Skip to content
Part 59 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Duk yadda suke fadin ta yi shiru ta saurare su hakan faskara ya yi har sai da Auntyn ta mike ta ce za ta yi tafiyarta, ta saurara tana raba ido.

Rarrashinta suke ta yi Innarta ta janyo wani kwano mai murfi ta buɗe ta ciro wani ƙullin magani a baƙar leda “Ga maganin masu fama da matsala da ta hana su haihuwa, na karɓo miki, an ce kasadin ne ki gwada.

Farha ta yamutsa fuska “Ni Inna na ce miki ban iya shan irin wadannan abubuwan.”
Ta ce “Da kin gwada, ana dacewa.” Ta girgiza kai ta ƙi karɓa Auntyn ta ce “Idan muka koma Abuja za mu je ki ga Dr Gobir.”

Ta dube ta “Ni Aunty bin ki Dubai zan yi, ba zan koma gidan nan ba mutane su taru ina nan, baƙin ciki halaka ni zai yi.” Dukkan su zuba mata ido suka yi Auntyn ta ce “Ta ya ya hakan zai kasance ke da kika taho biki? “Ki kira shi ki tambaye shi Aunty, zai amince.”
Kaɗa kai ta yi “To tashi mu tafi. Gobe zan kira shi.”

Don dai ita a duniya tana son Farha tunda aka haife ta, shi ya sa tana fara wayo ta ce a ba ta ita.

Nan take Farha ta har haɗa na ta ya na ta suka yi ma Innarta sallama suka tafi suka bar ta da juyayin Farha ba za ta tsaya gobe a yi buɗar kan ƙanwarta ba.

Washegari sai da suka gama karyawa ta kira Safwan da ya yi tunanin barka ta kira ta yi mishi sai ya ji saɓanin haka gaya mishi take za ta tafi da Farha Dubai za ta ga wani Dr kan batun haihuwa.

Haushi ya kama shi ta ko’ina kawai ya ce sai sun dawo.

Ta wurgar da wayar tana jan tsaki, Farha ta matso “Me ya ce?

Ta kuma jan tsakin “To zai hana ki ne, daga shi haihuwa ga ta nan an fara mishi ke kuwa fa?

Dole ya bar ki ki nema daga ya tattara ki ya ajiye, ya daina kai ki ko’ina ki nema.”

A ranar suka bar garin zuwa Kano a can suka kwana uku suka ɗaga zuwa Dubai, ita da Auntyn da yaran Auntyn.

Ranar suna yaro ya amsa sunan Abdullahi sunan Daddy a maimakon sunan Babana da tun ban haihu ba ya Safwan ya yi min albishir zai sanya min, abokin Daddy da suka zo a ranar da na haihu shi ya yi ma yaron huduba da sunan Daddyn.

Baban Kaduna ya zo a safiyar suna shi da Mama suna kuma ganin mu suka juya.

Na ga jama’a daga ko’ina Kaduna su Zainab sune gaba har da Amir ta je gidan su ta ce a ba ta shi za ta taho da shi Abuja Maman shi ta haihu. Sai kuma sannan ya Safwan ya gama komai na makarantar da zai sanya shi ana komawa hutu.

Maimuna ma ta zo, Ummu Hani su Khadija da ahalin su duk sun hallara, Raihan ma ta zo daga Bauchi. Ga kuma yan Malumfashi.

Na yi kyau har na gaji ga abin duniya da na samu abin sai dai godiyar Allah.

Mami ta bar mana Iya ga Inna Jamila ya Safwan ya nufi Lagos kwana biyu da yin suna sai da ya yi sati guda ya dawo, har kuma sannan Aunty Farha ba ta dawo ba sai da Mami ta zo ƙara duba mu take fadin da suka gama biki ta bi Auntynta Dubai.

Kwanan mu ashirin cif Aunty Farha ta dawo shigowar yamma ta yi, ina wanka ta shigo wurina sai ta zauna a falo da Inna Jamila.

Na fito wankan na shafa mai na murtsuka hoda na sanya turare sai na sanya doguwar riga mai girma saboda Inna Jamila don ba ta yarda ko kaɗan in yi wani abu da ya danganci kwalliya ba wai in kama kaina in yi jego mai kyau. Na daura dankwali na rufe har kunnuwana da ta ce iska na shiga ta kunne kafin na lulluɓe da mayafi sai na sha Supplement da nake sha na gyara kaina tun da na haihu.

Ina gama sha na fita zuwa falona na samu Aunty Farha da Inna Jamila Aunty Farhan na fadin ba ta iya riƙe jarirai ta dai leƙa shi a cinyar Inna.

Na ce “Barka da dawowa Aunty Farha.

Da fara’arta ta ce “Mai jego kun gan mu sai yau?

Na ce “Ai kam kamar ba za ku dawo ba. Afnan ma jiya aka mayar da ita gida fir ta ƙi komawa gidan Mami saboda Mashkur.

Ta ce “Ai dole ta koma an koma Sch.

Ta ɗan jima da mu ta tashi ta tafi Inna Jamila cikin murmushi ta ce “Kin dace abokiyar zama Bilkisu mai kirki da ita.”

Na yi murmushi a raina na ce “Ai fa sai kirkin.

Muka cigaba da hirar mu kafin ta tashi ta zubo min tuwon da Iya ta yi min, na ci na koma ciki.

Ya Safwan da ya dawo ya duba mu sai ya ɗauki Mashkur ya fita da shi.

Ba ma doguwar hira karfe tara mun kwanta ga sa’ar da muka yi yaron ba shi da rigima sai mu kwanta lafiya.

Na kan sha Tea kafin in yi barci na taɓa flask ɗin na ji ba ruwa nasan Inna ta shafa’a ne na ɗauki flacks ɗin zan fita ta ce ina za ni? Na ce mata ba ruwa ta ce to maza ɗauki mayafinki kul da barin jikinki haka.

mayafin da na cire na dauko na rufe jikina na sanya takalmi na fita. Saboda ya Safwan na falo a daidai wannan lokaci shi ya sa ba ta karɓa ta zubo min ba.

Da Aunty Farha idona ya fara arba ita da ya Safwan kamar za su manne da juna ta sha kwalliya cikin wata ubansun riga gashinta ya sha gyara ta sake shi ta yi kyau da gaske ƙamshinta mai daɗi ya cika wurin.

Wani abu ya zo ya tsaya min har na manta ya kamata in yi musu sannu don wuce su kawai na yi Kettle na jona na sanya kayan ƙamshi ina tsaye ina jiran ya tafasa zuciyata har lokacin ina jin abin da na ji da na gan su.

Da na gama na juye na ɗauka na fito ban same su ba, sun tashi har na kwanta ina tunanin ko me suke ciki yanzu, abin ya tsaya min a rai da kyar na yakice na yi barci.

Da safe Mami ta kira kamar yadda ta saba don jin lafiyarmu ta ce Iya ta taho gida daga matar gidan ta dawo na ce mata To.

Sai da Iya ta shigo da abin karyawa na fadi mata abin da Mami ta ce ya Safwan ma da ya shigo cikin shiri zai fita na faɗi mashi saƙon Mami.

Ya ce “Ita kuwa Mamina ta bari ta ƙarasa ladarta ki gama wannan jegon na ki da ya ƙi ƙarewa?

Ya ɗan rage murya “Wai yaushe za ki gama?

Na yi murmushi ina nuna mishi ƙofar bedroom ɗi na ya dubi wurin “Wai Inna? To tashi mu je wuri na. Na girgiza kai “Rufa min asiri mallakin Aunty Farha ne ita kaɗai.”

Kudi ya ciro ya ce in ba iya, na taya ta godiya, ni ma turmi biyu na atamfa na ba ta da kudaden na yi mata godiya sosai.

Direba ya tafi kai ta tare da Inna Jamila da za ta gaida Mami. Shiru na ji Inna Jamila da nake sa ran ta dawo ta yi min girki, don ita ke sakalta ni komai sai ta yi min, wai in kwanta in huta in yi jego mai kyau.

Ai kam na yi kyan ba na wasa ba na ƙara cika sai sheƙi nake.

Dole na fita na ɗora tukunya sai ga Alhajiya Hajjo ta shigo Ranki ya daɗe yau za a karbi turaka kenan?

Na juya na dube ta cike da mamaki ta yi yar dariya “Allah na tuba Haj ai ko daddaɗan girkinki ya sa Alh ya yi kewar ki, ballantana siga da sura ta mace kowa ya tabbata akwai banbanci.”

Kallona ta yi saurin yi, ganin na saki baki ina kallon ta sai ta shiga kame -kame “Kodayake ita ma Iya akwai baiwar girki ni da dayar hajiyar ce sai godiya Ina ruwan a ci kar a mutu, sunan wani abu a garinmu w…

“Hajjo na kira sunan ta da dan karfi ta zabura “Ranki ya dade. Me za a taimaka miki da shi?

Na ce ba komai.

Ta Ci Gaba da tsayuwa ta ƙi fita, nasan so take in yi da ita ta ce “Ina Baban masu gidan? Na ce “Ya yi barci.” Ta ce “Allah dai ya raya mana shi.”

Tana ta min surutu har na gama na zuba nawa na bar mata saura a tukunya na fita na zauna na fara ci kiran ya Safwan ya shigo na ɗaga mashkur ya fara tambaya ta na ce yana barci ya ce “To ki yi min girki da daddare.” Na ce “Ya Safwan ba fa yanzu zan karɓi girkin ba sai na yi arba’in.”

Ya yi ɗan murmushi da har na ji shi a kunnena Cool down Sarkin jego. Ai na yi haddar wannan sai kin yi arba’in amma ki taimaki mijinki.

Da plate din abincin da zai ci.”

Kamar zan yi kuka na ce “Wata da kwana da miji ni da girki.”

Ya ce “E lada za ki samu.”

Ya kalallame ni na amsa zan yi .

Sai kusan La’asar Inna Jamila ta dawo. Ganin na shiga wanka tun La’asar ta ce “Yau kuma wankan da wuri za a yi? Na ce “E. Ina ta fargabar yadda za ta gane zan yi girki, ba ta rasa cewa ma mijin nake so don kullum takararta kenan matuƙar mace ba ta bari ta yi arba’in ba ta koma ma miji ba ta komawa daidai. Na rasa sahihancin wannan hadisi na Innar tawa.

Na dai gama wankan na sanya riga da zane na atamfa bayan na tsuguna kan wani turaren wuta na tsugunow bayan masifar ƙamshin shi yana kuma tsuke gaban mace, kudi masu yawa na saye shi na daura dankwali har kunne na rufe na yi lulluɓi na fita na samu Inna zaune a falo tana jijjiga mashkur da ya tashi barci ta miƙo min shi tana faɗin ba shi ya sha. Na karɓe shi na zauna ina shayar da shi muna hira sai da ya koshi na sanya shi a kafaɗa ya yi gyatsa na tashi na miƙa mata shi ta sanya zane ta goya shi na kama hanya zan fita ta ce “Ina kuma za ki? Na ce ya Safwan zan yi ma girki Inna.”

“Girki kuma da wannan danyen jegon? Kenan ni gobe sai gida mai jego ta kama mijinta.”

Na ce “Ba fa haka ba ne Inna.” Ta ce “To ya ne? Na faɗa mata yadda muka yi da shi ta ɗan yi shiru “To kin amsa mishi ni na hana ki.”

Na sa kafa na fita.

Abincin da nasan yana so da farfesun naman kaza na yi masa, Sai na yi mishi zoɓo.

Har bayan magrib ina kitchen na gama zuba komai Inna Jamila ta leƙo da Mashkur a kafadarta ta ce ya tashi na bar daukar abincin da zan yi na ɗauki namu na bi ta ban dawo ba har aka yi Isha’i.

Tana sallar Isha’in ya kira wayata in zo in ba shi abinci na kwantar da Mashkur kujerar kusa da ita na miƙe na gyara daurin dankwalina na rufe kunnuwana na gyara rufa ta sai na fita.

Yana zaune cikin kujera Aunty Farha na gefen shi kamar za ta shige jikinsa zai zam na yi karya idan na ce ban ji abin ba na wuce su na shiga kitchen na kwaso abinci, na fara jerawa ya taso Aunty Farha kuma ta yi wurin ta.

Na gama zan juya ya ce “Ba ki zuba min ba.” Na fara zuba mishi, cikin kunnena na ji maganar shi “Wai wace irin rufa kike fama da ita? Na daga ido na dube shi “Ba komai. Sai da safe. Zan wuce na ji ya riƙo hannuna “Ki zauna mana ki taya ni hira.” Na girgiza kai “Mashkur zai tashi “To ki ɗauko shi.” Na ce To na wuce muka haɗu da Aunty Farha a hanya ina shiga Inna har ta kwanta ni ma na shirya na kwanta.

Tun daga nan kullum ni ke mishi girkin dare na safe ne dai yake fita bai karya ba. Daga dai shi ya tsani harkar Hajjo, gabaɗayanta ma ba ta yi mishi ba.

Idan na fito zuba mishi abincin daurewa kawai nake saboda yadda nake fitowa ina ganin shi da aunty Farha wadda koyaushe ke cikin nishaɗi miji ya zama na ta ita kaɗai. Inna Jamila kullum mita take min kan girkin da nake yi ni ma kan dole nake yi saboda shi ɗin.

Har na kwana talatin ranar kuma Inna Jamila za ta koma Taraba ba yadda ban yi ta bari in yi arba’in ta ƙi ta ce ta baro yara hankalinta na wurin su.

Sha tara ta arziki muka haɗa mata ni da ya Safwan har Mami da Daddy ya Safwan ya sa aka mayar da ita gida.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mutum Da Kaddararsa 58Mutum Da Kaddararsa 60 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×