Skip to content
Part 61 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Al’amura masu tsayawa a rai sun faru a wannan haduwa ta mu. Ya Safwan ya susuce ya nishaɗantu ya gamsu har ya sa da komai ya lafa na fara jin kunyar shi. Fitar da bai kuma ba kenan sai washegari, abinci ne dai ban samu nasara ya ci ba, na yi nadamar yin maganar nan, da na yi haƙuri ban tanka ba, ba ga shi ya wuce ba.

Da zai fita tare muka fita zuwa gidan Mami ya sauke mu ya wuce.

Tun da Afnan ta dawo makaranta tana liƙe da duk wanda ya dauki Mashkur. Mami ta ce “Sai a samo miki yarinya ƙarama da za ta riƙa taya ki reno, ga zuwa makaranta ga hidimar yaro ga girki abin zai miki yawa.”

Na ce “To Mami.”

Ina ce sai dare za mu tafi har na yi ma Ummu Hani waya idan aka yi la’asar zan shigo gidanta. Na yi sallar ina gyara fuskata sai ga shi ya shigo wai mu zo mu tafi, da na fito har ya dauki Mashkur na ce ma Mami za mu tafi, na samu Afnan ta tafi islamiyya da ba mu san yadda za mu rabu ba.

Har mun shiga mota na ce “Uhmmm. Ya waiwayo “Yaya dai? Na ce “Wunin bai ishe ni ba.” Bai ce komai ba na ce “Ko za ka kai ni gidan ƙawata? Ya ce “Wace ce? Na ce,
“Ummu hani.” Ga mamakina cewa ya yi ina ne gidan na faɗi mashi.

Muna fita layin ya shiga na su a waje ya tsaya na fita na shiga gidan, ban yi mamaki ba da na ga har an gama ginin part ɗin amarya gidan gabaɗaya sai sheƙi yake don ya sha fenti.

Magana kaɗan muka yi da Ummu hani ta bikin Hassan da ke ƙaratowa na miƙe Cake kawai na ɗauka na ci cikin kayan tarbar da ta jere min muka fito tana raka ni, ta miƙo min Mashkur na fita muka tafi.

Ya Safwan na sauke ni juya kan motar ya yi ya bar gidan, na ce ya san ba zama zai yi ba ya hana ni in kai dare.

Ina shiga ciki kaya kawai na canza na fito falo na zauna riƙe da Mashkur ina mamakin rashin jin motsin Hajjo.

Na mayar da hankali ga TV na ji motsi sai na waiwaya Hajjon ce riƙe da wata da sai da ta zaunar da ita a ƙasa kusa da ni na gane ba babbar mace ba ce yarinya ce sharaf a fuska sai dai a jiki kamar uwar mata gajera ce sosai komai na ta ya cika ba ta da haske sosai tana da kyanta daidai gwargwado.

Sai dai fuskarta a kumbure take tana kuma riƙe da hannunta na dama na ce “Lafiya Hajjo.” Ta fyace hanci muryarta har shaƙewa ta ce yi “Yarinyata ce sha’awa Haj, wadda ke aiki a Kaduna road, dazu bayan fitar ki aka kira wayata In ba da kwatance inda za a kawo min ita wai matar da take wa aiki ta bar mata yara ta tafi kasuwa yaran suka kunna ruwan bayi ya yi ta zuba ya jiƙa har falo shi ne da ta dawo ta samu sha’awa da duka kin ga yadda ta yi mata ta targaɗa mata hannu ta kumbura mata duk sassan jiki ta kuma share fuska “Kai talaka kowanne cin kashi sai a yi maka saboda rashin gata k….

Na ce , “Yi shiru Hajjo, yanzu bari a kai ta asibiti a duba ta, Allah ya sa ka mata.”
Ta shiga godiya na janyo wayata na kira ya Safwan na ce ya turo Direban shi zai kai yarinya hospital.

Muna nan zaune tana wash muna mata sannu direban ya iso na ce su tafi har Hajjon.

Sai bayan magrib suka dawo ashe ba ma targaɗe ba ne tsagewar ƙashi ta samu sai sheshsheka take abin tausayi, alamar ta sha wuya wurin gyaran.

Da kaina na zubo musu abinci don tausayin da yarinyar ta ba ni ta ma ka sa ci Tea na koma na haɗo mata, ta sha ta sha magungunan da aka haɗo su da su.

Suka tafi ɗaki.

Da ya Safwan ya dawo na faɗa mishi abin da ya faru, da zazzaɓi yarinyar ta kwana sai da aka mayar da ita Hospital din.

A hankali ta fara samun sauƙi har ta murmure.

Maganar cin abincin ya Safwan da abin ya ishe ni dole sai da na gaya wa Mami duk gudun kar ta ji da nake tare muka je da shi gidan da daddare ina ganin ta tafi daki na tashi na bi ta da ta gan ni ina sussunnewa ta ce ya aka yi na zauna bakin gadonta ina sunkuyar da kai na faɗa mata yadda ya ce in riƙa mishi girki da kuma ce mishin da na yi ya raba mana da Aunty Farha.

Dan shiru ta yi har na ɗago kai sai na ga kallona take na mayar da kan na ce “Ki ba shi haƙuri Mami.” Ta ce “Ba ki ji ne Bilkisu, amma idan Farha ba ta yi koyi da ke ba meye na ki na koyi da sakarcin da take yi?

Na dai yi shiru ta fita na bi ta a baya ina zama Afnan da ke kan cinyar babanta tana leƙa wayarsa da ya sa ma ido ta taso ta zo ta haye ƙafata.

Mami ta ce “Me ya sa ka daina cin abincinta? Kai ya ɗaga ya yi min wani kallo ta gefen ido da ya sa na yi saurin sunkuyar da kai “Haka ta ce miki? Ina ci mana kin ga yanzu ina zuwa cin abincin ku? Mami ta dube shi ta san ba zai yi maganar ba ne ta ce “To ta bada haƙuri, a yi mata haƙuri.”

Shiru ya yi. Daga haka na samu ta kwaranye.

Na koma makaranta a duk ranar da nake da lacture ta safe na kan tashi da wuri in bar Mashkur da babansa in haɗa abin karyawa sai na gama zan amso shi in shirya shi sai ni ma in yi wanka mu karya, gyaran wajena da na ogan sai na dawo nake samu in yi.

Sha’awa yarinyar Hajjo tana da matukar son yara Indai ina cikin gidan za ta zo ta ce Maman Mashkur kawo shi zan ba ta shi, hakan ya sa na ce ma Mami a bar nemo mai renon da ta ce za ta samo min don Hajjo ta zo ta same ni da roƙon yarta za ta zauna anan har ta kara da cewa “Tun tana yar karamarta Allah ya sa mata son yara kin ga sai ta riƙa renon Baban masu gida ko ba albashi.

Na ce “Zan faɗa wa maigidan, da na faɗa mishi kamar yadda na yi zato ba zai ce komai ba ba abin da ya cen.

Sai dai na sanya mata albashi.

Mafari kenan muka zauna tare da Hajjo da yarinyarta.

Aunty Farha ta koma gidanta ya Safwan ya raba mana kwana.

Wata ranar Laraba Hafsa ta shigo wajena sai muka shiga wurin Khadija tare don Khadijar na fama da zazzabi ciki ta samu yake dan ba ta wahala.

Mun samu Juwairiyya ƙanwarta a gidan, ita ce ma a kitchen. Muna cikin hirar mu ta kawo abincin da ta girka, wanda tun shigowar mu ya buwayi hancinmu da ƙamshi.

Abu nau’i uku ta girka kowanne kuma ya yi daɗi ba kaɗan ba kamar ka tsinke kunnenka.

Ta gabatar mana da abincin cikin wasa da dariya, na dube ta yadda ta ƙara kyau sai sheƙi take don daga gidan da ake mata gyaran jiki take Khadija ta ɗauki cokali ta ɗebo romon nama ta kai baki sai ta lumshe ido ta buɗe su kan Juwairiyya “Anya my Ju za ki bari kuwa angon ya ci girkin uwargidan? Ta dube ta tana dan murmushi “Me zai hana? “Allah na tausaya mata ne.”

Yadda Khadijar ta yi da fuska sai muka kama dariya. “Ga aikinki kin ajiye wai har wane irin so kike mishi?

Fari ta yi mata “Ban san iyakacin shi ba. Me kenan aka yi ni ina wurin aiki shi ba mazauni ba, zan zauna in kula da mijina, in mayar da kafata duk inda ya sa ta shi.

Khadija ta ɗan harare ta uwargidan fa? Ta ce “Sai mu riƙa bin shi tare don nasan ko da ba ta bin shi yanzu ta ga amarya na bin shi za ta fara.

Khadija ta ce “Haka ne.”

Mun dade gidan suna ta zantukan su, jin yadda juwairiya ta shirya wa zaman auren Ummu hani ta ba ni tausayi abin kuma ya tsaya min don har makaranta ta shiga ta koyon zama zinariya a wurin miji da kyakkyawar alaka, ga girki ta iya, ga gyara na fitina ana mata.

Dole na ce ma Ummu hani idan na tashi makaranta mu hadu gidan Mami. Nan ta same ni shawarwari na ba ta kan ta gyara kanta ta kuma tsaya kan kula da mijinta. Ta ce gyara tana yi. Na ce to ta yi ta addu’a ni ma zan taya ta.

Nan ta tafi ta bar ni sai dare ya zo muka koma.

An fara bikin Hassan da Juwairiya na tsaya fannin Ummu hani da na ce ma Khadija ƙawata ce ta kuma sha mamakin jin na auri Hassan, don na zaɓi in faɗa mata daga muna tare idan tafiya ta yi tafiya za su sani ban san fassarar da za su yi ma abin ba.

Dangin Hassan da na Ummu hani sun cika gida har da su Inna. Ranar ɗaurin aure ina tare da Ummu hani Haj Asiya ta dauki Mashkur tana ƙara yi min barka don lokacin da na haihu tana Umara.

Duk inda na gilma daukar ido kawai nake su Inna sai bi na da kallo ake suna ƙus-kus wannan gaya ma wannan ni ce matar Hassan ta da. Da kuma aka kawo amarya muka haɗe da su Khadija ana ta sha’ani.

Sai da aka ƙare bikin muka koma gida muka huta gajiya.

Da hantsi ina zaune a falo bayan fitar ya Safwan, Mashkur yana hannun sha’awa.
Hajjo ta zo ta same ni, muka ƙara gaisawa ta ce “Haj wurin ki na zo na ce To. “Taimako na zo nema na sutura ki ɗan ba Sha’awa ta samu na kwalliya ko a samu mai ɗauka.”

Ban kai ga magana ba sai ga Sha’awar ta fito tana ɗaga Mashkur yana dariya don ya matuƙar sabawa da ita.

Ta ce ” A ba mu Nono Mommy mu sha mu koma.”

Ina murmushi na miƙa mata hannu don har ga Allah ina son yarinyar don yadda take son Mashkur.

Sai da ya sha na miƙa mata suka tafi na dubi Hajjo “Zan duba mata.”
Ta yi godiya ta tashi ta tafi.

Ba iya suturun na ba ta ba har brezia na sawo mata don tana da nono manya da suke har sun kusa cikinta ga ba brezia ta kirki sai ta riƙa yawo da su kamar mai shayarwa tana fara samyawa sai ta koma cas.

Ina kyautata mata sosai saboda mashkur.
Ban samu na tafi Taraba ba sai da na ƙare karatuna ba wanda ya kai ya Safwan murna da karewar karatun nan. Kwanaki goma na yi na dawo sannan na tafi Kaduna na kwana uku na wuce Malumfashi na yi huɗu.

Watan Mashkur goma ya fara takawa lokacin ne na kama laulayi da na matuƙar shiga damuwa fargaba ta Mashkur kar ya lalace, kullum ina daki sai Hajjo ke walkamin ta kafin ita ma ta bi sahu na ciwon ya kwantar da ita da na ce su je Hospital ta ce shawara ce ta sha jiƙo sai shegen kwaɗayinta da ya ƙaru, don haka Sha’awa ce kadai mai lafiya sai Mashkur

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mutum Da Kaddararsa 60Mutum Da Kaddararsa 62 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×