Duk yadda suke fadin ta yi shiru ta saurare su hakan faskara ya yi har sai da Auntyn ta mike ta ce za ta yi tafiyarta, ta saurara tana raba ido.
Rarrashinta suke ta yi Innarta ta janyo wani kwano mai murfi ta buɗe ta ciro wani ƙullin magani a baƙar leda "Ga maganin masu fama da matsala da ta hana su haihuwa, na karɓo miki, an ce kasadin ne ki gwada.
Farha ta yamutsa fuska "Ni Inna na ce miki ban iya shan irin wadannan abubuwan."Ta ce "Da kin gwada, ana dacewa." Ta girgiza kai. . .