waje ya dube ni ina tsaye jikin murfin.

“Sai kun dawo ko? Ki kula da kanki ki riƙa cin abinci.”

Na ɗaga mishi kai ya ciro kuɗi ya miƙo min na amsa haɗe da godiya ya kamo murfin sai na matsa ina masa addu’ar Allah ya kai shi lafiya.

Ya ja motar sai da ya fita gidan na koma ciki.

Part ɗin Baba na shiga na yi sallama Mama da ke kitchen ta amsa na isa can ina gaishe ta.

Na taya ta aikin da take yi har muka kammala sai dai tun fara aikin na fara jera atishawa alamar mura ta ziyarce ni, ban yi mamakin hakan ba don da asuba da muka tashi muna son yin wanka cewa ya yi in shiga kitchen ɗin Nene ko zan samu yadda zan dafa ruwa na ƙi, daga zuwa gidan mutane a ji ni na shige musu kitchen, kawai sai na yi da ruwan sanyi kamar yadda ya yi.

Ina jera abincin a falo Baba ya fito na gaishe shi na gama jera mishi sai na zauna kasa kan carpet yana karin shi yana min hira da rabin ta nasiha ce da tambaya cikin hikima ta muna zaune lafiya ban da wata matsala.

Har yake gaya min Daddy ya yi mishi zancen tarewa ta nan da wata daya, don haka duka yan’uwana za su halarta.

Gwoggo Maryama ma ya kira ta ya gaya mata.
Ni dai ina sauraren shi har Mama ta kira ni na iske ta cikin kitchen, abin karyawa ta ta gabatar min na zauna na ci anan, da na gama na fito ba Baba ya fita sai na gyara mata wurin muna hirar su Zainab.

Wurin Mami na koma na yi wanka na shirya cikin atamfa muka fita tare da Mami sasan yayarta wadda ke aurarwar , nan muka zauna har aka yi azahar sai da za a tafi gidan amaren Raihan ta zo muka tafi tare da aka gama buɗar kai muka dawo.

Baba da Daddy duk sun wuce Mama sai gobe Baba ya ba ta kudi ta ba ni kamar yadda Daddy ya ba Mami ta ba ni.

Abinci kawai na ci wurin Raihan na koma wurin Mami sai ga kiran Gwoggo Maryama ya shigo daga gaishe ta da na yi da na fahimci cikin farin ciki take ce min “Ke kam Bilkisu sai sam barka, Allah ya yi miki sakayya kan wahalar ki ta baya.

Wannan irin miji da Allah ya ba ki na nuna ma sa’a, yau da ya zo kin ga yadda ake tambayar daga ina na yi bako?

Ji na yi kaina ya ƙulle da zancen da take “Zuwa ya yi Gwoggo? “E mana ya zo ya gaishe mu, ya baibaye mu da dimbin alherai. Don haka na kira ki, idan ya dawo godiya sosai za ki yi masa.”

Na ce “To Gwoggo.”

Ni ma ina nan ina haɗa ɗan abin da za mu fita kunya, Alh Kabiru ya ce ba sai na yi komai ba zai miki komai, amma ba za a yi haka ba ko kuɗi ne dole za a ba shi.”

Ni dai na ce uhmm! Kawai har ta gama gaya min abin da za ta gaya min muka yi sallama ina kallon cikina da riga mai girma kawai zan sanya in ɓoye shi saboda fitowar shi da ta hana ya ɓoyun.

Ake maganar biki kafin su tashi bikin ban san irin girman da zai yi ba.

Ina cikin tunanin Mami ta kawo min gasasshen naman rago da madara mai sanyi, sosai na ci na sha madarar na nemi wurin kwanciya sai dai mura ta uzzura min ta hana ni samun barci mai daɗi.

Da safe da na tashi muryata ta dashe Mami ta ce in shirya a kai ni asibiti cikin matasan gidan ta sanya mutum biyu suka yi min rakiya.
Magunguna aka haɗo ni da su muka dawo na sha magungunan na kwanta barci na yi ta yi ba ji ba gani wai auren kurma da makaho har sai da Mami ta ce wannan barcin na lafiya ne.

Na tashi ana kiraye-kirayen sallar laasar na dubi fuskata a mudubin da ke dakin duk ta kumbura sai dai na ji sauƙin ciwon kan da na kwana da shi na yi wanka da ruwa mai dumi na fito na murza mai da hoda na sanya riga ta wani yadi mai laushi na yane kaina da mayafinta, sai na ɗauki wayata na fito.

Mami ta sanya an jera min abin da zan ci har da farfesun bindin sa mai dan yaji da na ji dadin cin shi.

Sai sannan na duba wayata da tun safe ban duba ba saboda daɗin da ba na ji missed call ne rututu daga ya Safwan da ya kira a mabanbantan lokuta tun daga safe har zuwa yanzu, abin da ya ban mamaki har da kiran Daddy, kiran Daddyn na fara bi bayan gaisuwa da tambayar yadda ya isa jikina ya tambaye ni kafin mu gama kiran ya Safwan ya shigo muna yin sallama na ɗaga jikina ya fara tambaya ta na ce na ji sauƙi.

Jama’ar gidan suka yi ta shigowa gaishe ni har da tsohuwa Nene da ta iso tana dogara sandarta.

Washegari maimakon ziyara da Mami ta ce za mu kai gidan yayanta da shi ya fita daga gidan shirin tafiya muka fara saboda wayar da ta samu daga Daddy ya ce mu dawo gobe. Ita kuma ta ce shirin ya Safwan ne shi zai sa Daddy ya hana satin da ta yi niyya za mu yi.

Mun sha tsaraba daga jama’ar gidan muka kama hanyar ba mu fita da wuri ba don haka sai yamma muka isa.

Da daddare kuma da ya Safwan ya zo ya ɗauke ni muka je asibiti aka ƙara duba ni.

<< Mutum Da Kaddararsa 43Mutum Da Kaddararsa 45 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×