Skip to content
Part 15 of 26 in the Series Mutuwar Tsaye by Hadiza Isyaku

Bayan sun gama ɗaukar ma kansu abin da ya fi ƙarfinsu ne ɗayan halin Dr. Bello ya fito, inda ya ce “Ni a gidansu Deeni ma na ga wata matashiyar budurwa mai kyau, kuma da alamu ƙanwarsa ce”, take Dr. Jabiru ya gane wadda yake nufi, cewa ya yi “Ina zaton Asma’u ce ka gani”, Dr. Bello ya ce “Sunanta kenan?”, Jabiru ya ce “In dai a gidansu ne, toh Asma’u ce ka gani”, kai Bello ya jinjina “Okay, da a ce wani gida na daban na ganta ba gidansu Deeni ba da na leƙa, ƙila idan da rabo sai Allah ya sa a dace.”

Duk da cikin duhu ne, amma sai da Bello ya ankare da mugun kallon da Jabiru ya watsa mashi haɗe gatse ya ce, “Ai ko yanzu kana iya leƙawa! Kai da idonka idon mace sai ka ce kana son ta”, Bello na dariya ya ce “Toh miye dan na ce ina son duk macen da na gani”, da yake babu ƴar jin nauyi a tsakaninsu Jabiru ya ce “Rashin mutunta kai ne mana, duk namijin da ya amsa sunansa namiji ba kowace mace ce yake kulawa ba, tunda ba duka zai aura ba”, Ballo na cigaba da dariya ya ce “Ai ko bai aure su ba, zai iya rage time ko.?”

Cike da ƙuluwa gami da son ankarar da shi Jabiru ya ce “Ai wannan shi ne cikakken rashin mutunta kai ɗin da nake nufi, Allah kuwa ka dawo hankalinka Bello, saboda kaima ka haifa, kuma ko ba ka haifa ba ai kana da dangi, ba zaka so ayi masu abin da kake yi ma na wasu ba.”

Duk mugun halin Jabiru, toh a ɓangaren mata bai cika zaƙewa ba, saboda ya san illar hakan, yana tsoron kada watarana reshe ya juye da mujiya. Sannan ya fi kowa sanin yadda Bello ya ɗauki mata, shi ya sa baya gajiya wurin faɗa mashi gaskiya, duk da ya san ba ɗaukar gaskiyar yake yi ba, tunda ba yau ne farau ba.

“Jabiru, a bar maganar nan dan Allah, ni da mata dai akwai amana, shi ya sa da na tashi har a fannin lafiya na karanci sashensu, ta yadda zan basu gudunmawa yadda ya kamata”, cike da izgilanci Bello ya faɗi haka, lokaci ɗaya kuma yana dariyarsu ta ƴan air, cewa Jabiru ya yi “Toh Allah ya yaye maka”, ya ce “Amiiiin dai.”

Rufe wannan chapter suka yi, suka buɗe wata, sai da aka kira sallar Isha’i ne suka tashi.

Hajiyarsu Deeni kuwa haka kawai Dr. Bello ya tsaya mata a rai, ta kasa manta yadda a take fuskarsa ta chanja lokacin da MD ke maganar komawar Deeni a bakin aiki, tabbas hausawa sun ce labarin zuciya a tambayi fuska, mafarin ta shiga tunanin anya Bello na son Deeni kuwa.?

So take ta tantance, mafarin bayan sun sake haɗuwa a falonta cikin hikima ta ce ma Deeni “Abokan aikinka suna da kirki sosai, na ji daɗin zuwansu a gidan nan”, kafin ta samu amsa daga bakin Deeni Lalu da ke tsaye gaban Tv ya ce “In banda mutum ɗaya Hajiya”, abin da take son ji kenan, mafarin ta maida hankalinta wurinshi “Wa kenan?, kai da baka gajiya da tsegumi”, Baro wurin Tv ɗin ya yi “Dr. Bello mana, idan kina neman mugun mutum, kika same shi toh magana ta ƙare Hajja”, Asma’u da ke zaune a gefenta kan babban carpet ta ce “Na rantse kuwa siffarsa ta mugaye ce, shi ya sa ma ni sam bai yi mani ba, ga mugun kallon tsiya.”, Lalu da ya san halinshi a bakin mutane ya ce “Kaɗan daga cikin mugun halinsa ne ai.”

Basu faɗi halinsa kai tsaye ba, amma duk da haka ta fahimci wani abu da ke nuna bashi da kirki”, baki ta ɗan taɓe “Allah dai ya kyauta.”, sannan ta maida hankalinta wurin Deeni, shi dai bai ce komai a kan Dr. Bello ba, don baya da lokacinsa, sai dai ya yi mata bayaninsu da sunayensu kamar yadda ta buƙata.

Bayan ya gama ne ta ce “Suna da kirki, Allah ya saka musu da Alkhairi”, Deeni ya ce “Amiiiin ya Allah.”

Hira ta yi ta jan Deeni da ita, har ta samu ta saƙo batun neman maganin gargajiya, inda ta ce mashi “Ka ga yanzu maganin gargajiya za’a gwada Deeni, tunda an yi na asibitin, ba’a san ina ake dacewa ba”, da mamaki ya ce “Maganin gargajiya kuma Hajja?”, Ta ce “Eh mana”, ya ce “Toh shikenan, amma wani lokaci fa gargajiyar nan akwai matsala”, Lalu da tuni ya zauna kan two seater kusa da Deeni ya karɓe da “Na rantse kuwa Hajja, ƙara ciwo kawai suke”, kai ta girgiza “Ba dai ƙara ciwo ba, shi magani ai da gwaninsa ko?”, Deeni ya ce “Haka ne”, ta ce “Toh sai an haɗa da shi, idan da rabo sai ku ga an dace.”

Asma’u ta ce “Dama Islamic chemist aka je Hajjah”, cewa ta yi “Wannan ma za’a je ai, shi zuwansa na musamman ne Insha Allahu”, Lalu ya ce “Toh a fara zuwa can mana”, ta ce “Toh shikenan, ni ma na fi son can ɗin a raina, kawai dai ba’a zama wuri ɗaya ne idan ana neman magani”, Deeni ya ce “Haka ne”, ta ce “Sannan addu’ar da duk muke kada mu gajiya, wannan rayuwar baka tsare ma kowa komai ba, amma lafiyarka ma tsone ma mutane idanu take”, Lalu ya ce “Wallahi kuwa hajja, ai mu da ke fita waje muna ganin ikon Allah a wurin jama’a, haka kawai wani sai ka ga yana jin haushin ka, wani kuma baka taɓa zato, sai ka ga da shi ake haɗa kai a cuce ka”, Hajiyarsu ta ce “Ai haka mutane suke a ko ina Lalu, shi ya sa ku cigaba da neman tsarin Allah daga sharrin duk wata halitta mai mai numfashi, sannan ku dai kada ku cutar da kowa, madamar kuka tsare gaskiyarku Allah ba zai bari a cutar da ku ba, kuma ko cutarwar ta afku, toh sai ta zame maku Alkhairi a gaba.”

Bayan ta kai aya ne Asma’u ta ce “Allah kuwa Hajja, sai nake ganin kamar ciwon Yaya ma hada maƙiya”, tabbas ta sani akwai sharrin maƙiya a lamarin, amma bata son rasa imaninta wurin zargin wani zai iya cutar da Deeni, tunda ƙaddara mai kyau da akasinta duk hukuntawar Ubangiji ce, cewa ta yi, “Allah ne mafi sani Asma’u, kuma idan ma hada maƙiyan ai sun yi ma kansu, tunda duniya ba matabbata ba ce, abin da ka shuka shi zaka girba”, suka ce “Haka ne”, ta ce “Bare bana zargin kowa a kan wannan lamarin, kawai dai addu’a ce maganin dukkan bala’i da musiba, azkar ɗin nan duk wayewar safiya da yammaci ku riƙa yin su, wannan shi zai sa ko bala’i ya tunkaro mutum sai Allah ya tsaida shi, sai maƙiya su yi ta mamakin ta ya kake ƙetare sharrinsu”, Deeni da ya gamsu sosai da maganar mahaifiyarsu ya ce “Gaskiya ne Hajja, yanzu kin ga akwai masu jin daɗin wannan lalurar da ta same ni fa”, ta ce “Na sani Deeni akwai su, hausawa sun ce murnar mutuwa ai murnar banza ce, idan sun ji daɗi dan baka gani, Allah zai ba ka mafitar da zata tsorata su, dan Insha Allahu wannan sai ya zama silar ɗaukakarka”, Lalu ya ce “Allah ya amsa our great Mother”, suka ce “Amiiin”, sosai ta ɗora su a kan tafarkin rayuwa wanda zasu kasance cikin aminci da Alkhairin Allah.

Sai wurin ƙarfe goma ne Deeni ya koma ɗakinsa, ban ɗaki ya shiga ya watsa ruwa da alwala, yana fitowa ya zura jallabiyarsa wadda tuni Lalu ya fiddo masa ita, sallah ya kabbara, inda ya yi raka’a biyu da ya saba kullum kafin ya kwanta barci, ya lazimci wannan sallar ne saboda ya fahimci tana da ɗimbin Alkhairori masu yawa, babba daga cikinsu akwai amsa addu’ar da bawa ya yi a cikin wannan sallah.

Sosai Deeni ya kai kokensa a wurin Ubangiji kamar yadda ya saba. Gamawarsa ke da wuya ya lalubi wayarsa da ke gefe, kai tsaye number soul mate ɗinsa ya kira.

Ita kuwa tamkar jiransa take, da hanzari ta ɗaga kiran da sallama a cikin muryarta mai cike da nutsuwa. Buɗe idanu da rufe su duk ɗaya ne a wurin Deeni tunda baya gani, amma sai ya zaɓi lumshe su domin ba ma zuciyarshi dama jin daɗin muryar Deena.

“Wa’alaikumu ssalam Hajiyata, ya kike?”, ya faɗa tare da jingina da gado, daga can ta amsa “Ƙalau”, ya ce “Ƙalau kaɗai?”, ta ce “Yep, me kake so na ƙara?”, Ya ce “Komai ma”, ta ce “Like what?”, Ya ce “Some words related to love, or missing.”

Ɗan shiru ta yi, daga bisani ta ce “Okay my Jaan, na yi kewar mijina sosai”, Sosai yake jin daɗin saurin fahimtar Deena, cike da ƙaunar ta ya ce “Really?”, ta ce “Yep”, ya ce “Missed you too my baby, amma azumi ba zai yi nisa ba za ki dawo ko?”, ta ce “Insha Allah, nafi son in yi azumi a gidan mijina”, ya ce “Why?”, Ta ce “Saboda in yi ma mijina hidima”, ya ce “Da kyau tawan! Ina yarona?”, Ta ce “Gashi fa a hannu sai kallona ya ke, kamar ya san da Abbansa na ke making call”, ya ce “Ba shi wayar”, Dariya ta tuntsure da ita, “Kamar dai mai baki?”, yana dariyar shi ma ya ce “Yes, ai duk da baya magana, amma yana ji ko?”, Ta ce “Eh”, ya ce “Toh sa mishi wayar a kunne.”

Sai da ta tabbatar mashi da ta sa ma Raihan wayar a kunne ne ya ce “Assalamu alaikum sweet son, how are you doing?”, cikin murya mai kama da ƴar waƙa ya yi maganar.

Daga can Deena ta ce “Na rantse kuwa yana jin ka, ka ga yadda yake ta ware idanu ya ji muryar Abbansa?”, Ya ce “Na faɗa maki ai yana ji”, duk suka sa dariya.

Hira mai cike da tsantsar ƙaunar juna suka cigaba da yi, a nan take faɗa mashi ƙila ma gobe su zo, don ta ji Ummanta na faɗi, aikuwa ya ce “Zan yi farin ciki idan aka zo dake”, ta ce “Nima haka, dan ɗakinka ma zan aje jakata”, ya ce “Da gaske?”, Ta ce “Yes”, ya ce “Ni kuwa zan adana maki ita.” Sun daɗe suna hirar, tun Deeni na ƙasa har ya koma kan gado. Sai da Lalu ya dawo har ya yi barci sannan suka yi sallama.

Washegari da yamma mahaifiyar Deena ta shirya tsaf ita da ɗaya daga cikin manyan ƙawayenta zasu je su gano Deeni. Deena ta ɗauka da ita za’a je, mafarin ta shirya da wuri.

Sai da ta sauko rungume da Raihan Ummanta ta tambaye ta “Sai ina haka?”, Ras gaban Deena ya faɗi, don kaɗan zata kuskure ran kowa sai ya ɓaci a wurin, sannan ba za a je da ita ba.

“Ba tare zamu tafi ba?”, Cewar Dr. Safiyya, wadda itama shaƙiƙiyar ƙawarta ce, “A ina za a da ita?”, A shagwaɓe Deena ta ce “Inda za ku mana”, wani irin kallo Ummanta ta yi mata kafin ta ce “Tunda ƙawayenki ne zaki tafi tare da mu ko?”

“Toh miye a ciki dan Allah, mu tafi tare mana, kuma tafiyar ma da ita ya fi.” Dr. Safiyya mutuniyar kirki ce, ta san yadda ya kamata sosai, da ace Umman Deena zata riƙe ta a ita kaɗai, toh da ta zauna lafiya da kowa, toh amma su Aunty Hafsah sun yi kane-kane, ko Dr. Safiyya ta yi tufka, su ne ke warwrewa.

Shi ya sa Deena ke son ta sosai, saboda bata taɓa shigar mata rayuwa ba, Amma tsakaninta da su Aunty Hafsah Allah ya isa ce, don duk lokacin da aka ga Ummanta na mata faɗa, toh Aunty Hafsah ce sila.

“Ai shikenan, sai mu tafi da ita ɗin”, Ummanta ta faɗa tana harararta, bayan ta wuce ne Deena ta ce ma Dr. Safiyya, “Thank you Mammy, da ba ki saka baki ba, ba za’a je da ni ba”, dariya Dr. Safiyya ta yi “Ki yi ta haƙuri da mamanki kin ji ko?”, Kai Deena ta ɗaga alamar “Toh.”

Driver na zuwa suka kama hanyar tafiya. Sosai farincikin Deena na son ganin mijinta ya ƙaru, har ta kai ga Ummanta ta lura, ɗan raɗa ma Dr. Safiyya ta yi “Wannan zaɓolakar ta son ganin miji ce fa”, Dr. Safiyya ta ce “Ai ba laifi ta yi ba, kema idan Alhaji Lawan zai dawo ai haka kike”, Umman Deena ta san irin yanayin da take shiga idan Alhaji Lawan zai dawo, mafarin bata ce komai ba sai dai dariya.

Suna isa aka yi masu tarbar mutunci kamar yadda aka saba, bayan sun gaisa ne Aka miƙa ma Hajiyarsu Deeni Raihan, tana karɓar shi ta fara yi mashi tsokanar kaka da jika “Kai ina cefanen? Aanya wannan auren zai yi yu kuwa”, Dr. Safiyya ta ce “Me zai hana kuwa Hajiya?”, Hajiyarsu Deeni ta ce “Toh ba cefane fa, koda yake Hajiya Hadiza ta riƙe shi gam”, dariya sosai suka yi, Dr. Safiyya ta ce “Ai ya kusa dawo maku ku ma dai Insha Allahu.”, Ita dai Umman Deena bata ce komai ba sai ƴar dariya.

Deena kuwa sai raba idanu take bata ga Deeni ba, kitchen ta iske Asma’u “Ke ina mijina yake?”

Baki Asma’u ta taɓe “Uhmm! Masu miji, Deena ta ce “Eh ɗin”, tana dariya, Asma’u ta ce “Auren nan dai muma mun kusa yi, a daina yi mana fankama” Deena ta ce “Wallahi haka muke fata! Amma dai ina mijina”, Asma’u ta ce “Kai ƙwazaba! Toh yana ɗakinsa.”, Deena ta ce “Shi kaɗai ne?”, Asma’u ta ce “Yep”, ba tare da Deena ta sake magana ba ta juya.

A hankali ta tura ƙofar ɗakin, tsaye Deeni yake a gaban gado yana yana fesa turare”, a hankali ta riƙa taku har ta je bayansa. Duk da bata yi magana ba, amma ƙamshin turarenta sai da ya gaya ma Deeni ita ce, ƙarin tabbatarwar ma sai da ta rungume shi ta baya, a tare suka lumshe idanuwansu sakamakon wani daɗi da ya ratsa su.

A hankali Deeni ya juyo da ita suna fuskantar juna, cikin murya mai cike da shauƙi ya ce “Madam Dee, barka da zuwa”, amsawa ta yi cikin irin nata salon itama “Barka dai mijina, mun same ku lafiya?”, Ya ce “Ƙalau”, kallon sa ta yi tare da zumɓuro baki, a shagwaɓe ta ce “Ƙalau kaɗai?”, Sai da ya ƙara shigar da ita a jikinsa sannan ya ce “Ƙalau wasn’t enough my Dee-dee, am just kidding.”

A shagwaɓe ta ce “Toh ka yi missing ɗina?”, Cewa ya yi “What a silly question Deedee?, Missed you more than your thoughts.”, Ta ce “Really?”, Ya ce “Yep, do you want me to show?”, Ta ce “Yeah”, ya ce “Let’s great Mommah first”, yana rufe baki ya duƙo da kansa, ko da bai faɗa ba ta san sumbatar ta zai yi, dai-daita mashi kanta ta yi, tunda ba gani yake ba, duk abin da yake hasashe ne kawai.

Sumba mai cike da so, ƙauna gami da kewa suka yi ma juna, daga bisani Deeni ya kama hannunta “Toh mu je.”

<< Mutuwar Tsaye 14Mutuwar Tsaye 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×