Na ja su muka yi falona, na ce su zo mu ci abinci suka ce in mayar da hankali.
Kukan wayata da na ji na tashi na ɗauko ta, Maimuna ce ina dagawa ta ce “Ina kika shiga tun safe ba ki daukar waya?
Na ce “Barci na yi ban daɗe da tashi ba.” muka gaisa ta tambaye ni yadda muka zo gida muka yi yar hira sai muka yi sallama.
Na dawo kan mutane na muka yi ta hira kusan wuni suka yi min don sai karfe uku na dibar musu tsarabar da na zo da ita suka tafi.
Na dawo rakiyar su aka kira ni a waya baƙuwar lamba ce, Ina ɗagawa muryar da ba zan taɓa mantawa da ita ba ta daki dodon kunnena.
“Hello kina lafiya? Abin da ta fara ce min kenan.
“Lafiya lau.” Na ba ta amsa “Kin gane mai magana?
Ɗan murmushi na saki “Ya ba zan gane ba? Kawata ce Ummu hani.”
Yar dariya na ji ta yi “Gaskiya kam ba ki manta ba. Ina son ganin ki Bilkisu, ina so mu sasanta tsakanin mu, saboda dai saboda Allah nake son ki.”
Na ce “Ba damuwa Ummu hani.”
“Ki ba ni address zan zo har gida.”
Wata faɗuwar gaba na ji tuna abin da ya faru a baya zuwan Haj Asiya.”
Na dai yi karfin halin cewa “Zan tura miki yanzu.”
Sai da na yi saving din lambar sai na tura mata address ɗin ta Whatsapp.
Har dare ranar tunanin abin nake na yi daidai ko ganganci na tafka na kiran Ummu hani gidana? Kar in je in ja ma kaina wata matsalar.
Muna chatting da ita har sai ranar da ta ce min za ta zo, ranar Asabar ce ya Safwan na gida kuma ni na yi girki da daddare don haka da ranar ma ni na yi girkin.
Muna zaune a falo ana cin abincin har Aunty Farha maigadi ya ce ina da baƙuwa na miƙe don taro ta, muka shigo tare ta gaisa da shi da kuma Aunty Farha muka wuce falona.
Tana zama duba na take da murmushi “Haka kika tsufa Bilkisu? Ban da na neme ki sai dai mu ji kin haihu.”
Na yi murmushi “Bari in kawo miki ruwa.”
Bayan ruwan har da lemo da Cincin da na yi na haɗo mata “
Kasan carpet na zauna na buɗe kafafu ina ƙara mata sannu da zuwa tana ci gaba da duba na cike da sha’awa, “Ma sha Allah, na taya ki murna Bilkisu daga zuwa kin samu ciki abin sha’awa, mu ko shiru.”
Na ce “Allah zai kawo.”
Muna ta hira tana faɗi min auren da Hassan zai yi, su Inna na ta murna.”
Na ce “Ki yi haƙuri.”
Ta ce “Ai tuni na haƙura, burina in ga na haihu.”
Na ce. “Allah zai kawo, ki yi ta addu’a.”
Kiran ya Safwan ya shigo wayata ban amsa ba, ce mata na yi ina zuwa.
Ba shi falon sai na wuce wurin shi tsaye na same shi cikin shiri bayan shi na tsaya na ce.
“Afwan. Ya ce “Kin samu baƙuwa kin manta da ni.”
Na ba shi hakuri da hannuna.
Ni zan fita.”
Ya ce yana nuna min kuɗi a kan mirror, na kwashe na bi shi da godiya muka fita falo, tare da Aunty Farha za su fita don haka ban raka shi wurin mota ba daga nan na koma wurin baƙuwata.
Sai da na sanya ma kofata key sai na zauna, tun ranar da aka ɗauki hotona na koma sa ma kofata key da zarar na yi bako.
Muka ci gaba da hira har yamma lis don ta ce Hassan ya yi tafiya.
Da ta yi shirin tafiya rakiya na yi mata har inda ta ajiye motarta sai da ta shiga na rufe mata ta leƙo da kanta “Ba ki ce in gaishe da Habibi ba daga ba yara? Na girgiza ɗan yatsana “Ki rufa min asiri.”
Ta yi dariya ta ja motar.
Washegari muka shirya zuwa gidansu Khadija ni da ita da Hafsah, za mu yi wa mamanta barka da zuwa ta dawo Umrah.
Dole na hakura da barcin da nake na tashi na shirya saboda kiran da ta addabe ni da shi in fa shirya da wuri wuni sosai za mu yi.
Na fito na samu Aunty Farha da ogan zaune muka gaisa da ita na kwantar da kaina a kujerar da yake na ce zan tafi ya ce “Tun yanzu?
Na daga kai “Khadija na ta kira.”
Kai kawai ya daga na yi ma Aunty Farha sallama na fita.
Ina tura get din Khadijah tsaye na hango su ita da Hafsah suka bi ni da ido har na isa inda suke.
Hafsah ta ce “Matar nan fa ta kusa haihuwa,cikin nan ya yi ƙasa.”
Ina ma yarta da ke hannun Khadija wasa na ce.
“Ai gara dai ya fito duk na gaji wallahi.”
Amma ai lokacin da saura.” Khadija ta tsoma baki dan tsaki na ja “Yanzu ya shiga na takwas.
A motar Khadijan muka yi tafiyar, gidansu na nan a Garki.
Babban gida ne na alfarma kamar sauran gine-ginen da ke unguwar.
Gidan part part ne muka nufi wanda ke bangaren kudu, mahaifiyarta ta tare mu da farin ciki mai yawa,
muka gaishe ta da yi mata barka da dawowa.
Ba mu daɗe ba ta yi wasu bakin ta bar mana falon muna ta hirar mu.
Sai da muka yi azahar muka ci abinci muka shiga sauran part ɗin, iyayensu uku ne Maman Khadija ce ta biyu.
Na uwargidan muka fara shiga ta amshe mu da fara’a ita ma ta sanya aka kawo mana abinci Khadija ta ce mun riga mun ci a wurin mominta.
Wata matashiya fara doguwa da tsawon ta ke tafe da jikinta ta shigo falon da sallama, tana arba da Khadija fuskarta ta washe da fara’a ta ce “Sisina ce a gidan? Khadija ta wurga mata harara “Mara kirki kawai, ke ba a ganin ki sai an zo gida.”
Ta ƙaraso ta zauna kusa da Khadijan tana duban mu “Sannu ku.” Muka amsa tasan Hafsah ta ambaci Maman Nana, muka gaisa sai ta dubi Khadija “Uzuri Sisina, aiki ke hana ni ziyara.”
Ta ce “Ba wani nan rashin kirki dai.”
Yanzu kin san wannan? Ta nuna ni ta dube ni tana murmushi sai ta girgiza kai “To ki canza hali Juwairiyya, Neibour dina ce watanta nawa da tarewa amma ba ki san ta ba.
Ta ɗauki files ɗin da ta shigo da su “Zan gyara Sisina, bari in watsa ruwa ina zuwa.” Muna nan zaune matasa na ta shigowa daga yan makaranta sai masu aiki .
Juwairiyya ta dawo aka kawo mata abinci tana ci Khadija ta ce “Ƙanwata ce Babanmu daya, bikinta ya kusa.
Wani kallo Juwairiyyar ta yi mata “Ni ce kanwarki? Ta kama dariya E mana.
“Wata ukun da kika ba ni ? Tana fadi tana nunawa da yan yatsunta. Khadija ta yi mata gwalo “Sorry baby na dai girme ki yarinya kuma dole a kira ni yayarki.” Ƙwafa ta yi ban fa yarda ba.
Sai da ta gama cin abincin muka yi wa mahaifiyarta sallama muka fita
Part ɗin amaryar muka shiga wadda ma’aikaciya ce dawowarta kenan ita ma cikin haba-haba ta tare mu, na lura gidan suna da hadin kai zaman lafiya ya samu matsuguni.
Da Juwairiyyar muka koma part ɗin su Khadija, ita Khadija su uku ne ita ce babba sai mai bi mata Namiji autar su mace ce da ke sakandare a yanzu.
Kiran da aka yi wa Juwairiyya a waya ta tashi Khadija na mata tsiya hubby ne ko? Ta daga kai da ta tafi sai take cewa “Tun da muka taso ban taɓa ganin namijin da Juwairiyya ta saurara ba, sai haɗuwar ta da wannan gayen tana masifar son shi ko da yake da mata.
Yamma sosai muka bar gidan matan uku kowacce sai da ta yi mana kyauta tare da godiya.
Kwana biyu bayan nan muna zaune gaban Mami ni da ya Safwan, sallama muka zo yi mata za ta tafi Safana gaisuwa na wata yarinya mai haihuwar fari da ta rasu wurin haihuwar.
Ta dube ni da kyau “Don dai tafiyar nan ta kama da ban tafi na bar ki ba, cikin nan gabaɗaya ya sauka ƙasa yana dab da fitowa.”
Cikin jin kunya na ce “Har kin dawo in sha Allah Mami.”
Ta ce “Allah ya sa. Na yi magana da Maman su Fiddausi (Mamana) ƙanwarta za ta zo ta zauna da ke da cikin satin nan za ta zo, amma ta ba da uzuri.
Idan na dawo ba ta zo ba ka bar ta kawai ta dawo gaba na Sadauki.”
Ya ce “A’a Mamina ki dai bar ta can.
Ni dai ina jin su dan na san wata na taran ma bai kama ba.
Kwana biyu Mami ta yi ta dawo ta dawo ne kuma tare da yarinya yar budurwa da ba ta fi shekaru sha biyar ba. Ɗiyar yayanta ce mai suna Sakina.
Tun zuwan Ummu hani muna chat muna kuma waya tana yawan yi min zancen auren da Hassan zai yi da kuma damun ta da abin ke yi, ina ba ta haƙuri.
Sai ga ta ta ƙara zuwa ta ce daga shi idan ban je gidanta ba ba za ta kara zuwa ba.
Na ce ta yi haƙuri ga tsohon ciki ga karatuna da ya kusan zuwa karshe abin sai a hankali.
Nan kuwa ina tunanin yadda zan taka ƙafata gidan Hassan nake saboda ya Safwan.
Kuka mai yawa ta yi a ɗakina kan fargabar da take ciki na wadda zai aura, haƙuri na yi ta ba ta, da shawarar ta yi ta addu’a sai Allah ya kawo mata maganin abin da take tsoro.
Ta ɗago ido cike da hawaye “Na so a ce ke ce kika dawo muka zauna nasan ba za ki cutar da ni ba, amma ɗiyar tsohon Ambassador Zayyad Mahuta, yaran da aka haifa a Abuja suka tashi a cikinta, karshen ta ma ta kwace mini Habibi.”
Cikin wani irin mamaki nake duban ta “Diyar Zayyad Mahuta zai aura? Ta daga mini kai hawayen ba su daina gudu kan kuncinta ba.
Na miƙa mata tissue na ce “Ko shi zai auri Juwairiyya?
Ta yi saurin kallona “Kin san ta ne ? Na daga mata kai “Yar’uwar makociyata ce, gidan na su kuma ba yadda take tunani ba ne in sha Allah za su zauna lafiya.
Ta tashi tafiya na fito rakiyar ta na ga ya Safwan a falo da ban san shigowar shi ba. Na yi mishi sannu da zuwa Ummu hani ta gaishe shi, aunty Farha na zaune tare da shi.
Muna fita ba ta bari na raka ta wurin mota ba ta ce “Na yafe miki tafiyar nan, koma ciki ki ji da kanki Allah ya sa ina komawa ki kira ni kin haihu.”
Ina murmushi na ce “Lallai kam da yake haihuwar shan ruwa ce.” Ta wuce na koma ciki.
Ina zuwa tsakiyar falon zan wuce su in shige ɗakina na tsinkayi muryar Aunty Farha “Nana wannan kuwa ba matar Hassan ba ce tsohon mijinki? Gabana ya doka da mugun ƙarfi, Safwan ya ji kamar ta yarfa mishi wuta danganta Bilkisu da wani.
Na haɗiyi yawu ba shiri na ce “Ita ce.”
Na ci gaba da tafiyata na shige su.
Gado kawai na hau ina tunanin abin da zai je ya zo.
Da yake ba ni zan yi girki ba ban fito ba ban kuma ga ya Safwan ba har sai lokacin da tunanina ya ba ni Aunty Farha ta shiga barci sai ga shi kashedi ya min kan abin da duk ya danganci Hassan don yana kishin shi.
Ranar da zan koma asibiti da direba muka tafi da na ƙare kuma na kira ya Safwan na ce zan biya a tsefe min kai.
Ina zama kafin ma a fara taɓa kaina sai ga Umma hani ta shigo wurina ta yo aka fara mana gyaran tare na ce “Ashe har yanzu kina zuwa nan? Ta ce “Tunda muka zo da ke ban taɓa fashin zuwa ba matukar zan yi gyara.
Allah bai sa mun taɓa haɗuwa ba. Muka yi ta hirar mu har aka kammala mana ni na biya kuɗaɗen ta nemi in zo mu je ta sauke ni na ce a’a ta bari direban zai dawo.
Muka dai fito tare da niyyar in ɗan taka mata mun kusa isa na hangi motar da ya Safwan ya fita ba kuma ko shakka shi ɗin ne a ciki take na shiga kiɗima sallama muka yi sai na nufi motar na buɗe na shiga na yi mishi magana bai amsa ni ba sai glass dinsa da ya ciro ya manna a fuska ya tashi motar.