Skip to content
Part 20 of 26 in the Series Mutuwar Tsaye by Hadiza Isyaku

Farinciki marar misaltuwa ne ya bayyana a fuskar Md, kasantuwar fatanshi kenan dama a samu sanadin da Deeni zai fita ƙasar waje domin neman lafiyarsa, wanda hakan ne kaɗai mafita a gare shi.

Cike da wannan farinciki ya dubi Dr. Safiyya tare da faɗin “Amma na ji daɗin wannan ƙoƙari naku, Allah ya saka da Alkhairi, ya kuma bada iko Amiin”, Dr. Safiyya ta ce “Ai wannan shi ne kaɗai abin da zamu iya yi ma Deeni, duk da ya cancanci fiye da haka”, Md ya ce “Gaskiya ne wannan, Allah ya sa a dace”, ta ce “Amiiiin.”

Sun yi maganganu sosai masu matuƙar muhimmanci a kan Deeni, da kuma akan halin da al’aumma suke ciki dangane da sha’anin lafiya, daga bisani ne ta tafi.

Ran MD cike da farinciki ya wuce office ɗin Dr. Bello bayan ya dawo daga rakiyar Dr. Safiyya, zaune ya iske shi yana duba system ɗin dake gabansa.

Bello na ganin Md kawai gabansa ya faɗi, saboda jikinsa na ba shi akwai wata magana dangane da Deeni wanda kuma ko shakka babu Alkhairi ne, mikewa ya yi bakinsa na faɗin “Yallaɓai”, ɗan jinjina kai Md ya yi tare da ƙarasowa cikin office ɗin.

Bakinsa a washe ya ce “Ya maganar aikin da na sa ka?”, Tambayar sa Bello ya yi “Wane daga ciki?”, Duk da recently suka yi maganar da shi.

Cewa ya yi “Na Deeni mana, da gaugawa ake buƙatar report ɗin, saboda akwai ya yiyuwar za a fita da shi India.”

Tamkar wanda aradu ta faɗo mawa haka Bello ya ji a ransa, cikin sarkewar murya ya ce “Yallaɓai India kuma.?”

Tunda Md yake bai taɓa gane Bello na ma Deeni hassada ba sai yau da fuskar Bellon ta nuna, da yake ba yaro bane take ya maida maganar ambiguous, ta hanyar faɗin “Abin da muke masa fata kenan idan da iko, idan kuma ikon bai samu ba kawai ya cigaba da neman maganinsa a nan”, saboda MD ya san mutum mugun icce ne, ko ya mutu sai an haɗa da ɗauri.

Kai Bello ya ɗan rausaya, cike da son basarwa ya ce “Ai ya fita wajen shi ne mafita”, Md ya ce “Ai ba fidda shi wajen ba, ikon yin hakan ne mai wahala, yanzu kana ganin nawa za a yi spending wurin zuwanshi da waje?”, Bello ya ce “Kuɗin na da yawa Yallaɓai”, Md ya ce “Toh ka gani ko, kawai Allah ya bamu mafita”, Bello ya ce “Amiiin.”

Tabbatar mashi Bello ya yi da Salary ɗin Deeni na shiga cas a account ɗinsa har tsawon watanni biyar ɗin da bai da lafiya, sannan ta ɓangaren record ɗin Deeni he is reliable and punctual a wurin aikinsa wanda kowa ya sani, shi ya sa ma Bello bai iya yin ƙwangen da zai ɓata shi ba.

Md na fita Bello ya zauna jagwab, saboda ya gaji da jin maganar Deeni a abakin MD, dalili kuwa shi ne indai ana maganar Deeni, toh akwai yiyuwar watarana ya dawo wanda shi ne baya so, don haka dole a shafe tarihin Deeni a asibitin nan.

Shi kuwa Deeni yana can ta shirin dawowar matarsa ya ke, duk da damuwar da Deena ke ciki ta ƴan kwanakinan ta fara damunshi, saboda duk lokacin da ya kira ta sai taƙi ɗauka, ko kuma idan har ma ta ɗauka toh dawahala idan bata yi kuka ba.

Abin kuma ya fara damunshi, shi ya sa ya zaƙu ta dawo, don ya san shi ne maganin duk wata damuwa da ta samu kanta a ciki.

Da yamma gab da magarib ya na zaune a ɗaki shi kaɗai ya danna ma number ta kira, ya yi sa’a kuwa ta ɗauka, bayan sun gaisa ne ya ce “Deedee”, murya can ciki ta amsa, cike da kulawa ya ce “Menene damuwarki?”, Duk da tambayar da ya yi mata bata buƙatar sharhi amma ta ce “Me ka gani?”, Ya ce “Ina tambayar ki, kema kina tambaya na?”, Shiru ta yi, saboda yadda ya yi maganar kamar cikin fushi yake.

Cewa ya yi “Serious matter ne, bana son ki ɓoye mani komai, miye damuwarki?”

Tabbas idan Deena ta faɗa mashi damuwarta toh zai iya mutuwa, don ita ce cikamakon farincinsa, cewa ta yi “Yaya ka san Mommah da faɗa, toh two days ɗinan muna ta samun misunderstanding da ita, shi ne sai ta yi ta faɗa”, sosai ya gamsu da maganarta.

Cewa ya yi “Me ya sa kike mata laifin?”, Amsa ta ba shi “Ka san halinta fa”, ya ce “Duk da haka, ki kiyaye abin da bata so kin ji?”, Ta ce “Insha Allahu Yaya zan kiyaye”, yadda ta ƙarashe maganar cikin muryar kuka ne ya sa shi sassauta Murya ya ce “Deena, bana son kina fushi, sai in ji duk na kasa walwala.”

Daga can ta ce “Insha Allahu zan kiyaye Yaya”, ya ce “Yauwa tawan, yanzu kin ga on Saturday su Asma’u zasu je gyara mana gidanmu, na zaƙu na ji ki a kusa da ni.”

Kasaƙe Deeni ya yi yana jiran maganar ta, aikuwa sai ya ji akasin haka, don kuwa ƙit ta tsinke kiran.

Sake kira ya yi, kawai sai ya ji not reachable, bai wani damu ba, saboda ya san halin network da rashin tabbas.

Deena kuwa “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un bakinta ya shiga faɗi, don bata san ya zata yi da Deeni ba, ita dai ba zata iya ce mashi ga halin da ake ciki ba, bare har ta tsaida mashi hope ɗinshi na shirin komawarta.

“Allah ka bani mafita ta Alkhairi a cikin wannan lamari”, ta faɗa cikin ɗacin rai.

Lokacin sallar magrib ne, don haka ta shige banɗaki ta yi alwala ta fito, sallah ta gabatar da adduoin da ta saba na neman mafita.

Tana gamawa ta yi jugum a kan sallayar, zuciya ce ke ta saƙa mata da kwancewa, har ta saƙo mata yadda zata haɗu da Deeni kafin nan da Saturday ɗin da yake faɗar zasu je gyaran gida.

“Toh wace ƙarya zan yi ma Mommah?”, Ta tambayi kanta, saboda idan ba wani ikon Allah ba ta gama haɗuwa da Deeni a matsayin mijinta, shiru ta yi, don duk hanyar da ta ɓullo sai ta kwance mata.

Tana nan har aka kira Insha’i, tashi ta yi ta gabatar, bayan ta gama ne ta sauka kasa wurin ɗanta da ke a hannun masu aikin gidan.

A falo ta taras da Ummanta, bayan ta mata sannu ne ta zauna, idanunta da suka yi zuru-zuru ne ta kafe Tv da su.

Hakan ya ba Ummanta damar observing yanayinta, ta lura da da Deena ta rame sosai, kuma ko a yanzu tunani take yi ba kallo ba, saboda a cikin film ɗin akwai wuraren da ya kamata a ga reaction ɗin Deena, amma babu.

Cike da damuwa Umman Deena ta ce “Deena”, bayan Deena ta juyo ne ta ce “Abin nan yana damunki sosai ko?”, Deena bata yi zaton wannan tambayar ba, da ƙyar ta ƙakaro murmushi ta girgiza kai “A’a Mommah”, ɗan rausaya kai Ummanta ta yi “Gashi kuma duk kin rame?”, Sai da Deena ta kalli jikinta sannan ta ce “Allah kuwa Mommah bana damuwa”, cewa ta yi “Toh shikenan”, ɗan shiru ne ya ratsa wurin, daga bisani Umman Deena ta ce “Umm! Na faɗa maki gobe zamu je Kebbi da Alhaji?”, Tamkar suprise Deena ta ji maganar, cewa ta yi “A’a Mommah.”

Faɗa mata ta yi Yayan Alhaji Lawan da ke can Kebbin ne ya yi rashin lafiya, shi ne zasu je gano shi, ran Deena sal ta ce “Can zaku kwana?”, Amsa mata ta yi “Eh, kwana biyu ma zamu yi Insha Allah.”

Deena ta ce “Allah ya ba shi lafiya”, Ummanta ta ce “Amin.”

Suna nan suna taɓa ƴar hira Alhaji Lawan ya dawo daga masallaci, bayan ya amsa gaisuwar Deena ne ya wuce falonsa, yayin da Ummanta ta mara ma mijinta baya.

Deena ma ɗakinta ta koma bayan ta karɓi ɗanta, daga Flight mode ɗin da ta maƙala wayarta ta cire ta, aikuwa sai ga kiran Deeni ya shigo.

Tana ɗagawa ya ce “Me ya samu wayarki ne?”, Amsa ta ba shi “Network ne Yaya”, ya ce “Unguwarku ta fara zama ƙauye ko?”, Cike da shagwaɓa ta ce “Ba wani nan”, ya ce “Toh ai unguwarku ne kaɗai ba Network”, tana ƴar dariya ta ce “Ku ma a taku ai babu”, ya ce “Haka kika ce”, ƴar hira suka ɗan yi, daga nan ta ce so take ta ganshi, ya ce “Saurin me kike?”, Ta ce “Au har na yi sauri ma?”, Ya ce “Eh mana”, ta ce “Toh shikenan, na yi fushi”, lallaɓata ya yi ya ce “Sorry, duk lokacin da kike son gani na baki da damuwa tawan”, ta ce “Da gaske?”, ya ce “Yep”, ta ce “Toh za ka ganni unexpected”, ba tare da tunanin komai ba ya ce “Toh shikenan.”

Washegari da misalin ƙarfe goma Ummanta da Alhaji Lawan suka tafi Kebbi, ita kuwa ji ta yi tamkar ranar sallah ce a wurinta.

Tana zaune a kan sallayar ta da gama sallar walha ta danna ma number Deeni kira, ringing biyu cikin na uku ya amsa kiran, bayan sun gaisa ne ta ce “So nake na gan ka Yaya”, daga can ya ɗan yi shiru tamkar yana nazari kafin ya ce “Toh Deedee, ta ya kika shirya gani na?”, Cewa ta yi “Gida zan zo na ganka”, da mamaki ya ce “Gida kuma?”, Ta ɗaga kai tamkar yana a gabanta “Uhmm”, daga can ya ce “Ba kya gudun kada Mommah ta ce kin zaƙe?”, da sauri ta ce “Ai bata nan?”, Ya ce “Ina ta je?” Ta ce “Kebbi, kuma sai jibi zata dawo.”

Tana jin lokacin da ya sauke ƴar ajiyar zuciya kafin ya ce “Okay, toh ki bari zan zo anjima da yamma”, ta ce “Da gaske?”, ya ce “Insha Allah.”

Ta ji daɗi sosai, don dama ta fi son su haɗu inda zata sake sosai, duk da agidansu Deenin ba wata matsala ba ne.

A ɓangaren Dr. Bello kuwa kwana biyu baya iya bacci sakamakon maganar Dr. Safiyya da ta ce Soonest Deeni zai dawo aikinsa, a kwana na uku ne da asubar fari ya kira Jabiru tare da shaida mashi ya gaji da azabar da sunan Deeni ke gana mashi a zuciya, don haka zai sa a yi ma Deeni farraƙu tsakaninsa da Md, don muddin MD na tuna Deeni, toh fa sai ya dawo a bakin aikinsa.

Daga can Jabiru ya ce “Farraƙu ya wuce wanda surukarsa zata yi mashi?” Bello ya ce “Kamar ya?”, Ya ce “Zata karɓe ƴarta ne a cikin week ɗinnan, wannan bala’in kaɗai ya ishe shi masifar duniya, idan kuma kana son a daɗa mashi wani sai ka tanadi kuɗi da kayan aiki ka kai ma bokaye da ƴan tsubbu.”

Ko kusa babu Imani a zuciyar Bello, cike da rashin tausayi ya ce “Bala’in surukarsa daban, nawa kuma daban, don haka so nake a shiga tsakaninsa da Md a raba su, idan ya so ma ya mutu”, daga can Jabiru ya ce “A’a Bello, ka bi komai a sannu”, cewa ya yi “Hmm! Ai maganar bi a sannu ta ƙare, don haka dole na ɗauki mataki”, Jabiru ya ce “Shikenan ai.”

Da yamma yana tashi wurin aiki ya wuce wurin sabon Malamin da aka haɗa su, a nan ya zayyana mashi damuwarsa, shi kuma ya karɓi kuɗi tare da haɗa shi da wasu ƙullikan magunguna, da layu.

A wannan lokacin ne kuma Deeni tuni Lalu ya kai shi wurin matarshi, don shi ma so yake ya ji ɗumin jikinta.

Kaf gidan ba kowa, don masu aiki sun fita, Lalu ma wani uzuri mai ƙarfi ya fidda shi, hakan ne ya ba Deena damar yin zaman dirshan a jikin mijinta.

Tana kwance a ƙirjinsa murya can ciki ta ce “Yaya”, amsawa ya yi “Dee-Dee”, raɗa mashi ta yi a kunne “Na fara sallah”, ya ce “Really?”, Ta ce “Na rantse kuwa”, idanunsa a lumshe sakamakon yadda take ta ƙara shige mashi ya ce “Ki ce in fara shiri kafin ki koma”, a shagwaɓe ta ce “Har sai na koma kenan?”, bai yi zaton komai a maganarta ba ya ce “Eh mana.”

Kawai sai ji ya yi ta ƙanƙame shi tare da fashewa da kuka, a gigice ya ce “Ke, wai menene?” kasa ba shi amsa ta yi, sai dai ta cigaba da kukan, wanda ba na komai bane sai na tausayin kanta, don ta san kewar jikin mijinta kaɗai ba zata bari ta zauna lafiya ba yayin da aka raba su.

Cewa ya yi “Me yasa kike sa ni a damuwa da yawan kukanki?” Tabbas da Deeni ya san dalili da bai yi mata wannan tambaya ba, ita kuma da bata son damuwarshi sai ta tsagaita kukan.

Rarrashin ta ya yi da maganganu masu tsuma zuciya, tare da kai ƙarshensu da sumbatarta a baki, aikuwa da yake Deena ta amsa sunanta mace, sai da ta ja hankalin Deeni har ya ji baya buƙatar komai sai son kasancewa da ita, cikin wani irin yanayi ya ce “Deena, a gidanku ne fa, kada ki sa na ji kunya.”

Deena ta san nisan da mutanen gidan suka yi har Deeni zai iya samun abin da yake so a wurinta basu dawo ba, cewa ta yi “Kada ka damu Yaya, na ɗaukar mana matakin tsaro”, da wannan ta labbace shi har ya kasance tare da ita a falon, kasantuwar ya yi muguwar kewarta.

Sai da duk suka dawo hayyacinsu ne Deeni ya ce “Me kika sa na aikata? Tana zaune a gefensa ta ce “Oho!”, cike da tsarguwa da kansa ya ce “Oho ko?”, Ta ce “Eh”, ya ce “Ba damuwa”, wayarsa da ke gefe ya lalubo tare da kiran number Lalu a kan ya zo ya kaishi gida.

Anyi sa’a kuwa Lalu na hanya, ba a jima ba sai gashi ya zo. Duk irin wannan azarɓaɓin da Deena keyi idan zasu tafi, a yau bata yi shi ba har suka bar gidan. Kimtsa falon ta shiga yi, lokaci ɗaya kuma tana kuka, don jikinta ya bata kusancin ƙarshe ne suka yi ma juna, sai kuma wata ƙaddarar idan Allah ya nufa, shi ya sa take kukan kewarsa, bayan ta gama gyara wurin tsaf ne ta goya ɗanta, sannan ta koma ɗakinta.

Deeni kuwa yana komowa gida ya faɗa banɗaki, ruwa ya sakar ma jikinsa, lokaci ɗaya kuma yana ta recalling yadda ya kasance da Deena. Lallai ita ɗin ta dabance a cikin mata, don kuwa salonta na ƴa mace ya fi na can baya, don haka dole cikin week ɗinnan ta koma don cigaba da kwankwaɗar zumar da ke tattare da ita, daƙyar ya iya yin wanka da alwala ya fito.

A nan ɗakin ya gabatar da sallar magarib da Insha’i, yana gamawa ya fito, cikin varendar ya tarar da Ummansa da Asma’u, inda ya zauna suka sha hira, nan ne kuma suka yanke shawarar jibi su Asma’u zasu je sharar gida, a lokacin ne kuma a ka kira number Umman Deena tare da shaida mata, sannan aka buƙaci daga wurinta ta bada wasu da za a je gyaran gidan tare da su, buɗan bakinta a cikin waya sai cewa ta yi “Hajiya ina ganin a dakata da zuwa sharar nan”, ba tare da fahimtar inda ta dosa ba Hajiyarsu Deeni ta ce “Kamar ya a dakata Hajiya Hadiza?”

<< Mutuwar Tsaye 19Mutuwar Tsaye 21 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×