Skip to content
Part 49 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Hajjo na kwance ɗakinta bayan ƙare ayyukanta ta ji taɓa ƙofa alamar za a shigo duk da ta yi mamakin waye zai mata wannan aikin sanin uwardakin ta ta ta fita zuwa makaranta.

Ba ta tashi ba har ta buɗe ƙofar ta shigo, sai dai ganin wadda ta shigon ya sanya ta tashi zaune zumbur, ta shiga rawar jiki. “Ranki ya daɗe da kanki ba ki kira ni ba? Farha ta ɗan yamutsa fuska ta kara daure fuskarta “Ki same ni falona.” abin da ta ce kenan ta juya.

Hajjo ta saki wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya da ke ta shirin kuɓuce mata tana danne ta, ta haɗiyi yawu sai ta gyara daurin dankwalinta da ya fara kwancewa ta miƙe ta fita.

Da sallama a bakinta ta shiga falon da ke ta fitar da ƙamshi duk da ita ta shigo ta gyara ma Farhan ta sanya ƙamshin sai da ta ƙara kalle wurin don tsarin falon yana matuƙar ɗaukar hankalinta, kamar a fina-finan da take gani.
Ta zauna ta tsura wa TV da ke ta aiki ido da tun shigowar ta bariki ita ce abin da har yau ba ta gajiya da kallon ta.

Farha ta fito riƙe da wani cup a hannunta tana shan abin da ke ciki, ta zauna ta ɗora ƙafa daya kan ɗaya, Hajjo ta tattara dukkan nutsuwar ta ta miƙa mata, kamar ba za ta yi magana ba sai da aka ɗauki lokaci ta ce “Na neme ki ne saboda wani aiki da nake so ki yi min, kuma ki faɗi duk abin da kike so in riƙa biyan ki zan biya ki.”

Hajjo ta dube ta da sauri sai dai ganin ita ma ita take kallo sai ta yi saurin mayar da kai ta sunkuyar.

“Uhmmm! Ina jin ki.”

Hajjo ta haɗiyi miyau ta muskuta “Ai ban san wane irin aiki ba ne Haj.”

Na san za ki iya, don na saurari maganganun ki da yarinyar ki ta waya, kina karanta mata yadda za ta yi don dauke hankalin mijin matar da take wa aiki, ko bai aure ta ba ta samo kuɗi a wurin shi.”

Wata zufa ta shiga wanke Hajjo har cikin ɗan tohinta,

“No, kar ki fa damu ni wannan ba matsala ta ba ce, aiki nake so ki yi min kan kishiyata.”

Hajjo ta kara ɗagowa a karo na biyu suka ƙara haɗa ido sai ta sunkuyar “Me kike so a yi mata Haj.”

“Yawwa ina so ki sa mata ido duk abin da za ta yi ko tare da maigidan take ki ɗauko min duk abin da kika gani.”

Hajjo ta saki ajiyar zuciya
“Wannan ai mai sauki ne ranki ya daɗe, duk wata ki ba da dubu goma.”

Farha ta yi mata wani kallo na mamakin dolancinta ta ce “Ina zuwa.”

Ciki ta shiga ba a ɗauki lokaci ba ta fito da kuɗi rafa ta yan dari biyar ta cilla mata Hajjo ta bi su da azama ta dafe daga inda suka faɗa tana zuba godiya.

“Kar ki damu Haj, ni wannan ya fi ruwa sauƙin sha a wurina.”

Ganin Farha na gyara zaman jakarta ta san fita za ta yi sai ta mike ta fice Farha ta bi bayanta don fitar za ta yi.

Tun kuma a ranar ta soma aiwatar da aikinta don kuɗin nan ba ƙaramin gigita ta suka yi ba, daga kudin da Bilkisu ta ba ta sai wadannan ta taɓa riƙe kuɗaɗe masu yawa a rayuwarta.

Ta yi sa’a maigidan ne ya sauke Bilkisu daga makaranta suna shiga wurin shi kuma bayan ƙannen Bilkisu sun shige wurin Bilkisun ta ba su lokaci sai ta bi baya.

Ta kafar makulli ta shiga leƙen su suna zaune a kujera daya abin da ta hango yana yi wa matar ta shi kafin ya ɗauke ta sukutum su shige ciki su ɓace ma idonta ya ɗaga hankalinta.

Take sha’awar da take kwana ta tashi da ita tun barowar ta ƙauyen su ta taso mata, tuna silar barin ta ƙauyen nasu na kamata da mijin makobciyarta kuma aminin Marigayin mijinta tirmi da taɓarya ya sa ta ja wani ɗan banzan tsaki.

Hoton abin da ta gani na ta yawo a idonta sha’awar ta na daɗa ƙarfi, ta miƙe ta fita dakin sai kofar Isiya mai gadi da ke bakin get.

Ba ta tsaya neman izni ba ko sallama ba ta ɗura kai.

Yana kwance kan shimfiɗarsa ya tada kai da hannayensa daga shi sai dogon baƙin wando idanuwansa na kallon sama.

Ganin ta bai sa ya tashi ba daga kwancen ya ce “Hajjo lafiya? Ta haɗiyi yawu tana jin kamar ta faɗa mishi,don kullum ta kawo mishi hira da kyar take mallakar kanta, bare kuma yau da ta same shi ba riga ga Isiyan irin gabjejen mutumin ƙauye ne, a shekaru zai yi sa’an ƙanenta na biyu.

Hira na zo maka Isiya.”

Ya ce “To ai sai mu je daga waje.” Ta ce “A’a, mu yi abin mu anan.” Sai kawai ta isa gaban shi ta durƙusa hannunta ta miƙa ta fara shafa kirjinsa, ya ɗauke hannun yana “Hajjo lafiya? Ta ce “Ita ta kawo haka, kai ba mata ni ba miji, ai sai mu taimaki juna.”

Ya tashi zaune ta kara mayar da hannun ya kuma riƙewa “Ai sai ki yi bayani Haj Hajjo indai taimaka miki, amma ni ai da matata, mero na can gida tana jira na, abin da ma ya dame ni kenan wata ya yi nisa kuma ina neman abin da zan mata aike.”

Ta kwance zanenta ta tura hannu cikin ɗan tohinta ta ciro kudin da Farha ta ba ta ta ajiye su gefensa “Indai kudi ne matsalar ka ga su nan.” Wani mugun murmushi ya saki ya kai hannu ya dafe kudin sai da ya sama musu maɓoya mai kyau sannan ya dawo kan Hajjo.
Kudin suka sa shi mance tunanin maigidansa da ya dawo ya shiga ciki.

Satin Mamana guda suka wuce Kaduna ya Safwan ya sa aka kai su ta ki yarda sam da cewar da ya yi ta zauna har sai an gama gyaran gidanta da na tabbatar ko Mami bai faɗa ma wa ba. Gidana ma da kyar ta yarda suka zo da Mami ba su fi awa biyu ba suka juya, ta tambaye ni yadda za ta je wurin Amir na ce Zainab za ta kai ta ita fa nan duk cikin ƙarfin hali take min abin da take yin saboda fillanci Ni ɗin diyar fari ce.

Da muka je mata sallama bayan wucewar su daga ni sai Mami da ya Safwan a falon Mamin ta shiga ɗaki ta fito da wani ruwa a farar gora ta miƙa mishi ya karba yana duban ta “Na meye Mami?

“Saƙon ka ne daga yaya A’isha. (Yayar Mami) Bata fuska ya yi “Ba na son shan wadannan abubuwan Mamina.”

Ta ce “Na sani amma daga yaya A’isha ne dole ka sha.” “To ki ce mata na sha.”

Ta ja tsaki “Ban san me ya sa ka mayar da ni kakarka ba Sadauki, amma bari in kira ta ita ai da ka san uwarka ce ta ce ka sha za ka sha.

Yana Mami kar ta kira ta sai da ta kira ta da suka gaisa ta miƙa mishi ya amsa yana gaishe ta ta ce “Ka ga saƙo ko, maganin tsari ne da ku yan boko ba ku damu da shi ba ba surkulle ba ɓata, da iznin Allah ba dai mutum ba sai Allah ka sha. Allah ya kara tsare mana ku.”

Ya ce Amin Ammi.”

Ya miƙa ma Mami wayar suka yi sallama ta juyo kanshi “To sha.”

Ya buɗe ya kafa kai sai da ya shanye ya wurgar da robar ya ce min “Tashi mu tafi.”

Mami ta ce “Ba wuni za ta yi min ba daga yau Lahadi.”

Ya girgiza kai har ya soma tafiya “A’a gida za mu.

Na tashi na yi ma Mami sallama na bi bayan shi.

Kwana uku kawai da fara harkar su ganin ficewar kowa gidan Hajjo ta nufi dakin maigadi sai dai duk yadda ta so ya ba ta hadin kai ya ce shi damuwar shi waya da zai riƙa ganin duniya ta ce kar ya damu indai waya ce zuwa gobe ya samu.

Sai ya waiwayo daga juya mata ƙeya da ya yi.
Sai dai suna cikin aikata masha’ar ƙarar horn ya karaɗe kunnuwansu, duk yadda take ƙara manne mishi raba ta ya yi da jikinsa ya rarumi wandonsa ya sanya ya zura riga ta juye ya fita sai da ya leƙa ya ga motar ya dawo ya wangale get Farha ta cuso kan motarta, sai da ta ƙare mishi kallo ganin yadda yake a birkice kafin ta wuce da motarta.

Ya rufe get yana faɗin a huta gajiya Haj. Ya koma ɗakin mamakin Hajjo ya kashe shi ganin ta yadda ya bar ta hankalinta kwance ya sa ya ce “To ki tashi Haj ta biyu ce, kuma kin san da ta dawo ke take fara nema. Ta yamutsa fuska “Kamar makauniya ko kuturwa ba? Komai sai an yi mata.”

Shi dai yana tsaye ya ciro asuwakin shi yana gogawa.

Ta yunkura ta tashi zaune ta lalubo zanenta ta fara daurawa sannan ta mayar da rigarta takalminta ta zura karshe bayan dankwali. Ta bar dakin tana faɗin “Kar ka rufe kofa zan zo da daddare.

Tsaye ta samu Farha a falo da alama neman ta take ta kama mata barka da zuwa. Ba ta amsa ba tambaya ta watso mata “Daga ina kike? Cike da ƙwarewa a makirci irin na Hajjo ta saukar da kai Ina cikin shuke-shuken can ina kallo, gidan naku ne Haj akwai ababen ban sha’awa. Dama jira nake ki dawo Haj, aikin nan zai fi kyau ina da waya babba da zan riƙa dauko miki komai kina gani da idonki.

“Plate za ki kawo min.”

Farha ta ce ba tare da ta amsa maganarta ba
Cikin sauri Hajjo ta dauki hanyar kitchen zuciyarta na wasuwasin ko za ta sawo wayar?

Don idan ba ta sawo ba tana ruwa, Isiya ya gane tsananin matsuwarta kan abin don haka bai taba yarda komai ya gudana a tsakanin su sai ta ba shi wani abu.

Cikin sa’a kuma washegari sai ga Farha da waya sabuwa ba ta yi wata-wata ba ta damƙa ta ga Isya sai dai ta roke shi idan bukatar ta ɗan ara ta taso za ta zo ya ara mata.

Da na dawo daki na shiga na cire hijab na ajiye jaka sai na dawo falon na zauna mun gaisa da Aunty Farha da na samu ta fito jefi-jefi ina satar kallon su da Hajjo da take sa aiki yi min wannan ɗauko min wancan.

Sai yamma zan karɓi girki Aunty Farha ce ta kwana da ogan.

Aka yi knocking Hajjo ta je ta buɗe mai gadi ne tsaye ya ce ina da baƙuwa na ce ya shigo da ita ya koma wa zan gani Haj Asiya ce matar kawun Hassan ban san sa’adda na miƙe tsaye ba na taro ta ina faɗin Oyoyo! Oyoyo! Cikin matuƙar fara’a ta galla min harara idonki kenan Bilkisu? Daga rabuwar aure sai ya zam shi kenan an rabu? Don ba ki tare da Hassan ba za mu yi zumunci ba?

Na ce “Tuba nake a yi haƙuri sannu da zuwa. Ta ce “Ma sha Allah aure har da rabo haka da sauri? Na rufe fuskata da tafin hannayena na ce shigo na yi gaba ta bi bayana suka gaisa da Aunty Farha Hajjo ta gaishe ta za ta zauna na ce mu je wuri na.

Falona ta zauna na kawo mata ruwa da lemo har da wani Cake da na yi sai na yi abincin da na yi kafin in fita da niyyar in ci da rana, don girkin Aunty Farha da daddare ne kawai take shiga kitchen su yi abin su ita da Hajjo, da rana ko safe kowa ya gane har ogan.

Ita kuma ta shige motarta ta bar gidan, Hajjo ta yi musu ita da mai gadi.

Na ajiye abincin gaban ta na zauna ina gaishe ta ta ce “Ashe kina duniya Bilkisu? Na ce “Ina nan.

Muka ɓalle hira tana ba ni labarin watangaririyar da ta samu Hassan daga fita ta rayuwarsa da halin da Inna da ya’yanta suke ciki da Ummu hani, yanzu ma Ummu hanin ta maido Hassan ya kora ta gida saboda rashin hankalin da take mishi kan zai yi aure. Da zai kai ta gidansu wadda zai aura shi ne ya nuna mata gidan Mami ita kuma ta ce ya kai ta Mami ta sanya a kawo ta wurina.

Mun daɗe har ta yi sallar ta ci abincin an kusa la’asar ta ce min za ta tafi wata leda ta ciro a hand Bag ɗinta ta ciro wata baƙar leda wasu kwalabe ne masu ban sha’awa ta ce “Kayan gyara na kawo miki mai gadon zinare in ji Hassan. Na yi murmushi”Da za ki ƙara martaba a wurin mijinki, kuma ga shi kina da ciki, duka turare za ki riƙa yi wa jikinki bayan ƙamshi na musamman da za ki rika yi akwai kuma sirrin riƙe miji gam! Ki kula da su da kyau. Ta ware wata kwalba “Shi wannan kin ga na ruwa ne a ruwan wankan ki za ki zuba, amma shi kam ki adana sai kin haihu don yanzu ba za ki iya daukar al’amarin da zai janyo miki ba. Idan na samu mai zuwa zan riƙa aiko miki da su.

Na yi mata godiya sosai ta ce “Kwashe su ki adana sai ki zo ki ba ni lambar ki.”

Na ce “To na kwashe na shiga ciki da na fito muka yi musayar lamba ina ta tunanin abin da zan ba ta na tuna da wasu hijabai da na ɗauko wurin Khadijah saƙar ƙasar Jordan guda shida na cire daya don shi hade yake da riga na sanya biyar ɗin a leda na fito ina mata rakiya.

Hajjo da Aunty Farha suna nan zaune Farha ta harde a cushion Hajjo na gurfane kusa da ƙafarta.

Muka wuce su zuwa inda direba ke jiranta na ajiye mata ledar a gefenta ya ja motar suka bar gidan.

Na koma ciki ina shiga Hajjo na buɗe ƙofar Aunty Farha za ta shige na dubi wurin sai na wuce ina tunanin alaƙar Aunty Farha da Hajjo yadda take canza salo ta daina daka mata tsawa, kodayaushe kuma Aunty Farha ke cikin gidan za ki samu Hajjo na gefen ta.

Kaya kawai na canza na fita zuwa kitchen har na fara aikin ban ji motsin Hajjo ta shigo taimaka min ba kamar yadda ta saba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mutum Da Kaddararsa 48Mutum Da Kaddararsa 50 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×