Skip to content
Part 5 of 34 in the Series Mutuwar Tsaye by Hadiza Isyaku

Soka ma zancen wuƙa Hajiyarsu ta yi ta hanyar faɗin “Ke raba ni da aljannun Asma’u, na fahimci kawai so suke su maida mani ita ƴar mai ganye”, sosai maganar ta ba kowa na ɗakin dariya, saboda babu alamun fushi a tare da ita.

Lalu da ke neman abin da za a tsokani Asma’u ya yi dariya ya ce “Wai! Asma’u ta zama ƴar mai ganye za a ga ikon Allah”, Hajiyar na dariya ta ce “Kai dai bari Farouk, kullum da aljannunta sun tashi ta shiga ƴan jaye-jaye kenan, ana fara gasgata ta kuma ba a san me zai faru a gaba ba.”

Da ƴar dariya a bakin Deeni ya ce “Wallahi kuwa, ai a samu ma ta rabu da su”, Hajiyar ta ce “Toh ka gani, sam bana son ciwon iskan nan, ko don saboda aure, ba kowane namiji ne ba zai iya jurar tashin aljannu kullum a gidansa”, Hajiya Umma ta ce “Aikuwa dai, Allah dai ya yaye mata itama”, suka ce “Amiiin.”

Batun maganar ciwon Deeni aka dawo, inda ta cika musu zukata da tawakkali ta hanyar faɗin “Ko da wasa kada ku camfa mashi ciwo, ku bar shi cewar Allah ne ya ƙaddara mashi ba mutum ba, kuma ko akwai sa hannun mutum, toh ƙaddarawar Ubangiji ita ce a gaba, shi mutum ɗin ba zai iya abin da Allah bai yi ba.”

Sosai ta nuna musu illar ɗaura faruwar wani abu mai daɗi ko akasinsa a hannun wani mutum, duk da an san wasu mutanen sun iya mugunta, toh amma a bar ma Allah shi ya fi, gudun kada a yi asarar imani.

Sun ji daɗin wannan nasiha, kuma sun zauna daram a kanta. Cigaba ta tattauna tsarin hanyoyin nema ma Deeni lafiya suka yi, ba su suka tashi ba sai da lokacin sallar azuhur ya yi. A nan banɗakin Hajiyar su Hajiya Umma suka gabatar da alwalarsu, Salma kuma dama free take, don haka sai ta fito don ganin wainar da su Asma’u ke toyawa a tsakar gidan.

Lalu da Deeni ma suna fitowa daga ɗakin Deeni ya ce “Bari mu ga zan iya kai kaina na yi alwala?”, cike da ƙwarin guiwa Deeni ya zare hannunsa daga cikin na Lalu. Ɗan cak ya tsayar da nutsuwarsa, sannan ya cigaba da ƙare ma madaidaicin gidansu kallo da idaniyar zuciyarsa.

Gida ne madaidaici, wanda ke ɗauke da ɗakuna uku, biyu a jere, sai ɗayan kuma da ƙofar shigowa suna fuskantar ɗakuna biyun, inda duk suke a cikin babbar rumfar da ta cike tsakar gidan. 

Daga ɓangaren hagun ɗaukunan nan biyu na jere kuma kitchen ne, a gefensa kuma babban tankin ruwa ne da aka ɗora a kan rijiyar da ke ba gidan ruwa, ɓangare ɗaya kuma banɗaki ne yana opposite da tankin.

Gida ne na rufin asiri, wanda ƙarfin da su Deeni suka kawo ne suka taru suka gyara shi, don kuwa ba ƙasa ba, hatta rabin kowane lungu da saƙon bangon gidan duk tiles ne.

A hankali ya tako ya nufi tankin ruwa, Lalu kuma yana biye da shi a hankali shi ma, jikinshi ne ya ba shi Deena da Asma’u da kuma Salma suna kallon shi, saboda yana ɗan jin motsinsu a ƙofar kitchen.

Da zuciya ya kalli inda suke sannan ya ce “Kallona kuke ko?”, da ƴar dariya a bakinsa ya ƙarasa maganar.

Wannan ba sabon abu bane wurin Deena, don yana kwatanta irin haka a gida, Asma’u da Salma ne dai suka fara gani, inda Salma ta kasa ɓoye mamakinta ta ce “Yaya kana ganin mu?”, Amsa ya bata “A’a, kawai karanbani ne Salma.”

“Ayya, Allah ya baka lafiya”, ta faɗa tare da bin sa da idanu har suka kai wurin tankin, Asma’u kuwa tsoron kada Lalu ya gwalishe ta ne ya hana ta magana, sai dai kawai ta bi shi da kallon tausayi.

“Ka ga na kawo kaina ko?”, Ya faɗa tare da kallon inda yake zaton Lalu na tsaye.

Lalu ya ce “Gaskiya ka yi ƙoƙari sosai, idan kana haka komai ma zai zo da sauƙi In sha Allah”, saida Deeni ya dafa tankin ruwan kafin ya ce “Haka ne, Insha Allah zan riƙa kwantantawa.”

Buta Lalu ya miƙo mashi, da kansa ya ɗibi ruwa, sannan ya shiga banɗaki ya fito. Alwala suka gabatar, sannan Lalu ya yi mashi jagora, inda suka gabatar da sallarsu a nan cikin rumfar, wanda tuni Asma’u ta shimfiɗa musu abin sallah.

Da Hajiyarsu ta ji labarin Deeni da kansa ya yi alwala, ta ji daɗin ƙwarin guiwarsa, amma sai ta ce ya bi komai a sannu, ita tsoronta kada ya faɗa kan wani abu da zai cutar da shi. Sosai ya fahimce ta, kuma ya ɗaukar ma ransa kiyayewa.

Abinci Asma’u da Deena suka kawo, kusan duk ba sosai suka ci Jollouf rice ɗin ba, saboda ran ba wani daɗi yake musu ba, Hajiyarsu ma kawai dan kada su ce ta ƙi ci ne, amma da ba zata iya cin komai ba, saboda yunwar ma ta tafi.

Samun ƴar nutsuwar da suka yi ne ya ba su damar sanar da duk wani mai haƙƙin a sanar da shi a danginsu. Ƴan’uwan Hajiyarsu Deeni kuwa tun a ranar wasu suka fara zuwa saboda ciki ɗaya ta wuce wasa.

Su Deeni basu samu damar komawa gida ba sai da yamma liƙis, a nan ma neighbors ɗinsu har da nesa su ka yi ta shigowa, don tuni labari ya iske su. 

Dr. Bello kuwa ana idar da Magrib ya iso, an yi sa’a kuwa Lalu ya dawo daga masallaci, don haka shi ya buɗe mashi ƙofa, gaisawa suka yi, sannan ya ƙaraso cikin falon.

Deena na fitowa daga kitchen suka yi arba, ras! Ta ji gabanta ya faɗi, don ko kusa bata yarda da shi ba, saboda duk lokacin da suka haɗu, toh ya dinga satar kallon ta kenan. Murya can ciki ta gaishe shi, shi kuwa idanunsa ƙyam a kanta ya amsa, haɗe fuska ta ƙara yi, lokaci ɗaya kuma ta zagayo bayan kujerar da Deeni yake tsaye a gaban ta “Yaya bari in shiga ciki”, kai Deeni jinjina “Okay.”

Duban Lalu da shi ma yake tsayen ta yi tare da faɗin “Uncle Lalu”, sai ta ƙarashe da yi mashi nuni da ɗaki, kai Lalu ya ɗan rausaya alamar “Okay”, ciki ta wuce a ranta tana yi ma Dr. Bello tsaki.

Shi kuwa tuni yanayin Deena ya sa shi kama kansa, maido da hankalinsa wurin Deeni ya yi lokacin da ya miƙo mashi hannu. A yadda suka gaisa bai taɓa zaton baya gani ba, bayan sun zauna a kan three seater ne ya ce “Toh ya jikin Dr.?”, Sai da Deeni ya sauke gwauron numfashi, lokaci ɗaya kuma yana ɗan sosai gemunsa ya ce “Da sauƙi, amma bana gani fa.”

Ko kusa Dr. Bello bai fahimci me Deeni ya ce ba, cike da mamaki ya ce “Me ka ce?”, A natse Deeni ya ce “Bana gani.” Ya dakar da zuciyarsa ne saboda idan Dr. Bello ya ga karayar zuciyarsa zai ji daɗin kai labari a waje.

Duk da Dr. Bello baya ƙaunar mai ƙaunar Deeni, amma sai da hankalinsa ya mugun tashi, Sallallami ya shiga yi yana faɗin “Wata sabuwa kuma, ana zaune ƙalau sai wannan ƙaddara ta kasance?.”, Deeni ya yi mamakin rikicewarsa, ce wa ya yi “Toh Ikon Allah fa, Allah dai ya sa mu dace.”

Lalu kuwa rikicewar Dr. Bello bata wani ɗaɗa shi da ƙasa ba, don kallon munafiki yake masa tun da daɗewa. Tashi ya yi ya nufi masallacin cikin Estate ɗin domin gabatar da sallar isha’i. Hakan ya ba Dr. Bello yi ma Deeni kallon tsaf, take shaiɗaniyar zuciyarsa ta motsa, bai son lokacin da a ransa ya ce ba “Dama mutuwa ka yi. Koda yake wannan ai MUTUWAR TSAYE ce, don haka aiki kuma yanzu sai mu masu idanu”, a zahiri kuma cikin tausayin ƙarya ya ce “Deeni na tausaya maka, ina maka fatan Allah ya baka lafiya.”

Deeni ya san ba lallai ne addu’ar ta kai ransa ba, amma sai ya yi saurin faɗin “Amiin ya Allah, nagode sosai”, kasantuwar addu’ar maƙiyi tana saurin karɓuwa, saboda zai yi ta ne kawai da fatar baki, Allah kuma sai ya amsa domin ya kunyata shi.

Sun yi magana sosai, inda Deeni ya ce ya sanar da management ɗin asibitinsu. Deeni ya ba shi wannan damar ne saboda ba yadda zai yi, aikuwa tun a nan Dr. Bello ya fara kiran wasu yana faɗa musu, a lokacin kuma Lalu ya dawo. 

Aikuwa ya ji haushin haka, ƴan hare-hare ya riƙa yi, da abun ya ci tura ma sai ya riƙa sakin tsaki, Dr. Bello na lura da haka ya ce tafiya zai yi saboda kwarjini Lalu yake masa.

 Tashi Deeni ya yi da zummar raka shi, ransa cike da jin daɗin ganin naƙasun Deeni ya ce “Ai ka bar shi kawai Dr”, cikin jajircewa Deeni ya ce “A’a dai”, Dr. Bello ne ya riƙe mashi hannu, inda Lalu ya bi bayansu, sai da suka je bakin ƙofa ne ya sakar ma Deeni hannu “Dr. Ka tsaya nan kawai”, duban Lalu ya yi “Sai nake ganin ku nema mashi Stick mana, zai samu sauƙi, kuma zai rage muku wahala.”

Lalu da ya zo wuya ya ce “Ai bama ganin wahalar yi mashi komai, sannan bama tunanin ciwon ya yi worst ɗin da zamu neman masa stick”, sosai martanin da Lalu ya yi mashi ya daburtar da shi, dariyar yaƙe ya yi “Gaskiya kuma haka ne, Allah ya bada lafiya”, Lalu bai da sauran lokacinsa, sai dai Deeni ne ya ce “Amiin dai.” 

Bayan ya shiga motarsa ya tafi ne Lalu ya kama hannun Deeni suka koma ciki, a falo suka tarar da Deena zaune, cewa ta yi “Wancan ya tafi kenan”, Lalu ya ce “Munafikin ya tafi, duk ya cika ma mutane kunne da surutan banza da wofi”, cike da tsanar sa Deena ta ce “Sam ni bana son mutumin can wallahi.”

Maganar Deeni ya soka ma wuƙa, saboda baya son gulma, barin maganar suka yi, sai ma ta koma kitchen ta haɗo musu dinner.

Shi kuwa Dr. Bello kiran ɗan’uwan ɗayan ya yi, wanda a tare suke ƙulle-ƙullensu. Mahaɗa suka yi a chemist ɗin Dr. Jabiru a ƙofar gidansa don ya kai masa gulma.

“Dr. Namu”, Dr. Jabiru ya faɗa lokacin da Dr. Bello ya zauna a kan bencin da yake zaune daga wajen chemist ɗin, shaking hands suka yi tare da gaisawa, cike da zalƙi Dr. Jabiru ya ce “Bani in sha don Allah”, saboda Dr. Bello ya ce mashi akwai labari.

Dr. Bello na dariya ya ce “Yanzu ma kuwa zan baka”, gyara zamansa sosai ya yi a kan bencin kana ya dubi Dr. Bello da ya kasa kunnuwa yana jiran abin da zai faɗa.

Cigaba ya yi da magana “Yau na ga ikon Allah a tare da Deeni”, Dr. Jabiru na jin an ambaci sunan Deeni gabansa ya faɗi, saboda duk lokacin da aka ambace shi alkhairi ne zai biyo baya, shi kuma baya so.

Tsaki ya ɗan ja “Deenin me, dama a kan batunsa ne zaka sa mani rai?”, dariya Dr. Bello ya yi “Daɗina da kai ba ka cin ribar zance, ka bari ka ji ƙarshen labarin mana”, Dr. Jabiru ya ce “Ina sauraron ka.”

“Toh Deeni dai ya makance, ƙaryar ƙwararren likita ta ƙare”, Dr. Bello ya faɗa cike da jin daɗi.

“Ya makance fa ka ce?”, Dr. Jabiru ya jefo mashi tambaya mai ɗauke da ban mamaki, Dr. Bello ya ce “Na rantse kuwa”, cikin jinjina al’amarin Dr. Jabir ya ce “Ikon Allah, amma da mamaki fa al’amarin nan”, Dr. Bello ya ce “Ai sai ka gan shi ne mamakinka zai ƙarasa fitowa fili.”  

Cikin kasa gasgata batun Dr. Jabiru ya sake tambayar shi “Kuma ba dundumi ne ba?”, ma’ana irin makancewar da mutum ke gani biji-biji, wani kuma yana gani da rana, amma baya gani da daddare, wani kuma sai dare yake gani.

Dr. Bello ya ce “Ai ɗif ganinsa ya ɗauke, sam baya gani ko kaɗan.”

Ɗan shiru Dr. Jabiru ya yi, cikin ransa kuma yana tuna irin kakagidan da Deeni ya yi musu, wadda ta samo asali daga ƙwarewar aikinsa, ransa fal da murnar samun ƴancin yadda suka ga dama ya ce “Ka ji abin Allah, mutum dama sai ka ce shi kaɗai ya iya, ai yanzu sai na ga wurin uban da matan garin nan zasu je wurinsa ya duba su idan matsalar su ta koro su”, kaɗa kai Dr. Bello ya yi kana ya yi magana mai cike da mummunan zargi “Kai dai bari, duk wadda ta zo, da zarar an ce baya nan sai ka ga suna fushi, na rasa tsiyar da yake musu.”

Nan fa suka buɗe file ɗin aibata Deeni, har da su yi masa ƙazafin mu’amala da matan mutane, daga ƙarshe suka ce ai yawan kallon private jikin mata ne ya makantar da shi, tunda duk gynecologist sai ya ci karo da ganin irin wannan. Shaf! Sun manta da zasu bada shaidar abin da suke faɗa a wurin Allah, tunda basu taɓa ganin ko da ɗaya na mugun halin da suke siffata Deeni da shi ba.

Da suka dawo batun zamantakewarsa ta aure kuwa, Dr. Bello da ke ɓoyon wani abu a ransa dangane da Deena ya ce “Wai kana ganin matarsa zata iya zama da shi a haka kuwa?”, Cike da ƙwarin guiwa Dr. Jabiru ya ce “Ai ko zata iya, toh wannan miskilar uwar tata ba zata bari ba, saboda dama ba son auren take ba, kawai ƙwazaba ce ya ga ƴar masu kuɗi ya liƙe mata.”

Nan ya ba Dr. Bello labarin mahaifiyar Deena saboda ya san ta sosai. Daga ƙarshe ya fiddo waya aljihu domin ya ƙara tabbatar mashi da wacece ita. Numberta ya danna ma kira, sai da ta kusa tsinkewa sannan ta ɗaga da sallama, bayan ya amsa ne ya ce “Ranki ya daɗe, kwana biyu”, daga can ta yi magana a takaice”Wallahi kuwa”, kallon Dr. Bello ya yi tare da taɓe baki, kana ya ce

“Wai wani labari nake ji”, katse shi ta yi da faɗin “Na me fa?”, Dr. Jabir ya ce “Na surukinki mana, an ce wai ya makance”, daga can ta ce “Nima haka nake ji wurin mahaifiyarsa”, cewa ya yi “Toh Allah ya kyauta”, ta ce “Amiiin”, bata bari ya ƙara wata magana ba ta katse kiran.

Dr Bello da ya yi kasaƙe yana jin gulma ya dube shi “Ya na ji kamar bata son magana”, Dr. Bello da ya san halinta sarai ya ce “Ka san ita fa shu’uma ce kuma miskila, idan bata so magana ba zaka iya kiran ta sau ɗari bata ɗaga ba, idan kuma a waje ne kuka haɗu kuna iya shafe awa biyu a wuri, daga gaisuwa ba zata sake cewa uffan ba.”

Baki Dr. Bello ya taɓe, “Taɓ! Wanda ya damu da ita yana ruwa”, Dr. Jabiru ya ce “Kai dai bari”, wani mutum da ya zo siyen magani ne ya katse musu hirar, sallamar shi Dr. Jabir ya yi, sannan ya dawo suka cigaba daga inda suka tsaya na gulma da makircin tsiya.

Deeni kuwa yana tare da matarshi ake ta kwashe mashi zunubi. Bayan sun yi shirin bacci ne ya ɗan zagayo da hannunsa a jikin Deena da suke fuskantar juna ya ce “Ɗazu wai ɗingishin me ki ke? Hankalina ya tashi fa”, shigewa ta yi a jikinshi “Firgici ne kawai Yaya, ka san tsoron iskoki nake, musamman irin na Asma’u, sai kuma zaman da na yi wuri ɗaya ƙafata ta riƙe.” 

Shi kam ya fi kowa sanin haka, tunda ko labarin ban tsoro Deena bata sauraro, bare kuma ganin abin tsoron a fili.

“Nima na yi tunanin haka, amma ƙafar ta daina riƙewa ko?”, a ɗan shagwaɓe ta ce “Umm, tun a lokacin ma”, cike da kulawa ya ce “Toh Allah ya ƙara lafiya”, ta ce “Amiiin.”

Hira mai cike da kulawa gami da tausayin juna suka shiga yi, daga nan har bacci mai sa nutsuwa ya ɗauke su.

Washegari kuwa Deena na haɗa musu breakfast wayarta ta fara ruri, da hanzari ta duba don ganin mai kiran ta, sunan “Mommah” da ta gani ne ya ɗan kada mata gaba.

Da hanzari ta ɗaga kiran tare da komawa gefen gado ta zauna. Gaisuwa irin ta ƴa da mahaifiyar suka yi, daga bisani Maman Deena ta ce “Wai meke faruwa da Deeni ne nake ta samun mabanbantan wayoyi?”, A yadda ta ƙarashe maganar cikin sanyin murya ne ya ba Deena ƙwarin guiwar faɗin “Makancewa ya yi Mommah”, daga can ta ce “Shi ne kuke ɓoyewa ko?”, a gaggauce Deena ta lalubo hanyar kare kanta ta ce “Na ga bakyanan ne Mommah, shi ya sa ba a faɗa maku ba sai kun dawo”, daga can Maman ta ce “Hmm, Allah ya ba shi lafiya toh”, Deena ta ce “Amiiin”.

Tabbatar ma Deena ta yi da suna dawowa daga tafiyar zata zo ganin shi, daga nan kuma suka yi sallama.

Komawa ta yi wurin Deeni da ke zaune a ƙasan carpet yana sauraron ta, zama ta yi tare da tambayar shi “Ko wa ya faɗa ma Mommah baka da lafiya?”, Faɗa mata ya yi Hajiyarsu ce, saboda sun aje magana cewar ita zata sanar da ita.

Breakfast ɗinsu suka yi, suna gamawa Deeni ya koma kan sofa da zaman da ya zame masa jarabi, ita kuma ta dawo Kitchen ta cigaba da aikin gida ita da mai aikinta..

<< Mutuwar Tsaye 4Mutuwar Tsaye 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×