Skip to content
Part 17 of 22 in the Series Na Cancanta by Halimatu Ibrahim Khalil

A zaune na sameshi kan ‘daya daga cikin kujerun robar dake farfajiyar gidan gabana ya yanke ya fa’di idanshi na kaina har na qaraso inda yake da rawar jiki na ja kujerar na zauna ina faɗin.

“Yaya Samir gani.”

Shiru yayi kamar ba zai amsamin ba kafin yaja dogon numfashi”Sumayyah kin kyautamin kenan?, ko nace kin kyautawa kanki?,na daukoki dan kisamu kyakkyawar rayuwa ki zama Kamar Fatima,a raina na baki matsayin da yama zarce na fatimah,ni nasan ciwan ki,nafi dacewa ki tunkara da kowacce damuwa ko matsalar ki amma malaminku da Kika tsinta  rana tsaka shine zaizo har inda kike,a cikin rayuwar da nine nafi dacewa da ke, Sumayyah,ko da aurenki na ce zanyi ban yi laifi ba,duk tattalin da nake inaso na samu kusanci da ke ne.”

Hawayen naji suna zubarmin masu ‘dumi na ‘dago na kalleshi ba Zan jure kallan yaya Samir ba idanunshi sun Fara rinewa nayi saurin cewa”Yaya Samir Kaya haquri,baxan sake ba insha Allah.”

“Dago ki kalleni Sumayyah ki amsamin tanbayata.”

Dagowa nayi ba dan ina so ba na kalleshi da hawayen da ke cigaba da fitowa daga idanuna

“Sumayyah ina San aurenki ne, kece macen da na fara so da qauna tun bansan meye soyayya na,Sumayya ta Samir ce,na jawoki rayuwata ki saba dani da sauran Familynmu,duk da ni dake abu ‘daya ne amma babu sabo tsakaninmu,dan Allah karki kalli Abbah ni da shi ba ‘daya bane ki amince min,Dan Allah ki bawa wancen haquri idan soyayya ce tsakaninku ba dan Allah Sumayyah,idan ba kisan aurena ba zan miki dole ba.”

Shiru nayi kawai tunda ya fara maganar Yaya Samir dai ba shida wani makusa a ina sanina shi duk wani shashanci ba shi cikinsa Yaya AbdulMalik ne dai komai da ruwansa,nasan ba wai da Abbah ko Ummi zan zauna ba hayaniya kuma tunma daga kan AbdulHamid Abbah Hashim ya fara ta,bare Yaya Samir inasan Yaya Samir saboda halayyar shi,Amma ya zanyi da AbdulHamid ya bani dukkan yaqini akaina,ya zai ji idan na kawo masa wani zance daban,gaba ‘daya lissafina ya dagule so nake na bar musu rayuwarsu gaba ‘daya hankalina ya koma gida idan na koma gaba ‘daya wayarma Banga anfaninta ba,ba nida wata mafita anan, maganarshi ta katse ni

“Ba kicemin komai ba Sumayyah ,baki Sona ko?,Banda ce a soni ba ko?,kifadamin?,Dan Allah Sumayyah wancen ya fini matsayi da cancanta ko?,ki fa’damin mana.”

Kuka na fashe da shi amma bamai sautin sosai ba,waini Yaya Samir yakema wannan magiya abin kunya ne a wajena Yaya Samir yazo neman alfarma na kasa yi masa,ni Sumayyah cikin kukan na Fara
“Yaya Samir dan Allah ka maidani gidanmu gobe,dan Allah.”

“Daina kukan Sumayyah ko yau kikeso zan maidake kin gaji da zama dani ko? bakison ganina yanzu?,wani ya rigani ko Sumayyah?, shikenan,zan maidake gida,Ina jiranki amma dama ko da yaushe na rayu cikin jiranki saboda Jininmu ‘daya,kuma na dace dake Sumayyah a nawa tunanin nfi kowa sanin ciwanki ,fatana ki samu rayuwa me kyau,dan Allah ki yarda dani Sumayyah.”

Maganar nama gaji da jinta bare amsa masa waɗannan iyayen tanbayoyin wani ‘bacin rai yake tasomin musamman idan na tuna da Abbah Hashim da yadda zai ansa ƙudirin dake zuciyarmu hakan yasa na cirewa kaina wannan ƙudurin da a yanzu dama zuciyata ta zartar dashi, ciki na miqe zan  shiga,Yaya Samir ya biyo bayana.

“Sumayyah ki tsaya ki share hawayen ki dan Allah,Kuma yanzu gaban Abbah din Zan nunaki matsayin matar da nakeson aure,ke ce na tsaya jira a duk shekaruna,ke ce matata insha Allah tun kafin a haifeki din zuwa yanzu.”

Ko kallonshi din ban tsaya yi ba bare cigaba da saurararshi saboda komai ya kwancema lissafina da tunanina,kayana nakeson ha’dawa kawai katsina tamin zafi a yau da yafi na sauran kwanakin da nayi cikinta kofar falon na bu’de na shiga a zaune na samesu Kamar dama jirana suke yi Abbah Hashim da nake koqarin shigewa ciki ya dakamin tsawa.

“Ke Sumayyah zo nan.”

Hawayen da suke fitomin suka cigaba da zubowa na dawo jikina na kyarma  na dawo na tsugunna qasan carpet kaina na qasa ba tare da na iya furta komai ba face jiran tanadin Abbah Hashim akaina da nake da tabbacin yau na masa laifi.

Cikin alamun fa’da ya fara”karki qara kiramin kowanne namiji kofar gidana bare cikin gidana,ke ki mayi gaggawar bararmin gidana idan bada ubanki na siyeshi matalautan banza Kun kasa zuciyar tsayawa ku ne ma ku samu,ubanki na tare da uwarku dangin tsiya kaf dangin Hauwa’u matalautane,gadon ta kukayi qashin tsiya garesu, nayi Kuma rantsuwa Abdullahi da sisina ban taimakonshi sai ya rabu da uwarku ya auro wata ko ya zauna babu matar,kuma Fatimah ta dace da auran wancen yaron bake ba,yadda ubanku yake sai dai ku samu irinshi ku aura bana muku fatan cigaba,idan har ubanku bai haqura da wannan matar ba uwarku.”

Ummi ta miqe tsaye Kamar Mai Shirin fa’da ta ‘daga murya.

“Haba Hashim me ita wannan abar ta sani itace Abdullahi ko ita ce Hauwa’u, Abdullahi shugaban qasa ya zama nayi imani bazai wa ‘diyarka Fatima haka ba,Kuma ‘yata bada yawuna ba wallahi Fatima tafi qarfin a cusata Dan ba koma baya bace, addu’a nake mata Allah yasa ta gane waye ke Kai ta daina biyema,nima da naso biye ma wacce riba naci,’yan uwana da suke rufamin asiri so kayi nima na zama kamarka mu ‘bata,arziqinka naka na yaushe ne da baka dashi har ubanta ya taimakeka,bare ‘yan uwana amma sune abokan adawarka bakasan na zauna dasu,ai sun rufamana asiri yanzu budinka,yazo”

“Khadijah ki dakatamin kan wannan yarinyar ni Kika miqe kina fa’dawa magana san ranki”Abbah Hashim yayi maganar yana qarasowa gaf dani dukan da yafaramin ba abun wasa bane ball yake dani yana faɗin”yau ko, Abdullahi ne gidannan sai ya barmasa gida bare ‘yarshi.”

Maganar Yaya Samir na jiyo duk da dukan da akemin yana,

“Abbah ka kyaleta haka zata koma gidansu yau din nan ni na kawota Kuma zan maidata, tabarwa Fatima wanda kake magana kanshi,ni zan aureta,Abbah zan kawo maslaha dan Allah ka barta haka naji duk maganar da kakeyi ka yafe mata tayi kuskure kar ka illatata Ummi tayi magana ba ita ba,Abbah ka saketa ni zsn aureta.”

Abbah ne ya sakeni Ina kuka yayo kan Yaya Samir a zabure.

“Samir me kake cewa zaka aureta ita Sumayyah zaka aura masu qashin tsiyar Abdullahi kakeson zama kenan ,wannan yarinyar har tana da abinda zaka so wajenta har kayi girman tunkarata da maganar kanasan auren ‘diyar Abdullahi,ni Samir! wallahi muddin ka kafe kan maganar ka na zare komai da nake ma,Zan barka kaje gaka gata nan Abdullahi ya zama ubanka ba dai ni ba,karka sake ka nemi ni bare taimakon sisin kwabo na.”

Ummi ta ja tsaki.

“Wai Hashim yaushe akai dare garin ya waye,Ni zan wuce masa gaba indai har tana sanshi ko zaka la’anceshi wallahi sai yayi niyyar alkhairi gareshi bata sharri ba Kuma na fika kusanci dashi,Ni ce na haifeshi nina raini cikinshi na haifeshi nayi duk dawainiya dashi,qaryar arziqi kakeyi ‘dan baqin ciki da hassada ‘yan uwanka ga sunan ba da’dinka suke ji ba bare Abdullahi yasa rai da yake nesa da zama daku.”

Abbah Hashim ya nuna Ummin yana”Khadijah ya isheni haka tunda ba ku ganin girmana kuje kuyi abunda zakuyi ku gani, Abdullahi bazai baku ‘yar shi ba tun yanzu naga alamun jari yakeson maidata,tafi karuwa iya karuwanci.”

Ummi dariya ma dagaji maganar ta bata”Hashim kanada lafiya kuwa ko dai hassadar takai haka ne,fatanka iya kan kanka zai qare,’ya’yana bazai jefesu ba tunda baka da tunani har kake ma ‘diyar qaninka fatan karuwanci da ‘yarka mace budurwa gabanka tuni nadawo rakiyarka iyayenka ma bazan shaidar da’din ka suke ji ba.

Abbah Hashim yana huci Kamar zaki ya fara koqarin barin falon.

“Na fa’da muku karna dawo na tadda wannan matsiyaciyar yarinya gidana,karkiga kina magana san ranki wallahi na dawo na tarar daku ranku zai mummunan ‘baci”, daganan ya sakai ya fice.

Ummi ta bishi da kallo wajena sukayo ita da Yaya Samir suna lallashi na da bani baki a haka na shiga ‘daki na ha’da kayana Yaya Samir yana jaddamin nayi sauri na fito,wayata da take yashe gado na kalla,Hamid ya fa’domin raina ya zaiji idan ya samu labarin bana Katsina din da labarin kudirin Abba akanmu zai amince da Fatiman a madadina ko kuma zai haqura ne gaba ‘daya wayata na ‘dauka hannuna na rawa na danna lambarshi wajen message rasa ma me Zan tsaya rubutawa nayi na daure nasa.

“Kaya haquri”itace kawai kalma Mai saukin da ko tunanina bazan wahalar ba,wayar na kashe na yi kokarin turata qasan jakar karamar ma da ba Wanda yasanni da layin haka namata raina ina iPhone ‘din banza ma bata da sauran anfani a duniyata.

Ina kuka Abid mutumina yanayi,Ummi na bawa Abid baki tana zata kawoshi da kanta wajena ana hutu,Yaya AbdulMalik da Fatima ko leqowa basuyi ba Yaya Samir yaja motar muka bar gidan a lokacin 12:30pm.

Rayuwar nake tunani yadda komai yake tafiya yake cigaba da tafiya ba nida tabbacin zan riski farin ciki a rayuwata haka kawai nakeji duk da ina tuna ubangiji shine maji’bancin lamuran ko wanne bawa,amma na rasa dalilin da yasa rayuwar batamin da’di wajen wasu wannan qaramin matsala ne ni Kuma da take damu babbar matsala ne a nawa bangaren, nasan idan nayi linqaya duniyar wasu din suna da labarai mabanbanta da zanma ubangiji godiya duk da ko yaushe cikinta nake.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Na Cancanta 16Na Cancanta 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×