Skip to content
Part 47 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Ya Safwan gidana yake don haka ina yin abincin dare idan anan yake, saɓanin ranar da ba ni da girki da na kan yi sau daya, Hajjo na gefena har na gama na tafi daki na yi sallah na yi wankana, na fito ne karfe takwas zuciyata na ta kai kawo in kai ma Aunty Farha abinci ko in rabu da ita don har lokacin ba ta fito ba.

Ya Safwan ya shigo daga falon na yi mishi sannu da zuwa ban bi shi ba sanin tana ciki ya samu minti ya yi ashirin sannan ya fito na haɗiye wani abu da ya taso min kafin na bi shi na zuba mishi abinci sai ga ta ta fito, ta iso inda muke cikin shagwaɓa ta ce “Ka sa a dauko min kayana a mota.”

Bai ɗago daga abincin da yake ci ba sai na yi na yi ƙarfin halin yi mata tayin abinci ta dubi abincin ta girgiza kai “Ba na cin abinci mai nauyi da dare.”

Ban ƙara bi ta kanta ba na ci-gaba da cin abincina ta janyo kujera ta zauna da na gama na mike zuwa daki ina shiga sai ga kiran shi na dawo fruit salad ya ce min yana so, ba tare da na furta komai ba na shiga kitchen na haɗo mishi cikin sauri na kawo masa ina ajiyewa gaban shi Aunty Farha ta ce “Ni ma kam zan sha.” Na yi kamar ban ji ta ba zan wuce ya ce in ɗauko mishi maganin mura da ya sha shekaranjiya.

Na wuce na dauko na fito bedroom ɗin muka yi kaciɓis da Aunty Farha za ta shige na raɓa ta na wuce.

Ina ajiye mishi na tafi shirin kwanciya na fara na gama shafe jikina da turarukan Mami da suke na sirri ne sai na sanya riga da wando masu laushi na kashe wuta na hau gado na kwanta lamo ba don zan iya barci ba don kishin Aunty Farha da ke turnuƙo min, sai dai wani ɓarayin na zuciyata na faɗa min ni ma haka na yi mata, ashe ba ƙaramin haƙuri ta yi ba sai dai ita na ta akwai rainin hankali ciki ki zo kuma ki shige turaka ina jiran ganin matakin da zai dauka daga haka rarrashin zuciyata na yi da in manta da su kawai in yi barci.

Hasken da ya game idona ya sa na buɗe idon ya Safwan ne tsaye cikin wata rigar barci mai budaɗɗen gaba ya tako gaban gadon “Ya kika kwanta? Tashi mu je.”

Wani kallo da ban taɓa masa ba na wurga mishi “Mu uku za mu kwanta sai ka ce garin gaɓa-gaɓa?

Murmushin gefen baki ya yi “Ai wurin nawa biyu ne ki zo mu je dayan.”

Kallon na ƙara zabga mishi na juya “Ni ina nan ba inda za ni.”

Ji na yi kawai ya kashe wutar ya hawo gadon.

Anan muka kwana da ya dawo sallah ma nan ya dawo muka koma barci sai goma saura muka fito bayan mun yi wanka muka fita cikin shiri.

Na samu hajjo ta gyara ko’ina ƙal ƙal kitchen ma haka fes a ciki ma na same ta muka gaisa ta ce tana murmushi “Sai yanzu Haj? Ai na kasa jiran ki na dafa shayi na sha.

Na ce “Ba laifi.”

Na kama aikina tana gefena tana min hira, hirar Hajjo dai ba ta wuce ta dangin mijinta da rashin mutuncin da suka gwada mata da ya rasu.

Ina ta jin tausayinta da bayyana mata tausayin da ta ba ni.

Har na gama na shirya komai na dauko ban tunanin zan ga ya Safwan ba a falon sai na gan shi a inda na bar shi ya ce in kawo abincin gaban shi na koma na dauko ledar cin abinci na shimfida ina zuba mishi Aunty Farha ta fito muka gaisa na yi mata Bismillah ta dubi abincin ta ce ba abin da take so a ciki kitchen ɗin ta wuce ina jin su tana sanya Hajjo kafin ta fito ta fita waje suka dawo tare da mai gadi yana janye mata da akwati ya gaishe mu ya ajiye mata akwatin ta ja abin ta zuwa ciki har muka gama muna zaune ni ina kallo shi yana taɓa wayarsa Aunty Farha ta fito ta kame a Cushion Hajjo ta kawo mata abin da ta sanya ta ta buɗe tana yamutsa fuska ta tambaye ta “Meye wannan? Hajjo ta yi turus! Ta ce ta kwashe maza ta bar wurin da su.

Hajjo ta tattara ta mayar kitchen muna zaune sai sakin tsaki take kafin dai ta mike ta shiga kitchen ɗin indomie ta dafa ta fito da ita ya Safwan yana waya da ya ƙare ya dube ni “Ana jira na wani ciniki ya faɗo,bari in leƙa.”

Na yi mishi addu’a ya fita.

Ni ma miƙewa na yi na koma ɗaki ina gyarawa ina kallon lokaci azahar ta kusa Khadija ta yi min waya za ta shigo Oga bai nan?

Na ce E ya fita.

Na fita don in tare ta Aunty Farha na zaune har lokacin tana cin abincinta suka gaisa muka wuce falona ta ce “Baƙuwa kika yi?

Na yi yar dariya “Ba baƙuwa ba ce uwargidan mai gidan ce.” Ta zaro ido wuni kenan ta kawo miki?

Na ce “Ina fa wuni, zama dai ta zo.”

Ta fidda ido da gaske? Na ce “Wallahi. Na ba ta labarin yadda na gan ta sama ta ka, ta ce “Lallai ma ki ji mata, wallahi idan ni ce ba ta isa ba.”

Na ce “Kwantas Madam.”

Na ba ta labarin da ɗaura nawa auren ta ja ni na je na zaune mata gida har wata uku.”
Ta riƙe baki “Lallai abin naku sai ku, amma dai gara ta tattara ni ban son neman magana.”

Na ce “Oho mata ta dai yi ta zama.”

Na kira ya Safwan na ji ko zai dawo in mishi girki ya ce a’a sai dare. Don haka zaman mu muka yi muka yi ta hira Khadija ta kira mai aikinta ta ce ta kawo mata abinci idan ta gama, nan ta kawo muka ci har muka rage na kira Hajjo na ba ta na ce su ci da mai gadi.

Sai da ta yi sallar laasar ta wuce na raka ta na dawo sai na yi shirin girki duk da na so in ƙi yi daga yau aikin Aunty Farha ne, khadija ta ce in yi yau sai in ga inda suka dosa in zama ta zo yi sai in ba ta girkinta.

Ban gama ba ya dawo yau ma ban bi shi ba don tana ciki sai da ya yi wanka ya fito ai muna fara cin abinci Aunty Farha da ban san yadda ta kare da rana ba ta fito ta zauna ta zuba abinci mai yawa ta cinye ta tsiyaya lemo.
Ina tafiya ɗaki ya Safwan ya biyo ni wai me nake mishi haka?

Na ce “Ba komai, amma daga matarka zuwa ta yi zama to ta tashi daga turaka da ta shige, ni ma ina buƙatar shiga dakin mijina.

Kallona kawai yake har na gama sai ya juya ya fita.

Wani takaici ya rufe ni ganin wulaƙancin da ya yi min ya juya ya yi tafiyar shi bai ɗauki magana ta komai ba.

Na kwanta shiru wucewar kamar minti
biyar sai na ji shigowar shi ya hau gado tunani na yi ta yi me kenan haka to yau ba girkinta ba ne ya za a yi ya zo min nan? Har barci ya ɗauke ni.

Yau da na tashi ban koma ba kitchen na shiga na samar da abin karyawa muka karya Aunty Farha na can tana barcinta muka fita tare ya sauke ni makaranta.

Da muka fito ma abin da ya ban mamaki samun shi na yi ya zo yana jira na na shiga muka koma gida kamar yadda kafin in fita ban ga aunty Farha ba, yanzu ma da muka shigo ban gan ta ba. Ban haɗu da kowa ba na shiga falona, Sallah na yi na fito na shiga kitchen, ina shiga kamar tana jira na sai ga Hajjo ta shigo muna gaisawa ta ce “Haj ban taɓa zaton kina da abokiyar zama ba, don dai wannan matar daga zuwa ta kama shigewa turaka, ni kuma ta ishe ni da baƙin mulki. Yau ma da kika tafi tsare ni ta yi na yi mata girki ta kuma ƙi ci ta ce bai yi ba, Isya ta kira ta ce ya sawo mata. In ban da ma Namiji me kamar Haj ya ɗauko wannan mata kamar maburgi b…

Hajjo! Na kira sunanta da karfi ta amsa “Na’am Haj.”

Jin ban kara magana ba ta san ban son zancen da take yi juyawa ta yi saɗaf ta bar kitchen ɗin.
Plate daya na dafa don Hajjo na gaya mata idan ba na nan ta riƙa yi musu ita da Isya mai gadi.

Na ɗauka na kai daki ban ma tsaya falo ba na shige kasan carpet na zauna cokali biyu kawai na yi na ji duk ya ishe ni don mun ci abinci da Hafsa a makaranta.

Aka murɗa handle ɗin kofar aka shigo na san shi ne sai ban daga kai ba don cikin takaicin shi nake ina zargin saboda Aunty Farha ya dawo da rana suka shige daki suka bar sakarai.

“Ina nawa abincin? Na ɗago na galla mishi harara sai na maida kai ya dauki cokalin ya ɗebo abincin ya fara ci muka zauna shiru yana ta cin abincinsa “Ki je ki gyara min wuri.”

Hawaye kawai na ji suna zubo min na dube shi “Dole in zama ba komai ba a wurin ka, don ce maka aka yi ka neme ni ita kuwa da ka gani ka ce kana so ba cewa aka yi ka neme ta ba ba za ka mayar da ita me hidima ba.”

Wani irin kallo yake min mai cike da mamaki “Ban son ki kuma, ta ya? Na ƙara maka mishi wani kallon “Ka taɓa furta kana so na? Ita da kake son ba ga shi ta zo ta shige wurinka ba kuna harkokin ku, amma ni kake cewa in je in gyara muku wuri bayan kun gama abin da za ku yi? Na fashe da kuka sosai na miƙe na fada gado gane ba zai yiwu in yi rub da ciki ba sai na juya mishi baya, na ci-gaba da kukana.
Ji kawai na yi ya birkito ni “Me zan miki mi gane irin son da nake miki? Na ƙi magana na ci-gaba da kukana “Ina son ki ina son ki Bilkisuna, ina son ki Bilkisun Mami ni kuwa ke son ki sonki ya kama ni har wuya, na fara son ki tun ganin farko da na fara yi miki.

Allah ya yi ma Daddy sakamako da aljanna da ya haɗa aurena da ke.”

Na buɗe idona muka haɗa ido ya daga min gira sai na yi saurin rufewa.

Ina kwancen ina juya maganganun da ya faɗa min ya kira sunana na buɗe ido “Ina kike so ta zauna inda take yanzu ni in koma can ko kuma ta koma can.”

Cikin shan ƙamshi na ce “Ta koma can.”
Ya mike “Bari in fita Ya miƙe na bi shi da kallo har ya fice.

Wurin shi ya shiga ya samu Farha zaune a falo ta ɗora ƙafa daya kan daya idonta na kan TV tana cin Cake da lemo.

Farha.” Ya kira sunanta ta dube shi ganin yadda ya ƙara tsare gida sai ta shiga nutsuwarta “Tun jiya na ce ki koma gida, amma yau na dawo na same ki ta miƙe tsaye “Ya kake so in yi Dear? Sai in koma gida in zauna in yi yaya da ƙaunarka?

“Ko ma ya za ki yi da ita, ba ke kika matsa sai an miki gyaran gida kamar na Mami ba? Sai ki je ki zauna gidanku har a gama.”

“Ni dai ka bar ni anan pls Dear.”

Hannuwansa na soke cikin aljihu ta iso gaban shi ya ce “Ba zai yiwu ba. Ta faɗa jikinsa ta ƙanƙame shi ta fara zuba kuka tana gaya mishi kalmomin kaunar da take mishi.

Jikinsa ya yi sanyi, ya ja ta suka zauna kan kujera tana jikinsa bayan ta ya shafa “Ki yi shiru, zan ba ki keys ɗin wancan flat din nawa, ki shiga sai nan ya zama nawa duk me girki sai ta shigo.” Ba ta so haka ba amma dole ta daure.

“Kuma ranar girkinki za ki yi naki ranar na ta ta yi.”

Shi ma wannan hukuncin ba ta so shi ba ta Bilkisu ta yi ta yi kamar yadda ta yi zaman ta gidanta.

“Zan kira Larai ta riƙa yi min aiki.”

“No Farha, nan fa gidan Bilkisu ne za ki zauna ne kafin a gama gyaran naki, ba wata Larai da za ki kira.”

Ta ji zafin yadda yake ba Bilkisun mahimmanci, amma ya ta iya za ta haɗiye komai har sai ta cika burin da ta zo da shi.
Ya zare jikinsa sai ya bar wurin.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mutum Da Kaddararsa 46Mutum Da Kaddararsa 48 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×