Skip to content
Part 15 of 22 in the Series Na Cancanta by Halimatu Ibrahim Khalil

Sai da ta gama ringing number din Hamid da na Kira harta katse ba’a ‘daga ba tunanina ‘daya biyu ya bani ko dai baya ‘daga baqon number ko baya kusa da ita.

Wayar na cigaba da dannawa, ina jin mamaki wai wannan wayar ce ta haura hamsin ta tafi ‘daruruwa, kuma an kashesu ba’aji wani ‘dar ba,ni Kam da ku’din aka bani ai ba ni ba, harsu Halima da Batul sai sun san Ina da ku’din, amma ga abunda yakamata suyimin da ku’din su ‘bige da siyamin waya ba zance ban gode ba dai hakan ma da sukamin yana cikin kulawa,amma babbar kulawar da nakeso ba ta ma shige da waya,ni iPhone ma saving number sai dai dake na iya karatu,duk inda zan shiga zan karanta shi,ni tunanina ma ni kam na koma Kano ya zanyi da wayarnan ai ajeta kawai zanyi. Jigilar jonata caji ma ya isheni.

Inaji Ruqayyah Muhammad na labarin yadda yayanta ke jigilar jona tashi caji ko kaiwa a class namu,ta ce dole ya saidata ya canza wata,amma ya ce ku’di na zauna masa zai sake siya tana da da’din anfani to ni dai har zuwa yanzu banga da’din anfaninta ba,da tunane tunanen nawa naji karar wayata number din Hamid ce ‘baro ‘baro da kyar na lalubi yadda zan da’ga kiran na ‘daga da sanyin muryar da tafi ta wa ha’da kalmomin da zan ha’da na bashi idan ya tanbayeni wacece ni

“Assalamualaikum”na furta nayi shiru ina jiran abinda za’a furta ‘daya ‘bangaren dan na kasa tantance waye ma zai fara yin sallamar nayi hanzarin farata dukda Mai kiran naka zai fara yin ta

“Wa’alaikumussalam Sumynah”

Murmushi nayi jin ya gane nice Mai kiran,da muryarshi mai da’din saurara ya daura

“Ai banyi tsammanin zaki kirani ba,yanzu na gama waya da Halima jiran ta turomin number naki,sai Naga baqon number an kirani ‘daya wayar,na mayi mamaki ba kowa ya sanni da layin ba,tom gwara ma Batul last week ta kirani da wancan layin da suke dashi,ba kati ban tsaya siya ba ta bank na kirata da wannan ‘din ashe har tayi saving,Batul kenan,ba ruwanta,kinji da’di ke Kam”

Na sake sakin murmushi jin kalmar qarshe ta Hamid ya sani saurin cewa “Da’din mene Malam ni ko naji haka”

Ya ‘dan yi ‘yar dariya mara sauti “Ah to kinji da’di mana Sumy,a’a ba dai Malam ba AbdulHamid Zaki fa’da min,aini ‘dalibinki ne”

Na jinjina maganar Hamid ‘din kafin na ce”Uhmm uhmm ban yarda ba Allah ina kunyar fa’dar sunanka,yawwa ni dai fa’damin mene nayi na jin da’din”

Ya ce “kalle ni Sumynah”

Dariya ya bani zancen nashi taya zan kalleshi ban ganshi kusa da ni ba

“Au dariya ki kemin ko?,saboda ‘dalibi yace malamarshi ta kalleshi,Allah gaske nake na daina amsa Malam,haba dai nifa dama can ‘dalibi ne,tom Sumynah me zan fa’da miki kawai fa kinajin da’di nace,nasan kina kwance ne kina hutawa yanzu haka ko ba haka ba?”

Ni dai duk zancen na shi ya dabaibayeni na dai daure”tom shikenan Abdul”

Ya ‘dan min muryar shagwa’ba
“Uhm uhmm gaskiya Sumynah Abdul to na waye ba kice Abdul ‘dinki ba,ko dai ba ki yarda da soyayyata ba ne,naga kinata shamin qamshi ne,Sumy da gaske nake ina qaunarki bama iya so ba dan Allah ki bani dama,Ya Abid na fa’da dai dai ko?”

Na ‘daga kai Kamar yana kallona duk ya kashemin jikina daga fara ‘yar firar tamu na daure”tom Abdul I’m sorry kunyarka nake,ka sa zuciyarka kawai na ce ne,yana lafiya lau”

“Tom ya zance miki tunda qinqi fa’damin,a gaidashi yaushe ne zanzo nifa ko yanzu ma a shirye nake da zuwa”

Na dai yi murmushi”zaiji a’a fa yau fa muka ha’du ka dai saka ranar dai banda gobe amma”

“Saboda me Sumayyah kuma yaushe raban na ganki Sumayyah ko dai da matsala ne baki so na ko,na haqura shikenan idan kince hakan zan yarda amma kuma bansani ba ko wani ne ya rigani karki ji nauyina kinji”

Murmushi nayi kawai sainaji jikina duk yayi min sanyi Hamid kenan ni kam banga wani abu da zance na gani tare da shi ba, kawai naga Kamar yana tsoro ne,ganina ni ‘din ba wai ‘yar wani ba ce ba”A’a fa bahaka bane,amma ko goben kazo shikenan”

Da farin cikinshi da naga alamu a muryarshi”Yawwa Sumynah ko da yaushe ina qara sanki ina addu’ar Allah y bani ke matsayin mata,ban wai ta’ba jin a guri kusa ma zan Fara soyayya ba sai akanki,ji nake Kamar almara ne,lallai kam yau Hajiya zan qarasa yini ina ma hirarki fa,kinsan anan ina wajen iyayen mamana da zama ne,ina tunanin ma ai na fa’da miki”

“Eh ka fa’da min ina tare da su Halima lokacin ace ina gaidata nima”

Ya furta”zata ji,wai sumy na tanbayeki?,gaske ne su Halima iya friends na ki ne”

“Eh mana,friend nawa ne tundaga junior class har yanzu”nayi maganar ina sake sauraronshi

“Ayya gaskiya,banyi tunanin ba kuda wata alaqar jini ba,ai har Kama ma kukemin,na kasa yarda Mukhtar teacher na ku na English ya cemin ba familynku ‘daya ba,shine ma ya fara fa’damin a gwarzo kuke namasan garin muna wucewa idan nazo Kano zan koma katsina wata Friday anan na tsaya nayi sallahr Juma’ah ma,tom gaskiya kun wuce qawaye dai,sai dai triplets,i mean ‘yan uku,tom amma Sumynah ce babba”ya qarasa maganar yana dariya

Nima dariyar ya bani nayi sama sama”eh hakane zuwa mukayi, anytime ma zamu iya komawa garinmu, a’a fa ka rabani da Halima ai tuni mun bar mata girman tom ita fa kasan lallai ita abin matured takeson yi Batul harta haqura da girman,tafa girmema Halima amma ta ce ta bata girman,bare Kuma ni”

Dariya yayi yana “wayyo ni Hamid kice haka kuke fama da ita,ai daga yanayi dai na lura Haliman zakuyi fama,nima Muna da Halima yarinyace amma har mun fara fama ‘diyar qanwar mamana ce,yini take qiriniya idan suka zo,wato itace babba na gama alama tom gashi ta shiga zuciyata ta min maganar zata turomin number naki kafin na furta,hala bata kwace miki position a school ko ni banma ta’ba ganin results naku ba,”

“Uhmm Ni Kuma Batul ta turomin ita,ai Halima,Kuma nayi mamaki da ta saba da Kai haka,ah kana da sa’a kam,ko dan saboda Yaya hakim ne dai nake tunanin,duka sunayenku kusan is the same,tana shiriritarta din nan duk wuceta muke,amma ta fimu qoqari fa,kawai ai mu ba muda aikin yi da muke karatu jinta ta ke a higher table wannan da kake kallonta”

Ya sa dariya “Eh haka ne,suna Abdul suma da yawa kenan ma qila ko?,nima gidanmu  hakane zaki kwana Abdul ba za’a gane wanne ba cikin mu ba,dan ma anan nake zama,akwai AbdulHalim,Abdulshahid, Abdulra’ouf, gani AbdulHamid shiyasa idan ba zaki kira in full ba sai dai kice ko Hamid, Shahid,Halim,Ra’ouf,yanzu ne ma muke da Mahmud,Amir,wato gifted ce kenan”

Na ‘dan ta’be baki”ta’b wanne gifted shiririta dai,ai Halima mashiririciya ce tun muna biye mata har muka daina,Ayya Suma gidansu Halima ya wanci hakane sunayen su”

“Ayya Masha Allah,gaskiya kam ta san kan ta ne a karatu da alama,naji ana mata Mrs Aliyu a class,ina kokarin shigowa”yayi zancen yana dariya

“Uhm uhmm, stubborn girl kenan Halima batajin magana duk qiriniyarmu ka saba da mu duka zakasan ta wucemu, amma Halima ba dai kirki”na yi zancen ina daurawa da bashi labarin soyayyar Aliyu da Halima yana bina da abin da yaji na dariya yayi abarsa ,a haka ya katse kiran

Sai dare na samu kiran su Ummah gaisawa kawai mukayi Ahmad ya karbe wayar yana koromin jawabi da tanbaya fa’di ba’a tanbayeka ba kenan nasha surutu tun ina biyewa har ya zama daga uhm sai uhm uhmm,saida ya gama zancen Khadijah tayi saurin kar’bewa kafin Rumaisa ita ma surutun nata ta gama ina biye mata,har dai na gaji itama,ta bawa Rumaisa ba jimawa mukayi ba ita Kam akwai sanyin hali,ni da ita tafiyarmu tafi zuwa ‘daya,sai Sadiq sarkin rashin ji ya amsa da ganan Khalil,daga shi na katse wayar ina ya gaidamin Aisha yana gata na katse kiran Dan nasan shiriritar Khalil,gashi na farajin barci

Lokaci ‘daya wata fa’duwar gaba ta zomin bayan katse wayar ba abun na sake Kira ba saboda a yanayi naji su lafiya da akwai damuwa Ahmad zai fa’da min,dukda nasan ummah zata iya kwa’barshi addu’a nayi kawai,da tunane tunanen duniya da addu’a Allah ya kawo abunda za’a yi a Gwarzo na Alkhairi da zamu je daganan na bi Abbahmu mu koma gida,dan tunani da zullumi ka’dai sun isheni anan ko da babu wata cusgunawa,ga tunanin zuwan Hamid ‘din a goben ya ma abun zai kasance da ma sauran tunanikan da suke sake zuwarmin barci yayi gaba dani kasancewar dama nayi Shirin kwanciyar tawa, harda addu’a kafin ma ta kira su Ummah.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Na Cancanta 14Na Cancanta 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×