Skip to content
Part 1 of 13 in the Series Mutuwar Tsaye by Hadiza Isyaku

BISMILLAHI RRAHMANI RRAHIM

Ƙarfe tara na dare a agogon Nigeria da kuma Niger, amma idan ka fito waje zaka yi tsammanin ukun dare ne, a dalilin ɗaukewar sauti da kuma motsin mutane, wanda madarar sanyin da ake zubawa ta haddasa.

 AL-MU’AB HOUSING ESTATE: rukunin gidaje ne da aka fi ganin kaikawon mazauna cikinsu da daddare, domin kuwa kaf a cikinsu babu cima zaune, sai gashi a wannan lokacin mai gadinsu ne kaɗai wanda da ake jin motsinsa a waje, shima hakan ya biyo ta hanyar abincinsa ne, da idan ya ɓuya a ɗakinsa bana jin wani zai san da zamansa.

Tamkar iska zata yi awon gaba da flowers gami da matsakaitan itacen da ke cikin estate ɗin, don kuwa tana ratsa su ne da ƙarfin da ake zaton jaura ce zata wuce, hakan ya sa kowa ya toshe duk wata ƙofa ta part ɗinsa. Ba don hasken wutar nepa ba, da na ce ko da kuɗi matsoraci ba zai iya fitowa waje ba.

Dr. Deeni, na ɗaya daga cikin mazaunan wurin. A nashi ɓangaren sam baya iya tantance gumurzun iskan da ake, sakamakon matsanancin ciwon da kansa yake. Zaune yake a ƙayataccen bedroom ɗinsa, lokaci ɗaya kuma kansa na jingine da lallausan kan gadon da yake zaune a kai, sai da ya sauke nishin tausayin kansa sannan ya lumshe idanunsa da yake jin kamar za su faɗo, “Allah ka yaye mani wannan lalura”, a ransa ya yi wannan addu’a, lokaci ɗaya kuma ya fantsama tunanin wane irin ciwon kai ne wannan mai taɓa idanu?, Don kuwa baki ba zai ya misalta uƙubar da yake sha ba. 

Yana cikin wannan yanayin ne Deena da ke sanye cikin pink color ɗin pajamas ta turo ƙofar bedroom ɗin ta shigo, ba tare da ya iya ɗago kansa ba ya amsa mata sallamar da ta yi.

Ita kuwa sautin muryarsa da ya fito a dakushe ne ya tabbatar mata da mijinta na cikin damuwa, don kuwa ba haka ya saba tarbar ta a ɗakinsa ba. A can baya duk idan ta shigo tun a bakin ƙofa yake fara yaba duk kalar dressing ɗin da ta yi, domin ita ɗin gwana ce a wurin iya tsara ado a kowane dare da rana, amma yau bai iya ɗago kansa ba, bare ta sa ran kalmominsa masu sanyaya mata zuciya.

 “Yayana” ta faɗa cike da kulawa lokacin da ta ƙarasa kan gadon tare da zama a gefensa, sai da ya ɗan matse hannunta da ta saƙa a cikin nasa kana ya amsa “Na’am”, tambayar sa ta yi “Meke damun ka?”, da ƙyal ya ɗan buɗe idanunsa kafin ya ce “Ciwon kai mai zafi Deena”, tunda suka yi aure bata taɓa ganin ya shiga irin wannan yanayin ba, hakan ne ya tabbatar mata da sosai yake jin jiki. 

Cike da tausayin sa ta ce “Sorry, bari na yi maka addu’a”, lallausan hannunta ta sa a goshinsa da ya yi rau da zafi, sannu ta sake yi mashi, daga bisani ta cigaba da yi mashi addu’ar kamun ciwon kai, shi kuwa a yadda ta riƙe kan da ɗan ƙarfi, sai ya ji dama kada ta saki saboda sassaucin da riƙon ya haifar mashi.

 “Thank you my love”, ya faɗa bayan ta gama yi masa addu’ar, ɗan rausaya kai Deena ta yi tare da saita idanunta cikin nasa da suka yi jajur, murmushi ya yi gami da shafar kumcinta, dan ya fahimci ta shiga damuwa da yanayinsa, cike da zaulaya ya ce “Malamarmu”, ƴar dariya ta yi “Malamarku kai da wa?”, Amsa ya bata “Ni da babyn za ki haifa mani”, ta ji daɗin ƙarfin halin sakewarsa, cikin salon shagwaɓa ta koma gefensa, kwanto da kanta ta yi a kafaɗarsa “Abin da babyn ma fushi yake”, ta ƙarashe maganar hannunta na a kan cinyar sa, “Fushi kuma?”, ta ce “Eh mana, a ce Abbansa ba lafiya, amma Ummansa bata sani ba sai yanzu”, domin ta yi nazari tun safe yanayin Deeni ke nuna baya jin daɗin jikinsa.

“Sorry my baby”, ya faɗa tare da rungumo ta gami da shafar cikinta da zai kai wata bakwai da samuwa, murmushin jin daɗi ta yi, lokaci ɗaya kuma ta yi lamo a jikinsa dake mantar da ita tsananin sanyin da ake.

 Shirun da suka yi ne ya ba Deeni damar samun nutsuwar shaƙar daddaɗan ƙamshin jikin Deena mai ƙara mashi son ta, sosai ya yi mata riƙon da ke nuna tsantsar ƙaunar da yake mata. Babyn da ke cikin Deena kuwa motsi ya shiga yi, kamar ya san ƙarƙashin kulawar Abbasa yake, don Deeni ya kasa ɗauke hannunsa daga kan cikin Deena

Cikin ɗan sauƙin da Deeni ya samu ne ya ce “Laa! Deeena kin ji babyna?”, Kanta da ke kwance a ƙirjinsa ta ɗaga “Eh na ji, ya jiki yake ma Abbansa”, murmushi mai sauti ya yi, tare da faɗin “Wow! Toh na gode.”

Ita ɗin ƴar taya ɓera ɓari ce a zantukanta, shi kuma tsaf yake biye mata domin yarinya ce da almost shekarunta ba zasu wuce sha tara ba. 

Kaɗan-kaɗan suke ta hirarsu mai cike da nishaɗi, har aka zo inda suka yanke shawarar idan Deena ta haifi namiji, toh sunan mahaifin Deeni za a sa, idan kuma mace ce toh za a sa sunan Umman Deena.

Daga ƙarshe cikin zaulaya Deena ta ce “Allah ya sa na haifi mace”, dariya Deeni ya yi “Ke kauce! Insha Allah takwarar Abbana za ki haifa”, baki Deena ta turo “Selfishness”, ɗan zungurar ta ya yi “Ai ke kika fara”, duk suka sa dariya, daga bisani suka tabbatar ma junansu duk wanda Allah ya sa aka haifa abin alfaharinsu ne, tunda duk mahaifansu ne.

Ɗan baccin da Deena ta fara ne ya tsagaita musu hirar, a hankali ta zame ta kwanta a gefensa, cike da kulawa ya ƙarasa lulluɓe ta da balanket ɗin da tuni dama ƙafafunsu na ciki.

Ƙuri ya yi ma fuskarta mai natsattsen kyawu, godiya ya ƙara yi ma Allah da ya tsaya mashi har ya mallake ta a matsayin matar aure, domin kuwa sai da aka kai ruwa rana kafin Umman Deena ta amince ya auri ƴarta.

Hannu ya kai da nufin gyara mata hular sanyinta da ta ke shirin zamewa, kwatsam ya ji kansa ya yi muguwar sarawa, bai san lokacin da ya fasa ba tare da rumtse idanunsa da hanzari, sanar da Ubangijinsa halin da yake ciki ya shiga yi har ya ɗan samu nutsuwa. A hankali ya fara buɗe idanun, aikuwa ya ga dunɗum ba hasken da zai iya ganin ko da tafin hannunsa.

Bai ba ransa komai ba, duk da yana jin ƴar faɗuwar gaba, laluben wayarsa ya yi, amma bai ji ta ba, tashin Deena ya shiga yi, duk da bai so hakan ba.

A hankali ta buɗe idanunta, lokaci ɗaya kuma tana kange su daga hasken fitilar ɗakin da ya cika su.

“Yaya menene?”, Ta tambaye shi cikin muryaryar bacci, “Ina phone ɗina, kin ga nepa sun ɗauke wutar.”

Sai da ta kalli ɗakin dake fayau da haske sannan ta ce “Yaya me ka ce?” , Ya ce “Phone za ki bani in haska, kin ga nepa sun ɗauke wuta”, da mamaki ta ce “Wannan hasken fa Yaya?”, gabansa na muguwar faɗuwa ya maido mata tambaya “Haske, da wuta kenan?”, da sauran mamakin da ke ranta amsa mashi “Eh mana Yaya”, zuciyarsa a kiɗime ya rufe idanunsa da kuma buɗe su domin tabbatarwa, still dai duhun ne cike da su, “Toh kuwa an samu matsala, domin bana ganin komai sai duhu.” Ya ƙarashe maganar kansa na wani irin juyawa.

Deena bata san lokacin da ta wartsake daga magagin baccin ba, domin ta fahimci abin ba na wasa bane. Ƙwayar idonsa dake shaking side by side ta kalla, hannunta na kyarma ta taɓa fuskarsa, cikin tsananin firgici ta ce “Yaya, ni fa ban fahimce ka ba, kamar ya baka gani, Ni dai ko dai zaulaya ta kake?”

 “Wace irin zaulaya kuma, na rantse miki bana ganin komai sai duhu”, ko kusa baki ba zai iya fasalta tashin hankalin da Deena ta tsinci kanta a ciki ba, “Yaya, kana nufin ka..”, kasa ƙarasa maganar dake ranta ta yi saboda gani take abun is impossible, sai dai shi ya ƙarasa faɗin “Na makance Deena, am a blind..”

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” suka haɗe baki suna faɗa. Wace irin ƙaddara ce wannan ta zo musu a lokacin da ba su shirya ba. Tamkar mafarki suke jin lamarin, mafarin suka sauka daga kan gadon domin ƙaryata wannan baƙin yanayin, hanyar banɗaki Deeni ya nufa shi kaɗai, maimakon ya nufi ƙofar, sai ya nufi bango har yana shirin kai masa karo, da hanzari Deena ta dakatar da shi tare da rungumo shi ta baya ta fasa sabon kuka, cikin ƙarfin hali Deeni ya zagayo da ita, hannunta ya kama, ita kuma ta yi masu jagora suka koma gefen gado suka zauna, kuka mai tsuma zuciya suka cigaba da yi duk da Deeni ya san ba shi ne mafita ba.

“Deena, mai aukuwa ta riga ta auku, don haka mu bar ma Allah kawai, ni tawa ƙaddarar kenan, kuma na karɓa da hannu biyu, fatana shi ne Allah ya sa na ci jarabawa”, cike da tawakkali Deeni ya yi wannan magana, hakan ne ya ƙara narkar ma Deena da zuciya. Abin da kuma bata sani ba shi ne, kukan da take ba ƙaramar illa yake ma Deeni ba, don ya fi tausayin ta akan kansa, lallashin ta ya yi da faɗin “Ki dena kuka kin ji, nima da lalular ta sama na haƙura.”

“Yaya ba zan iya dena kukan ganinka a wannan yanayi ba”, sai da ya matse ƙwallan da suka cika masa ido kafin ya ce “Toh ki sassauta kin ji, yanzu addu’a irin ta ɗazu za ki yi mani.”

Kasa magana ta yi, bare ta yi mashi addu’ar, tambayar ta ya yi “Za ki iya addu’ar?”, Ta ce “Eh, amma Yaya bayan addu’ar zaka je asibiti ko?”, Kai ya ɗaga “Eh, da safe sai ki kira mani Lalu”, maganar yanzu Deena take, “Yaya har sai safe? Me zai hana ka je yanzu?”

Deeni baya son ɗaga hankalin kowa a wannan daren, ce mata ya yi “Duk mai so na ba zai iya barci ba idan ya ji wannan labari, don haka mu jure, yanzu da safiyar duk ɗaya ne a wurin Allah”, ba don Deena ta gamsu da uzurinshi ba ta amince.

Dr. Deeni, professional gynecologist ne da ya yi suna a cikin gida har ma da wajen jiharsu, mafarin burin kowace mace mai ɗauke da lalurar da ta shafi mata take burin ta haɗu da shi, domin ganinsa kaɗai alamun waraka ne da iznin Allah.

Babban tashin hankalinsa biyu ne yanzu: Mahaifiyarsa idan ta ji labarin ƙaddarar da ta same shi ya zata yi? Gashi ba cikakkiyar lafiya ne da ita ba. Sai kuma aikinsa da yake proud da shi.

Apart from these! Shin zai ma warke daga lalurar? Idan kuma bai warke ba, shin ya makomar aikinsa zata kasance??

Deena kuma firgicinta shi ne mahaifiyarta, domin idan akwai wanda ta tsana toh Deeni ne da ya liƙe ma ƴarta. Babban burin Ummanta shi ne ta samu hujjar da zata raba Deena da mijinta, wanda kuma hakan daidai yake da raba ta da rayuwar ta, domin ƙaunar idan ba kai ba sai rijiya take masa.

“Allah ka shiga lamarin mijina, kada ka bari wannan lalurar ta yi tsayin da zamu fuskanci ƙalubalen rayuwa”, emotionally Deeni ya amsa “Amiin my wife…”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.2 / 5. Rating: 5

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Mutuwar Tsaye 2 >>

6 thoughts on “Mutuwar Tsaye 1”

  1. ammarharunagumau@gmail.com

    Gaskiya wannnan labari cike yake da darrusa, Allah ya mana tsari daga mummunan ƙaddara ya bamu dacewa da rabauta duniya da lahira Allahumma amin Ya Allah,
    Haka fa ya faru ga kantawa amma ita nata bangaren ji ne ta zama kurma tun da tayi jinya a ƙarshe 2022 gashi har zuwa yau bata warke tun kafin aurenta , gashi yanzu har tayi aure,
    Allah ya bamu lafiya da imani Allahumma amin Ya Allah

    1. Allah Sarki, Amiiin ya Allah

      Mutum kam ba a gama halittarsa sai ranar da ya koma Ubangijinsa.

      Fata dai Allah ya barmu da cikakkiyar lafiyarmu Amiiin.

      Nagode sosai

  2. Ma sha Allah. Sannu da ƙoƙari mai awarar ƴan gayu, labarin ya ja hankali na. Shi kuma Deeni irin tasa ƙaddarar kenan. Allah ya kara zaƙin hannu.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×