A zaune na sameshi kan 'daya daga cikin kujerun robar dake farfajiyar gidan gabana ya yanke ya fa'di idanshi na kaina har na qaraso inda yake da rawar jiki na ja kujerar na zauna ina faɗin.
"Yaya Samir gani."
Shiru yayi kamar ba zai amsamin ba kafin yaja dogon numfashi"Sumayyah kin kyautamin kenan?, ko nace kin kyautawa kanki?,na daukoki dan kisamu kyakkyawar rayuwa ki zama Kamar Fatima,a raina na baki matsayin da yama zarce na fatimah,ni nasan ciwan ki,nafi dacewa ki tunkara da kowacce damuwa ko matsalar ki amma malaminku da Kika tsinta. . .