Skip to content
Part 58 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Ta dube ni da sauri! Sai ta tambaye ni cikin kwanciyar hankali “Me yake miki?

Shi ma zuba min ido ya yi na ce “Zuwan nan da Ummu Hani ta yi shi ma wani laifi ne da zai tuhume ni akan shi.” Fuskarta ta cika da mamaki “Akan me? Ya hana ni mu’amala da duk wanda ya shafi Hassan.”

Wannan shi ne ƙarya Sadauki, akan me? Shi kenan mutum idan aka hore mishi mace, mai ladabi da biyayya sai kuma ya shiga cikin lamarin ta ya hana ta sukuni?

“Ba haka ba ne Mamina.”

Ya Safwan ya faɗi “Haka ne mana. In ban da haka me ya dame ka da yan’uwansa? Ina ce mata ne suka yi ƙaurin suna kan kishi, to wannan dai matarsa ce kuma tana sane Bilkisu ta auri mijinta ga shi kuma tana mu’amala da ita. Sai kai shugaban yan kishi za ka hana ko shi ma an faɗa maka tana hulɗa da shi?

Ya ce “Kai Mamina.”

Ta ce “Allah kuwa ai zai iya yiwuwa haka.

Ƙawarta ce sun hadu da juna tun ba su san sun auri miji daya ba, suka so juna saboda Allah, yanzu kuma kowacce da mijinta ka bar ta su yi zumuncin su, ko ka taɓa kama ta da wata mu’amala da shi?

Ya ce a’a ta ce “To na roƙe ka ka bar ta da ƙawarta. Ina ƙara roƙon ka ka riƙe wannan kyauta da Ubangiji ya yi maka ta mace ta gari.
Ba kowane namiji ake ma wannan baiwar ba.”

Jin ta yi shiru ya ce ta yi haƙuri ya bari in sha Allah.

Ta sanya Sakina ta dauko min jakata da mayafi, ina miƙewa marar ta dauka hakanan na cije har na isa wurin motar.

Mun isa gidan, Aunty Farha ba ta nan sai Hajjo bai zauna ba ya ce min yana zuwa ana neman shi kan wata harka.

Kwanciya na yi na yi ta fama da marar sai da ta lafa na kwanta barci, na daɗe da na tashi na tashi lafiya na shiga kitchen na girka abincin da zan ci na fito muka yi kaciɓis da Hajjo na san me ya kawo ta abincin da na dafa ta gama fadancinta ni kuma plate daya kawai na yi, na ma yi mamakin inda ta makale har ta makara na gama girkin, don da ƙamshin girkin ya isa hancinta za ta garzayo.

Na ce “Ba ki yi muku girki ba ne? Ta rausayar da kai “Na yi.”

Na wuce ta zuwa falona, ban yi girkin dare ba da nasan ni ce zan yi ban kuma fito ba sai ga shi ya same ni na yi ‘mishi sannu da zuwa ya ce “Ya ya dai lafiya kike ko?

Na ce “E. “Abinci fa na ga wayam! Na ce “Ban yi ba.”

“Saboda me? Na tura baki “Na karɓi kuskurena na ce a yi haƙuri.”

Nan ma ban yi magana ba “To taso ki raka ni in ci abinci.”

Na ce “A gajiye nake sai ka dawo.”

ya ce “Ba sai kin fito ba, ki yi zaman ki a mota in shiga in karɓo, idan muka dawo sai in ci.”

Na tashi don sanyo takalmi da mayafi da na fito yana a inda na bar shi muka fita tare.

Aunty Farha tana zaune na ce mata ina wuni? Muka gaisa ya ce mata yana zuwa.

Daidaita tafiyarsa da tawa ya yi har wurin motar don da kyar nake cira ƙafafuwan, ji nake kamar abin da ke cikina zai fito.

Farha da ta raka su da wani mugun kallo ta buga mummunan ƙwafa da har ta sa Hajjo da ke jiran umarnin ta saboda kiran da ta yi mata saurin kallonta.

“Kan wannan banzar shashashar yar aikin Maman shi yake wannan lalacewar.”

Ta ja wani ɗan banzan tsaki!

Kalmar yar aikin Maman shi ta daki Hajjo ta kuma tsaya mata duk da halin da ta ga Farha ta shiga na mummunan ɓacin rai kasa daurewa ta yi “Ranki ya daɗe kina nufin ita ɗin me aikin babar Oga ce? Farha ta dube ta da yake cikin ɓacin rai take sai ta buɗe baki tana ba Hajjo amsa “E mana aiki aka kawo ta daga nan Daddyn shi ya haɗa shi aure da ita. Shi ne yake wannan sakarcin.”

Daga haka wucewa ta yi cikin sauri ta shige wurin ta.

Hajjo da ta zura wa wuri guda ido tun jin maganar da ta daskakar da ita ta zabura ita ma ta kama ta ta hanyar.

Kan katifarta ta kwanta ta tafi duniyar tunani tuno zubin Bilkisu take da gogewarta wai nan kuma daga aiki ne ta zama haka, tirƙashi! Ta kuma samu nasarar aure namiji mai tsada kamar Safwan.

Take wani tunani ya shige ta in kuwa haka ne ma zai hana ta gwada ta ta sa’ar, take idonta ya fara hasko mata yar ta Sha’awa ta zama matar gida, ba ta kuma dace da mijin matar da take wa aiki ba don ba wani shege ba ne ya dai mallaki gidan kanshi da motar shiga a Kaduna road.

Shi ya sa suna samun aikin ta yi ƙoƙari ta tura yarta ƙauyen ita ta shigo birnin.

Amma yanzu dole za ta ɗauko Sha’awa ta dawo da ita nan su farauto Safwan Abdullahi Safana.

Ta san Haj Bilkisu da sauƙin kai tana marairaice mata za ta amince ta ɗauko ta, bari za ta yi sai an yi albashi na wannan sabon watan da aka shiga sai ta ɗauko ta.

Kamar yadda ya ce shi kaɗai ya shiga ƙayataccen wurin da jama’a ke ta karakaina motoci ne na alfarma suka cika wurin kai idan ka ga jama’ar da ke zuwa za ka sha mamakin wai ake talaucin da kullum ake faɗi.

Don masu riƙe da Nigeriar da ya’yan su ke zuwa wurin.

Bai dade ba ya fito a baya ya ajiye ledojin ya shiga sai da ya zauna ya dubi inda nake “Yaya dai? Naē ce “Lafiya lau.”

Ya tashi motar.

Kamar yadda na yi zato ba wanda za mu samu a falon hakan ce ta kasance.

Wurina na wuce ya biyo ni da ledojin ya zauna ya buɗe ya ce in zo mu ci.

Na zauna a ƙasan na buɗe ƙafafuwa, kaɗan na ci ba don na gane daɗin abin da na cin ba sai don matsawar shi kan in cin

Ba wai ciwo ke damuna ba akwai ciwon amma kadan ne, abin da ya fi damu na ji nake yi kamar ana turo ni .

Da kare cin ta sa ni ya yi zuwa wurin shi da na ji kamar ya ƙyale ni in kwanta a ɗakina zan fi sakewa don ban son abin da zai raɓe ni.

Muna shiga na ce zan koma in ciro key na ƙofata da na manta ban cire ba, ya ce bari ya ciro min.

Yana fita ya ga kamar mutum a duhu ya kunna wayarsa yana mamakin wanda ya kashe komai na wurin ya kunna wayarsa sai ga Farha cikin mamaki ya ce “Me kike yi cikin duhu Farha? Wai ruwa za ta sha, ya ce shi ne za ki kashe komai kina tafiya cikin duhu, dama ba ki yi barci ba?

Ta yi shiru ya wuce ta ya cire keyn tana tsaye har ya shiga ya rufe.

A wannan dare wata irin kwanciya na yi mai tsananin wuya, wadda barci ya gagara dauka ta.

Kwana na yi zuwa bayi fitsari duk da yawaitar fitsarin da na samu tun fara girman cikin na yau daban ne.

Na dai yi kokarin hana kaina motsin da zai tayar da ya Safwan don har yanzu ciwon ya ƙi kankama. Kusan asuba ya sake ni ana yin sallar asuba na kwanta barci da ban tashi ban tashi ba sai karfe goma na safiya ya Safwan ya ce min zai fita zai kai Farha gidansu daga can za ta wuce Zaria.

Na ce To. Na zura hijab saman rigar barcin da ke jikina na bi shi muka fita a falo na zauna ya shiga wurin ta ba jimawa suka fito tare muka gaisa na yi mata fatan alheri suka fita na koma daki na fara shiga wanka sai dai ina watsa ruwa ciwo ya ce gani nan da kyar na gama wankan na fito na zauna bakin gadon kamar ba wanka na fito ba zufa ce ke wanke ni ta ko’ina, na janyo wayata na kira Mami tana ɗauka na ce mata ba ni da lafiya. Ta ce ina Sadauki na ce ya riga ya fita.

Na wurgar da wayar ina kiran sunayen Allah na sauka gadon na durƙusa a ƙasa ina fama.

Mami ita kadai ta iso ta kama ni zuwa mota sai da na zauna ta tambaye ni inda kayan haihuwar suke na faɗa mata ta fita ta dauko muka kama hanya.

Ana shigar da ni dakin haihuwa haihuwar na zuwa da taimakon Nurses guda biyu da ke tsaye bisa kaina jaririna katoto ya iso duniya.

Sai kuma da aka shirya shi aka miƙa wa Mami ta tuna ba ta kira ya Safwan ba ta kira shi ta sanar da shi sannan Daddy sai Baba na Kaduna, sai Gwoggo Maryama, sai yayarta Mamana ta kira karshe ta ce gobe ƙanwarta Inna Jamila na nan tafe.

Nan ta shiga amsa kiran waya ana ta yi mata barka har aka zo aka ce mata an fito da ni za ta iya shigowa ta gan ni.

Ta same ni a dakin da suka mayar da ni abokin ya Safwan likita da ke ta kai da kawo a kaina tun kawo ni har aka sallame mu ba tare da mun jima ba na huta kamar yadda ƙa’idar su take ya ji roƙon da na yi mishi na ce a sallame ni in je in huta a ɗakina.

Motarmu na fita asibitin ta ya Safwan na kunno kai Mami kuma ta hana direban tsayawa kamar yadda ya Safwan ya so sai dai ya bi mu a baya.

Motocin na tsayuwa rumfar adana motoci na gidan ya Safwan ya fara fitowa ya nufo mu inda Mami take ya bude ta fito riƙe da babyn ya karɓa ta leƙo tana cewa in fito, ta so ta kama ni na ce zan iya. Isya ya zaburo fuskantar abin da ke faruwa sai Barka yake bakinsa ya ƙi rufuwa.

Muna shiga ciki Hajjo ta cika da mamaki haihuwa kika yi Haj ina cikin gidan nan ban ko ji motsi ba?

Tana so ta ga yaron ya Safwan ya riƙe abin shi a ƙirji.

Da shigar mu daki kwanciya na yi a gado na lalubi wayoyina duka biyun kiran Zainab ne . Sako na tura wa Hafsah da Khadija har Ummu Hani sai na kira Zainab.

Iya mai aikin Mami da ta ce ta zo tun muna hanya ta iso ita ta haɗo min Tea na sha ta kuma shiga kitchen yi min abinci.

Hafsah da Khadija tare suka shigo ya Safwan dai sai hakura ya yi da gani na ya turo min saƙo ya fita ba abin da ke damu na.

Duk da sururun su Khadija barci na yi sai da na tashi na ga Ummu Hani.

Da yamma bayan mun yi wanka Mami ta tafi tare da Daddy da ya zo ganin abokinsa. Ta dai bar min iya.

Ya Safwan ya dawo suna tafiya ya shigo ya same ni Ni kadai da babyn ya yi ta kallona yana kallon yaron ba sai an gaya maka yana cikin farin ciki ba, sai da aka kira sallah ya fita masallaci ni ma na samu damar kallon yaron ina ta jin dadi sai kuma na tuna Amir sai na ji duk ba daɗi.

Da ya dawo nan ya dawo Iya ta kawo abinci ya tafi ya tuɓe kayan jikinsa ya dawo muka ci abincin sai ya kira Aunty Farha sai da suka gama maganar su ya miƙo min ta yi min Barka na yi mata murnar biki.

Anan muka kwana tare da shi muka sanya babyn tsakiya da ya motsa ya Safwan zai tashi Ni kam kyale ni ya yi na sha barcina.

Ɗagowar hantsin washegari Gwoggo Maryama ta iso. Inna Jamila ce sai dare tare da su muka kwana ya Safwan ya kwana na shi.
Kwanan mu huɗu Gwoggo Maryama ta koma ta bar ni da Inna Jamila da ke matukar kula da ni.

Farha da ke zaune dakin Mamanta ranar ɗaurin auren ƙanwarta da daddare gidan ya dauki shiru duk da yake na yawa saboda kusan duka jama’ar gidan sun tafi raka amare dakunan su, da yake yammatan hudu ne aka aurar a gidan.

Daga Mamanta sai Auntynta da ta iso da yammaci suke zaune su ma gidan Auntyn na nan Zaria za su tafi can Farha za ta kwana da safe Auntyn za ta wuce Kano can ma suna da gida don can ne mahaifar mijinta.

Kiran Safwan ya shigo wayarta tana ɗagawa ya ba ta albishir Bilkisu ta haihu namiji.

Kamar ta yi cilli da wayar don yadda ta ji amma ta dake suka gama maganganunsu ya haɗa ta da Bilkisu ta yi mata barka, suna gama wayar ta barke da kuka! Mamanta da Auntyn suka shiga tambayar abin da ya faru cikin kuka ta faɗa musu Bilkisu ta haihu kuma namiji ta haifa shi kenan an karɓe mata gida da miji.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mutum Da Kaddararsa 57Mutum Da Kaddararsa 59 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×