Skip to content
Part 21 of 22 in the Series Na Cancanta by Halimatu Ibrahim Khalil

A washe garin ranar dana dawo Aunty Asma’u ta dawo daga Katsina da zallar abunda yafaru dani acan ta dawo qarya da gaskiya,haka suka tattara maza da mata a gidan suna maida yadda akayi Abbah ne da yaji Hajiya ta fara zaginshi akan zancen har tana cewa bai bamu tarbiyya ba mu tattara mu bar mata gida baza ta iya ba kar a ‘debo mata abun fa’da a gari ashe shine sakamakon komawa kanon da Abbah yayi saboda mu zamar masa jari yanaso yaji da’din mu zama ‘yan iska har yaran ‘ya’yan masu ku’di suna sona inba da lalata ba dame zasu so ni ina ‘yar matsiyata tana sake jaddada zasu ga qaryar Hamid Fatima zasu ha’dashi da ita suga ko gaskiya yakeyi zancen ni dama munsa ba lalata a Kano bincikeshi zasuyi inko suka samu bahaka bane Kuma yaqin amincewa da Fatima to itama bada yawunta ba akan Abbah ya aura ma Hamid ni saboda ban cancanci aure a zuriyya irintasu Hamid ba,su Aunty Asma’u da Abbah Jafar qanin Abbah bane shima sai Abbah Imran suke sake zuga Hajiya suka rufarwa Abbah da cin mutuncin su Aunty Luba kuwa su tunzurawa sukeyi da sake cin mutuncin Mamanmu suna fa’din sun yafeshi ga Hauwa’u,ina tsakar gidan ina share bangaren Hajiya nake jiyo zancen nasu har nagama basu gama ba, shiko Abbah sun hanashi tasowa dama nayi tunanin haka zata faru ko fiye da hakan maganar wayar da banji anyi ba tunanina ya bani ko basu san zancen ba inako Shirin barin wajen naji Aunty Asma’u na cewa”Ai iskancin Sumayya harda tsohon saurayina qanin wannan matsiyaciyar matar ta Yaya Hashim, matsiyata ne fa ba suda komai indai ba lalata sukeyi da Sumayya ba,ina xai kwashi maquda ku’di ya siya mata waya iPhone kunsan tulin ku’din da ake siyan wayar kuwa.”

Hajiya naji tana qoqarin rushewa da kuka”Abdullahi yanzu mazinaciya kake qoqarin maida ‘yar ka ta tabbatar shine dalilin turata Katsinan kenan,Hashim kuma yayimin waya namanta ma yace ko ku fito masa da ‘dansa ko ya maka ku qotu.”

Abba murya rau rau naji yana cewa”Hajiya Dan Allah ku daina jifan ‘yata da kalma Mai muni kalmar zina,duk talaucinmu da halin da muke ciki da rashin taimakonku insha Allah bazan haifi mazinaciya ba,koni nasa ta ta yi zina dakaina ni uba,danasan abinda Hashim zai sakamin dashi kenan da ban amince Samir ya daukarmin ‘yata ba,sun tozartata a qarshe ya Mata dukan da koni uba ban ta’ba yimata ba,Kuma yana jifana na boye masa ‘da,ina kiranshi yazo yayi min duk abunda yaga zai iya yi,kuma Ni ban ta’ba ma ‘yata sha’awar aure nan kusa ba bare ma mai ku’di.”

Abba Imran naji muryarshi yana kuma tafa hannu”dama Abdullahi ina zakayi sha’awar aurar da Sumayya kana qoqarin maidata karuwa tana kawoma ku’di,wallahi Hajiya fitinar da ke damun al’umma kenan yara ‘yan 17,18 zuwa sama sun zama karuwai qarfi da yaji saboda sun ha’du da uba mai matattar zuciya,kuma mata da maza yaran manyan ke wannan shai’dancin dasu wayasan mai Mahmud ‘din yayi da ita ya bata wannan wayar.”

Hajiya tasake rushewa da kuka”Abdullahi ka cuceni kuwa ashe da mazinaciya nake zaune a cikin gida,shegiya munafukar yarinya kalar uwarta,tunda na haifeka abun goma bazan ce wannan ‘dana Abdullahi ya bani ba,wallahi bazan iya zama da ku ba inko na zauna daku tsinke na daina daukewa saidai mazinaciyar ‘yar ka tayi shi.”

Abbah a fusace naji ya fara magana”Hajiya ki dakata iya nan da izinin ubangiji ban haifi mazinaciya ba kaf ‘ya’yan dana Haifa da zuriyyar su Kuma ba Wanda cikinku nake bi da baqin baki,Kuma rashin taimakon da kuka kasa yimin , aiki kuka kasa samarmin bai hana Ina kyakkyawar rayuwa ba Mai tsafta zama cikin ku Kuma na barshi kenan,ke uwata ce amma kan talauci na gaji da munanan kalman da kike jifana dashi da matata harda ‘ya’ya ma yanzu,kuma ni Hauwa’u ko wacce ‘ya zata haifarmin wallahi ta fiyemin harke a gurina na gaji da cin mutuncin da kukeyi min,bani na halicci kaina ba,kuma ‘ya’ya na wallahi sun fiyemin kaf ‘ya’yan ku daga yau Zan iya cewa babuni babu ku gida kuma ku Bari mai gidan yazo ya koreni da kanshi bazan rasa inda zan tsugunna ba da talaucin nawa, za’a kar’be ni.”

Kofar ‘dakin na je na tsaya ina zubar da hawaye inajin yadda Abbah ke fa’da a fusace ban ta’ba jin haka daga Abbah ba yana juriyar abunda ke faruwa kai kace bai San wani abu ba’cin rai bare yadda akeyi ba.

Maganar Abbah Imran a tsawace,tasa ni nima tsorata “Abdullahi kayi haukane Hajiya da ta haifeka kake fa’da wa magana haka saboda bakada tarbiyya bakasan mutuncin iyaye ba bakasan zafin haihuwar da ta sha ba.”

Tsaki Abbah yaja”ita wacece Imran ka fita harkata haihuwata tayi bata halicceni ba,tarbiyyar da ta bani nake gwadawa yau ainayi haquri ma kuda kullum kuke cikin gwada musu ita fa amma kune mutane ni talauci ya maidani bare,yaranku sai su bangajeni ma a haya saboda ina yawo a tsiyace,abun ya wuce nida matata ina koqarin bawa ‘ya’yan dana haifa tarbiyya kuna qoqarin iskantamin Sumayya indai ta lalace to duka ‘ya’yan da na haifa haka suke da yardar ubangiji ba zamu ga haka Kuma ga ‘ya’yan ku ban muku fatan suga haka,dan zina babban illah ce ga rayuwar namiji ma bare mace.”

Abbah Imran naga ya dauke Abbah da mari “mu kake fa’da wa haka Abdullahi”

Abbah a zafafe ya ‘dago ya wanke Abba Imran da marin shima
“Imran na fa’da ma kuma zan cigaba da fa’dama kowannenku muddin cin zarafin da kuke mana nida matata bai isheku ba Kun daura min da yarana,kunsan hukuncin zina a addinance,maiyi hukuncinshi ko Sumayya kuka kama tanayi muraran saiku fallasata ku qaramin wani masifar da ya ha’darmin na samun iyayena da ‘yan uwana amatsayin baku qaunata saboda abunda ban isa nayiwa kaina ba.”

Dakin na fa’da na rungume Abba ina kuka ina” Abbah ka kyalesu dan Allah mun fisu laifi da muke qoqarin zama dasu da shiga cikinsu duk da bamu cancanta da haka ba” rarumar da aka yomin ta baya yasa ni sakin Abbah nayi ta baya baya,Aunty Maimuna na gani ta zabgamin mari”Sakeshi dan uwar uwarki,matsiyaciya munafuka masu la’be kun rabamu da ‘dan uwanmu wallahi ko ba Abdullahi kuka nememu a dangin uba sai kun tabbatar da mun da’de da yankeku a cikin jininmu.”

Abbah a zuciye shima ya wanke Aunty Maimuna da mari haka Abbah yaja hannuna jiri na qoqarin ‘dibarshi na kakkamashi dan ko abincin safe a yau dinma bai ci ba har ukun rana tayi,ina riqe dashi muka qarasa ciki Mama muka samu tana kuka Kamar qaramar yarinya ko ni nayi dauriyar qinyi sai hawaye bare ita danasan daga ‘daki take jiyo hayaniyar kasancewar dakunan da muke jikin na Hajiya ne,gurinmu ta nufo ta kamashi ta shigar da shi falon sai da muka zauna Mama ta dubeshi.

“Haba mana Abdallah zakaje ka sawa kanka wani ciwan a banza baka da mai damuwa da hakan,tunda suka fara ka fito mama amma kamar,an dasaka.”

Tari Abbah ya fara,na tashi na dauko masa ragowar pure water na bashi Mama ta amsa tana cemin”Jeki kawo masa abincinsa a kitchen ,kitchen na nufa na kawo masa ha’de da cokali na saka a ciki” lokacin dana dawo ya tashi zaune.

Mama ya kallah bayan Fara cin abincin”Hauwa’u nagode miki da halaccin da kike min da kyautatamin na qoqarin zama dani cikin wannan halin da hantarar ‘yan uwana itace gaba da komai a yanzu gareki abun ya wuce wajenki har wajen Sumayya, Hauwa’u familyna basa tare dani saboda ni ‘din bawani bane,face talaka,abun yana damuna,bansan ya abun zai daura ba idan bana nan.”

Mama hawaye ta share nima ta ‘bangarena hakane
“Dan Allah Abban Ahmad ka daina wannan maganar wallahi inajima tsoron hawan jini,yanzu ya zama abun da ya zama abun kasa ba ne,da abunda ke faruwa,kafiso ka d’aga hankalinka muka ‘daga mana.”

“Hauwa’u dole na damu da yawa wannan fitinar tasu yau taron dangi kina ji sukayi min yakamata ma,ku bar musu gidan ki tafi gidan Gwaggo,yanzu ni na riga nawa ne ,Zan fiki juriya kawai nasan nunamin kike kina jurewa.”

Mama jin maganar Abbah ta ‘dago ta na kallanshi”Amma Abban….”katseta yayi  da cewa”Dan Allah Hauwa’u karkimin musu ku tafi ke da Sumayyah tunda yara nacan ma,idan suka gama shuka tsiyartasu zuwa dare suka tafi sai ku dawo kinsan Asma’u sai ta shigo har ciki ta fa’da miki magangana,ga Mubaraka ma sun ha’du،ni kinsan ba bakin komai nake a wajensu ba ni nasu ma bareke sunajin haushinki.”

Ba yadda muka iya Mama tasa hijabi nima na zari mayafina na yafa, kasancewar munyi wanka,muna fitowa ‘bangarenmu ni da mama muka qara sauri muka bu’de get gararau muka fice muna jin Aunty Mubaraka na cewa.

“Wanne ‘dan iskane ya bu’de mana kofa ya fita da gudu”

Aunty maimuna muka jiyo Muna qoqarin tura gate ‘din tana
“Futa ki gano mana ko barawo ne,ko yaron Yaya Abdullahi ne aka fara sace sace ya na bin yaron nan Shu’aibu na gidan Malam Habu.”

Ni abunma dariya ya bani su dai lamuransu sai addu’a mama ta kalle ni” ya da dariya Sumayya”Na ce “mama bakiji mai Aunty Maimuna ke fa’da ba”ta ce”naji mana kinsan shashasha ce Maimuna,ni dan kar siyo kaina na qara saurin nan gwara su ci kansu indai sune kafin kowacce ta tafi sai kinji kansu batse batse kuwa.”

Muna tafe muna fira har muka qarasa gidan su Mamah,gidan na qasa ne da simintin shi amma da sauri na  na riga Umma shigewa da Omm Habibah qanwar mamah da Zainab da itace qaramar qanwarsu Mamah naci Karo a tsakar gidan da na kwa’da sallamata juyowa sukayi suna kallona da amsawa suka bini da kallo “oh Sumayya anyi girma”Omm Habibah ta kalli Zainab ta ce”ke kinga Zainab har ta fiki girma ma.”

Zainab takalleta”to dama Sumayya ai ta girmeni kusan kece tsararta ma ya kike ha’da ni da ita.”

Da wannan Mama ta shigo itama sallamar da tayi muka amsa Omm Habibah ta kalli Mama “yawwa Yaya Hauwah Zainab ce sa’ar Sumayya ko ni”

Mama tayi dariya”ke ce Mana kiyi zuciya kiyi girma naga kin maida Zainab ce babba tunda kin maida Sumayya sa’ar Zainab.”

Dariya nayi na ce”wallahi Mama tunda nashigo Omm da zancen ta tareni ko nice sa’ar Zainab.”

Mama ta harareni da cewa”Qaniyar ki da Zainab in ba Zaki ce mata Aunty ba itama Omm Zainab ce.”

Zainab ta ce”barta Yaya nima zan hana Ahmad  yana cemata Yaya,ba dai na hannun dama na bane.”

Dariya mama tayi ta shige ciki ta barni da su Omm Habibah,da suke wanke wanke dama kujera na jawo na zauna kusa dasu hirar littafi suke yi”omm Zainab tace “yawwa Ommu an turo without my dreams ‘dinnan kuwa Dan Allah Kika anso charge ku bani na karanta nima,naji labarin Munira ni kinsan ina team din ta.”

Dariya naji omm Habiba tayi”lallai yarinyar nan,tom ko ki canza sheqa team din Hidaya yafi,saboda mamarta ta nada kirki ita ba Kamar kaltume ba.”

Ommu Zainab ta kalle ni”kinji fa Sumayya yakamata ki bawa Sumayya ta karanta ita ma,amma Munira ai tayi qoqari a dai matsayin roll ‘din da tafi to,kuma indai kinsan Hidaya kinsan Sumayya Kamar fa nida Omm Habiba din ne, ka’dan ya banbanta,su Kuma sa’anni ne ma Kamar twin suke.”

Nace “wai Aunty Zainab bazan gane ba gaskiya adai ‘yanmin nkaranta,yawwa ni ko ina wannan book din na Rufaidah da Abdurra’uf akaqi musu aure sun ha’du ne a super market ShopRite ne ma,tom basu sake ha’duwa ba sai bikin wata friend ‘din Rufaida Samiha,namanta sunan littafin ya min da’di Allah yasa an qarasa wancen zuwannamu  na tarar ana posting nashi.”

Tsaki Aunty Zainab tayi tace”kinji fa Ommu kinsan littafin da take nufi JININMU ‘DAYA,na wannan sabuwar marubuciyar da kika cemin Sadiya Khalil ne ko Halimatu Khalil ne oho ita tasan da wanne take using sai ku masu wayar.”

Omm Habiba ta ce”nafa ganeshi naji ana zata qarasa shi yanzu ma duk anma manta shi qila sabon updating zata qarayi ko ta daura tasa mutane na neman document din na baya,kinsan rubutu na da cin rai inji su dai masu qoqarin yi amma ta iya book wasu ke cewa Kamar irin ta gwanance tun farko da ta fara,tasan me take kamar dai,amma ni yanzu fav ‘dina a rubutu marubuciyar without my dreams wallahi,Kuma littafinta ‘daya na karanta wannan da take rubutawa without my dreams.”

Ni kam nace “ta’b ai ni kam ko dan Halima tom Halimatu  Khalil ce fav dita a masu tasowa a rubutu,gashi a littafin maman Rufaidah sunan Mama gareta gashi akwai Abdul Abdul a littafin Abdulahid,Abdulmalik waye waye kuma gata sunan Abbanku Abbanta gareshi.”

Aunty Zainab tace “ke wannan lissafin naki,munji ni bance ina qin book nata ba da Habiba ,zaki ma,ko yanzu tayi saban book ommu taga ana poster wa zan ansa na karanta shi,ba laifi ta iya,amma baruwana da lissafin nan ni da ake bawa waya dakyar Ni bama na duba sunan marubuciyar ma,nake karantawa,Ni karatun bai dameni ba littafi ana farawa ba continuation ko na tura wayar Gwaggo document wasu ma su damu mutane na ku’di ne,ni fa ko zasu dinga Allah ya isa an karanta saina karantashi kuwa,abin duniyar mu talakawa Ina muka ga ku’din biya duk ribar da zasu ci,Kamar abun samun lada mtsew”

Aunty Zainab uwar jaraba shiru muka mata har tagama zancen,can za ma wani mukayi tunda Zainab ta ‘bata firar share wajen na taya su kafin muka shiga dakin Gwaggo muka gaisa aka fara fira su Rumaisa an nausa cikin gari gidan yayar Mamah Aunty Maryam kasancewar mamah ce ta biyu a gidan nasu.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Na Cancanta 20Na Cancanta 22 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×