Soka ma zancen wuƙa Hajiyarsu ta yi ta hanyar faɗin "Ke raba ni da aljannun Asma'u, na fahimci kawai so suke su maida mani ita ƴar mai ganye", sosai maganar ta ba kowa na ɗakin dariya, saboda babu alamun fushi a tare da ita.
Lalu da ke neman abin da za a tsokani Asma'u ya yi dariya ya ce "Wai! Asma'u ta zama ƴar mai ganye za a ga ikon Allah", Hajiyar na dariya ta ce "Kai dai bari Farouk, kullum da aljannunta sun tashi ta shiga ƴan jaye-jaye kenan, ana fara gasgata ta. . .