Skip to content
Part 13 of 26 in the Series Mutuwar Tsaye by Hadiza Isyaku

Tun bayan da Dr. Rahila ta tabbatar ma Deeni da cewar ba da jimawa ba za’a yaye shamakin da ke tsakaninsa da idanunsa fargabarsa ta ƙaru, don bai san wane sakamako aikin zai bayar ba, kawai dai ya fawwala ma Allah lamarin, domin yadda Allah ya so haka yake kasancewa, sai dai ya na fatan Allah ya sa a dace, idan kuma an samu akasin dacewar toh Allah ya ba shi ikon ɗaukar wannan jarabawar.

Mahaifiyarsu da matarsa kuwa sun fi kowa eager son jin sakamakon, musamman Mahaifiyarsu, don kuwa ta kira ya fi a ƙirga, burinta kawai a ce Addu’arta ta karɓu.

Su Hajiya Ummah da ke tare da shi kuwa ba a maganar su sakamakon wata fargaba ta rashin tabbas da su ma ta hana su saƙat, tun a gida Hajiya Ummah ke tambayar Rahila yadda take ganin sakamakon zai kasance, Dr. Rahila bata san gaibu ba, sai dai ta yi amfani da ƙwarewarta wurin kwantar musu da hankali, a asibitin kuwa sun so a shiga wurin Deeni tare da su, amma ƙa’idar aikin ta hana su, dole suka haƙura, amma gabaɗaya hankalinsu na can.

Yaya Asiya da ta rasa duk wata lakka ta jikinta ta ce “Allah ya sa dai a dace da wannan aikin”, duk suka ce “Amiiiin”, lokaci ɗaya kuma kaf idanuwansu na kan ƙofar ɗakin da Deeni ya ke, basu ƙi kawai su gan shi ya fito da kansa ba, don haka Rahila ta faɗa musu lokacin da suka so shiga.

A can ciki kuwa Dr. Rahila ce ke ba ma Deeni magana mai nutsar da zuciya, inda ta ce “Kamar dai yadda ka sani waraka ta Allah ce, mu iya aikinmu kaɗai mu yi maka surgery, kuma mun yi iya namu wurin ganin lafiyarka ta samu”, Dr. Jameel ne ya karɓe da “Wannan gaskiya ne, Insha Allahu ma we have a good expectation akan aikin, fatan mu dai Allah ya sa an dace”, Dr. Rahila ta ce “Amiiiin ya Allah.”

Deeni na jin duka maganganunsu, kuma tun kafin su faɗa mashi haka ya gama yanke yadda zai karɓi result ɗin, idan an samu nasara dole ya yi ma Allah godiya ta musamman, idan kuma ba a samu ba, toh har ya tsara irin haƙurin da zai yi, don ba zai iya jayayya da lamarin Ubangiji ba.

Cikin raunin murya ya ce “Thank you so much da efforts ɗinku, kuma ina ji a jikina Insha Allahu na samu lafiya, idan kuma har ban samu lafiyar ba, toh bana jin zarginku a raina, don waraka ta Allah ce.”

Sun ji daɗin maganarshi, musamman Rahila da burinta kenan ta ji ya yi magana, saboda tana kwaɗayin sautin muryarsa, ranta sal ta ce “Yauwa Dr, Allah ya sa a dace”, suka ce “Amiiiin.”

Har Dr. Jameel zai fara warware bandage ɗin da ke fuskar Deeni wayarshi ta shiga ruri, alfarma ya nema saboda Deena ce ta kira, cike da mutumtawa suka ba shi, ɗaga kiran ya yi, maganar farko daga can Deena ta ce “Yaya, hankalina ya kasa kwanciya”, Dr. Rahila na jin muryar Deena gabanta ya faɗi, bata san me ya sa Matar Deeni take ɗaga mata hankali ba.

Ƙunci bai ida mamaye ta ba sai da Deeni ya ce “Oh Sorry Dee-dee! Yanzu za a cire bandage kenan kika kira”, daga can ta ce “Da gaske?”, Yana ƴar dariya ya ce “Da gaske mana”, ta ce “Ni da yaronka muna ta addu’ar Allah ya sa ka dawo gida da idanunka tangaram”, ya ce “Amiiiin Tawan.”

Da a ce Deeni ya san bala’in da Rahila ke shiga idan yana making call da Deena da bai riƙa ɗaga kiran a gabanta ba, saboda shi mutum da ke mu’amala da mutane socially, toh bai sani ba bare ya kiyaye.

Wayar bata yi tsawo ba suka yi sallama, Dr. Rahila kuwa ta kiɗime, a hankali ta sulale kan chair ta zauna saboda ƙafafunta basa iya ɗaukar ta. Dr. Jameel na lura da sanyin jikinta ya shiga warware bandage ɗin da aka naɗe ma Deeni idanu ba tare da ya yi magana da ita ba.

“Ki nutsu mana Rahila”, wani sashe na zuciyarta ne ya ankarar da ita, saboda tsaf za a gane mata ta kamu da son maso wani, dan kuwa yadda ta yi noticing riritawar da Deeni ke ma matarshi da wahala wata mace ta sake birge shi.

“To ta ya zan iya nutsuwa; bayan sudden na ke samun kaina a irin wannan yanayin?”, Tambayar da ta yi ma kanta kenan, sai dai kafin ta samu answer Dr. Jameel ya katse mata tunani da faɗin “Dr. Result ne ya rage.”

A hankali ta lumshe idanunta, lokaci ɗaya kuma ta ja dogon numfashi tare da sauke shi, ta yi haka dan ta samu sassaucin wutar kishin da ke babbaka mata zuciya.

Kaf sun san wannan salon, mafarin Dr. Jameel ya yi mata kallon tsanaki tare da faɗin “Ya dai?”, Cike da pretending ta ce “Nothing”, kai kawai ya rausaya don ya fahimci Akwai wani incident, kuma is related to Deeni, because zuwansa ne ta fara shiga irin wannan yayin.

Deeni kuwa kawai abin da ya ba ransa fargabar result ɗinsa ce ta sa ta wannan yanayin, take tausayinta ya kama shi, saboda ya san irin pain ɗin da Doctors ke ji idan suka yi aiki aka samu matsala.

Cike da zaƙuwa Dr. Jameel ya ce ma Deeni ka buɗe idanunka a hankali, Kamar yadda suka buƙata haka Deeni ya yi, sai dai da yake kaɗan-kaɗan ya buɗe bai ga komai ba.

Acikin nutsuwar dole Dr. Rahila ta ce “Ya dai Dr., me kake gani?”, da a ce Deeni zai iya yin ƙarya, toh da ya yi ƙaryar yana gani duk don ya faranta musu rai, toh ko ya yi ƙaryar a take za su gane mashi.

A dake ya ce “Dishi-dishi nake gani”, Ba tare da tunanin komai ba Dr. Jameel ya ce “Okay, ka cigaba da buɗe idanun”, yanzu ma kamar yadda ya buƙata Deeni ya yi, Dr. Rahila kuwa, kafe shi ta yi da dara-dara idanunta, burinta shi ne Deeni ya fara yin arba da ita yayin da ya buɗe idanu, domin duk abin da ya fara gani ba zai taɓa goge mashi a zuciya ba.

Cikin sanyin murya ta ce “Yanzu kana gani?”, Ta inda sautin muryarta ke fitowa Deeni ya juya kansa, shiru ya yi , cikin ransa yana jin ba daɗi, kai ya girgiza wanda shi ne kaɗai abin da zai iya.

Tunda Rahila take bata taɓa jin tashin hankali da ƙunar rai irin na yau ba, a hankali ta lumshe idanunta da take suka ciko da ƙwalla, “Ya Salam”, ta furta cikin dakusasshiyar murya, lokaci ɗaya kuma ta dafe goshinta, cikin murya mai kama da raɗa ta riƙa cewa “Lahaula wala quwwata Illa bi Llah!”

Take zargin kanta ya mamaye ta, cikin rawar murya ta tambayi Jameel “Me ye matsalar?”, hannayensa ya ware tare da faɗin “Allah ne masani Rahila.”

Duk yadda suke ji bai kai ga Deeni ba da ya rasa wane kalar tashin hankali yake ciki, tabbas mutuwar tsaye ta same shi, duk da bawa na gari baya yanke tsammani daga rahamar Ubangiji, amma kam ya karaya a yanzu, fatanshi kawai Allah ya ba shi karfin ɗaukar nauyin wannan jarabawa Amiiin.

“Toh yanzu miye mafita Jameel?”, Rahila ta sake tambayar Dr. Jameel bayan ƴan dubarun da suka yi a take, idan har akwai wata mafita a yanzu toh bai san ta ba, dan bai san ta ina aka samu akasi aikin bai yi ba har sai an yi ƙwaƙƙwaran bincike.

Deeni ne da dukkan tawakkali a ransa ya bata amsa “Mafita na wurin Allah, sannan abin yi shi ne mu bar ma Allah lamarin, shi ya san yadda zai yi da ni”, dukkansu sun fahimci sarewa a Maganar Deeni, cike da tausayinsa Dr. Jameel ya ce “A’a Dr., Ai ƙa’idar aiki bai ce haka ba”, Kai Deeni ya jinjina “Toh shikenan, Allah ya datar da mu.”

Rahila tuni bakinta ya kulle, tunaninta ma ya toshe, idan ka tambaye ta me ye takamaiman tunanin da ke ranta?, Amsar ita ce bata sani ba, sai da wayar Deeni ta dawo da ita daga tunanin da ta lula, shi ma saboda ta riƙe Deena ce ta kira.

Kallon Deeni ta yi, a zaton ta zai ɗauki waya, sai ta ga shiru, ita kanta ba ta kishi take ba, bare har ta iya damuwa da wayarsa, shi kuwa abin da ya hana shi ɗaukar waya shi ne bai san me zai iya faɗa ma Deena ba, bare kuma Mahaifiyarsa.

A can waje kuwa su Hajiya Ummah ƙagare suke su ji result ɗin Deeni, Khamis kuwa sai kai kawo yake a bakin ƙofa, Hajiya Ummah da ta ji shiru ne ta taso, bakinta na faɗin “Ko yaya?”, Kafin Khamis ya ce wani abu ne aka buɗe ƙofa, da sauri suka kalla dan ganin mai fitowa, Rahila ce, ba tare da sun lura da yanayinta ba Hajiya Ummah ta ce “Ƴata, an dace?”, Cikin yaƙen gaske ta ce “Alhamdulillah dai.”

Sosai jikin Khamis ya yi la’asar, sai dai kawai ya danne inda ya bi su Hajiya Ummah da Yaya Asiya suka shiga ciki.

Tun a bakin kofa suka tabbatar da ba kanta, Hajiya Ummah ta ce “Ya dai Deeni?”, Dr. Jameel kuwa nauyi da tausayinsu ya ji, ya san Kunya ce ta sa Rahila ficewa, don haka dole ya yi iya bakin ƙoƙarinsa wurin ganin ya kwantar musu da hankali.

Zagaye Deenin da suka yi ne ya hana shi magana, sai dai ya ja Khamis da Lalu suka fita, a can ya tabbatar musu da aiki bai yi ba fa, kamar yadda Deeni shi ma ya sanar ma su Hajiya Ummah. Sun ji tashin hankali da ƙunar rai ba kaɗan ba, amma tunda Musulmai ne dole su yi haƙuri, sannan su ɗauki mataki na gaba.

Bayan duk sun gama ƴan koke-kokensu ne Rahila ta zo da batun sake ma Deeni aiki, nan fa ya ce atafau bai yadda ba, kawai dai su cigaba da ɗora shi akan magani, mai yiwuwa sauƙin ya zo daga baya.

Mahaifan Rahila basu so haka ba. Sai dai duk da haka Babanta ma bai goyi bayan sake yi ma Deeni aiki a yanzu ba, sai ma ya yi mashi alƙawarin zai taimaka mashi da duk iya ƙoƙarinsa wurin ganin ya samu lafiya ko da za a fidda shi abroad ne. Kwana ɗaya suka ƙara domin ɗora Deeni a kan treatment ɗin da ya dace da shi, washe gari bayan sallar azuhur ne suka kama hanyar Kaduna, can da yamma suka isa gida, inda dama tuni an san da result ɗin tun kafin zuwansu, aikuwa tamkar gidan makoki haka gidan ya kasance.

Hajiyarsu Deeni na kukan tausayin ɗanta ta ce “Wannan ita ce ƙaddararmu Deeni, Allah ya bamu ikon ɗaukar ta.”

A ɓangaren Deena kuwa tana jin sun shigo gari itama Alhaji Lawan ya sa Driver ya kawo ta wurin mijinta. Tana samun damar keɓewa da shi a ɗakinsa ne suka ci kukansu son rai, Deeni ya ce “Deena, haka Allah yake son gani na, idan na ce dole sai na yi yadda nake so ban kayauta ba, kuma ba zan samu yadda nake so ɗin ba”, cikin kukan da take ta ce “Ba komai, sai wanda Allah ke so ne yake jarabta, kuma mu duka ta shafa ai, Allah ya bamu ikon ɗauka”, ya ce “Amiin.”

Wayarta ce ta katse musu hira, number Mommah ce, ba dan kada ta yi laifi ba da taƙi ɗagawa saboda zuwan ma ba da son ranta Deena ta yi ba har sai da Alhaji Lawan ya sa baki, daga can Mahaifiyarta ta ce “Nan za ki kwana halan?”, Kai Deena ta girgiza “A’a, na kira Driver wayarsa not reachable”, kuma ƙarya take bata kira ba.

Allah ya taimake ta ta ce “Ya je can cikin gari ne ɗazu, amma gashi nan yanzu zai zo tunda ya dawo”, Deena ta ce “Toh”, bayan sun gama wayar ne ta shige jikin Deeni, cike da kewarsa ta ce “Kamar na kwana a nan”, Deeni ya ce “Koh?” Ta ɗaga kai, ya ce “Ai mun yi kewar juna sosai, wai yaushe ma zaki dawo?”, tana manne a jikinsa ta ce “Nima ban sani ba, amma dai sai mun gama wanka ko”, ya ce “Saura kwana nawa?”, Ta ce “Nan da few weeks”, kai ya jinjina “Allah ya dawo mani da ke lafiya matata.”, Ta ce “Amiiin”, ƴar soyayyarsu suka sha a gurguje, kasantuwar Raihan na can wurin jama’ar gidan.

Ba a jima ba Driver ya zo ya ɗauki Deena, tana komawa gida Tambayar farko da kowa fara yi mata ya “Idanun Deeni?”, Ta ce “Da sauƙi”, Ummanta ta ce “Kamar ya da sauƙi, ya warke?”, Deena ta ce “A’a”, Ummanta ta ce “Ahaf..! Ai addu’a ce kawai mafita”, Alhaji Lawan ya ce “Allah dai ya ba shi lafiya” suka ce “Amiiiin ya Allah.”

Ciki Deena ta koma don bata son tambayoyin bin ƙwaƙwaf ɗin da Ummanta ta fara yi mata a kan Deeni. Alhaji Lawan ne ya dubi Umman Deena “Al’amarin Deeni na ba ni tausayi wallahi”, baki ta ɗan yamutse” Toh ya fa za’ayi da ƙaddarar Allah”, saboda ta fahimci baya son tana sukar shi, bare har ta bijiro da ƙwace ƴarta, wanda ta rantse indai tana numfashi sai ta raba auren.

A ɓangaren Deeni kuwa sai da dare ya raba ne ya tashi, bai wani tada Lalu da nufin jagora ba ya shiga ban ɗaki ya yi alwala ya fito, duk da zuciya ya ke ganin ɗakin, inda yake zaton nan ne Gabas ya kalla tare da kabbara sallah a kan carpet ɗin da ya mamaye ɗakin, sai da ya yi raka’o’i masu yawan gaske, sannan ya tsagaita, Salatin Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya yi sau ba adadi, sannan ya karanta Al-ƙur’ani Ma-tayassara.

Hannu ya ɗaga sama, idanunsa na zubar da hawayen tausayin kansa ya shiga yi ma Allah kirarin da ya fi so, sannan ya ɗaura da Salatin Annabi wanda shi ne maganin dukkan bala’i da masifa.

“Allah ni ne bawanka Nuraddeni ɗan gidan bawanka Abdullahi, kai ne ka jarabce ni da wannan jarabawa, ina rokonka idan ganina Alkhairi ne a gare ni, ka dawo mani da shi ya Allah, idan kuma ba Alkhairi bane, ka riƙe shi ya Allah, sannan ka ba ni haƙuri da juriyar rashinsa ya Allah, domin ni ɗin mai rauni ne.”

Addu’a ya yi sosai, tare da kuka kamar ransa zai fita. Lalu na cikin barcin gajiya ya ji kamar ana kuka, firgirgit ya buɗe idanunsa, yana jin Deeni ne gabansa ya faɗi, tabbas ya san dama dole ya yi damuwa, mafarin bai yi mamaki ba, sai ma tausayin ɗan’uwansa da ya cika mashi rai.

Ba tare da wani ɓata lokaci ba ya diro daga kan gadon, sakamakon baccinsa da ya yi ɓatan dabo, banɗaki ya faɗa ya yi alwala sannan ya fito, a gefen Deeni ya kabbara ta shi sallar wadda specifically don nema ma Deeni agajin Ubangiji yake yinta.

Duk duminiyar da yake Deeni na jinsa, mafarin ya ɗan samu relief, saboda ya ƴan’uwansa kaɗai gata ne daga wurin Ubangiji, tunda suna son sa tare da tausayinsa.

Dukkansu gaba ɗaya kushu’insu ya koma wurin Allah Madaukakin Sarki. Bayan sun gama kwarara addu’oin ne sun shafa Lalu ya matso daf da Ɗan’uwansa, hannunsa ya ɗaura a kan na Deeni da ke shimfiɗe kan lap ɗinsa, cikin murya mai cike da zallar tausayi ya ce “Allah ya baka lafiya ɗan’uwana..”

<< Mutuwar Tsaye 12Mutuwar Tsaye 14 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×