Bayan sun gama ɗaukar ma kansu abin da ya fi ƙarfinsu ne ɗayan halin Dr. Bello ya fito, inda ya ce "Ni a gidansu Deeni ma na ga wata matashiyar budurwa mai kyau, kuma da alamu ƙanwarsa ce", take Dr. Jabiru ya gane wadda yake nufi, cewa ya yi "Ina zaton Asma'u ce ka gani", Dr. Bello ya ce "Sunanta kenan?", Jabiru ya ce "In dai a gidansu ne, toh Asma'u ce ka gani", kai Bello ya jinjina "Okay, da a ce wani gida na daban na ganta ba gidansu Deeni ba da na leƙa, ƙila idan. . .