Cike da kumfar baki Umman Deena ta nuna ta da yatsa, lokaci ɗaya kuma tana faɗin "Kitattara kayanki ki bar mani gida don Ubanki, in dai a kan Deeni ne kamar yadda na faɗa yafe ki, kin ga na daina ganinki bare baƙincikinki ya kashe ni, wanda kuma ya zalinci wani ni da ke Allah ya isar mashi."
Mutuwar zaune Deena ta yi, don bata yi zaton abin ya yi girman gaske haka ba, duk da raba ta da Deeni fitina ce a gare ta da bata misaltuwa. Idanunta a rumtse ta riƙa naɗar maganganun. . .