Skip to content
Part 14 of 34 in the Series Mutuwar Tsaye by Hadiza Isyaku

Duk da irin zafin damuwar da Deeni ke ji a ransa, bai hana shi jin sanyin farincikin raɓar shi da Lalu ya yi ba, “Ɗan’uwa mai daɗi..” abin da ya faɗa kenan a ransa, kafin ya buɗe bakinsa da ya yi nauyin gaske ya ce “Amiiiin Lalu, Nagode sosai.”

Shiru dukan su suka yi, ƙasan ran Lalu yana jin wani irin ƙuncin da ba zai iya misalata shi ba, domin duk abin da ya shafi Deeni su ya shafa kamar yadda kowa ya sani.

Deeni kuwa wannan ce damar da yake da ita wurin expressing abin da yake ransa, cikin asalin nutsuwarsa ya ce ambaci “Lalu”, shi kuwa cike da ladabi ya amsa, “Na’am”, lokaci ɗaya kuma yana kallon Deeni cikin hasken fitilar da ta game ɗakin.

Deeni ya ce “Lalu, so nake in tursasa ma zuciya ta ɗaukar wannan ƙaddara, toh amma na fahimci wahalar da kaina nake, don kuwa idan na ce ban damu da wannan ciwon ba na yi ƙarya, kuma tashin hankalin uku ne suke raunatar da ni.”

Kai Lalu ya jinjina yana kallon Deeni, tabbas kowa ya san yana cikin tashin hankali, domin babu masifar da takai mutum ya rasa idanunsa, domin sila ce ta tsayawar al’amura masu yawa. Toh amma waɗannan damuwoyi har uku da ya faɗa ya suke?, Su Lalu yake son sani.

Cike da kulawa ya ce “Gaskiya ne, ai ka daina basarwa a kan wannan damuwar, duk abin da in dai ka yi shi zai kawo maka sassauci a ranka, toh ka yi shi kawai ko da kuka ne, feel free ɗin da kake yawan yi illar gaske ne da shi, don ba zai iya kawar maka da damuwar da ke can ƙasan zuciyarka ba, ita kuma damuwar zuciya ta fi komai illa.”

Ɗan tsagaita magana Lalu ya yi domin ya ba Deeni damar magana, don tunda ya ɗauko doguwar maganarsa har ya sauke ta Deeni bai ce komai ba sai “Gaskiya ne Lalu.”

Mafarin Lalu ya ɗaura da “Sannan waɗanne irin damuwoyi ne haka?, Ina ce duk abin da Allah ya tsara maka bayan wannan makantar mai kyau ne, kuma Insha Allahu mafita zata biyo baya”, Deeni ya ce “Haka ne Lalu, amma waɗannan su ne jigon rayuwata, wanda dole makantar nan ta shafe su. Na farko ku ƴan’uwana, ina da yaƙinin kuna jin ƙuna fiye da ni, don na san tausayi ba zai bari zukatanku su zauna lafiya ba”, sai da Lalu ya lumshe idanu sakamakon gasgata maganar Deeni kafin ya ce “Gaskiya ne”, Deeni ya ce “Toh ka gani, damuwata taku ce Lalu, ina tausayinku nima.”

Kamar Lalu zai yi kuka ya ce “Allah ya bamu ikon cinye wannan jarabawa”, Deeni ya ce “Amiiiin”, sannan ya ɗora da damuwarsa ta gaba “Na biyu Lalu, ita ce my wife, ina masifar son Deena son da baki ba zai iya misalta shi ba, sannan ina tausayin ta domin ta ɗaukar ma ranta zata iya rayuwa da ni a haka, duk da hakan naƙasu ne a gare ta, don kyakkyawar mace kamar Deena, ina da assurance na maƙiya zasu yi mata dariyar tana rayuwa da makaho.”

Lalu ya san kowacece Deena wurin nagartar hali, cewa ya yi “Ai samun yarinya ƙarama mai kirki da sanin ya kamata irin Deena sai an tona, yarinya ce mai matuƙar sadaukarwa, sannan batun ayi mata dariya duk wanda zai yi ga fili nan”, Deeni ya ce “Gaskiya ne, amma ka san wata damuwar?”, Lalu ya girgiza kai, Deeni ya ce “Mahaifiyarta, bana zaton zata bari mu cigaba da zama, jikina na faɗa mani raba mu zata yi.”

A wannan karon abu biyu ne ya zo ran Lalu, tausayin Deeni da matarsa, na biyu kuma tafarfasar zuciya, don mugun haushin mahaifiyar Deena yake ji, saboda ita kaf rayuwarta matsala ce a wurinsu, cewa ya yi “Akwai damuwa sosai a wannan issue ɗin, amma kada ka damu, Allah na nan, idan ma ta karɓe Deena toh Allah zai iya baka wadda ta fi ta”, Deeni baya jin akwai wadda zata maye mashi gurbin Deena, amma sai ya cije ya ce “Gaskiya ne, Allah ya bamu mafita”, Lalu ya ce “Amiiin, amma miye damuwar ta uku?”, Deeni ya ce “Aikina, wanda shi ne gatana, kuma gatan duk wanda yake related to me, bana son rasa shi”, Lalu ya ce “Allah da ya ɗaura maka, shi ne zai baka mafita, da sannu Allah zai chanja maka da dukkan mafi alkhairin abin da ka rasa, don shi ɗin mai adalci ne, baya karɓar wani abu na ni’ima a wurin bawansa, face sai ya chanja mashi da mafi Alkhairinsa”, sosai ya yi ma ɗan’uwansa nasiha, ya kuma nutsar mashi da zuciya har sai da Deeni ya ji sauƙi sosai a ransa.

Sun daɗe wurin a zaune, sai can wurin uku saura Deeni ya tursasa ma Lalu a kan ya je ya yi barci, saboda akwai gajiya. Lalu kam yana son ya ɗan rumtsa, tunda shi barci ba a cin bashin sa, tashi ya yi ya je ya kwanta.

Daga kwancen yake ya buɗe data tare da leƙawa Binance ɗinsa don ganin riba aka samu ko faɗuwa a harkarsa ta crypto, kasantuwar shi ɗan crypto ne number ɗaya. Notification na saƙon Rahila ya gani a WhatsApp ya shigo, sam babu tunanin WhatsApp yanzu a ransa saboda dare ya raba, amma da yake ita ce, bai san lokacin da ya yi wuff ya shige ba.

“Salam, ya kuka isa gida, ya kuma jikin Dr. Allah ya bashi lafiya Amiiiin.” Abin da saƙon Rahila ya ƙumsa kenan.

Maimakon Lalu ya yi mata reply, sai ya ɓige da kallon Profile picture ɗinta wanda ta ɗauka cikin wani peach ɗin leshi, da aka ƙawata adon jikinsa da sea green ɗin color, yayin da mayafin jikinta ya kasance shi ma sea green ne. Haƙiƙa Rahila tana da natsatssen kyawu, wanda da Allah zai sa ya mallake ta, da ya nuna mata ƙauna daidai da siffarta.

“Alhamdulillah, lafiya lau muka koma, and jikin Dr. da sauƙi”, reply ɗin da ya yi mata kenan, Lalu bai taɓa tunanin zai same ta online ba at this time, amma sai ya ga blue tick, wanda ke nuna har ta buɗe saƙonsa, inda ta yi reply da “Toh Allah ya huta gajiya”, ya ce “Amiiin ya Allah.” Ƙuri Lalu ya yi ma chat ɗin, lokaci ɗaya kuma yana ta saƙa me zai ce mata wanda zai neme ta da doguwar hira, toh yana jin ɗan nauyin ta ne bisa ga kwarjinin da take masa.

A nata ɓangaren kuwa tamkar da sauran kuzarinta su Deeni suka tafi, duk wata walwala da take da ta ƙare, wadda kuma ba son Deeni ne kaɗai damuwarta ba, hada rashin nasara a kan aikin da aka yi masa. Ta yi kuka ita kaɗai, sannan ta yi a bainar jama’a bisa ga zargin kanta da take, har sai da mahaifanta suka nuna mata komai na a hannun Allah sannan ta rage damuwa. Daddare bayan ta kwanta ne abin ya dawo mata sabo, mafarin ta tashi ta kai ma Allah kukanta a kan ya share mata hawayenta, domin babu mai yi sai shi, gama sallar ne ya bata damar shiga WhatsApp har ta yi ma Lalu magana.

Ta wani ɓangaren kuma tamkar son maso wani ke damunsu ita da Lalu, ita tana son Deeni, Lalu kuma yana son ta, sai dai bata ankare da son da Lalu ke mata ba saboda idonta ya rufe a kan son Deeni.

Yanzu haka itama contact ɗin Deeni ta shiga, Dp ɗinsa mai ɗauke da side view ɗin fuskarsa sanye da baƙin gilashi ta buɗe, tabbas wannan hoton da lafiyarsa ya yi shi, “Bai dai ji da kyau da kuma gayu ba”, Rahila ta faɗa a ranta tare da miƙe ƙafafunta a kan prayer mat.

Wani irin so da tausayi na daban take ma Deeni, idanunta ƙyam a kan hoton, lokaci ɗaya kuma zuciyarta na azalzalarta a kan son ta ce “Ya Allah, ka sa in zama sanadin warkewar wannan bawa naka”, domin ta ɗaukar ma ranta zata yi iya yinta ita da mahaifinta wurin ganin Deeni ya samu lafiya, kuma wannan ne zai sa ta zauna daram a zuciyarsa.

Buɗe ƙofar banɗakin da Fadila ta yi ne ya sa ta duban ta lokacin da ta fito, “Ki kashe fitilar ɗakin kafin ki kwanta”, Rahila ta bata umarni, don ta ga alamar kan gado zata wuce.

“Toh”, ta faɗa tare da sauke hamma, ɗaurawa ta yi da “Ke dai kina son zama cikin duhu” lokaci ɗaya kuma ta kashe fitilar ta kwanta.

Tuni hankalin Rahila ya koma kan phone tana duba maganar Lalu da ya ce “Dr. Baki yi bacci ba?”, A ranta ta ce “Ta ya zan yi bacci, bayan zuciyata na ta dakon son Yayanka?”, A zahiri kuma smily emoji ta aje mashi, sannan ta bi bayanshi da “Ina ɗan wani aiki ne shi ya sa.”

Hira suka ɗan taɓa, a nan ta samu informations sosai a kan Deena, domin ta ƙara faɗa ma Lalu irin kulawar da Deeni yake so wanda sai na kusa da shi zai iya yi mashi, nan yake faɗa mata ai Deeni na gida, matarsa kuma tana can gidansu wanka, a nan ta gane amarci ma suke ci da matarsa, tunda me aka yi a haihuwa ɗaya, “Lallai da sauran aiki a kaina”, ta faɗa cike da yanke ma kanta ƙaunar samun Deeni a wannan ƙurarren lokacin.

Rayuwa kenan, a lokacin da duk wani mai ƙaunar Deeni ke kukan baƙincikin rashin samun nasarar aikin da aka yi mashi har suke kasa bacci, a lokacin ne kuma Dr. Bello da tawagarsa suke murna su ma hada kasa bacci, domin idan akwai wanda ya fi kowa yi ma Deeni muguwar fata, toh shi ne.

Washe gari da sassafe haka ya zo hospital ranshi fal da farinciki, tamkar bushara haka ya riƙa bin collegues ɗinsa yana faɗa musu Deeni fa ya dawo, da an tambaye shi ya result amsar ita ce “Wannan fa ai sai dai ya yi haƙuri da idanunsa”, mafi yawanci sai dai su bi shi da dariyar yaƙe, da sun keɓe sai su riƙa gulmar shi.

Farincikin ransa bai ƙaru ba sai da ya shiga office ɗin Deeni, daga bakin ƙofa ya tsaya yana ƙare ma office ɗin kallo yana dariyar mugunta, ya ɗan ɗauki lokaci a haka, daga bisani ya ƙarasa tare da zama kan desk chair ɗin, “Deeni sai dai wani ba kai ba, idan kuma ka matsa toh ba office ba, har duniyar tsaf zaka bar ta”, cikin sautin da kowa zai iya ji ya faɗi wannan magana, yana kuma cika baki ne saboda a ganin shi mugun abin da ya ƙulla ne ke ta ɗawainiya da Deeni, bai san babu mai yi ba sai Allah.

Idanunsa ya lumshe tare da juyi na musamman a kan desk chair ɗin, lokaci ɗaya kuma yana tsara yadda zai ci karensa babu babbaka ta hanyar cin kuɗin marasa lafiya. Yana cikin wannan yanayin ne aka turo office ɗin, da hanzari ya buɗe idanunsa tare da miƙewa tsaye “Yallaɓai”, ya faɗa yana duban MD da ke ƙarasowa cikin office ɗin.

Ran MD ba daɗi bisa ga ganin Dr. Bello a kan seat ɗin Deeni ya ce “Duk lokacin da na shigo office ɗin nan sai in ga kamar zan samu Deeni a ciki”, cikin dariyar yaƙe Bello ya ce “Ai idan da rabo zai dawo wurinsa Insha Allah”, cike da ƙaunar wannan fata MD ya ce “Allah ya amince”, sai dai wannan karon ka sa cewa “Amiiiin” ya yi, saboda mugun abin da ya cika ma ransa.

Zagayowa ya yi, inda suka yi magana da MD cewar da yamma su shirya su je ganin Deeni, cike da ladabi ya ce “Toh Yallaɓai”, a cikin ransa kuma yana zalƙin ganin Deeni cikin kunci.

Kamar yadda MD ya buƙata haka suka yi, da Yamma suka shirya suka je gidansu Deeni, a falon mahaifiyarsu suka yada zango, inda duka suka nuna jimaminsu a kan yadda aikin ya kasance, MD ya ce ma Hajiyarsu Deeni “Wallahi muna jin damuwa sosai a kan halin da Deeni yake ciki, zan ma iya cewa dukanmu damuwar ta shafa, saboda samun wanda zai yi replacing Deeni sai an tona.”

Wani irin kallo Dr. Bello ya yi mashi ba tare da ya san ya yi ba, a ransa ya ce “Har abada kuma ba zai koma aikinsa ba, sai damuwar rashinsa ta kashe ku.”

Ba kowa ya lura da yanayin da Dr. Bello ba sai Hajiyarsu Deeni kaɗai, don an ce labarin zuciya a tambayi fuska.

Sam ita bata zargin Dr. Bello, amma kuma jikinta na faɗa mata akwai wani abu a ransa, wanda muddin ba Alkhairi bane, toh tana fatan Allah ya maida masa kayansa.

Wurin MD dake ta nanata damuwarshi ta maida hankalinta tare da faɗin “Rayuwa ce Alhaji, shi kalar tashi ƙaddarar kenan, sai mu yi masa fatan Allah ya ba shi tare da mu ikon cinye jarabawa.”

Da aka zo batun aiki MD ya tabbatar ma Hajiyarsu da Insha Allahu zasu yi iya ko ƙoƙarinsu wurin ganin Deeni ya koma aikinsa, ta yi murna sosai, duk da tana ganin abin a yanzu bai mai yiyuwa bane, a samu ma damuwar ta bi jiki, idan suka saba da ita ne toh zasu yi abin da ya dace.

Duk wannan tattaunawa da suke Dr. Bello sai tsuma zuciyarsa ta ke, suna tafiya ya kira Dr. Jabiru tare da tabbatar mashi da bayan Magrib zai je chemist ɗinsa. Ana yin magrib kuwa ya isa cikin gaugawa.

“Wai me ya hana ka zuwa ne”, Dr. Bello ya tambayi Jabiru bayan sun zauna a kan bench, “Toh me zuwan nawa zai amfana masa?”, Dr. Bello ya ce “Babu kam”, Dr. Jabiru ya ce “Toh ka gani, addu’a ce daga inda nake ma zan iya yi mashi”, baki Bello ya taɓe, “Kai da ke yi masa addu’ar ma”, Jabiru ya ce “Toh wai abinka ga ɗan’uwa musulmi.”

“Uhmm!” Kaɗai Bello ya faɗa, don idan ba muguwar fata ba bai san komai ba a rayuwarsa, kuma ba Deeni kaɗai yake yi ma haka ba, shi duk wanda ya gani a kan nasara, toh sai ya masa baƙinciki, shi ya sa sam bai cigaba a rayuwarsa, kuma ma ko ya samu cigaban, toh daga ƙarshe sai ya koma cigaban mai haƙan rijiya.

Zama ya gyara a kan benchin, tare da ɗauke idanunsa a kan motocin da suke wucewa a kan titin ya maido su ga Jabiru, “Ka san me?”, Jabiru ya girgiza kai “Ai sai ka faɗa.”

Bello ya ce “Bana son Deeni a rayuwata, don ya wahalar da ni kafin in samu abin da nake son samu a rayuwa, shi ya sa nake fatan ya dauwama a haka.”

“Aikuwa a hakan zai dauwama”, Jabiru ya faɗa cike da mugunta, Bello ya ce “Shi ya sa nake kallon MD da yake faɗin Deeni zai dawo aiki”, tarbar numfashinsa Jabiru ya yi “Ta ina?, Ai na rantse ba wannan maganar, kuma da wane idanun zai iya.?”

Bello ya ce “Only Allah Knows..!”, Da mugun gatse ya faɗi haka, sai dai tunda ya sako Allah a lamarin, toh magana ta ƙare, don shi ke ba makaho dama da kuma baiwar da bai ba mai idanu ba.

<< Mutuwar Tsaye 13Mutuwar Tsaye 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×