Duk da irin zafin damuwar da Deeni ke ji a ransa, bai hana shi jin sanyin farincikin raɓar shi da Lalu ya yi ba, "Ɗan'uwa mai daɗi.." abin da ya faɗa kenan a ransa, kafin ya buɗe bakinsa da ya yi nauyin gaske ya ce "Amiiiin Lalu, Nagode sosai."
Shiru dukan su suka yi, ƙasan ran Lalu yana jin wani irin ƙuncin da ba zai iya misalata shi ba, domin duk abin da ya shafi Deeni su ya shafa kamar yadda kowa ya sani.
Deeni kuwa wannan ce damar da yake da ita wurin expressing. . .