Skip to content
Part 64 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

“Cigaba.” Ya ce ma Hajjo.

Duk makircin da suka ƙulla ta kwance shi tsaf.

Ni dai zuwa lokacin na kasa tsayuwa ƙasa na zauna ina hawaye me na yi wa Aunty Farha ballantana Hajjo da na san alheri ne tsakani na da ita.

Na dube shi yana riƙe da Farha wadda tun a ranar na daina ce mata Auntyn tana ƙara ji, sai da ya kikkifa mata maruka sannan ta yi shiru tana zubar da hawaye.

Na ce “Ka ga wannan lalatacciyar matar ciki ta kwaso yanzu haka ciwon da nake ce maka tana yi ciki ne.

Sai sannan Hajjo ta fara kuka “Wallahi sharrin Isya ne yaudara ta ya yi.”

Na zuba mata ido cikin takaicin sunan Isya kanen bayan ta da ta ambata wai ya yaudare ta ya mata ciki. Kamar in ta zunduma mata ashariya haka na riƙa ji na ce “Tashi ki ɗauki yar ki ku bar gidan nan.”

Da rarrafe ta iso gaba na ta kama ƙafata tana tuba, na ce yanzu zan fita in nemo masu fitar da su. Ko motsi ba ta yi ba sai da ya Safwan ya daka mata tsawa Sha’awa da ta manne da bango ta miƙe suka fice dakin.

Sai kuma da suka fita ya saki Farha duk hakurin da nake da zama da ke Farha bai ishe ki ba sai kin raba ni da matata ta ƙwarai ko to ki je Farha na sake ki.”

Ta ƙwala wata uwar tsawa daidai da daukar karar wayarsa ya ɗaga amma ƙarar da Farha ke yi ba ta bari ya ji ba, Farha ta kwasa da gudu ta bar dakin, ji na yi ya ce Ina gida Mami. Ya tsaya ya ɗan saurara sai ya ce “Na saki Farha Mami.” Ya saurara sai ya kuma cewa “Muna nan gidan Mami, anan ta same ta .”

Ya jefa wayar aljihu ya fita. Ni kuma na tsaya kallon dakin da tunanin halin dan Adam ka yi mishi rana ya yi maka dare.

Na bar dakin a sanyaye cikin ƙuncin zuciya na abin da Hajjo ta yi min don ya fi min ciwo kan na Farha.

Zan shiga falona na ji kamar hayaniya sai na fasa na fita, dambe ake ci a get na koma kiran ya Safwan ya kwanta ya yi matashin kai da hannayensa ya dubi sama.

Duk bayanin da nake masa na abin da ke faruwa a get bai ko yi motsi ba, na juya na fita sai da na kusa isa inda suke na gane Sha’awa ce ta danne Farha take kuma dukan ta duka kuma ba na wasa ba.

Hajjo kuma na kwance wuri guda tana mayar da numfashi.

Na leƙa dakin Isya ba shi ciki na kwasa na koma ciki na dauko wayata Khadija da Hafsah na kira sai ga su a guje amma dukkan su sun kasa ɓanɓare Sha’awa a jikin Farha, sai da Mami ta shigo a ƙafa magana ɗaya ta yi wa Sha’awa ta daga ta, rigar Sha’awar duk ta yage Mami ta ce “To ku fice.”

Sha’awa ta ɗaga uwarta sai ga Isya ya shigo Hajjo ta fara Allah ya isar mata cutar da ya yi mata ya jona mata alaƙaƙai.

Ya tsaya ya ce “Ta ina na cuce ki?

Ta ce “Ka ƙunsa min ciki, yau ina zan dosa da wannan abin tsiyar? Bai tanka ta ba dakin shi ya shige.

Su Khadija suka nuna ma Hajjo hanya suka fice, Farha na kwance ta kasa motsawa don ko numfashi da ƙyar take yi Mami ta dube ni “Dauko zane a sanya mata.” Ban taɓa ƙin bin umarnin Mami ba amma yau sai na fashe da kuka ina faɗin abin da suka haɗa kai da Hajjo suka yi min.

Su Hajjo suka kama salati.

Mami ta leƙa ta kira direbanta ta sanya su Hafsah tattagar Farha suka sa ka ta motar da ta zo ciki direban Mami ya ja ya fita gidan Mami ta ce “Ina Sadaukin? Na ce “Yana ciki.”

Muka ɗunguma cikin tunda muka zauna nake hawaye har Mami ta kira ya Safwan a waya ya fito su Khadija suka mike suka yi ma Mami sallama suka fita.

Kan carpet ya zauna ta ce “Ya aka yi ka saki Farha? Ta ce “Ya aka yi ka saki Farha? A takaice ya maida mata bayanin da na yi ta jinjina kai “Amma an yi mutanen banza. Ki yi shiru Bilkisu ki yi haƙuri, mu gode ma Allah da ba su samu kai ga yadda suke so ba.

Ta daɗe da mu sai da direba ya dawo daga kai Farha gidan su ta tafi.

Amir dai wuri ya samu ya raɓe ya yi shiru ganin ina kuka.

Haka muka wuni muka kwana cikin jimamin abin.

Washegari kuma muka samu sammaci Auntyn Farha ta maka ya Safwan kotu, ba ɓata lokaci aka fara sauraren ƙarar, lauyoyi ta dauka na ji da gani don ta sha alwashin sai an wulaƙanta mata ya Safwan, sai dai hakan ba ta samu ba saboda shi ma yana da uwaye a gindin murhu.

Ƙarshe dai korar ƙarar aka yi gane abokiyar makircinta ce ta yi mata duka bayan tonuwar asiri shi ya Safwan sakin aurenta kawai ya yi.

Ga sun yi neman Hajjo da diyarta kaf faɗin Abuja ko me kama da su ba su gani ba.

Da hutun Amir ya ƙare har da ni aka mayar da shi na kwana ɗaya na dawo.

Sai sannan kuma Farha ta fara bibiyar shi da bayar da hakuri ta dawo ɗakinta, sam ya ki sauraron ta yayin da Auntyn ta ta gano abun da take yi sharadi ta kafa mata ba ta ba Safwan matuƙar ta koma gidansa ba ta ba ta sai dai ta zaba a tsakanin su.

Farha ta kasa bin umarnin ta ƙarshe fata-fata ta yi mata Farha ta koma Zaria.

A can ɗin malamai iyayenta suka riƙa tadowa su ba ya Safwan hakuri ta dawo ɗakinta sai dai su ma ya ba su hakuri da abin ya ƙi Daddy suke samu zuwan su na uku Daddyn ya tilasta ya Safwan ya dawo da Farha ko dan yarinyarta tun kuma da aka yi haka ya fara shirin barin ƙasar ni kuma na shiga damuwar tafiyar da zai yi

Wani dare da ya shigo yake faɗa min har ya sayi ticket saura sati biyu jirgin su ya tashi zuwa kasar Canada fuskata ba walwala na ce mishi Allah ya nuna mana.

Har muka zo kwanciya ban da walwala ya kwanta na ƙi kwanciya shi dai sai bi na da ido yake ina zaune a kujerar madubi ya gaji ya taso ya kama ni sai da muka zauna bakin gado ya ce “Meye damuwar? Ban yi magana ba da ya ƙara maimaitawa sai ya sa ni jikinsa, a hankali na ce “Me na yi maka za ka tafi ka bar ni? Ya ce ” Shi ne matsalar ki to yi haƙuri mu kwanta.”

Ya ja ni muka kwanta sai da komai ya lafa a tsakanin mu na fara lumshe ido ina so in yi barci ya fara shafa cikina “Watan cikin nan nawa? Na ja ajiyar zuciya sai na faɗa mishi “Amma shi ya ƙi girma ba kamar na Mashkur ba.”

Na ce “Kowane da irin shi.

Ya ce “Haka ne.” “Zan tafi da ke ba zan bar ki ba Bilkisuna.”

A lokacin na tuna tare muka je muka yi intaview na biza sai dai da bai taba cewa za shi da ni ba sai ban kawo ba “Za mu fara yin Umrah sati biyu sai mu shiga Canada.”

Na daga ido muka haɗa sai na mayar da kaina jikinsa tunani na min yawo a cikin kai Idan ya tafi bai jin tausayin Mami da shi kadai gare ta?

Ga Farha sati daya ya rage ta dawo haka zai tsallake ta ya tafi? Na bar ma cikina har ya zare ni a jikinsa ya faɗa bathroom sai da ya fito ya miƙe na yo wankan na dawo na kwanta cike da tunani kafin barci ya yi awon gaba da ni.

Da safe da zai fita tare muka fita zuwa gidan Mami sai da ya tashi da yamma ya dawo ya same ni suna ta hira da Mami na ji irin dadewar da zai yi a can, ita Mamin ce ta ce mishi “Shekaru biyu Sadauki ba ka shiga hakkin Farha ba?

Ya ce “Na faɗa ma Daddy ya faɗa ma wakilan da take turowa ta ce ta amince.”

Mami ta jinjina kai sai na ji ta ba ni tausayi duk da ba ta nuna tana da wata mas’ala ba dole nasan tana da damuwar rashin ganin tilon danta na tsawon shekaru.

Da muka koma gida na yi mishi magana kan hakan ya ce “Zan bar mata Afnan da Mashkur kamar tana gani na ne.”

Na ce “Haka dai ka ce.

Sauran kwanakin sallama na yi ta yi da yan’uwa da abokan arziki tare muka je Taraba Malumfashi da Kaduna, har Kano na raka shi na yi amfani da wannan damar na leƙa Haj Asiya na yi mata wuni.

Kwanan Farha uku da dawowa muka daga kasa mai tsarki da muka shafe sati biyu muka shiga Canada.

Rayuwar da na yi a wannan kasa rayuwa ce ta jin dadi wadda ba zai yiwu in manta ba a tarihin rayuwata.

Na samu Safwan Abdullahi Safana yadda nake so ya gwada min so ya tarairaye ni mun yi rainon cikin tare a can na haihu na samu Hauwa’u sunan Mamana muna ce mata Jidda.

Ummu Hani ma tsakanin mu ba nisa ta samu mace, Juwairiya namiji, yarinyar Ummu Hani ta ci sunan Inna da Allah ya yi wa rasuwa. Na Juwairiya kuma ya cinye sunan Alhassan.

Muna can aka yi bikin ƙanwata ba mu zo ba amma sakon mu ya isa don daga ni sai ya Safwan muka yi komai.

Ba mu dawo kasar ba sai da ina ɗauke da karamin ciki don tuni na yaye Jidda

Ranar da muka dawo gidan Mami muka sauka na ga tsantsar murna a wurin ta ita da Daddy an yi mana girki kala-kala mun samu Afnan a gidan Mami ta sanya aje a dauko ta don Farha na dawowa ta aika mata da ita Mashkur ya yi girman da ya ba mu mamaki da muka tashi tafiya ya ce zai bi mu, muka tafi da shi har Afnan ina ce za mu sauke ya Safwan ne sai ya ce mu wuce tare zama ya yi kamar ba zai tafi ba sai goma na dare ya tafi yaran duka sun yi barci amma sai da ya dauki Jidda ya tafi da ita wadda a can ta ma fi yarda da shi a kaina.

Kwanciya kawai na yi daɗi na daya an gyara min gidan kuma mai aikin Farha Iya Larai da ya Safwan ya sallame ta san da ya rabu da Farha ta roki ya maido ta wuri na shi ne ya bar ta gidan Mami yanzu da na dawo na same ta na ji dadi don ba ta da wani hali na assha.

Da safe ina cikin barci bayan na sallami yaran na ji an haye ni na bude ido Jidda na gani na buɗe ido da kyau babanta na tsaye ya naɗe hannu na tashi zaune ina gaishe shi muka fita tare bai daɗe ba ya tafi.

Kwanan su uku na mayar da Mashkur gidan Mami ya maida ma Farha Afnan.

Shekarar Jidda uku na haifi Safwan junior. Amir ma kusan zaman shi ya dawo wurina, yaro mai tsananin nutsuwa da son ibada.

Rayuwa ta yi min kyau bayan fuskantar ƙalubalenta daban-daban, na mallaki yarana hudu da mijina da ba ni ba duk wanda ya san ni yasan yana matuƙar so na tsakanina da Ubangiji alhakimu gwani sai godiya, islamiyya na koma na cigaba da karatu na addini.

*****

Assalamu alaikum mutanen da suka yi jimirin bi na a wannin tafiya, anan zan tsaida alkalamin. Godiya ga Allahu Subhanahu wata’ala da ya yi ni musulma ya ba ni iko da basira na rubuta wannan labari tsira da amincin Allah su tabbata bisa ga shugaban mu Manzon tsira Annabi Muhammad (S.A.W).

Abin da na rubuta daidai Ubangiji ya haɗa mu a ladar wanda na yi kuskure Allah ya yafe min, ina fata za a ɗauki abu mai kyau a yi watsi da na banzan. Sai Allah ya sake sa da mu a wani littafin nawa na gaba idan rayuwar mu ta kai yar’uwarku a Musulunci

Maryam Ibrahim litee
Malumfashi Mrs Muhammad Nasir Sa’id

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mutum Da Kaddararsa 63

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×