Skip to content
Part 57 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Tana isa tuƙin da ta yi ko zaman da suka wuni suna ludo ji take duk ta gaji. Wanka ta yo ta sauya kwalliya ta fito ta ba Hajjo umarni ta shiga kitchen ta yi ma Safwan girki.

Shigar ta kitchen ɗin ya yi daidai da knocking ɗin Isya, Hajjon ta fita ta buɗe ya fara shigo da kayan mai gidan, ta ce “Alh ya iso kenan? Ya daga mata kai.

Cikin takun shi ya shigo falon Farha ta iso ta rungume shi suka wuce bedroom ɗinshi neman haɗe bakinsu take yi ya janye ta “Ban ci komai ba tun safe, ki ba ni abinci sai in gano Mami daga nan hakan sai ya biyo baya idan na watsa ruwa.”

Kamar ta yi mishi shiru sai dai ta ce “Indai Nana ce rabon ta da gidan nan tun ranar da ka tafi.”

Gaban shi ya buga halin da ya shiga ya kasa ɓoyuwa akan fuskarsa, kayan jikinsa kawai ya tuɓe ya ciro jallabiya ya zura ya dauki keys ɗinsa.

Farha ta yi turus! Ganin zai fice da sanyin jiki ta ce “Ina za ka? “Gidan Mami, zan dubo ko tana can.”

Cikin sauri ya fice ya bar ta da addu’ar Allah ya sa ba ta can.

Yana tuƙi yana addu’ar Allah ya sa ya same ta a gidan Mami, don yana can tunanin kar sharetan da ya yi ya sa ta shiga wani hali ga ta tana dauke da tsohon ciki, wannan zullumin ya hana shi wucewa gidan Mami direct kamar yadda ya saba duk tafiyar da ya yi can yake fara sauka. Ya yo na shi gidan ga babban tashin hankali kuma ba ta nan.

Ina kitchen ina yin farfesu na kayan ciki da na ji ina so duk da cewar da Mami ta yi in zauna a yi min na ce zan yi.

Har zoɓo na haɗa, ban fita kitchen ɗin ba ciki na zauna ina jira sai ya yi a haka na ji shigowar ya Safwan, ina kuma jin shi da Mami bayan tambayar shi hanya ya ce mata ina nan?
Ta ce mishi E.

Sai ga Sakina ta shigo ta ce in ji Mami ya Safwan ya zo.

Na fita na yi mishi Barka da dawowa fuskata ba walwala sai na koma kitchen tukunyar na sauke daga na kammala na ba mai aikin Mami wuri.

Na hada komai a tray na fito ban tsaya falon ba ina ajiye ma Mami na ta daki na wuce na zauna a ƙasa romon na fara diba a cokali ina sha sai ga shi ya shigo, na dube shi sai na maida idona cikin kwanon “Me ya kawo ki gidan Mami ba ki faɗa min ba?

Na ce “Ka yi haƙuri.”

“Wayoyinki fa da kika kashe?

Nan ma hakurin na ƙara ba shi.

Ya zauna gaba na zobon ya tsiyaya ya sha ganin sai kallon cikin kwanon yake na saki cokalin ya dauka ya fara ci, sai da ya gama ya kara shan zobon ya dube ni “Tashi mu tafi.”
Kai na girgiza na ce “Ka bar ni nan.”

Wani kallon hasala ya yi min “Wace irin magana ce haka in bar ki saboda me? Na mayar da hawayen da na ji za su zubo min “Ka bar ni nan, idan ka gama gyaran gidan na ta ta koma sai in koma.”

Wai saboda me? Ya kuma tambaya ƙin magana na yi amma a zuciyata cewa nake saboda zamana wuri guda da Aunty Farha babu alheri, neman ganin bayan aurena take.
Ina kuma ta jin ina ma zan iya faɗa mishi hakan.

Gajiya ya yi ya fita.

Na tashi na zauna bakin gado sai ga Mami “Lafiya Bilkisu, Sadauki ya ce kin ƙi tashi ku tafi? Ko jikin ne?

Na girgiza kai “To Yunƙura ki tashi ku tafi.”
Hawayen da nake ta tarewa suka kasa ruƙuwa saukowa suka fara suna ta gudu ! Ta shiga ruɗu sai ta shigo dakin sosai “Me ya faru Bilkisu me Sadaukin ya yi miki?

Kuka na fara sosai har na ji shigowar shi Mami kuma ta fara mishi tambayar me ya yi min? Ina fama da kaina, kai yanzu ba ta ba ka tausayi?

Ta fadi a karshe.

Ƙin fadi ya yi ya dai ce a yi hakuri mu tafi
Ni ta kara yi ma magana cikin sigar ba da umarni ba ta sigar lallashi ba. In share hawaye in fadi mata matsala ta.

Hakan na yi kaina na ƙasa na zayyane mata yadda aka yi ina gama fadi ina ba jin ajiyar zuciyar da ta saki ta dube shi “Ai ta gaya maka yadda za ka yi daga ka kasa gane me yakama ka yi. Ba zan saurare ka ba har sai ka karɓo abin da aka nuna maka da sunan magani ka je Islamic chemist ka tambaya, abin da duk suka ce maka sai ka zo ka same ni.”

Daga inda yake ya ce “Ki yi haƙuri Mami.”
Ba ta tsinka ba har ya fita.

Kusa da ni ta dawo “Ki yi haƙuri ki yi shiru makircin kishiya ya fi da haka, shi ya sa na ce ya je ya karba gara ya je da kan shi ya tambaya kila ko zai gano irin matar da ya ajiye.

Kar ki ƙara kuka ki yi ta addu’a kar kuma ki ƙara zama a daki kina tunani.”

Na daga mata kai ta tashi ta fita sai da na yi hawayen mai isa ta amma na halin Mami ne da ita har ta yarda da ni ta yarda ba zan yi abin da aka jingina min ba.

Da na gama na je na wanko fuskata na fito ina kallon kaina a madubi na dan jima a haka sai na dauko dankwalina bisa gado na daura na fita don bin umarnin Mami amma indan ni kwanciya kawai nake so in yi.

Ya Safwan na zaune sai kuma Daddy da ke saukowa daga saman shi ya isa wurin shi suka gaisa da yan maganganunsu, Daddy ya zo ya zauna na gaishe shi ya ce “Ba a tafi ba.”
Na ce “E Daddy.

Ya Safwan ya yi musu sallama zai tafi Daddy ya ce “A’a ya za ka tafi matar taka fa? Ya Safwan ya dubi Mami bai yi magana ba shi ma Daddy ya dubi Mamin “Anya kin kyauta Bilkisu ki riƙe mishi mata ya dawo tafiya? Ya Safwan ya ɗan tsaya ko zai ji Daddy ya bada umarni in tashi mu tafi sai ya ga Daddy duban Mami yake yana jiran jin ta bakinta sai ta ki magana.
Ya ce “Ka je zan roƙar maka ita gobe ta ba ka matarka idan na ji dalilinta na riƙe tan.”

Ya Safwan ba dan ya gamsu ba ya ce “Mu kwana lafiya.

Suka bi shi da Allah ya huta gajiya.

Anan na zauna har na ci abinci ana ta tsokanar Afnan ta kusa yin kane tana ta tsalle. Karfe tara na yi musu sallama ina yunƙurawa zan tashi na ji mara ta amsa, na dai yi kokari na mike na nufi daki a daddafe na yi shirin kwanciya na hau gadon ina sauraron mara ta sai dai ciwon bai yi tsanani ba yana kuma dainawa na shiga barci.

Tunda ya fara tafiya yake cikin tunanin abin yi har ya kai gida Farha ta tare shi tana tambayar ina Nanar ya ce tana gidan Mami.

Wanka ya shiga ya fara yi suka fito a wurin cin abinci aka sha bambam don girkin Hajjo ne ci daya ya yi ya tashi ya kuma kafa mata dokar kar ta kara ba matar can girkinsa. Ta ce to. Ya ce ta girko mishi abu mai sauki ya ci.

Daɗin ya dawo ba Bilkisu ya sa ta tashi ba bata lokaci ta daho mishi indomie ya ce hakanan ba su wani zauna ba ta kira Hajjo ta gyara komai suka wuce ciki.

Bayan lafawar komai a tsakanin su Farha ta shiga barci , shi kuma ya shiga tunani.

Da asuba da ƙyar ya tashe ta ya wuce masallaci.

Bai shigo da wuri ba har sai da gari ya fara haske ya koma don ya kara barci jiamma barcin ya gagari idonsa wayarsa ya yi ta latsawa har takwas ta yi ya shiga ya yi wanka ya fito ya shirya Farha ba ta motsa ba, a hankali ya rika taɓa ta har ya samu da yake barcin safe ne ta farka “Ina maganin nan? Ta ji tambayar a sama take kuma ta wattsake “Wane magani? Ita ma ta tambaye shi.

“Maganin da kika ga Mami ta sanya.”

Ɗan duru-duru ta yi har sai da ya maimaita.

“Na mayar na ajiye mata.”

“Shi ne ai na ce ki ɗauko min.”

Me za ka yi da shi Dear?

Ya fara gajiya

“Ki ɗauko min, Malama, kina ɓata min lokaci.”

Ganin ba fuskar da za ta kuma cizawa ya sa ta miƙe ba da son ranta ba ta koma kitchen ta ɗauko a hanya suka haɗu, ta ba shi tana tambayar inda za shi gidan Mami ya ce mata bai tsaya ba ta ce ya jira ta ta shirya za ta.

Wani kallo ya jefa mata ya yi tafiyar shi don bai san adadin sau nawa yana cewa su je tana ƙi ba.

Ta koma ciki tana taɓe baki tuna rabon ta da gidan, tunda suka ƙulla munafurcin ba shi Bilkisu suka sire mata.

Da asuba da na tashi ba ciwon komai sai dai ina fara wanka na ji ya dawo na shirya a daddafe, Sakina ta shigo ta gaishe ni ta ce.

“Mami na kira. Na bi bayanta.

Su biyu ne a falon ita da ya Safwan na gaishe ta sannan shi sai na kama hanyar saman Daddy ta ce “Rufa mana asiri ki hau sama a yadda kiken nan, Daddy ma ya fita wani soja da suka yi aiki tare yar shi ta rasu.”

Na furta Allah ya mata rahma.

Na zauna a hankali Iya mai aiki ta iso dauke da ƙaton tire ta ajiye gabana.

Na yi mata sannu ya Safwan ya ce “Ni Mami ba ku ba ni abincin na ku? Ta ce “Ka fito a gidanka wa zai ce ba ka ci abinci ba? In za ka ci sai Iya ta kawo maka.”

Ya ce “Ga na Mami zai ishe mu.”

Ba ta yi magana ba ƙasa na sauka ya taso ya zauna muka karya tare da yake na samu marar ta rage ciwon. Kafin mu gama ya kira waya ta yi sau uku yana gamawa kuma aka kira shi sai ya mike ya dauki makullan motarsa “Ina zuwa Mami.

Abin da ya ce kenan ya fice.

Muna nan zaune ya dawo yana zama ya ce ma Mami “Ki yi haƙuri Mami ta tashi mu tafi.”

“Ku tafi fa? Me na faɗa maka jiya?

Ya ce “Komai ya wuce Mamina, abar tone-tone.

Ta ce “Sai an tone komai.”

Ba don ya so ba sai don dagewar ta, ya ciro garin Habban ya miƙa mata.

“Ga shi Mami, daga Islamic Centre nake, sun tabbatar min da garin Habba ne har ma ga shi can na sawo mata da yawa.”

Za ta yi magana aka yi knocking Iya ta je ta buɗe Ummu Hani ce ta shigo da sallama ban ji ko ɗar ba har ta ƙaraso ta zauna kusa da ni tana gaishe da Mami, da suka gama gaisuwar ta gaishe shi sai ta dube ni ina yunkurin miƙewa mu je ciki “Yi zaman ki a hanya nake, na je ganin Dr ne na ce bari in leƙo in tambayi Mami lafiya kike wayoyinki a rufe?

Na ce lafiya lau nake.

Ta ce “Bari in wuce Mami a huta lafiya.
Kafin ma in mike har ta kusa ficewa na koma na zauna ina cije leɓe, Mami ta ce “Yaya dai?

Na ƙirƙiro murmushi “Ba komai.”

Ya ce “To mu tafi Mamina?

Ta ce “Ba za ta ba sai matarka ta koma na ta gidan, ba zai yiwu ta zo ta same ta a gidanta kuma ta rika shirya mata al’amuran da kai ba za ka gane shiri ba ne sai ka hau kai ka ƙuntata mata.”

Ya yi kalar tausayi “Haba mana Mamina, ki daina komawa gefe daya dukkan su naki ne.”

Sai na ga jikinta ya yi sanyi ta ce “To ya kake so a yi?

“Ki ba ni ita mu tafi, in sha Allah ba za a ƙara ba, zan matuƙar kiyayewa.

Yau za a ci-gaba da aikin gidan Farha ba kuma za a tsaya ba sai an gama. Gobe kuma za ta wuce Zaria bikin ƙanwarta.

Ta ce “Yau ne na biyu Sadauki, aka ƙara na uku ba zan saurare ka ba, har Daddy sai ya ji.”

Ya ɗan buɗe ido “In sha Allahu ma wannan ne na karshe ba za a ƙara ba har Daddy ya ji.

“Tashi mu tafi.” Ya ce min amma na ƙi motsi ya kara maimaitawa ban tashin ba. Mami ta ce.

“Tashi ki yi haƙuri Bilkisu ku tafi.”

Na share hawayen da suka taho min “Ban da wannan akwai abin da yake min Mami.”

Ta dube ni da sauri sai ta tambaye ni cikin kwanciyar hankali “Me yake miki?

Shi ma zubo min ido ya yi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mutum Da Kaddararsa 56Mutum Da Kaddararsa 58 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×