Skip to content
Part 50 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Farha na ganin fitar baƙuwar ta miƙe ta koma falonta.

Sai kuma da ta bada tazarar mintoci sai ta janyo wayarta ta kira Hajjo ringing ɗaya ta daga ta ce ta shigo.

Ta same ta tsaye ta haɗe hannayenta ta zube a ƙasa tana jiran ji daga gare ta.

“Ba wani labari? Farha ta fadi ba tare da ta waiwayo ba.

Hajjo ta gyara zama “Babu kam, don ban samu nasarar jin komai ba sai da hoto da na samu nasarar ɗauka na ta da wannan baƙuwa.”

Ganin ta miƙo hannu ta matsa ta miƙa mata wayar da ta amso da sauri wurin Isiya ganin isowar baƙuwar.

Farha ta zura wa hoton da aka dauka ido baƙuwar na kokarin ciro abu daga leda
Sai dai wace ce wannan baƙuwa da ta zo wajen ta Allah ya taimake ki?

Ta juyo ta yi mata wani kallo kamar ba za ta yi magana ba sai kuma ta ce “Ina ganin dangin tsohon mijinta ce, don na ji ta ambaci Hassan, Hassan kuma shi ne tsohon mijinta da ta bari.”

A ran Hajjo ta cika da mamaki dama Haj Bilkisu ta taɓa aure kafin mai gidan nan? Sai ta muskuta.

“In ko haka ne kaya ya tsinke mana a gindin kaba, indai dangin mijinta ce da haka za mu yi amfani kiɓata ta wurin Alh.”

Farha ta yi mata duban mamaki “Kamar ya? Sai ta fara karanta mata yadda za su yi karshe ta dire da cewa “Za mu saurara har in samu in fita in samo abun da za a sanya mata a daki.
Farha jin abin ya shige ta sai ta nemi guri ta ɗora mazaunanta ta zuba wa Hajjo ido, jin ta kai karshe ta ja ajiyar zuciya “Hakan ya yi na ji dadin shawarar ki, ki je kuma ki sanya min ido kan duk wani motsi na ta.”

Ta ce “An gama ta miƙe”Na barki lafiya ranki ya daɗe.”

Ta fadi tana ranƙwafawa sai ta fice.

Ɗakinta ta shiga ta kwanta kan katifarta cikin tunani ina ma Bilkisu ce ta nemi shawarar ta kan kishiyarta ta san ba karamin samu za ta yi ba.

Amma ita wannan komai ba ta iya ba ka, tun daga kudin farko ta kuma miƙawa Isiya ba ta kara dan ba ta wani abu ba kafin watan ya yi ta yi ƙwafa tuna dolancin da ta yi ta ce dubu goma ba ta san me ya ruɗar da ita ba da ta ambaci goman.

Amma in ta san wata ba ta san wata ba da sannu zan shirya mata gadar zaren da za ta riƙa ba ni kudi.

Ta yi dariya ta buga ƙafa tana yi wa kanta kirari.

Har na gama girki zan koma daki Hajjo ba ta fito ba.

Na fita zan je daki ta fito tana bata fuska “Sannu da aiki Haj, kin ga shiru ban fito ba kaina ke ciwo.”

Na yi mata fatan samun sauƙi da tambayar ta sha magani ta girgiza kai na ce idan na shiga ɗaki zan dauko mata. Ta hau godiya a zuciyarta kuma kudin ta so ta ba ta ta ce ta kai wa mai gadi ya sawo mata sai ta soke abin ta.

Ina cikin shiri kiran ya Safwan ya shigo ya ce ya dawo.

Na yi saurin kammala daurin dankwalin da nake yi na fita.

A bedroom ɗinshi na same shi sai muka fito tare na fara shiga kitchen na ba Hajjo abincinta da na mai gadi ta miƙa mishi.

Na samu Aunty Farha da mai gidan har sun fara ci.

Muna cin abincin ya ce ina lissafin gobe ne komawa ta asibiti?

Na ce “E.

Yana gamawa Aunty Farha ta miƙe ta ce tana son ganin shi sai ta yi gaba ya ɓata minti ya yi biyu sai ya mike ya bi bayanta.

Zaune ya same ta, kaya ta gabatar mishi da wata dandatsetsiyar sarka Dubai ta buƙaci ya ba ta kuɗin su suna da biki, a Zaria su take so ta yi amfani da su.

Ya dubi kayan da total na kuɗin su da ta ba shi ya ce “Kuɗin sun yi yawa Farha kina da yawan kashe kuɗi.

Cikin wani uban mamaki ta dube shi Safwan ne yau ke ce mata kudin da za ta yi hidimarta sun yi yawa.

“To ya kake so in yi? “Ki rage.”

Abin da ya ce mata kenan ya juya ya bar ta cikin takaici diyar Auntynta da ita ke sayar da kayan ta kira ta faɗi mata maganar banzan da Safwan ya gaya mata, bayan ya sha sai mata abin da ya fi haka.

Ta ce “Wallahi kar ki yarda,auren da ya yi zai sa ya tsiro miki da wannan banzan halin.

Da safe da na yi shirin komawa Hospital doguwar riga da hijab da na rage ban ba Haj Asiya ba na sanya sun yi matuƙar yi min kyau sai ƙara kallon kaina nake a madubi na fita muka yi kaciɓis shi ma cikin kwalliyar yake ya kuma yi kyau ba kaɗan ba.

“Kin yi kyau.” Abin da ya ce min kenan kamar mai raɗa.

Ba shiri murmushi ya ƙwace min,har a cikin mota murmushin nake ta yi ni kaɗai, don yau ce rana ta farko da na yi kwalliya ya Safwan ya yaba.

Ya jira ni har aka gama min komai aka yi min Scanning aka tabbatar da lafiyar abin da ke cikina.

Sai dai tun latsa cikin kasan marata ya fara min ciwo kaɗan-kadan, hakan ya sa da muka fito a hankali nake takawa don akwai yar tafiya zuwa inda ya ajiye motarsa.

Sai da ya yi nisa ya waiwayo gani na can nesa ya sa ya tsaya har na iso inda yake “Me ya faru? Ya tambaye ni “Na ce “Marata ke ɗan min ciwo.”

Mu koma ciki to, mu yi ma Dr complain.”
Na girgiza kai “Ba sai mun koma ba, yana yin haka idan suka lallatsa cikin.”

Wayarsa ya ciro ya kira Dr ya tambaye shi ya kuma tabbatar mishi ba matsala sai ya ce min mu je. Shi ma a sannu yake takawa muka jera muna ƙara tafiya muna ƙara kusantar wasu mace da namiji da ke tsaye jikin mota, sai kuma da muka zo daf da su na shaida Hassan ne da Ummulkhairi, gabana na ji ya fara bugawa ganin dukkan su biyun kallona suke ina kuma ganin alamun ummu hani magana take son yi min don har ta fara takowa na yi saurin buɗe mota na shiga gudun abin da Oga Sadauki zai tuna idan ya ga na tsaya wurin su.

Muna tafiya na ce ya kai ni gidan Mami, can ɗin ya kai ni sai kuma yamma sosai ya zo za mu tafi Mami ta dauko wata gora da aka zuba saƙe-saƙi a ciki ta miƙo min “Idan kun koma ki zuba ruwa a ciki kina sha, maganin zaƙi ne yaya A’isha ta aiko miki daga Safana.”

Na yi godiya ya ce “Mu gani.”

Na miƙa mishi ya ɗago yana duban ta “Mami meye amfanin shan waɗannan? Ga fa magunguna an ba ta a asibiti.”

Ta ce “Su ma da amfanin su, kar ki sake ki biye mishi na gaya miki, ranar naƙuda ke za ki yi a bar ki ba shi ba.”

Ya miƙe riƙe da hannun Afnan muka fita.

Sai da ya ciro duk abin da ya zo mata da shi ta karɓa ta koma ciki tana murna na bi ta da murmushi ina mamakin yarinyar ba ruwan ta da iyayen, tun ya Safwan na ƙoƙarin ɗauke a bar shi har ya hakura tana like da Mami.

Da muka koma kamar in ƙi fitowa cin abincin Aunty Farha sai dai ina idar da sallar ishai na yaye hijab ɗin na ɗauki wayata na fita.

Na zo taka step ɗin karshe da zai hau da ni dinning area wayata ta suɓuce ta kusa da ƙafar Aunty Farha ta faɗi fas! Ko ba a gaya min ba na san ta fashe.

Kai kawai na dafe Hajjo da ke kusa da wurin tana goge-goge ta ce “Subhanallah Allah ya kyauta Haj.”

Aunty Farha ta dauko wayar ta riƙe a hannunta tana jujjuya ta “Wayarki kenan Nana? Sai ta fashe da dariya “Mijinki na dilan waya, kina riƙe Iphone 11 ana yayin Iphone 14? Sai ta kuma kwashewa da wata dariyar ta ajiye wayar gefen plate din abincinta.

Duk da harbawar da kirjina ke yi na baƙin cikin abin da Aunty Farha ta yi min ƙarasawa na yi ƙafata sanyi ƙalau saboda yadda duk nake jin na muzanta, na zauna shiru ban dauki wayar ba ban kuma zuba abincin ba har sai da jikina ya ba ni kallona ake, na ɗaga ido ya Safwan ya tsare ni da idanuwansa na sunkuyar da kai don ban jin zan iya bin umarnin shi na san nufin shi in zuba abincin.

Miƙewa na yi na ɗauki fasasshiyar wayata na sauka wurin na wuce Hajjo da har lokacin tana ta goge-gogenta.

Gadona na hau na zuba wa wayar ido wayar da Mami ta ba ni ce lokacin da ya Safwan ya karbe wayata.

Gefena na ajiye ta na gyara kwanciya ba tare da na tuɓe kayan jikina ba.

Na yi nisa a tunani kafin na buɗe idona jin motsin shigowa, ya Safwan ne har ya zauna “Tashi ki tuɓe kayan nan ki kwanta.” Ya fadi idonsa na bisa kaina na tashi na fara neman kaya “Ki fita ki nemi abin da za ki ci.” Ya kara ce min.

Kai na girgiza “Ni na koshi.

Sai da na gama shirina na kwanta sannan ya ja min kofa ya fita.

Da safe ina kitchen Hajjo ta zo ta same ni izni ta nema za ta gano yarinyarta a gidan da take aiki.

Na ce “Ba laifi.”

Har yan kudin mota na ba ta.

Yau ma da na yi kwalliya da wata riga da na saya wurin Khadijah ya Safwan ya kuma cewa na yi kyau don haka ina dawowa makaranta Hafsat ta kira ni za ta shigo wuri na, sai na ce mata mu hadu gidan Khadijah.

Da na ce ma Khadijar “Kaya na zo dubawa, da na sa kayanki sai Oga ya yaba.”

Suka yi shewa ita da Hafsah ta ce “Sai ki duba kala uku na ɗauka don kayanta akwai kyau sai dai akwai kuɗi.

Muka gama hirar mu don ban wani daɗe ba muka fito tare da Hafsah.

Cikin kayan na ɗauki daya na sanya yana gama cin abinci na tashi na shiga wurin shi ina zama a falo sai ga shi wata leda da tun dawowar shi ya dawo da ita ya dauko sai ya zo ya zauna kusa da ni, kwalin wayoyi ya ciro guda biyu,ta farkon Iphone 14 ce sai ta biyun Galaxy S 23 Ultra. “Ina wayarki? Ya tambaye ni “Tana daki.” Dauko ta.” Na mike na tafi hango Hajjo da Aunty Farha a dan Corridor can idan za ka kitchen wurin da dan duhu ya sa na ji faduwar gaba “La’ilaha illah anta subhanaka inni kuntu minaz zalimin. Ita na shiga faɗi har na shiga na dauko na fito na kai idona wurin ba su.

Inda na tashi na zauna ya karɓi wayar ya buɗe ya ciro sima-siman ciki ya sa ma kowacce waya daya ya kunna wayoyin ya fara daukar daya yana shiga ko’ina ina jikinsa muna kallo tare.

Aka bude kofa muka dubi wurin a tare Farha ce “Sorry! Kawai ta ce ta saki ƙofar ta koma ya ja siririn tsaki sai ya cigaba da abin da yake da ya gama ya miƙa min su duka.

Na yi mishi godiya.

A ranar har tashi na yi a karshen dare na yi raka’a biyu na miƙa godiyata ga mahaliccin kowa da komai bisa sauyin da ya kawo a rayuwata.

Sai washegari da na dawo makaranta Aunty Farha ta ga wayoyina. Duk son fara’arta sai da ta gintse aka yi sa’a kuma ya Safwan ya dawo da wuri yana shiga wurin shi ta yi wuf ta bi shi.

Tun ba ma jin me suke har muka fara jin ƙarajin Aunty Farha na rasa wace shawarar zuciyata zan ɗauka me cewa in bar su su ƙara ta daga sun fi kusa, ko in shiga in ba su hakuri.
Ga Hajjo gefe daya tana ta Safa da marwa.

Na yunƙura na isa tana riƙe da kwalar shi duk tagwayen marukan da take amsa ba su sa ta sake shi ba daga jikin kofar na tsaya jin abin da yake faɗi.

“Wadda ba ta san mutunci ba, tun da na auri yarinyar nan ko ke za ki iya lissafin abin da na ba ki ita fa me na ba ta, kuma ba ta taɓa tambaya ta ba sai don na ba ta wayoyi za ki tsare ni kamar tare muke neman kudin, ai kin mata gorin mijinta na saida waya amma tana fama da tsohon yayi. Sake ni! Ta kara cakume shi ya kara kifa mata mari na ce “Don Allah ku yi haƙuri, ka ƙyale ta.

Ya ce “Fita anan ba ruwan ki.”

Na buɗe ƙofar na fita na koma ɗakina na kwanta hankalina na kan irin marukan da Aunty Farha ke amsa.

Da safe gaba ɗaya fuskarta ta tashi wata da ban sani ba ta zo suka fita sai kuma da ta kwana hudu fuskar ta dawo daidai.

Tana zaune a falonta Hajjo na tsugune gabanta wata baƙar leda ta ciro a jikinta “Kin ga abin da na samo Haj ranar da na ce mata zan je gano yarinyata.

Farha ta ce “To yanzu ya za a yi mu sanya shi a ɗakinta? Ta ɗan yi nazari “Zan ji da wannan Haj.”

Ta gyaɗa kai ta mayar da kanta ta kwantar ta san ta gama magana kenan don haka ta mike ta fice ta bar ta da tunanin yadda za ta samu su shirya da Safwan da ba su kula juna tun ranar da ta sha maruka a hannunsa.

Dole ta cire girman kai su shirya ta bi shi dakinsa zuwa safiya idan ta shawo kan shi ya huce sai ta aiwatar da kudurinta.

<< Mutum Da Kaddararsa 49Mutum Da Kaddararsa 51 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×