Tun bayan da Dr. Rahila ta tabbatar ma Deeni da cewar ba da jimawa ba za'a yaye shamakin da ke tsakaninsa da idanunsa fargabarsa ta ƙaru, don bai san wane sakamako aikin zai bayar ba, kawai dai ya fawwala ma Allah lamarin, domin yadda Allah ya so haka yake kasancewa, sai dai ya na fatan Allah ya sa a dace, idan kuma an samu akasin dacewar toh Allah ya ba shi ikon ɗaukar wannan jarabawar.
Mahaifiyarsu da matarsa kuwa sun fi kowa eager son jin sakamakon, musamman Mahaifiyarsu, don kuwa ta kira ya fi a ƙirga, burinta kawai a. . .