"Cigaba." Ya ce ma Hajjo.
Duk makircin da suka ƙulla ta kwance shi tsaf.
Ni dai zuwa lokacin na kasa tsayuwa ƙasa na zauna ina hawaye me na yi wa Aunty Farha ballantana Hajjo da na san alheri ne tsakani na da ita.
Na dube shi yana riƙe da Farha wadda tun a ranar na daina ce mata Auntyn tana ƙara ji, sai da ya kikkifa mata maruka sannan ta yi shiru tana zubar da hawaye.
Na ce "Ka ga wannan lalatacciyar matar ciki ta kwaso yanzu haka ciwon da nake ce maka tana yi ciki ne.
Sai sannan. . .